Join Our WhatsApp Group

BAKINA YA JAMIN Complete Hausa Novel Document by BAKINA YA JAMIN


BAKINA YA JAMIN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13411



BAKINA YA JAMIN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 06, Oct 2023

Author: Dr Maryama Ibraheem ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : AREWA WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 93.56 kb

File Type: txt

Views: 612+

Download: 134+

Last download: 5 days ago

Description/Story: *👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️.*




*_MALLAKAR👇🏽._*


*DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_Marubuciyar👇🏽._*

*TAWA K'ADDARAR KENAN!!!*

*AUTAR MATA*
_{rikitacciyar yarinyah!!!}._

*_And now👇🏽._*


*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️.*




*بسم الله الرحمن الرحيم.*



*GODIYA.....*

*DUKKANIN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAHU SUBUHA NAHU WATA'ALA, TSIRA DA AMEENCI SUK'ARA TABBATA ZUWA GA FIYAYYEN HALITTAH MANZON TSIRA* *محمدرسولله صلله عليه وسلم*



*_GODIYA...._*

*HAR KULLUM BAZAN GAJI DA GODEWA ALLAH BA, DOMIN SHINE YA'ARAMAN RAYUWA DA LAFIYA HARNA KAWO WANNAN LOKACIN,IKON SANE YASA HARNA DAURA HANNAYENA DA SUNAN FARA RUBUTA WANNAN LABARIN....*
*DON HAKA NA GODE MASA NA K'ARA GODE MASA.*

*YA ALLAH INA ROK'ONKA KABANI IKON RUBUTA ALKHEREE KA HANENI DA RUBUTA SHARRI, YA ALLAH KASA DUK WACCE TA KARNCIN WANNAN LABARIN ALLAH YASA TAYI AIKI DA ALFANUN DAKE CIKINSA🤲🏼🤲🏼.*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*_JAN KUNNE......_*

*WANNAN LABARIN K'IRK'IRARREN LABARI NE,DON HAKA A GUJI JUYAMAN LABARI TA WATA SIGA, DUK WACCE TA AIKATA MAKAMANCIN WANNAN NA BARTA DA RABBUSSAMA WATI......*


*_NUSARWA........_*

*BANYI DAN WANI KO WATA BA, NAYI SANE DOMIN FAD'AKARWA TARE DA ILMANTARWA ,DAN HAKA A GUJI ZARGI, DUK WANDA YAYI DAI DAI DA MASA RAYUWAR ARASHI NE KAWAI.....*


*_DA WANNAN DAMAR DANA SAMU ZAN MIK'A SAQON GODIYA ZUWA GA👇🏽._*

*_YAYANA😍 AMINU D'AN KADUNA AMANAWA, UBANGIJI ALLAH YASAKAMA DA MAFIFICIN ALKHEREENSA YA BIYAMA BUK'A TOCINKA NA ALKHEREE DUNIYA DA LAFIRA ALLAH YADAFAMA A DUKKANIN LAMURRAN KA, YAKARE MAMU KAI DAGA SHARRIN MUTUM KO ALJAN, MATA TA GARI I PRAY BABBAN YAYA😍._*


*_TAKU TA DABAN CE👇🏽 ._*


_*AISHA ABDULLAHEE IDREES {SHATU}BAJIDA BAKIN DAZAN YI MAKI GODIYA SAIDAI KAWAI ZURI'A TA GARI I PRAY🤲🏼._*


*_ANTY HAUWAH {MMN USWAD} BANIDA BAKIN DAZANYI MAKI GODIYA SAIDAI KAWAI NACE ALLAH YAQARA DAUKAKA DA NISAN KWANA YA RAYA MAKI ZURI'ARKI AKAN SUNNAR MA'AIKI🤲🏼._*



*_HUSSAIN 80K TAKA TA MUSAMMAN CE ALLAH YAKAWOMA MATA TAGARI YA QARA DAUKAKA DA NISAN KWANA YASAWA RAYUWARKA ALBARKA🤲🏼._*


*_UMMU AFFAN GODIYA JIKKA JIKKA ALLAH YARAYA MAKI ZURI'ARKI AKAN TAFALKI MADAI DAICI DAN NABIYURRAHMATY🤲🏼._*



*_K'AWAYENA KUNA RAINA👇🏽..._*


*_UMMU MUHAMMAD NAJAMAGA {KULSUM} INAYINKI TA HANNUN DAMANA....._*



*_HAUWA'U SANI {UMMEENMUST} ALLAH YABARMU TARE🤲🏼 ._*


*_AISHA MUHAMMAD {AMARYAR LUKUUUU😜}ALLAH YAQARA DANKON SYYY ANA TOGETHER FAR....._*


*_KHADEEJA MUHAMMAD {SHEHYN TA'O🤗}ALLAH YAQARA DANKON LOVE QAWA TOGETHER FOREVER🤝🏽._*...


*_SAFEEYA ABUBAKAR SULAIMAN {FIYYART}GAISUWARKI TA DABAN CE MIJI NA GARI I PRAY🤲🏼..._*


*_SA'ADATU MUHAMMAD LADAN {SA'AMLAD} FARTAN ALKHEREE🤝🏽😊._*



*_TAKI TA MUSAMMANCE👇🏽._*

*_HABEEBA IBRAHEEM {UMMY HABEEBA} TAKI TA DABAN CE ALLAH YAKAWO MAKI MIJI NA GARI MUJE MUSHA BIKI💃🏽💃🏽💃🏽🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️._*




*_DEDICATED TO ALL MY PANS LOVE YOU WIJIGA WIJIGA🤝🏽🥰😍._*




_Not edited❌._


*بسم الله الرحمن الرحيم.*

*PAGE 1️⃣ ↘️ 5️⃣.*


______________Kinga lawisa wallahi kidaina wahalda kanki dan kinsan bazanma ta6a daukar wannan banzar zancenna naki ba....

Haka kawai na tsahi cikin talauci sa'annan kuma na k'are cikinsa.....

Ina bazai ta6a yuwaba ,kinga gwanda ke ,dama sunanmu ba d'aya ba....

Duk Wanda yakalleki yasan kina cikin halin ha'ula'ii a cikin gidannan....

Haka kawai , gaki kintashi gidanku talauci duk yayi maku kanta , kuma shine kikazo kika auri talaka dan bakisan gunda keyi MAKI ciwo ba......

To gaki ga d'an tasallah idan kin'iya ki jik'asa ki shaaaanye🙅🏽‍♀️.....

Wacce aka kira da lawisa tabud'e baki dakyar tace"

anyaa *khady* *BAKINKI* bazai ja maki bala'i ba?

Dame kud'in da talaka waye yayi sune¿

Duk far Allah yayisu.....,!

Katseta tayi ta hanyar cewa ....

"Dakata lawisa!!!

bana buk'atar duk wani wa'azinki a halin yanzu....

Bakina ba'abinda zai jaman face alkheeree !!!.

,kuma zan jamaki kunne as from today wallahi karki kuskura ki k'ara d'aga wannan akwalar wayar taki da sunan kirana wai nazooo akwai matsala...

Kika kuskuara kika sake!!!!

Allah saina baki mamaki ,.....

Bud'e baki lawisa tayi da sunan yin magana SAIDAI kamin takai da maganar wacce naji ankira da *khady* tarigata d'aga mata hannu....

Kana tace " karki kuskura ki k'ara ceman tappp anan gurin.......

Tana gama maganr taja mayafinta dake kan igiyar shanya tayi waje da shamu d'ad'd'in k'afa fuwanta🤭...........


Tafe take awa ta k'arye laud'i kawai takeyi awa WATA lagwaniii🤣 BAKIN titi tanufar DOMIN jiran taxi ......

Tsaye take rik'e da k'ugu sai faman girgiza kai takeyi da Jan tsaki.....


Wani me aca6ane yaje wucewa ta gun har yayi gaba sai kuma yajawo dan aca6arsa yadawo ta gunn....

Ameencin Allah yatabbata zu ga ma'abuciya kyau kamala had'i da kwarjini......

D'ago face nata tayi takai kallonta zuwa gunda yake zaune saman d'an aca6arsa...

Wani wulaqantaccen kallo tabishi dashi kana , takau da kanta gefe taci gaba da harare hararenta kace wata zararra ce😳😂😂🤐🤐.......


Ganin irin kallon data watsa mashine yasa shi, gurgusawa gaba dai dai gunda keda Gini , ya'ajiye aca6arsa kana ya tako a hankali zuwa gunda take tsaye......


Haba kyakykyawa wulaqanci banaki bane be kamaceki ba, yakamata ki saki ranki mugaisa kana daga bisani na zayyane maki abinda ke cikin zuciya....

Bata vari ya'iyar da maganar daya fara ba, hannu kawai tacira ta wankesa da mari har biyu,kana tace "kai banza kalleniii ka kalli kanka kaga nayima kama da sa'arka¿

Ni bara na gayama ko mahaifinka nafi karfinsa balle kai dako gama wankema kashi ba'ayi ba.....


Dallah matsamam can , Abu sai faman d'auyi kakeyi Amman shine dan rashin hankali zakazoman da wani zance.....

Miyon bakinta ta tattaro kana ta fesa masa shi a fuska....

Kallon tsana da nuna 6acin rai yabita dashi kana yace " lallai yarinya tabbbas wuyanki ya'isa yanka tunda har zaki iya d'aga hannu ki mareniiii!


To bara nagaya maki bazan rama marina a halin yanzu ba, Amman ki rubuta ki ajiye ni hameed nadau alk'awarin mijin aure saiya gagareki a cikin duniyarnan , saikinyi da kinsani marar misaltuwa, saina mesheki abi misaltawa a cikin wannan garin .....

Oya jeki zaki ganine duniyace ta'ishi kowa Riga da wando.....✍🏽






*_idan naga ruwan comments zan daura daga inda na tsaya, idan kuwa naga akasin haka gaskiya bazan ci gaba ba!!!......_*




*_kuma sharhi nake buqata ba thanks or tabbas littafi yayi dadi or dan Allah aci mamu gaba......_to gaskiya bazan lamunta da wannan ba wannan karon dan haka idan kunne yajiii👂🏽........._*




*More comment more typing✍🏽🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️.*




*_tabbas alqalami🖊️ yafi takobi🏌🏽‍♂️._*




*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*PLX👏🏽.*



*_~Y'AR MUTAN {BUBARE}CE✍🏽 .........~_*

*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{k'alubale garemu mata}._



*_MALLAKAR👇🏽._*



*DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_MARUBUCIYAR👇🏽._*

*TAWA K'ADDARAR KENAN.*

*AUTAR MATA*
_{rikitacciyar yarinya}._

*_and now👇🏽_*
*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{k'alubale garemu mata}._



*_jinjina a gareku👇🏽._*

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION Allah yaqara mamu had'in kai da kaunar juna🤝🏽.*


*ATK PALACE GROUP taku ta musamman ce Allah yaqara had'a kawunanmu Ameeen🤲🏼🤝🏽.*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_Not edited❌._


*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*PAGE 6️⃣ ↘️ 1️⃣0️⃣.*


___________Nufar gunda aca6arsa yake ajiye yayi yana tunanin wanne irin hukunci ya dace da wannan fitsararriyar yarinyar.....


Tana samun taxi tagaya masa gunda zai kaita, tafe suke ba'abinda takeyi face faman Jan tsaki had'i da sanya gefen mayafinta tana faman rufe hancinta....

Suna shiga unguwar takama nuna mawa me taxi hanyar dazaibi domin sadata da gidansu...

Ganin kwanonin sunqici sunk'i cinyewa yasanya me taxi taka burki kana yakai kallonsa akanta....

Yace "malam haryanzu bamu kawo gun bane¿

Eh ai nagayama saika shiga dani sosai ko¿

Dan haka dallah ja muje kud'ifad Zan baka ba kyauta zaka kaini ba , haba!!!!


Ke dallah rufeman baki ko miye zaki bani nikaaam bazan k'ara d'agawa dake daganan ba ,kunjiman ja'ira yaushema kika ceman saina Shiga dake wannan k'asungumin gurin¿

Dallah ficeman daga taxi tun ban kakkarya way'annan shegunayen k'afa fuwanna kiba......


Zanfice daga cikin wannan matsiyaciyar taxi Amman wallahi bazan baka ko kwa6o ba, haka kawai !!!

Aikuwa wlllh baki isaba saikin bani halak d'ina ko yanzunnan na canja maki kamanni.....

A tare suka fita daga cikin taxi d'it....

Duk'awa tayi da sunan ta cire talkaminta sai kawai ya ficike jakar dake hannunta , bud'eta yayi yaci karo da ~N~ 200 takarda gudu duk tasha jiki, daukarta yayi yasanya a aljihunsa kana ya fincika mata Jakarta a saman ka...

Kururuwa tahauyi had'i da zage zage da ashariya sai wacce ta manta....

Ba Wanda ya kulata domin kuwa ba meshiga sabgarta, kowa sha'anin gabansa yakeyi.....

Shigewa yayi cikin taxi Yakama gabansa,
duwa tsuna takama d'iba tana antaya wa taxi had'i da d'ura masa ashariya.......
{ni kuwa doctor nace anya wannan lafiyarta kalau kuawa🤔}......

To muje dai zuwa🚶🏽‍♀️.



Gidansu tanufar had'i daci gaba da zagin me taxi dabesan wainar da take toyawa ba🙅🏽‍♀️....


Ba sallama ba komai tasanya kanta gabaki d'aya a cikin gidan....

Wata dattijuwa CE a zaune saman y'ar tsakar gida tana tankad'en garin tuwo...

yayin da sauran mutanen gidan ko wacce na hidindimun gabanta.....

Ba Wanda ya kulata kowa yaci gaba da safgar gabansa....

D'akuna ne Jere birjik sunkai 10.....

Wani d'an madai daicin room tanufar had'i da fara rage kayan jikinta kana ta fito ta kinkimi bucket dake cike da ruwa ta fad'a ban d'aki sai faman Jan tsaki takeyi....



lokacin data shige ban d'aki , wannan matar dake tankad'an garin tuwo tsagaitawa tayi da aikin data keyi , kana tace


"Rabbu ya taroki ki gane hanyar tsira Nana khadija....

Kana taci gaba da aikinta.....



Tafi 20minutes a band'aki kana tafito tana tafe tana laud'i idan kaganta kace lagaunice🤣.!


{Ni kuwa Doctor nace wato ko toilet aka fito sai ansayar da hali🤔 muje dai zuwa🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️ l}.



*Shin Wacece khady¿.*


Muhad'u a page na gaba😜




*More comment more typing🤸🏼‍♀️.*





*ąƖƙ'ąƖąɱıŋ ɖơƈɬơཞ ɱąཞყąɱąɧ🖊️*



*_tabbas Alk'almi🖊️yafi takobi🏌🏽‍♂️._*




*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*Plx👏🏽.*



*_~Y'AR MUTAN {BUBARE}CE✍🏽!.~_*

*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{k'alubale garemu mata}._



*_MALLAKAR👇🏽._*



*DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*




*_MARUBUCIYAR👇🏽._*

*TAWA K'ADDARAR KENAN.*

*AUTAR MATA*
_{rikitacciyar yarinya}._

*_and now👇🏽_*
*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*
_{k'alubale garemu mata}._


*Wowwwww Ashe haka BAKINA YA JAMIN yasamu k'ae6uwa agun masoyana😁 gsky dolema na taka rawar shoky💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽😍😍.*


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*masu kirana da masu yiman text message banida bakin dazanyi maku gdy da irin soyayyar da kuka nunaman saidai kawai nace Allah YAQARA danqon syyy tsakanina daku Doctor nayin kowa da kowa 💞💕💞.*



_Not edited❌._


*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*PAGE 1️⃣1️⃣ ↘️ 2️⃣0️⃣.*


________________Khadeeja Abdussalam shine cikakken sunanta mahaifinta haifaffen garin kano ne , anan yake zaune da iyalansa a shiyar sheka dake cikin birnin kano.

yanada mata ukku hunaisa itace ta farko wacce suke kira da inna , sai ramatu wacce suke kira da amarya, sai lubabatu itace ta ukkunsu wacxe suke kira da inna amarya .


y'ay'an sa goma sha ukku mata goma maza ukku .
Nusaiba itace ta farko sa'annan zainab,sai sumayyah , sai huwailat ,sai zubaida , sa'annan, shema'u, sai asma'u sai khady, sai fateema, sai Aliyu, sai usman, bara'atu sai abubakar shine auta a gidan.


Hunaisa wato inna itace da biyar, Nusaiba da sumayya Aliyu da usman sai autarta asma'u.

hakama ramatu wato amarya itama biyarne da'ita, zainab da zubaida da fateema , sai bara'atu sai autarta wato shema'u.
sai inna amarya dake da ukku huwailat kana khady sai autansu abubakar.

Khadeeja wacce ake kira da khady itace ta takwas a gun mahaifinsu agun mahaifiyarta itace ta biyu y'a a gun inna amarya kenan wato lubabatu....

Yaran sun taso cikin tarbiya da kuma mutunta nagaba dasu ....

saidai kash! Ansamu zakka d'aya aciki wacce ko kad'an ba godiyar Allah a zuciyarta balle wani Abu shine mutunci..

A kullum mahaifiyarta tana kuka da'irin halayenta ko kad'an bata biyo dangin mahaifinta ko mahaifiyarta ba..

Domin kuwa su mutanene masu wadatar zucii..

Dukta da malam abdussalam bashida Amman akwai wadatar zuci , a haka Kuma ake zaune cikin y'ardar Allah da amincewarsa..

Gwargwado tasamu ilimin addinin Islam domin kuwa ta safke alqur'anic.

A fannin boka ma, ta samu iya abinda ta samu abinda ta samu domin kuwa takai matakin k'ark'are secondary school saidai halin rayuwa Allah be nufi ta k'ark'aren ba....


Saidai wani Abu d'aya dukta datana da ilimin islama bata aiki dashi ko kwayar zarrah...

Idan akwai abinda khady ta tsana be wuce talaka ba, sai kuma gashi tatashi cikin talakawa tsantsa.


Alhmdllh kuma tanada farin jinin jama'a saidai kashh!!!!..


ta dak'ushe tauraruwarta agun jama'ar...

Domin kuwa batada aiki sai canyewa al'umma mutunci..

Idan har kaga khady ta girmama mutum to tabbas ta ganshi da masu gidan rana...

Tanada manema gwargwado Amman duk ta koresu a cewar me sukaci suka bata taci¿

K'annenta da yanyenta mata duk suna d'akunan maza jensu sa6anin ita data tsaya ruwan idanuwa...

Ayanzu shekarunta sunkai kimanin 22 , k'awayenta duk wat'anda sukayi secondary school harma da primary duk suna suna d'akunansu ...

Sa6anin ita data tsaya jiran me kud'i da mota...

Haka rayuwa taci gaba da tafiya mahaifiyarta na k'ok'arin ganin ta fahimtar da'ita..

Amman inaaa!!!!

Wanda yayi nisa bayajin kira..

Domin kuwa khady tayi Nisan da har abada bazataji kiran da'ake yi mata ba...


Wannan kenan.....!




Sannu a hankali ta fito daga cikin d'aki hannunta rik'e da mayafinta da wayarta...

Hanyar barin gidan ta nufa sai faman tartsatsin yawu takeyi .

TAKU takeyi sannu a hankali idan kaganta bazaka ta6a zaton y'ar talawa bace ganin yadda take yiwa fuska kace taga kashine....



Wani d'an madaidaicin gida tashige had'i da kwala sallama , Matar guidance tafito hannunta dauke da kayan wanki da sabulu a hannunta...

A'a a'a kawata yau kece a gidannanmu¿


Wallahi nice surayya ykk?

Lpy kwana da yawa kindaina lek'oni...

Hummm kedai bari kinsan sha'anin rayuwa..

Wacce aka kira da surayya tace hakane kuma...

Zoki zauna kamin na kammala wankinnan...

Wani kallo tabita dashi kana tace "wanki far kikace¿


" yanzu surayya kina nufin wa"'azin danake yi maki hara yau beshiga junnnen kiba¿

"Haba haba yazaki zauna yiwa k'ato wanki¿

Sai kace yakowa haka a ...

Saurin d'aga mata hannu surayya tayi kana tace " dakata khady!!!


Karki k'ara cewa mijina k'ato...

Ni shine abin alfaharina dashi nake tunk'aho acikin garinnan a halin yanzu..

Dan haka baki isa ki hanani samun lada ba , dan haka idan har kinsan wannan banzan zancen ne yakawoki dan girman Allah ki kama gabanki wallahi bana buqata nagode✍🏽




*More comment more typing🤸🏼‍♀️.*



*ąƖƙ'ąƖąɱıŋ🖊️ ɖơƈɬơཞ ɱąཞყąɱąɧ✍🏽*



*tabbas alk'alami🖊️ yafi takobi🤺.*








*#Comment*
*#Vote*
*#Share*


*PLX👏🏽.*
*👄🤦🏽‍♀️BAKINA YA JAMIN👄🤦🏽‍♀️*


*MALLLAKAR👇🏽*

*DOCTOR MARYAMAAH IBRAHEEM*




*_MARUBUCIYAR👇🏽_*

*_TAWA K'ADDARAR KENAN!!!_*

*_AUTAR MATA_*
_{rikitacciyar yarunya}._

_And now👇🏽._

*BAKINA YA JAMIN*
_{k'ubale garemu mata}._



_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com.






_Not edited❌._


*بسم الله الرحمن الرحيم.*



*PAGE 2️⃣1️⃣ ↘️ 2️⃣5️⃣.*


_____________Ta6a hannayenta tafarayi tana kallon surayyah a kai kaice, kana tace "tabbb!

" Lallai surayyah yanzu dannashigo wannan a kurkin gidannanki kike Neman wulaqabtani¿

"Yes dan kinshigo naki Neman wulaqantaki d'in Oyo kama hanya fitarmab daga cikin gida...

"Barin irinku a cikin al'ummah wallahi bala'ine!

Haka kawai ina zaune da mijina lami lafiya kinzo kina batun hureman kunne!

Wato nadaina yiwa mijina biyayyah nakoma tamkar ke ko¿.
To hakanne bazaki gani ba wallahi ...

Kuma muddin kika koma shogoman gida da wannan banzan zancen naki Allah saina fasa maki baki....

Jan hannunta surayya tayi bata sakar mata hannu ba , saida takaita zauren gidan kana tace " kama hanya ficeman daga cikin gida...

Baki sake khady ke kallon surayyah domin kuwa ko a mafalki bata zaci irin wannan wulaqanci daga surayyah...


Batare datace komai ba tafice daga gidan gwiwa a salu6e...

Gidansu ta nufa , kai tsaye d'akinta ta nufa ta rage kayan jikinta kana ta zube a saman y'ar shamu d'ard'ar katifarta...




""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""


Ga pic natanan INA buqatar Ku nemomin komai da komai Wanda yadan ganci tarinhin rayuwarta ..

Sa'annan waye mahaifinta a cikin garinnan..

"Okey sir!

Wani matashin saurayine zaune a saman lumtsumemiyar kujera, kaima kanka me karatu dazaran ka kallesa kasan nera da Hutu sun zauna masa...

Umurni ake bawa wani màtashin saurayin Wanda da alama wannan dake zaune uban gidan sane....

Ficewa yayi daga cikin d'akin .

Yayinda shikuwa yamik'e daga gunda yake zaune yanufi wani sashe dake cikin d'akin...


Wata kyakykyawar dattijiyace zaune hannunta rik'e da tuffa wato Apple...

Sannu a hankali take kutsirata yayinda a hannun damanta wata matashiyar yarinyace keyi mata fitara...

Da sassarfa ya k'araso gun yafad'a a saman wannan Matar,.

Mom!

Shafa sumar kansa tafara kana tace " yadai my son¿

"Mom nagaji wallahi!

" aikin me kayi my son?

"Kedai bari mom baya fad'uwa...

Murmushi tayi kana tace anya son yau kaci abinci kuwa¿

Girgiza kansa yayi kana yace " a'a mom yau komai bansawa cikinnan nawa ba..

Juyawa tayi gun wannan matashiyar yarinya kana tace bintu oyo jeki ko had'awa...


Read / Download BAKINA YA JAMIN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album