Join Our WhatsApp Group

NA SHIGA ALJANNAH Book 2 Complete Hausa Novel Document by NA SHIGA ALJANNAH Book 2


NA SHIGA ALJANNAH Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28134



NA SHIGA ALJANNAH Book 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 23, Dec 2023

Author: Maimuna Idris Sani Beli ,Maimuna Idris Beli ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 150.14 kb

File Type: txt

Views: 472+

Download: 157+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: A JIYA MUN TSAYA

Aka yi gaisuwar mutumci tare da ambatar sunan juna tsakanin Husna da Salma na shaidar an san juna, kai tsaye kuma Salma ta fara gabatar da Adamu a wajen Husoa a matsayin dan uwanta, sannan ta zarce da cewa, . * + “Kuma shi ne wanda zan aura in Allah ya so” . Duk da Husnha macace mai siyasa, amma siyasar tata ta kasa galaba a wannan muhallin, » sai da idanunta suka KanKance suna.shirin fara zubar da hawaye, ta bi Salma da kallo wadda fuskarta ta nuna alamar da gaske take. Da ta juya ta dubi Adamu shi nasa.arzikin ma sai ya ci uban na jiya, domin kada mata kai yayi cikin tabbatarwa ya kuma amsa mata da baki.’ “Haka ne, za mu yi aure cikin Kankanin lokaci” Husna ta dauke kai daga kallonsa lokacin da – wani malalacin hawaye ya sulmiyo mata ta yi ~ dabarar gogewa da mayafi.
Ko Adamu ya san tarkon sonsa ta fada ne shiyasa takanas ya shiryo mata wannan cin fuskar? , Sai ta daga kai ta cigaba da tsura musu ido su duka dan ta gane siyasar ce, cin fuska ce ko kuma iyakar gaskiyarsu kenan? . : Kamar sun manta da ita sai suka lula cikin hirarsu da ke bayyana son da suke wa juna kai tsaye

ZAMU TASHI


“Tashi-tashi ka taya ni jaje na haukace Salmanu” . Cikiz shassheKar kuka da nuna firgita Adamu ya dinga dukan Salmanu wanda ke

_ kwance da alamun dogon bacci har yana jan tirKa-tirkan raguna, alhalin ba baccin yake ba tsabar takaici ne ya hana shi tanka Adamu wanda ya share guri ya fara tikar kuka tun ~ farkon dare. —

Tun yamma da ya zo gidan ya tararda Adamu cikin mawuyacin hali na damuwa da ciwon kai, ko abincin dare bai iya kai shi bakinsa ba, hatta sallah cikin jam’i da bata . wuce shi, a jiya sai kara’in sallar isha da magariba ya hada ya gabatar wajen karfe . goma na dare. : ” Abin haushi da yayi ta cizon Salmanu shi ne, yayi-yayi Adamu ya fada masa dalilin damuwarsa ko abinda ya birkita shi haka amma Adamu ya KeKasa Kasa ya Ki sanar da shi.


sa Damuwar ta Adamu ce ta hana shi — komawa tasu unguwar kawai yayi niyyar kwana a nan, ba da niyyar rarrashin Adamun ba sai dan sanin-shanun da yayi wa Adamun, ya san da kansa in ya gama damuwarsa zai fito ya fada masa. Sai gashi kuwa ya farkar. – da shi da sigar da ta kusa sa cikin Salmanu farkewa da dariya, amma ya kanne, ya tashi zaune yana muttsikar ido tareda mika, – “Wai da gaske kake ka haukace Adamu?” * Ko ma shegantaka ce Adamu ya Ki yarda da hakan, cikin hawaye da kada kai ya amsa, – “Wallahi da gaske nake Salmanu na haukace, kai ba ka lura bane?” . Salmanu ya: sake murza ido yanaKarewa Adamu kallo, — , – “Kuma fa kamar haka ne, yaya aka yi_.. ka gane ka haukace?” Adamu ya sake kecewa da kuka, ‘ “Abinda nake mai hankali bai taba irinsa ba, a mahaukata na san sahun farko na shiga,

kaicon rayuwata, wallahi duk cikin burikana babu hauka Salmanu, amma ka ga Allah ya jarrabe nidashi” Salmanu ya canja kallon da yake wa Adamu saboda zaton da gaske ya haukace . din, sai tsoro ya fara kama shi, don haka ya rasa ta cewa illa bin Adamu da kallo lokacin da ya janyo ledar pure water ya huda ya hau – tsiyayewa a kofi ya miKo. masa, “Ungo karbi ka yi min addu’a na sha ko “zan samu kullin Kirjina ya warware, ko da ban warke daga haukana duka ba, to wai idan ~ . mana warke illar da yayi min zata gogu ne Salmanu? Wai zata gogu?”- -Salmanu yayi ta maza ya karbi ruwan ya hau’ yin mus-mus da baki yana tofawa cikin tsoro, amma yayi fuska bayan wani lokaci ya _ mika wa Adamu ruwan, “Ungo yi Bismillah ka shanye” – Ba ja Adamu ya karba ya shanye ya Ja _ _‘ jiki ya kwanta yana cigaba da hawaye. – ‘ ‘Dakin yayi tsit illah bugawar zuciyoyinsu su duka wanda kunnuwansu


. kadai ke jiye musu, Adamu na bacin rai da _ sarKkewar al’amura, Salmanu na tsoro da tunanin hanyar tserewa. Ya daga kai ya dubi. agogo sai ya tarar hudu ta Karato, in ya ce fita zai yi ya tafi gida yanzu komai yana iya faruwa da shi ko hannun miyagu ko kuma. – jami’an tsaro, kuma dai da kunya ya shiga gida ya tayar da Hajiya yace mata Adamu ya . haukace, in haukan Karya Adamun yayi Kila a_ mayar da kalmar haukan kansa, idan kuma yace.zama zai yi a nan daga nan zuwa ko wane lokaci Kila Adamu ya iya ballewa da duka. – Sun shafe mintuna goma sha biyar a haka, ban da kuka babu abinda Adamu yake,_. . idon Salmanu akan sa yana tsoron ya tashi. – Can da ya ji kukan Adamun ya lafa sai ya — daga kai ya dubi agogo sannan ya mayar kan ‘ Adamu, . _“Yau ba zaka yi sallah ba ne? na ga hudu na neman sako kai” Cikin Sarin jiki Adamu ya tashi zaune, .

“In roki Allah me Salmanu? Husna nake – roka dama ya ba ni, kuma ya bani jiya na tankwabe na karbi abinda kullum nake rokon kar ya bani” Tsoron Salmanu ya fara raguwa, cikin rashin fahimta ya ce, ae “Ban gane ba Adamu, ko duk a duniyar ~ haukan kake Magana?” Cikin kuka da girgizar kai Adamu ya _ kwashe labari ya bawa salmanu. Shi kansa Salmanu sai abin ya bashi , – mamaki, cikin jinjina kai ya Ce, , “Anya? Da gaske ne zuciyarka ta fara haukan da-idan an kira shi na Allah da annabi an yiKarya” Adamu yayi masa duban rashin fahimta, _ kafin yayi Magana Salmanun ya tanka, “Ni ban san me zan kira abinda nake ‘hasashe ba Adamu, abinda kawai na sani shi ne kana son Husna kuma ba ka son Salma, don haka abinda ka yi jiya ba zaka yi shi haka . kawai ba” . “Shiyasa ai na ce maka na haukace” –


“Ni ma na yarda” ; In ji Salmanu, wani irin takaicin Salma na ninKaya a Kahon zuciyarsa. * ‘Har ya bude baki zai yi Magana sai _kuma ya fasa bayan wani mugun tunani ya. – Ziyarci ransa, tabbas in Salma bata yi wasa ba sai ya sassaba mata kammani. . Adamu da yake jin kamar ba shi da wani gata a yanzu ban da Salmanu a duniya kuma ~ shi kadai zai iya fahimtar matsalarsa sai ya tattara dukkan hankalinsa ga Salmanu yace, “Ka ce wani abu mana da zai sa naji Karfin gwiwa Salmanu” – Salmanu ya riko kafadar Adamu yana. ~ jinjinawa cikin fuskar alhini, – Ka share zuwa gobe, na yi alkawarin ‘” daukar wani mummunan mataki, duk — tsinannen da ya nemi jazawa zuciyarka rudu da hauka na rantse da Allah shi ma ba zan bar duniyarsa lafiya ba” _ Cikin tattara fata Adamu ya Kurawa Salmgnu ido ya ce, Alkawari?” ;

Salmanu ya jinjina kai, “Na dauka, kai ma ka yi min alKawarin ‘ kwantar da hankali har zuwa lokacin da, zaka “ji nawa matakin” a Adamu ya koma jiki a sanyye ya kwanta cikin dasasshiyar murya ya ce, . “Na yi”
.
**********

Tsawon lokacin da aka ci bikin Amina aminiyar Husna aka side, sam Husna ba ta da – walwala ko kadan, ba ma wai rashin walwala kawai ba, duk wanda ya dube ta sai ya gane lallai wani murkusheshen abu ya _ taushe – _.° . Zaciyarta da Karfin hatsi,.ya fi Karfinta ita da zuciyar har ya bayyana a fuska da gangar jiki. Ba a cikin Kawayenta kadai ba, hatta a cikin gidansu ta rasa walwala a matsayinta na mace mai kazar-kazar da shiga mutane, yanzu ta kasalce sai son kadaici da’yan Kananan ” hawaye. . . , Matan babanta sun dan binciki © damuwarta, ba don su san ainihin matsalarta

su maganace mata ba sai don kar ace sun . ganta cikin damuwa basu tambaya ba, wato tambayar je-ki-nayi-ki, don haka ne ma basu sami amsar komai daga gareta ba duk da kuwa daidai wannan lokacin tana jin matsalar da take ciki ta cancanci abokin tattauna ta, zuciyarta zata babbake bata san babu ko hakuri a waki’ar son da ta fada ba, lallai kenan ta nemo wanda zai taya ta nemo ruwan – da zasu kwara wa zuciyar kafin ta gama Konewa.

Kwanan Amina uku gidan angonta Husna ta tattara buhunhunan matsalarta ta kai mata, bayan ta kwashe mata labari ta KarKare da Magana cikin hawaye, “In dai yadda nake ji akan son gayen nan haka masoya SUkeji a ZUCiyarsu, to ina da . tabbacin zuwa yanzu da yawan mutanen duniya bai kai haka ba” Cike da mamaki da alhini Amina ta jahilci maganarta ta Karshe, tace mata, Ban gane ba” Husna ta shaki hanci tace,

“Eh mana, yadda rayuwa ta gaji ba yawancin abinda kake so kake samu ba, in dai yadda nake jin so haka kowa yake ji to kuwa in bai samu abinda yake so din ba sai dai ya mutu, Allah na rantse miki” – Sai mamaki ya cigaba da kashe Amina, kawai ta tsurawa Husna ido ta ma rasa abinda – za ta ce, sai juya ido da kafada kawai take. . “Abinda yake Kara sakudar zuciyata shi ne, wai duk matan’da ke fadin duniya a rasa macen ‘arzikin da zata Kwace saurayi a wajena sai banzar Kawarki Salma… shegiya. tsinanniya…” . _

Amina ta rufe mata baki . cikin matsananciyar dariya duk da tana yi tana rage mata Karfi kasancewar ta fahimci lallai Husna da gaske take, in kuwa haka ne bai kamata ta wanko Kafa ta kawo mata kukanta ba kuma ta kasa bata muhimmanci, cikin ta tausasawa ta ce mata, “Kar ki rage mata alhaki don baki da yakinin ke ya fara so ko ita, kuma shi so ai ba ruwansa da wani kyau Husna, Salma macace

mai shegen wayo, zata iya hada kafada da ke a wajen iya jan zaren maza…” oo – Cikin tsawa da kuka Husna tatare, . “Wallahi Karya ne ban yarda ba…., na . san so , akwai Karfa-Karfa cikin abinda suka – _ yi min…. kuma wallahi ba zan yarda ba”. Sai ta zarce da kuka. Amina ta zurfafa a tunanin yadda zata tunkari lamari, da gaske ne har cikin ranta damuwar Husna ta shalle ta, Husna ba ta saba’ da Karya ko Bata lokaci kan’ abinda bata yi ra’ayi ba, don haka kamata ita ce duk abinda ta yl ra’ayi a taya ta nema don da gaske take ba da wasa ba. .Cikin bulayinta ne.ma ta ji ai kawai . Adamu yana son Kawarta, bugun cikinta , kawai suka shirya shi da Salma tun da dama abokin wasanta ne. . Ta janyo wayarta ta shiga kiran Salma don ita ma ta bugi cikin nata amma cikin akasi ta tarar da wayar a kashe, dole ta sauke _ cikin saduda da sanyin jiki idonta akan Husna _ wadda ita tun dazu ta baza mata na mujiya.

“Wai wa kika kira?” Husnatatambaya. Kai tsaye Amina ta amsa, “Salma ce…” .

Husna ta banka mata harara cikin munin fuska, Kirjinta na ta faman bugawa ta ce, “Amma dai da kin same ta kin zalunce

ni, wai ki kira ta ki ce me?”. A sanyaye Amina tace, ‘“A’a bugun cikinta zan yi in ji da’ gaske ne shi zata aura? Komai zamu yi yakamata~- mu fara sanin wannan gaskiyar Husna” Husna ta sawa Amina ido tana yi mata. © wani irin kallo wanda ya sanya Aminar shan jinin jikinta ta yi sororo ita ma tana kallon Husna da fuskar nuna rashin fahimta, . Husna ta kada kai ta rausayar abin tausayi, . “Abinda kawai na sani shi ne, Amina ina son Adamu, sanin gaskiya zai aureta ko zai fasa ba zai hana ni sonsa ba, don haka a bi wata hanyar wadda ba ta shafi Salma ba, don

ko a lahira ba na fatan ma Allah ya hada _ mu sabgadaya”. . ok Amina ta sake yin shiru cikin mamamkin irin wannan zafin kan na Husna a yau, fada babu gaskiya. Can a tunane-tunanenta ta samo dabara, “Ina kayan ankon da kika ce ya ba ki, ba * shi kayansa kika yi lokacin da suka Kuga miki rashin mutuncin shi da-Salma ko tafiya da abinki kika yi?” .Husna ta tabe baki, . “Wallahi da zuciya ta debe ni na dire _masa abinsa sai kuma na ga asarar hakan, na juya na tafi da abina” – Amina ta yi shewa, Yauwa ‘yar gari, gara da kika yi hakan ai kin ga sai ya zame mana tsanin haduwa da shi” Husna ta jahilce ta da ido amma bata tanka ba. Amina ta ce, ‘ “Da kina da lambarsa dama kyakkayawan sakon godiya zamu shirya

masa don bugar cikinsa mu ji inda taki sarautar ta kwana, amma tunda babu ma sai a tuna da, ki sami takarda da biro masu kamshi ki kashe shi da baki , na san zaki iya Hajiyata”

Husna ta Balle da murmushin jin dan Kwarin gwiwa kadan, muryarta a bude ta ce, – “An gama, zan gwada” .

“ Daga nan Amina tayi dabarar da suka kashe bos din a nan saboda gabadaya lamarin wannan murdaddiyar soyayyar ta Kawarta, aminyarta tsoro yake bata, bata taba tsammanin Husna a irin wannan duniyar da ake mutuwa kan son masoyi ba:

Kasancewar Husna ma’aboyiyar kaifin kwakwalwa da iya tsara samari, wasiKar data. rubutawa gwarzonta ta ji suga.sosai, ga ta kuma ‘yar faki wadda ba yawa sai lada, rabin shafi kwata-kwata ta ci, amma ta san in dai akwai burbushin sonta a zuciyar Adamu ko yaya son yake kamar yadda ya fara bincina mata, to tana da yaKinin sai ta shallo dukkan sonsa da Kaunarsa, sannan kasancewar Amina

ta fada mata matsayin karatun Salma, wadda ‘ta tsere mata don ita iyakacinta sakandare, sai – ta yi wasiKar da gwanewar turancinta wanda ba duk kai ba, don tana ja a ingilishi sosai ko “a makaranta shi ta fi kawowa sama da komai, dalibai da Malamai kowa ya san ta akan haka. ; Da sassanyar la’asar ta so ta wanki Kafa ~ takai takarda, a zuwan in tayi ruwa-rijiya in bata yi ba masai, ma’ana in ta hadu da « Adamu ta gabatar da zantukan cikin takardar _ da fatar bakinta, in yaso duk ma abinda zai biyo baya ya biyo. Idan kuma bata ganshi ba sai ta sami yaro ta aika masa da ita.. Amma wata mace mai karbar dinkin sunan ta da...


Read / Download NA SHIGA ALJANNAH Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album