Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KARSHEN ZALUNCI Book 1 Complete Hausa Novel Document by KARSHEN ZALUNCI Book 1


KARSHEN ZALUNCI Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 7631



KARSHEN ZALUNCI Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 06, Jan 2024

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 40.36 kb

File Type: txt

Views: 706+

Download: 212+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: Karshen Zalunci book 1 chapter 1
ƘARSHEN ZALUNCI
Haƙƙin mallaka
Sufi
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
BABI NA ƊAYA

Wata mata ce mai shekaru talatin sanye da kayan fata riga da wando, ɗauke da juna biyu a jikinta ke ta faman tafiya babu sassauci,
A wasu lokutan har tuntuɓe take yi ta faɗi ƙasa, amma sai ka ga ta miƙe tsaye da ƙyar ta ci gaba da tafiya a cikin kasaitaccen birnin ma’abocin dogayen gine-gine.


Sa’adda ya zamana ta shafe rabin rabin sa’a tana wannan tafiya sai kishi ya addabeta sakamakon tsananin zafin rana. Duba ɗaya za ka yi mata ka fahimci cewa tana cikin matuƙar buƙata, domin ƙafarta ko takalmi babu.
Lokacin da ya zaman ta shafe sa’a ɗaya cur tana wannan tafiya sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a dai-dai wannan lokaci ne wani saurayi ma’abocin kwarjini da haiba ya durfafo inda take, yayin da ya iso daf da ita sai ya durƙusa bisa gwiwoyinshi. domin ya ga mene ne ya same ta cikin alamun tashin hankali.


Nan take ya lura cewa tsananin kishi ne ya addabe ta har ta yanke jiki ta faɗi, cikin matuƙar kaɗuwa ya ciro wata salka dake maƙale a kwiɓin cinyarshi ta dama ya buɗe murfin. sannan ya sanya hannunshi ɗaya ya tallafo wuyan matar ya kafa mata salkar ruwan a baki, take ta shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ta sha ya ishe ta, tana kammalawa sai ta ja gwauron numfashi sannan ta yi ajiyar zuciya ta miƙe zaune tana mai ƙurawa saurayin idanu hawaye na zuba.
Al’amarin da ya bawa saurayin mamaki kenan kuma ya ji ya kamu da matuƙar tausayin, ya dubata cikin damuwa ya ce
“Ya ke wannan mata shin ina dalilin wannan zubar da hawaye naki? Koda jin wannan tambaya sai hawaye suka sake kwaranyowa daga idanuwanta kuma ta yi shiru ba tare da ta ce uffan ba.


Daga bisa ne ta buɗi baki muryarta na rawa ta ce. “Ya kai wannan saurayi ma’abocin tausayi da jin ƙai ka yi sani cewa a halin yanzu ba zan iya baka amsar watdannan da ka yi mini ba. Kuma bani da abin da zan saka maka bisa wannan taimako da ka yi min sai dai kafin mu rabu ina neman wata alfarma guda daya a wajen ka.” Cike da mamaki saurayin ya ce, “Ke kuwa wace irin alfarma ki ke nema a gare ni?” matar ta yi murmushin karfin hali, sannan ta ce “Alfarmar ta farko da nake
nema a wajenka ita ce, ina so ka taimake ni da abin hawa haɗe da guzuri, sannan ina so kar ka bayyana labari na ga wani domin matsawar wani ya sani tamkar ka rushe taimakon da kayi mini ne.”


Da jin wannan batu daga bakin matar sai saurayin ya sake cika da tsananin mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne; “Mene ne dalilin da ya sanya wannan mata tace na ɓoye labarin ta? idan na ba ta abin hawa da guzuri shin ina za ta je?” Amsar tambayoyin da saurayin ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar wani gida ya shige ciki.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo gare ta janye da wani ingarman doki fari ɗauke da guzuri mai tarin yawa. Koda ya iso daf da ita sai ya taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya riƙe mata linzamin dokin ta kama ta haye.
Sannan ta sakarwa dokin linzami ta ci gaba da tafiya tana mai waigen saurayin hawaye na kwaranya daga idanuwanta. Nan take ya ji ya ƙara kamuwa da tsananin tausayinta, bai san sa’adda kwalla ta cika mashi idanu ba, ya ji a zuciyarshi cewa tamkar zai rabu da ɗan uwanshi na jini.
Har sai da ya zamana sun daina hangen junansu sannan saurayin ya juya ya fice daga unguwar zuciyarsa cike da tausayin halin da matar za ta kasance a ciki.
Bayan kamar shudewar daƙiƙa hamsin da tafiyar ta sai aka jiyo ƙarar takun sawaye gami da haniniyar dawakai ta cika unguwar. Koda jama’a suka leƙo daga cikin gidajensu domin su ga mene ne yake faruwa sai suka ga a she waɗansu gabza-gabzan Samudawan dakaru ne su kimanin dubu biyu shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, hannayensu rike da zaratan makamai.
Bawasu bane waɗannan dakaru ba face na Sarauniya Abidat da ke mulkin Birnin Sin. Duk wanda ya leƙo ya yi arba da su sai ka ga ya rufe tagarshi da kofar gidanshi, tamkar ya hango mutuwarshi.
Ya yin da dakarun suka iso izuwa tsakiyar unguwar sai wani garjejen kato ma’abocin kwarjini da ya fi sauran kirar sadaukantaka, ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Sannan ya kama linzamin ya sakko. Kwai sai ya dakawa sauran dakarun tsawa, kafin ya gama rufe bakinshi duka sun shiga karya ƙofafin gidajen unguwar suna fito da mutanen, mata da maza yara da manya. Kafin cikar daƙiƙa arba’in an tara gaba ɗaya jama’ar unguwar a waje guda suka yi masu ƙawanya.
Garjejen ƙaton ya tako tafka-tafkan ƙafafuwanshi har izuwa inda jama’ar suke
ya yin da ya zamana tazarar tsakanin su bata wuce taku biyu ba sai ya ja ya tsaya ya zare wata sharɓeɓiyar takobia gadon bayanshi ya dubi gaba ɗaya jama’ar da jajayen idanuwanshi masu kama da garwashin wuta yana mai nuna su da tsinin takobin cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce, “Shin a cikin ku wane ne ya taimaki wata mata mai ɗauke da juna biyu? Ina so ku yi sani cewa rashin nuna wanda ya taimake ta dai-dai yake da rasa rayukanku baki ɗaya.” Koda jin wannan batu daga bakin badakaren sai hankalin gaba daya jama’ar dake wajen ya dugunzuma ainun, kuma su ka kamu da tsananin tsoro da yawa daga cikin su ba su san sa’adda suka saki fitsari a wando ba saboda firgici, kuma aka rasa wanda zai ce ƙala.
Da ƙyar aka samu wani dattijo mai ƙarfin hali ya buɗi baki ya ce “Ya shugabana mu a yau babu wani baƙo da muka sauka a wannan unguwa tamu.” Kafin dattijon ya ƙara she zancenshi shugaban dakarun ya sanya takobinshi ya datse wuyan dattijon, kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jikin, jini ya yi tsartuwa gami da feshi take gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica! Kawai sai badakaren ya dinga sanyawa aka dinga kawo mashi jama’ar unguwar ɗaya bayan ɗaya yana yi masu yankan rago kai har ƙanan yara, mata da tsofaffi bai ƙyale ba.
Haƙiƙa komai rashin imanin mutum da rashin tausayin shi idan ya ga yadda waɗannan dakaru ke yin wannan ta’addanci, dole ne ya zubar da hawaye saboda matuƙar tausayi.
Koda kammala wannan kisan gilla ne sai ya sanya aka cinnawa unguwar wuta. Al’amarin wannan mata mai ɗauke da juna biyu kuwa, tun sa’adda ta rabu da wannan saurayi suna zubar da hawaye sai ta ci gaba da tafiya babu sassauci.
Ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni har ta fice da birnin baki ɗaya ta nausa izuwa cikin daji.
Tana cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabi sai dokinta ya kama sassarfa a cikin wannan hali ne ta ji alamun na guda sun zo mata. Kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak ta kama ta sauko sannan ta durfafi kofar wani kogon dutse, kafin ta isa sai ta yanke jiki ta faɗi kasa, a cikin wannan hali naƙuda ta kamata ta haife abin da ke cikinta.
Cikin matuƙar farin ciki maras misaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga ko mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar jaririya ce ta gaban kwatance, duk da cewa tana cikin halin laulayi ba ta san sa’adda hawayen farin ciki suka zubo daga idanuwanta ba.
A dai-dai wannan lokaci kukan jariri ya cika dajin baki ɗaya, cikin azama ta ɗauki wani siririn itacen mai kaifi ta yankewa jaririyar cibiya. Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Ba zato babu tsammani sai ta hango waɗansu zaratan dakaru haye bisa dawakai sun rugo izuwa inda take. Kafin ta yi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗana bakanshi ya harbe ta da kibiya a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da zugin da ta ji ba ta san sa’adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta na ci gaba da tsala. kuka.
Har badakaren ya sake zare wata kibiyar ya saka a cikin bakan ya ja ya taɓe da zummar ya sake harbawa matar.
Kwatsam! Sai aka ga wata irin murgujejiyar zakanya ta yo fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse ta dako suma ta bangaji kirjin badakaren da dukkan ƙarfin ta. Saboda ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokinshi suka yi sama kamar an janye su da ƙugiya, sannan daga bisa suka faɗo ƙasa tim ko shurawa ba su yi ba. Al’amarin da ya firgita sauran dakarun kenan kuma ya fusata...


Read / Download KARSHEN ZALUNCI Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album