Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BAYAN NA MUTU Complete Hausa Novel Document by BAYAN NA MUTU


BAYAN NA MUTU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 159972



BAYAN NA MUTU

Reading Time: 13 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Aysha Shafi'ee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08067794315

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 869.79 kb

File Type: txt

Views: 515+

Download: 1135+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.*

*BAYAN NA MUTU..!*

*©AYHA SHAFI'EE*

*(☆_☆)*

*Da sunan Allah Mai rahma Mai jin ƙai.*

*SHIMFID'A*

______

Rayuwa.

Mece ce ita?

Nasha tambayar kaina hakan.

Wannan lokacin dake tsakanin haihuwa da mutuwa.

Lokacin da ruhi ke tare da gangan jiki.

Ko kuma lokacin da dukkan wata halitta walau d'an adam, dabba ko tsirai ke iya numfashi.

Dukkan wad'annan bayanai ne na ma'anar rayuwa, amma wani ya tab'a fad'a min cewa rayuwa itace abinda yake faruwa a lokacin da ka shagala cikin harkokin gabanka, itace dukkan gwagwarmaya da k'addarar dake samun Bawa a tsakanin zamansa na duniya da mutuwa, rayuwa itace lokacin da matsaloli suka sa ka kaucewa hanyar layin da zai kai ga nasararka, sannan rayuwa itace ke d'aukanka daga cikin mafarkan da ka shirya a zuciyarka zuwa k'addarar ka dake jira a zahiri.

Amma ni a tawa fahimtar, zan iya fassara rayuwa da wannan motsin dake gefen k'irjinka na hagu, wannan dukan dake sawa ka riski abinda gobe ta tanadar, wannan bugawar dake baka kwarin gwiwar fuskantar abubuwa, sannan wannan kid'an dake sawa ka sami fatan canji a rayuwarka.

Bayan wannan ma'anar ta rayuwa... Meye kuma DANGI? Su waye su? Ka tab'a tunanin cewa DANGI suna da muhimmanci a rayuwar kowanne d'an adam? Ka taba sanin cewa suna da damar da zasu hargitsa su kuma kuntata rayuwarka ba tare da ka iya wani katab'us ba? Sannan ka tab'a tunanin cewa DANGI zasu iya zama silar ajalinka?

Sunana Fatima Bintu, Biyo ni in baka labarin k'alubalen DANGI, har kuwa BAYAN NA MUTU!

****

07:1 AM.

"Allah ya sani, ina sonki Fatima." Muryarsa mai dad'i da zurfi ta fad'a.

Na k'ara sunkuyar da kaina k'asa sanda tarin kunya fal ta cika kumatuna, idanuna na kallon yatsuna da suka kasa tsayawa waje d'aya saboda na san cewa idanunsa na kaina ta yadda ko yaya na d'ago da nawa, zasu had'e ne cikin nasa.

"Na san dukkan halin da kike ciki kuma na san irin ra'ayinki daya banbanta da namu, nayi miki alk'awarin zan tallafa miki ki cimma burinki in har kika bani dama."

Kwalla ta cika idanuna a lokacin da naji hakan, wad'annan kalmomin su na shafe tsawon shekaru biyu a rayuwata ina fatan jin irinsu daga bakin wani a cikin 'yan uwana, koda kuwa mutum d'aya ne da zan samu tallafi daga wajensa.

Zuciyata ta cigaba da bugawa da k'arfin da yasa na kasa gane a cikin zahiri nake koko a mafarki, na kasa yarda cewa tsawon wannan lokacin abinda nake nema zai zo ya same ni a daidai wajen daya tarwatsa rayuwata ta baya, wajen da kullum nake ganinsa kamar kurkuku sab'anin gida da aka san d'an adam yana rayuwa cikin mutunci da girmamawa.

Sai dai dama ance dukkan nasara tana zuwa ne cike da k'alubale dake k'ara mana fahimtar wasu abubuwan, kuma zamana a cikin gidan ya koya min tarin ilimin da yasa na fahimci wani b'angaren mai duhu na rayuwa sab'anin wanda na taso a ciki.

Nayi murmushi a hankali zuciyata na fatan wannan ya zama mafarin wata sabuwar rayuwar da zan fuskanta.

"Ba zan takura ki ba, zan jira har zuwa lokacin da yayi miki, ki bi tunaninki a nutse Fatima."

Ya fad'a sanda shiruna yayi tsawo.

Sai dai kuma zuciyata ta buga da yadda muryarsa ta ambaci sunana a hankali, naji kamar zan iya narkewa cikin gulbi.

"Ke!"

Wata k'atuwar murya a gefe ta janyo ni daga cikin tunani na, na zabura da sauri sanda atamfar rigar da nake wankewa ta sub'uce cikin bokitin kafin in d'aga idona akan siffarsa, Yaya Sule.

Wani kwayan mutum guda d'aya da baya tab'a barin inyi yini guda a rayuwata ba tare da hargitsi ba, a lokuta da yawa da tunani na ke tafiya rubutun wasik'ar jaki, nasha hasko cewa rayuwata a cikin gidan nan zata fi sauk'i in har zai matsa wani wajen, don shi ba mutum ne mai yawan fita ba, saboda haka kusan kullum yana gefen hajiya yana k'ara b'antare ragowar rusashshiyar alak'ar dake tsakaninmu.

"Me kike yi anan?"

Ya tambaya yana kallon bokitin dake gabana.

Me? na zata kana zaune a wajen lokacin da Hajiya ta jefo min tarin kayan wankinta da sanyin safiyar da ba kowa ya gama tashi ba taje inje in wanke.

Naso ace zan iya gaya masa hakan ba tare da na jawowa kaina wani abun ba.

"Kayan Hajiya nake wankewa." Ba yadda na iya, na amsa a hankali.

"Toh tana jiran kokonta in kin gama."

Na gallara wa bayansa harara sannan na janyo wata k'atuwar rigarta mai kama da Buba akan yadda take matseta in ta saka a jikinta, a shekaruna kaf! ban tab'a ganin mace mai k'iba irin Kakata ba.

A lokacin da nake matse kayan ina shanyawa, zuciyata ta shiga tunanin irin fad'an da zan sha inda sai yanzu da na gama zanje in had'a kokon, Allah yaso Aunty Habiba taji tausayina da sassafen nan tace zata had'a nata dana hajiyan sai inje in karb'a in na gama, duk da cewa kuwa abin ya bani mamaki sanda ta tsaya tayi min magana.

"A'ah Bintu kayan wa kike wankewa da sassafen nan?"

"Kayan Hajiya ne." Na amsa bayan na gaishe ta.

Ta d'an tab'e bakinta kad'an. "Ai da an barki sai rana ta d'aga, amma a sanyin nan haka kamar yak'i..."

Dama na san zata fad'i hakan saboda duk da cewar Hajiya surukurarta ce, basa shiri ko kad'an da ita akan wani dalili da ban san shi ba. Har tayi gaba sai kuma ta juyo tace.

"Kin had'a mata kokon safen ne?"

"A'ah, sai na gama tukunna."

"Toh ai kya jawa kanki wani fad'an tunda kafin ki gama wannan wankin ai rana ta d'aga, je ki d'auko filas d'in nata sai had'a nawa da ita, in ki gama kya zo ki karb'a."

Da murnata a lokacin nayi mata godiya sannan na koma b'agaren Hajiya na d'auko filas d'in ba tare da kowa ya ganni ba, ashe hakan shine mabud'in k'addarata!

______

10:30 AM.

"Kin gama dukka?"

Hajiya ta tambaya a lokacin da na shiga cikin d'akin. Tana manne akan tabarmar kabarta dake shimfid'e a tsakiyar d'akin.

"Eh na k'arasa, har na shanya."

Ba kallon fuskarta nake ba, amma ina iya jiyo tasirin hararar da take aiko min a jikina. Na mik'a mata filas d'in kokon dana karb'o daga wajen Aunty Habiba amma bata karb'a, sai ta nuna min k'ashen tabarmarta da sandar dogaronta kamar shi d'in wani abin kyankyami ne basha zata yi ba.

"A ina kika yi shanyar?"

"Bayan d'akin Aunty Sadiya."

"Kinga ki tabbata, ki tabbata ko d'ankwali d'aya bai fad'i ba in ba haka ba sai ki sake wanke su wallahi."

"Ai Hajiya na k'ulle k'asan su ta yadda iska ba zata d'iba ba."

Daga yadda ta kalle ni, na san ba haka taso taji ba, amma duk da haka ta sake manna min wata hararar gargad'in kafin ta kad'a hannunta a iska alamun sallama.

Na mik'e a hankali na nufi wani waje daga can k'arshen d'akin, wajen da ya zama makwanci da wajen zama na tun lokacin da k'addara ta jefo ni rayuwa cikin BABBAN GIDA.

Gidan dake cike taf! da tarin zuri'ata na dangin uba, tarin zuriar da basa tab'a jin k'aina kuma basa k'aunata a dalilin turbar da Hajiya ta d'ora su akai tun farko, na k'in mahaifiyata da kuma ni da 'yar uwata da muke jininta.

Mahaifina shine d'a na shida a wajen Hajiya, kuma yana da tarin k'anne kusan bakwai a k'asansa, a lokacin rayuwarsa, ya auri mata uku kuma yana da 'ya'ya takwas.

Gwaggo Lami itace matarsa ta farko mai 'ya'ya shida dukkansu maza, ita d'in 'yar uwarsa ce da ta zama 'yar k'anwar Hajiya, saboda haka da ita da 'ya'yanta sune mafi soyuwa a cikin zuri'armu.

Amma mahaifiyata da ta kasance d'iya ga 'yan gudun Hijira bata tab'a zama abu mai daraja ba a wajensu, duk kuwa da cewar sun san yarintarta don ta taso ne a gidan maigari kasancewar iyayenta sun rasu tun tana yarinya, kuma sun san halinta na hak'uri da juriya, don ba kowa ke iya rayuwa a gidan maigari tare da azababbun mata da 'ya'yansa ba.

Amma a lokacin da mahaifina ya nuna yana son aurenta, ba irin tashin hankalin da ba ayi ba akan zai auro wadda bata da asali, sai da maigarin yasa baki tukunna sannan suka hak'ura ba don son ransu ba. Bayan shekaru uku da auren ne ta haifi Yayata mai suna Maryam da muke kira da Mairo sannan ni kuma nazo bayan wasu shekaru ukun, a lokacin Baba ya sake aure.

Ya auro 'yar gidan wani attajiri a garin mai suna Saratu, mace mai tsananin kirki data k'arb'i Innata damu 'ya'yanta hannu biyu ta rik'e, don bayan mahaifinmu zan iya cewa duk k'auyen babu wanda ke k'aunar mu sama da ita, munyi zama na aminci tare da ita kafin k'addarar Mairo tazo ta gifta.

Lokacin da Mairo ta kammala karatunta na sakandire ne Baba yace zaiyi mata aure da d'an gidan wansa Ibrahim, abinda ya haifar da rikici a cikin gidanmu da kuma Babban gida a lokacin kenan, su can Babban gida suna fad'an basu yarda da...


Read / Download BAYAN NA MUTU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album