Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

AKAN SO Complete Hausa Novel Document by AKAN SO


AKAN SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 155844AKAN SO

Reading Time: 12 Hours

Added On: 25, Jul 2023

Author: Lubna Sufyan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 870.7 kb

File Type: txt

Views: 1285+

Download: 860+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [6/10, 9:50 AM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: Thursday, 4 May 2017
AKAN SO 1
*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

01

*18/02/2017*

Coffee dinta take hadawa hankalinta a kwance tana kallon NTA don tana son shirin da MTN suke yi na tabo rayuwar mutane.

Yarinyar data fi burgeta "Yusra fari" ta karbe show din da fadin.

"Yau muna samu wata wasika ne datai matukar bamu mamaki ta kuma taba zuciyarmu.

Bamu taba cin karo da abin mamaki ba irin wannan"

Hankalinta ta sofi ta mayar kan t.v din tana cakuda coffee dinta da cokali. Aka soma karanta wasikar kamar haka:

*NEMAN MOH DA GAGGAWA*

*Kai babana ne!!!*

Bansan abubuwa da yawa ba akanka.Nadai san sunanka Fu.ad. Kuma kai dan wasan kwallon kafa ne saidai bansan ko wanne club ba.

Sannan da jimawa kana shaawar wasannin mota na stunts. Mutane suna kiran ka Moh.

An gayamun bakasan dani ba. Ancemun zan fahimta wata rana.

Ni nawa mai sauki ne.

Wannan shine : shekarata goma sha biyu. Mutuwa zan.

Nasan mamata ba zata taba jin dadi ba. Inaso inganka kamun in mutu.

Wata rana zata gane. Har yanzun tana sonka sosai.

Moh idan ka karanta wannan dan Allah ka dawo. Ba ma saika zama babana ba. Ba saikace kana so na ba ko kabani hakuri.

Kawai kazo kaganni.

Ina jira amman banida lokaci sosai.

*Nana*

*

Ana gama karanto wasikar mug din coffeen dake hannunta ya subuce ya fadi ya ko tarwatse ko ina na kitchen din.

"Nanaaaa..........."

Sofi ta kwala mata kira cikin tashin hankali.

Ji tayi kafafunta basu da kwarin daukarta.

Tsugunnawa tai ta jingina da locker din kitchen din tana maida numfashi.

"Ya Allah! Me nana taje tayi ne?"

Ta furta a fili.

"Mumy......."

Ta juya ta sauke idanuwanta cikin na nana data kira sunanta da yanayin tambaya da shakku.

Kallon ta take sosai. Jeans ne a jikinta blue sai riga itama blue mai haske. Kanta sanye da hular data lillibe askakken kanta.

Duk da ramar da tayi sosai. Bai hana kyawun nan nata fitowa ba. Hawayen dake cike da idanuwan ta ya zubo.

Lokaci daya sofi taji zuciyarta ta karye. Hannu ta mika ma nana alamar taje.

A hankali ta karasa ta rike hannunta sannan ta zauna kusa da ita.

"Nana zaki bata kayanki. Tashi kigani na zubda coffee a wajen"

Kaman bata ji mai tace ba ma ta riko hannunta.

"Mumy kiyi hakuri. Kawai ina so ingan shi ne ko sau daya"

Sauke ajiyar zuciya sofi tai tana kokarin tarbe hawayen dake zubo mata.

Ta ina zata fara ce ma Nana tun wata biyu da haihuwarta tai kokarin nemo Moh amman a banza.

Ta gaji ta hakura. Haka ma da yanzun shi ne karshen zatonta akan samun saukin Nana din.

Bata san duniyar da yake ba. Bakuma tasan inda zata nemo shi ba. Haka ta yanda zata soma gaya ma nana.

"Nana bana son ki daga zatonki akan nemo shi ne. Karkizo ba.a ganshi ba"

Hawayenta nana ta goge sannan tai mata wannan murmushin dake siye zuciyar mutane.

"Ko ba a ganshi ba. Bazanji kaman banyi kokarin nemo shi ba"

Murmushin sofi ta mayar mata hadi da fadin.

"Badai naso ki kwallafa rai. Oya tashi daga cikin coffee din nan. Ki wuce ki sake kaya ki kwanta"

Babu musu nana ta mike. Matsawa tai sosai kusa da sofi ta manna mata sumba a kunci hadi da fadin.

"I love you mumy"

Mayar mata da sumbar tayi tace

"I love you too princess. Maza ki wuce"

Har nana tazo fita daga kitchen din sofi ta kirata da cewar.

"Ya akai kika kai gidan t.v?"

Wani murmushi tai tace.

"Mumy a school ne fa muke maganar da fa.iza shine tacemun muje gidan radio can ake kai cigiyar mutum.

Shine na rubuta a takarda da aka tashi bamu tsaya lesson ba mukaje.

Suka hanamu shiga ma. Saida inata kuka ne wani mutum yazo ya tambaya nace ina neman babana ne kuma ni mutuwa zanyi.

Inaso ingan shi. Shine fa yaje damu har ciki ya biya kudi muka bayar da wasikar.

Wallahi mumy bance su sa a t.v ba"

Tunda ta fara bayanin sofi kallonta kawai take. Tama rasa me zatace dan haka ta daga mata kai kawai.

Kallonta take harta bar kitchen din. Sai lokacin tabar hawayen da take kokarin tarbewa suka zubo.

Tana jin muryar fu.ad cikin kanta tamkar yanzun abin ya faru.

"I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.

Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Inada su haneef. Ina da su pha.iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu"

Mikewa sofi tayi ta dauki wayarta ta kira Ansar kamun tunani ya haye mata bugu daya ya daga.

"Sofi lafiya dai ko?"

Shine tambayar farko da ansar yai mata da wata damuwa a muryarshi.

"Nana tana lafiya. Tana dakinta......"

Ta amsa shi. Jin yanda ya sauke numfashi yasata murmushi.

Ansar kenan badon ita ta haifi nana ba saita rantse yafita sonta.

Jin yayi shiru ta ce.

"Ansar nana ta ballo aiki"

Cike da damuwa yace.

"Me tayi?"

Cikin nutsuwa ta soma bashi labari iya abinda tasani.

"Good. Ni banma san yanda akai wannan tunanin bai zo mun ba"

Ansar din ya fadi.

"Ni fa banajin za.a ganshi ansar. Bana son nana ta saka ranta akan abinda ba zai taba yiwuwa ba. Nafiso ta samu duk wani farin ciki dazan iya bata kamun ta........."

Katse ta ansar yai da fadin.

"No sofi. Please No karki karasa. Za.a ganshi and he is going to be a match"

Dafe kai tayi dan ya soma mata ciwo da yanayin tunanin data cika shi dashi.

"Zamuyi magana anjima dai"

Ta fadi muryarta a gajiye. Sallama sukai da ansar din ta fita daga kitchen din zuwa bedroom dinta.

***

Tana shigowa office ringing din wayarta yai mata maraba. Kamun ta karasa inda wayar take harta yanke.

Ta dauka ta duba. Missed calls har biyar. Ta bude ta lumshe idanuwanta ganin Jabir ne. A ranta tana fatan Allah dai ya sa lafiya.

Tana shirin kira kenan. Ya sake kiranta ta dauka da fadin

"Honey J....."

Kaman yanda take kiranshi. Muryarshi dauke da yanayi na bacin rai yace.

"Sai yanzun kika ga damar daukar wayar kenan?"

Glass din dake manne a fuskarta ta cire ta ajiye kan table sannan tace

"wallahi wayar nabari a office munata fama da marassa lafiya"

Tanajin yanda yake jan numfashi ta cikin wayar. Tasan halin shi sarai. Ranshi a bace yake.

"Idan kina da lokacin mu kizo gida. Ikram bata da lafiya. Akamun waya naje na daukota a school"

Cikin damuwa tace

"Ya Salam aida ka kawomun ita nan asibitin mana honey J kasan....."

Katse ta jabir yai da fadin

"Idan ba zaki dawo ba Jana ki fadamun kawai. Insan yanda zan da yarinyata"

Shiru tai hakan yasa jabir kashe wayarshi. Ta sauke wayar daga kunnenta hadi da maida numfashi.

Saida ta kira Dr.Farida ta fada mata zata je gida akwai wani abu daya taso ko da an nemeta sannan ta dauki duk abinda take bukata ta fita.

*

Da sallama ta shiga. Ba kowa a falon dan haka ta taka zuwa dakin baccin su. Nan ma da sallamarta ta shiga. Bataga kowa ba.

Jakarta ta ajiye. Ta cire lab suit din dake jikinta ta rataye sannan ta fita zuwa bangaren yara.

Saida ta tura kofar sannan tai sallama. Yana zaune gefen gadon ikram yana danna wayarshi.

"Honey J......"

Hannu ya daga mata tare da fadin.

"Shhhhh......."

A hankali. Shirun tai ta karasa inda yake. Ikram tana kwance da alama bacci take.

Tashi jabir yai ya nufi hanyar kofa ya bude ya wuce. Jana ta sauke wani wahaltaccen numfashi.

Sam sam bata son rikici. Ciwon kai yake saka mata. Ta kuma kula yau jabir rikice ne fal a cikin shi.

Taba jikin ikram tayi taji shi zafi rau. Musamman kanta. Ta kula da wata leda da take gefe.

Ta dauka ta duba.Magunguna ne da katin asibiti. Da alama jabir asibiti yakai ikram.

Gyara mata lulluba tai sannan ta fita daga dakin ta samu jabir a dakinsu a tsaye.

Karasawa tai inda yake. Ta dora hannunta akan kafadarshi tana kallon idanuwanshi da suke cike da rigima.

"Da kinyi zamanki ma. Na rigada nakaita asibiti"

Hannunta tasa ta shafi fuskarshi. Yana wani kauda idanuwanshi daga cikin nata.

"Sai da nai handing over ne fa na taho. Ya jikin nata?"

Hannuwanta ya cire cak daga jikin shi ya wuce ya zauna. Bata dai gaji ba. Dole ta lallaba shi.

Dan haka ta bishi kan gadon ta zauna gefe.

Hannunta ta dora kan cikinshi.

"Kaci abinci?"

Ta bukata. Muryarshi a dake yace.

"Karki samu damuwa. Indai patients dinki sun samu yanda suke so. Meye matsalarki damu?"

Da gaske yau jabir rikici yake ji. Tashi tai ta shiga toilet dan ta watsa ruwa. Inya gama fushin sunyi magana.

Jabir gyara kwanciyarshi yai kan gadon. Jana ta gama kaishi bango tana daukar rigimar nan karama ce.

Tazo tana wani lallabashi da soyayyarta din nan zata wargaza mishi plan.

***

*EUROPE*

20/02/2017

Kwance yake abinshi yanayin yammacin ya saukar mishi da kasala. Yau bayajin zuwa ko ina.

Sunyi da Logan zasu fita sai dai bayajin zai iya zuwa ko ina.

Wayarshi yaji tana ruri ya dauko ta gefenshi ya daga. Logan ne.

"Hello logan. I am sorry......."

Kamun ya karasa Logan ya katse shi da fadin.

"You are not in the mood huh?"

Dafe...


Read / Download AKAN SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album