Join Our WhatsApp Group

MAH NOOR Complete Hausa Novel Document by MAH NOOR


MAH NOOR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 86802



MAH NOOR

Reading Time: 7 Hours

Added On: 03, Aug 2023

Author: Mrs Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 468.41 kb

File Type: txt

Views: 848+

Download: 659+

Last download: 8 days ago

Description/Story: MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 0️⃣1️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
https://www.wattpad.com/981993411?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published

#Destination
From lagos to Yola...
Gudu suke a cikin jirgin kasa, wanda yake tafiya cikin sauri, fuskarta lullube da wani yadi me hade da fari da baki, sai motsa gashin Idanu ta take cikin jin dadi, sannan ta mai da glass ɗinta, duk da bata wuce shekara goma sha biyu ba, amma haka ba zai hanaka fahimtar tsantsar kyan da Allah yayi mata, tab'ata kanwarta tayi tare da cewa.
"Adda, zan sha madara."
Kallon iyayen su tayi sannan tayi magana cikin shagwaɓa tare da faɗin.
"Mom! Ni fa idan muka isa kawai gidan su Nunu  zan sauka ba gidan kaka ba. Ina zuwa rinka damuna da A'isha kaza Aisha kaza."
          Kallonta matar daya gefen tayi cikin murmushi tace mata, "Ya sunanki?"
"A'ishah!"
Ta faɗa a sanyayye, kamar yadda muryanta yaƙe,
Murmushi matar tayi sannan tace mata.
"Toh baki nuna mana fuskarki ba, hanya ba zamu yi na gida dake ba, Hidaya, Raziya. Umar.  Alhaji Ina Maher yaƙe? Kuzo nan."
Lokaci guda suka haɗu, tare da cewa.
"Ummin Maher lafiya?"
Dafa shi tayi sannan ta nunawa Mutumin Aisha da take zaune, tana kallon su. Sannan ta kalli Iyayen Aisha, tace musu.
"Yar su na gani ina so! Tunda zasu sauka a Gombe ne mu kuma A Yola, shine nace ko zamu hada iri da ita shi Sunan shi Muh'd ita Aisha kuma kunga hadin zai yi ai?"
   Dariya suka yi sannan suka ce.
"Toh wallahi sai kin buɗe mana fuskarki mun gani,"
Cike da mamaki ta d'aga mayafin kyakyawan fuskar ta ya bayyana,
Masha Allah. Gaskiya tayi mana.
Sai Lokacin Mahaifiyar Aisha tayi magana tare da cewa.
"Toh indai haka ne toh ba sai ayi magana ba,"cikin Dariya ta kai karshen Maganar ta.
Shima baban Aisha din yace.
"Kun shirya kenan? Toh ni zan amshi auren kenan."
Jin haka yasa Yar yarinyar ta mike da gudu tabar gurin su.
"'laaa! Kunga ta gudu."

     Garin gudu ta bangaji wani mutum, tsayawa tayi tare da kallon shi badan kome ba, sai yadda ya rike mata arms ɗinta, kallon shi tayi cikin idanu ta buge hannun shi, tare da fallasa zata gudu ya dawo da ita, gaban shi, ya kai hannu zai d'aga mayafinta, yana kallon cikin idanun ta, sai ji suka yi kamar jirgin zai sauka kan digar shi kuma ya cigaba da tafiyar... Ya kuma dage sai ya d'aga mayafinta. Tana buge hannun shi. Ya kuma fusata zai bude mayafinta abokan shi suna musu dariya, ta kuma buge hannun shi, cikin dan banzan tsiwa tace mishi.
"Dalla kyale ni, an ce maka kowa irinka me mara kirki, ka nace sai kaga face dina, who are you?"
Yadda tayi maganar cikin rashin kunya da Rashin mutunci ya sake fusata shi.
"Waye Babanki?"
Cikin ɓacin rai ta d'ago kanta idanun ta na cikowa da kwalla tace.
"Babanka ne!" Ta bashi amsa kai tsaye.
      "Laaa! Man kai ne ta gayawa magana yarinyar da bata fi sa'ar Sister ka ba, lallai ka ci ubanta!"

       Bude eyes din shi yayi akanta, ya kai hannun shi ya dafe inda take, sannan ya sunkuyar da kanshi, dai dai fuskarta kamar zai sumbaci ta, ta saka hannunta da karfi ta ture shi tare da barin wajen da gudu, tsaki yayi yana faɗin.
"Fawwas kai banza ne, sai ta rena ni"
     "Idan ka buɗe fuskarka ba, ko ka manta akwai hirami a fuskarka."

     Dariya suka saka, ya koma mazaunin shi yana wasa da wata yar takarda shedar shiga jirgin, wanda aka rubuta Yola.
......
"Toh Sadakin wannan zinariyar dai ya fi karfin kudi sai dai mu biya da zinari irinta."
    Dan haka gashi wannan zai dauki kudi masu yawa, na bada sadakin." Amsa Maman Aisha tayi tare da kallon ana dariya aka cika sharudan auren babu b'ata lokaci aka daura auren, a gurin a ranar goma ga watan Maris, ala dubu biyu da tara. A cikin jirgin kasa da zai kai mutane zuwa Yola da abuja.
          Bayan sun gama, kenan Maman Aisha ta mikawa Mahaifyar Mahir, kayanta suka ci-gaba da hira, jin wasu alamomin da jirgin yake zai sauka akan hanyar shi ya mugun daga musu hankalin.
Take masu yara suka fara niman Yaran su, Aisha iyayen ta suka mike niman ta, kafin su isa inda take jirgin tayi wani irin kara tare da fadawa hanyar da ba nata ba, kafin kace me sun hadu da wani jirgin da ya dibo kaya zuwa Lagos, dake jirgin dasu A'ishah suke ciki.akwai mai  taragon farko, suna haduwa da juna suka wani bada sauti dammmm. Kafin kace me. Jirgin ya kama da wuta, sosai a take, yayita bin jikin jirgin gashi babu halin tsira, domin kana fita ma faduwa zakayi a wani abu dan wasu sun gwada haka, amma babu ci, domin suna fita jirgin mutum yana faduwa zaka ga bai shura ba, gashi a hatsarin ya faru ne a garin Barikin Ladi, na garin jos. Sabida jirgin zai bi ta garin bununu na bauchi state, sannan zai sauke fasinjar Gombe, har dasu Aisha a cikin masu sauka gombe...

          ★★★
2019....

Kar'ar Alarm ce ta tashe mu daga nannauyar barcin da muke, na danna kan Alarm din, cikin jin mugun gajiya na kalli Tasleem, mik'ewa nayi.. tare da ɗaukar towel ɗina, na kalli agogon da yayi kukan sannan nufi ban dakin mu.

     Yau zamu fara aiki da ina aka tura mu service, kasancewar Daddy ya hana a turamu ko ina bautar ƙasa, wai muyi a Yola, hankalin shi zai fi kwanciya idan yana ganin tagwayen shi a tare da shi.
     Kallon ta nayi tana murmushi, kamar yadda ta saba, d'aka mata duka nayi sai da ta tashi zaune tare da zuba min ido, kafin ta tura baƙi.
    Baka ce mai kyau da ita, sai dai doguwa ce Irin mutanen nan da ake kira Muciya da zani, murmushi nayi sannan nace mata."asuba tayi har na dibo ruwan wanka na, saura ke. Mun gama training daga yau sai inda zamu yi Attachment kina nan kina mafarkin kanzon kurege da kika saba.

      Wani irin blush ta bada, tare da lumshe idanunta, dafe goshina nayi tare da wuce ta, tana mafarkin da ta saba.

     Idan da sabo yaci ace na saba da halin Tasleem, na wuce na dauki brush tare da nufar ban daki naje na sille wanka, sannan na fito, ganinta har zuwa lokacin tana zaune. Tana mafarkin da ta saba.
  
Cikin nutsuwa na fita, na shiga shafa mai, ban cika son makeup ba, dan ina da kyau dai-dai gwargwado, Ni fara ce sol kasancewar Mahaifiyata da yar kasan Algeria ce. Mahaifina dan Akko na garin gombe,

  Sannan idan ka kalle ni ina da kiba dai dai misali, sannan ban da Tasleem bana magana da kowa, sabida ban cika son hayaniyar mutane ba, haka Yasaka ake min kallon ina da girman kai.
        Ina da matukar hakuri, bana daukar reni ko wulakancin.

            "Tasleem, bamu da lokaci yau zamu fara aiki da, inda aka tura mu. Kuma kina zaune."
    Tashi tayi a kafitar sannan tace min.
"Noor! Ina son duniyata! Ta zama babba, ina son auren babba mutum me daraja, wanda duk inda na shiga ana ce min Matar wane"
         "Idan kinyi hakuri! KOME DA LOKACIN SA, zaki yi nasara. Kuma ki nemi zab'in Allah, dan ni nafi sha'awan nayi rayuwa ta low class, ban son daukakan duniya, bayi da amfani."

     Murmushi tayi sannan ta shiga wanka. Tasleem da Parent din tq, suna da mugun son kai. Duk abinda zan samu na rayuwa na Tasleem ne. Sannan duk abinda zata samu na tane.  Zai yi wuya ta nasan ta samu domin b'oyewa ake kar na sani, tun tasowar mu suke nuna mana ita ya kamata ta ta sami nasara ba ni ba. Shi yasa sai na koma a rayuwata bana son nasara ko dan na kasance marainiya ce bani da uwa bani da uba.
     My First choice na karatu, Medicine ne. Itama shi ta cika, abin mamaki koda mukayi jamb ta fadi sai ni na samu,  ita kuma bata samu ba, dole aka canza mata course, har dani. Ita aka bata accaunter ni kuma aka bani Mass communication. Ban damu ba, dan na fahimci su kar nayi gaba na barta a baya ne, sai na amshi sakamakon nayi godiya.
      Ni da ita mun taso kome namu iri daya ne, amma a ta bangaren Cigaba na rayuwa nata daban ne, Mommy da Daddy sun koya mata buri, kuma haka ya faru ne sabida kasancewar ni nafita kyau, na fita halittar jiki me kyau, dayawa suna zab'ena a barta, dukda itama ba laifi tana da nata kyan but ta taso da kazamin buri da kishina.

        A gaban mutane zata wofantar da ni, dan kar na samu yabo a gurin mutane, shi yasa ban damu da kwalliya ba, domin idan zamu fita, tare ita zata gama b'ata lokaci. Ni kuma za a azazalamin na fito. Idan na fito suka ga nafita kyau su tsiro min da damuwa har sai nayi zuciya nace ta tafi kawai.

       Na hakura, abin yana mugun min ciwo, sannan sun basu kyautatta min ba, su kuma basu barni na koma gurin dangin Mahaifiyata ba.

               Koda muka shiga makaranta ma, haka take wulakantani, amma idan tana son koyan wani abu na karatu, haka zata saka ni a gaba da magiya, haka zan koya mata tana tashi zata nuna min itace ta iya ni ce me koyan. Dan haka na daina koya mata. Ina da mugun zuciya shi yasa suke d'aga min kafa.

            Dan kokari nafita mai da hankali na akan karatu, ita kuma tayi kwalliya ta sha gaye, kowa ya san itace wata. Shi yasa ban damu da ita ba, har yau ita ke bina. Koda muka shiga aji na biyu a jami'a, sai Mommy ta hanani yawo da gyale, suka sani ina yawo da hijab, sabida wai kar ana gani na, aki kula yar su. Ni ina kyan da yake dakushe na yar su, na hakuri idan ta sami miji sai na cigaba da yawo ba hijab da niffab. Haka ya sani hakura da saka gyale, duk kwalliyar da zanyi da hijab ne. Amma a haka ban tsira ba, idan nayi saurayi sunyi ta kunshe shi kenan, har sai na rabu dashi. Ita kuma ta fara soyayya dashi.

    Wani lokacin kuma ita ke kore min su, nayi samaruka  dayawa amma ana kore min su, sabida ita bata samu ba, ni da na samu kuma an kore su. Bawai farin jini na fita ba, kawai ita tana duba Wanda ya kasan best Man in earth, ko nace world wanda yake da good career, rich man wanda ya maida hawa Bugatti kamar hawa mashin. Wanda zai yi mata kyautar Mansion a cikin Unguwar maitama na Abuja ko a lekki. Ko banana island ko a  Tobago island U.S. Mutumin da ya shirya wa rayuwar shi Luxury life, yadda zasu shiga su fita. Yana da gidaje a kasashen Turai da wasu yanki na Afrika, wannan shine mafarkin Tasleem Elhussain Jimeta....
Hey guys Am back da wani story! Don Allah idan ba zaka karanta ba, karka damu kanka Please And Please idan baki yi karki zage ni, don Allah bana son tashin hankali, kamar yadda wasu suka min A KOME DA LOKACIN SA. Sannan zaku yi hakuri zan rinka posting din duk bayan Four days insha Allah.
Idan kuma kika yi voting da comments insha Allah zan mai dashi After few two days...
#Vote
#Comments
#Share🤩😍😘
https://my.w.tt/DBOvuwPDAbb

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 0️⃣2️⃣
    MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~#meet hot guy~

Juyawa tayi ta kalle ni, cikin wani irin kallo, kafin tace min.
"Ki tsaya anan, naje cikin idan kuma kika biyo ni, zan fahimci  you Are ready to destroye my happiness!"
   Sake baki nayi ina kallon Tasleem. Kafin na tsinci kaina da jin wani irin yanayi..."ok shiga"
"Better!"

Sunkuyar da kaina nayi tare da jin wani irin kwalla zai zubo min. Sautin tsakinta naji a hankali ta tsaya a bakin kofar ta gyara zaman rigar ta, tare da  gyara ko ina sannan ta shiga.
A hankali ta sake bakinta, tana kallon cikin office din. Tare da kallon halittar da yake zaune akan wani kujera, yana aiki da laptop. 
"Excuse me sir!"

"Koma ki kira wacce kika hana shigowa!" Jin wani irin Muryar da yayi magana, yasanya ta diriricewa, he look Handsome guy,.kasa motsi tayi tana mishi sani irin kallo, har wani Luv bird take gani tare da wing dinsu suna zaga kanshi.
"Cewa nayi ki kira ta."
Ya daka mata tsawa, da sauri ta juya tare da fita tana faɗin.
"Ok..ok... ok!"

Ta fito da sauri, ina tsaye sai ji nayi Tasleem ta wanke ni da mari sai da gurin ya dauka.
"You are bad luck, me yasa mike covering Destiny dina, wannan kika sake wani abu ya shiga tsakanin ku, sai na kashe kaina sannan na rubuta letter akan kace kika yi sanadin mutuwa ta. Please Noor, karki rabani dashi we deserve each other please."

        Rike hannun ta nayi tare da jin wani irin kuka, yazo min nace mata.
"Har yanzun abokin rayuwata bai iso gare ni ba, daga lokacin da yazo gare ni, babu wanda ya isa dakatar dani, don haka babu abinda ya dame ni, but shine kuka mare ni."

Cikin tashin hankali, ta shiga tab'a fuskana, tana shirin kuka..
"Am sorry, ba zan kuma dukar ki ba."

      Fada tana sauke kwallar ta, a hankali na goge fuskana, sannan muka shiga cikin office din kamar bai ga abinda ya faru ba, kallon mu yaƙe, kai na a sunkuye dan ban damu naga waye ba.

"Have sit"
Zan ja kujeran tayi maza ta buge hannuna, ta zauna, dayar kujeran kuma ta juyar dashi ta daura jakarta akai.

"I said have sit!"
Wani irin harara tayi min, sannan ta dauke jakar ta, ta barni na zauna. Tunda muka zauna mun kai kusan awa daya da rabi, kafin ya d'ago kan shi. Tunda muka zauna Tasleem ta zuba tagumi, tare da zuba mishi ido.

         D'ago kai yayi tare da daka mata tsawa.
"Bana son kallo, da ugly face dinki nan."

Wani irin kunya ce ta kamata,.ta kuma shiga nutsuwar ta. Sannan ta kalle ni, ganin yadda nake kallon kasa yasata take min kafa. Sai da nace.
"Auchww!"

Da sauri ya d'ago kanshi, yana kallon yadda nake yatsina fuska, tare da cire takalmin kafana,  sai lokacin da tuna yau da asuba nayi tuntube da kofar kitchen, na kuma ji ciwo domin farcen ya fita.

      Kura min ido yayi cikin nutsuwa, yana kallon yadda nake jan zafin ina hura iskar bakina, mik'ewa yayi ya bude wani wardrob ya dauko a kwatin first ya iso gaba na, sannan ya bude akwatin, da sauri Tasleem ta iso tare da kai hannunta kan...


Read / Download MAH NOOR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album