Join Our WhatsApp Group

GA IRINTA NAN Complete Hausa Novel Document by GA IRINTA NAN


GA IRINTA NAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 152795



GA IRINTA NAN

Reading Time: 12 Hours

Added On: 24, Jul 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITES ASSO????️????

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 832.9 kb

File Type: txt

Views: 1831+

Download: 2198+

Last download: 8 days ago

Description/Story: GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*
_______
*DANDANO🥰*
*1*
Cikin tsananin gajiya da ishirwa nake tafiya burina kawai na isa gida na samu na watsa ruwa a jikina na kwanta na hutawa rayuwata. gabana ne ya fad'i! lokacin dana tuna d'an iskan yaron nan yana gari nasan da wuya ya barni na sha ruwa a gidan Khalid mugun fitinan nan yaro ne wallahi........Daf da zan shiga layin namu motar Alhaji Nura take kokarin fitowa d'auke kaina nayi na bashi hanya domin ya wuce! girgiza kaina nayi ganin yayi parking din motar ya tsaya cikin raina nace"Ai dama na san sai ya tsaya, galashin motar ya sauke muka had'a ido fuskata na saki nace"Alhaji barka da rana." Cikin kulawa yace."Barka dai Sa'ida ya aiki."? Nace" Aiki Alhamdullihi." kokarin wuce wa nake ya dakatar dani da fad'in "Sa'ida ina al'kawarinmu."? Gefan hijab d'ina nasa na goge gumin fuskata nace" Alhaji al'kawari yana nan inaso na ware ranakun da zan fara gudanar da aikin naka."

Yace."Me zai hana ki ware ranaku biyu a cikin sati wato alhamis da juma'a tunda a ranakun yaran basa zuwa isilamiyya in yaso idan sun dawo daga boko misalin biyu ko uku sai ki dinga shiga kina musu lesson d'in."

Shuru nai ina nazarin maganarsa nace"Shikkenan Alhaji zan duba maganarka insha Allahu." Yace."To godiya nake gimbiya duk shawarar da kika yanke sai ki kira waya ta ki sanar dani."


Nace"To shikkenan babu damuwa." Har nayi yunkurin barin gurin ya dakatar dani! cikin k'osawa na tsaya amma ban nuna masa ba, kudi ya miko min kusan dubu biyar.....murmushi nai nace"Kasan ba zan kar'ba Alhaji nagode." da sauri na bar gurin ina mamakin yawan kyautar da yake min duk had'uwar da zamuyi sai ya dauki kudi ya bani bayan uwar hidimar da yake mana a gida........Tun kafin na karasa na hangoshi dogare a bakin kofar gidan namu yana sanye da k'ananun kaya 3qutar da singlet wacce ta matse shi gabad'aya suffarsa ta mazantaka ta bayyana Gabana ya yanke ya fad'i! duk sanda zan ganshi a haka hankalina yakan tashi ni kaina ina mamakin halin da nake shiga wannan dalilin yasa idan yana gida bana sakewa sosai mutukar zai dinga shige da fice a gidan babu sutturar arziki a jikinsa.

Fuska a murtuke na 'karaso...."Malami Bani hanya na wuce." babu wasa nayi maganar.

Hanyar ya sake tarewa yana kallona da 'batacciyar fuska yace."Aunty Sa'ida me ya tsayar dake a gurin wancan mutumin."? wani irin kallo na watsa masa nace"Ina ruwanka da shiga sabgar da bata shafeka ba, dan Allah ni bani guri na wuce na gaji."

Hanya ya matsa min naja tsaki had'e da kokarin ra'bashi na wuce kawai naji ya matseni a jikin kofar fuskokinmu suka hade numfashin mu na had'uwa.


Cikin fad'uwar gaba na tureshi! nayi saurin fad'awa soron ina addua akan Allah yasa wani bai ganmu ba! hannuna ya rike yana marairaice fuska yace."Kina so zuciyata ta buga ko na hanaki kula wancan Alhaji kin raina magana ta ko." Cikin takaici nake kallonsa a fusace! nace"Wallahi Khalid ranka zai 'baci! mutukar baka fita harkata ba shin wai ni sa'arka ce da zaka dinga yi min iskanci."

Zuba min idonsa yayi fuskarsa a had'e yace."Ni ina sonki Aunty Sa'ida kuma kin san Allah baki da miji sai ni da kika raina zaki gane baki da wayo."
Yana gama maganarsa ya fita, na dinga kallon bakin kofar ina mamakin maganarsa, bani da miji sai shi! Lallai Khalid baida hankali da tunani. tsaki naja na shiga gidan raina duk babu dadi.

"Ummatu sannu da aiki." ciki-ciki ta amsa min ban damu da yanda ta amsa maganata ba kawai na shige ciki gidan, Gwaggo kakarmu na samu tana kad'in lagwani! hijab na cire na nemi guri na kwanta ina mayar da numfashi.

Kallona tayi tana cigaba da kad'in ta tace" Yau kin dad'e baki dawo ba Sa'ida anya baki fara yawace yawace ba ni wallahi wannan aikin naki ban yardar dashi ba."


Cikin mamaki na kalleta, tace"Ai da gaskiyata wane irin aiki ne wannan da za'a fita tun karfe takwas ba za'a dawo ba sai karfe uku ko biyu haba jama'a."


Murya na rawa Nace"Gwaggo mai kike nufi dani."? ba tare da wata damuwa ba tace"Abinda nake nufi ai kin san shi."


"Kina nufin ina yawon karuwanci kenan."? da sauri tace." Ooh! ni kada ki daura min jakar tsaba ba haka nake nufi ba." hawaye na zuba nace"To meye na cewa baki yarda da aikina ba wato kema kin fara daukar magana aikaina ko."


Shuru tayi tana cigaba da kad'in ta, komawa nayi na kwanta hawaye wani nabin wani! nace"Wato saboda 'kasa ta rufe fuskar mahaifina shiyasa kike nema ki d'ora min kazafin na zina kamar bake kika haifi ubana ba."


"Kinga Sa'ida kada kisa hawan jinina ya tashi da wannan magana taki ta isheni haka aiki kije kiyi tayi tunda ba zakiyi aure ba sharrin zina da bin maza dole jama'ar gari suyi miki."


Da sauri na mike Nace"Gwaggo na gaji zan tattara kayana na koma gurin mahaifiyata tunda keda kika haifi ubana kin kasa yi min uziri a rayuwa ta ni ba ni zan dauki kaina nakai gidan aure ba sai ranar da Allah ya nufa to tunda kun kasa fahimta zan bar muku gidanku." Saukowa nayi na fara hada kayana,


Kayan kad'in ta ajiye a gefe tace"Ke Sa'ida bana son shashanci da rashin tunani babu inda zakije kinji na fada miki maganar aure kuma ba zan fasa yi miki ba har sai kin tsayar da miji zanja bakina nai shuru to kaji."

Jakar kayana na dauka na kama hanyar fita, sai ta fashe da kuka da fad'in" Au! takani zakiyi ki wuce to bari Babanku Iro ya shigo zan fada masa rashin mutuncin da kike min." Saboda nasan banyi abinda take zargina dashi ba yasa ko sauraranta banyi ba na fita daga dakin da kayana a hannu, haba jamaa na gaji da masifar Gwaggo.

Turus! nayi ganin Baba Iro a tsaye suna magana da matarsa! ya kalleni yana kokarin yayi magana! Gwaggo ta fito daga daki tana kuka da fyatar majina da sauri ya karaso gurin yana fadin"Gwaggo lafiya kukan me kike."? Ta 'kara rurucewa da kuka da fadin"Gatanan saboda nai mata maganar aure shine ta hada kayanta wai gurin uwarta zata koma shine har tana sa kafarta tana taka ni ta wuce."
Da sauri na kalleta ina mamakin sharrin ta gwaggo tsohuwa mai sharrin tsiya.

Baba Iro murmushi yayi inda sabo ya saba raba fad'a tsakanin mahaifiyar tasa da 'Yar d'an uwansa Yace."Haba Sa'ida in da sabo ai yaci ace kin saba da halin Gwaggo me yasa ba zakiyi hakuri ba yanzu da kika had'a kayanki ina kike nufin zuwa." Gwaggo da sauri tace" Zataje can gurin Uwarta ne." Cikin k'unci nace" Baba Iro wai kamar gwaggo itace take min k'azafi to meye amfanin zamana da ita."

"Aa ni kada kiyi min sharri Sa'ida daka fada miki gaskiya sai kice nayi miki sharri." Baba Iro yace."Gwaggo maganar ta 'kare haka." Tace."To kace mata kada ta tafi dan taurin kaine da ita."

Baba Iro yasa hannu yana kokarin kar'bar jakar hannuna, nace"Baba dan Allah ka kyaleni na tafi wallahi na gaji da rashin hakurin gwaggo ka gafarce ni idan maganata ta 'bata maka rai."

Yana 'kokarin magana ya shigo gidan hannunsa ri'ke da leda indomee yaje ya siyo, babu walwala a fuskarsa yace."Me yake faruwa ne naga duk kunyi cirko-cirko a tsaye."

Da sauri gwaggo tace"Yawwa d'a nagari ka ganta nan wai barin gida zatayi saboda nai mata maganar aure." wani irin kallo yayi min kafin ya kalli jakar kayana dake hannun mahaifinsa, cikin yanayin takunsa ya karaso inda muke jakar kayan ya kar'ba hannun mahaifin nasa ba tare da yace wani abu ba ya shige dakin Gwaggo da jakar gwaggo bayansa tabi tana surutai!

Baba Iro ya kalleni a nutse yace."Sa'ida kiyi hakuri kinji ko gwaggo tun kafin ta tsufa take da rikici ki fahimci halinta sai ki zauna lafiya kada wani sa'bani ya sake shiga tsakaninki da ita kice zaki bar gida nan shine tushenki, sannan kuma inaso ki bawa Alhaji Nura dama ya turo da maganar aure kamar yanda ya nuna alama.

Nace"Kawu babu wata maganar aure data ta'ba shiga tsakanina da Alhaji Nura kawai muna gaisawar mutunci dashi ne." Cike da mamaki yace."Sa'ida babu maganar aure data ta'ba shiga tsakanin ki da Alhaji Nura amma yake mana hidima a gida." murmushin takaici nayi nace."Wallahi Kawu babu maganar aure a tsakanina dashi." girgiza kansa ya shigayi yana mamakin maganar, yace."Shikkenan to tunda kince haka dukkaninmu zamu cigaba dayi miki addua akan Allah ya baki miji nagari." a cikin zuciyata na amsa da ameen. gurin ya bari nima a sanyaye na d'aga labulan dakin Gwaggo na shiga, abinda naji suna tattaunawa yasa gabana fad'uwa....


*Masoya ayi min sharing A gruops👏🏻*



*IDAN KINA BUKATA KARANTA LITTAFIN NAN #400 NE NORMAL VIP GRUOP #600 ZA'A TURA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT DIN.....0542382124....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURO SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*
*2*
"Haba 'Da nagari ai idan da gaske kake wallahi ni zan baka goyon baya kaga sai ayi towo na maina dama hausawa na cewa gida bai koshi ba ai ba za'a kaiwa dawa ba insha Allahu Sa'ida matarka c.....Shigowa ta dakin ya hanata k'arasa maganar gabad'aya ita dashi suka bini da kallo, ni kam jiri ne naji yana nema ya kayar dani a gurin dan tsaf na fahimci akan abinda suke tattaunawa Khalid yayi masifar raina ni da har yake iya bud'ar baki ya furta min kalmar so ina a matsayin yayarsa wacce ta girme masa nesa ba kusa ba na rasa wane irin tsaurin ido ne da yaron a matsayina da tsayin shekaruna sai nake ganin bai cancanta ya iya kallon tsabar idona yazo min da wata banzar maganarsa ba, Khalid da wayo na da shekaruna yayi girman jikin da yake tunk'aho dashi kuruciyarsa kaf a gaban idona yayi ta amma yau wai an wayi gari ni yake tare wa hanya yana cewa yana sona.

Kwanciya nayi ba tare dana cire hijabin jikina ba kawai na dinga binsu da kallo ina jin tsantsar takaici a cikin zuciyata ni kam ko zan rasa miji a gidan duniya banga abin aure a jikin wannan mara mutuncin yaron ba........Tun sanda na kwanta a gadon yake min wani d'an iskan kallo irin na manufarci a hasale! nace"Wallahi idan baka daina yi min wannan d'an iskan kallon ba sai ranka ya 'baci shashashan yaro mara kunyar banza da wofi."

'Bata fuskarsa yayi dan har sai da fatar saman goshinsa ta tattare haka yake tun yana yaro idan ransa ya 'baci sai goshinsa ya tattare ya watsa min kallon banza had'e da girgiza kansa.......Yana kokarin yin magana ta rigashi da fadin" Ke Sa'ida meye kuma na kiransa shashasha ina laifin wanda zai tallafe ki ni wallahi naji dadin maganar da yazo min da ita duk girmanki da shekarunki ba zaki gagareshi ba dan mace komai girmanta bata fin karfin namiji."

Tsaki! naja ba tare da nace komai ba na juya musu baya....'Kawataccen sajan fuskarsa ya shafa idonsa 'kur! a mazaunanta da yake bala'in 'kwa-'kwa! duk da da hijabi a jikinta hakan bai hanashi ganin tudunsu ba, ya dinga jin wata lafiyayyar sha'awa na taso masa, a sanyaye ya kalli Kakar tasu yace."Gwaggo ga indomee na nan ki dafa min zanje na dawo." da sauri tace"To d'a nagari bari na kunna risho ai ina da kalanzir a ciki." Fita yayi daga dakin yana shafa sumar kansa.

Sama-sama nake jin surutan ta kafin bacci mai nauyi yayi gaba dani......Can cikin baccin naji maganarsa sama-sama! "Haba gwaggo kefe ba'a abin arziki dake yanzu dan Allah haka ake dafa Indomee duba kin zabga mata ruwa sai iyo take a ciki kawai kinsa nai asarar kudina." Zaune na mike nai saurin cire hijabin jikina jin yanda ya jike da gumi! ina kallonsa yasa hannu yana sosa kansa idonsa kur! a kirjina. girgiza kaina kawai nayi na fara yunk'urin mikewa......Tace."Sa'ida duba dan Allah wai duk wannan gwanintar da nayi masa ban birgeshi ba cewa yake banyi daidai ba."

Tukunyar indomee din na kalla da sauri na dauke kaina jin dariya na nema ta sub'ce min indomee guda uku amma ta cika tukunya da ruwa indomeen tayi tsululu duk ta narke a ciki.........Yace." gwaggo bafa zanyi asarar kudina ba ki cinye wannan indomee ki bani dari ukuna ba." da sauri tace ." Wallahi baka isa ba ba zanci kayan atini ba hakan nan zaka daure kaci idan kuma ba hakaba Sa'ida ta baka wata indomee tunda tana da ita in yaso sai ka kaiwa babarka ta dafa maka tunda ni ban iya ba."

Ta'be bakinsa yayi yace."Sai dai na kwana da yunwa akan na kar'bi abunta ni ba shashashan namiji bane kamar yanda take kira na nafi karfin ta ciyar dani sai dai ni na ciyar da ita."

Gwaggo sakin baki tai tana kallonsa sai kuma tayi dariya da Fadin"Khalid jarumi a gida da wajan ya'ki ka burgeni kwarai da gaske yanzu dai kayi hakuri akan 'barnar da nayi maka." Girgiza kansa yayi yace."Bafa zan hakura ba bari ma ki gani." da sauri ya fara lalaben inda take ajiye Pose d'inta....
Da sauri ta ri'ke gefan rigarsa "Aa Khalid kada ka daukar min kudi wallahi zanyi maka rashin mutunci idan ka daukar kwabo a cikin jakata.....Fita nai daga dakin na barsu suna bugawa dama inda sabo sun saba idan 'yan abin arzikin na kusa suyi ta mutunci idan kuma 'yan tsiyar na kusa suyi ta bugawa, Gwaggo san kudin tsiya ne da ita duk neman da take ba zata ci a cikinta ba sai tai ta tara kudin tana 'boyewa a cewarta sai auran Sa'ida ya tashi sai tayi mata kayan daki da kudin......Pose din ya bude yaga kudi...


Read / Download GA IRINTA NAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album