Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AUREN WUCIN GADI Complete Hausa Novel Document by AUREN WUCIN GADI


AUREN WUCIN GADI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 95797



AUREN WUCIN GADI

Reading Time: 7 Hours

Added On: 10, Aug 2024

Author: Usman Umar Gombe ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137017208

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 380 kb

File Type: doc

Views: 668+

Download: 357+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: sai gashi ya dawo da kaya niki-niki tare da wani yaro daya rike masa kayan a bayan mashin.

Yana gama bata kayan da ya sayo matan ne ita kuma ta fara aikin sarrafashi, Ta dauko fulawanta ta fasa koyaye ta shirya masa Shash kabab, saboda ta taba yi masa ya sanya shi santi, Tana gamawa dashi ta dauko blandern ta ta markada strawberrynta ta shirma masa lemonsa. Ta dafa masa Dan wake kuma ta yanka masa dafaffen koyi akan saboda ya kara armashi, saboda tasan yadda yake bala'in son dan wake a rayuwarsa, ta dauko kazanta ta gida ta jara ta masa dahuwar kazan larabawa saboda tasan baya cin kajin Bitnary.

bayan ta gama shirya su akan dinning table kai kace abincin mutum goma aka ajiye wa, ita a tunaninta kowwan ne sai ya taba, Karfe biyar takawo kai ita kuma tana ta dauki akan bazata kira shi ba, sai dai yazo yaga bazata, Taga karfe biyar tayi kai har shida shiru bataji motsin saba hakan yasa ta yanke shawarin kawai ta kira shi a waya ta tambaye shi ko lafiya bai iso ba ta dauko wayar sanda tazo har kan sunansa data rubuta MAI SANYI NA Da manyan bakake, Sai tace a zuciyar ta wata kila ma yana bakin terminus Sai ta fasa kiranshi, akan kawai bari tadan jira kadan ta rinqa jeka-ka-dawo tsakanin ciki da falo tana cike da tunane-tunane ta saka wannan ta sunce wancan da taga ta gaji sai ta je kan kujerar dinning table ta zauna ita daya zamanta keda wuya sai taji ana kiran sallar isha, sai a lokacin ma ta tuno ashe ma batayi magriba ba, take ta tashi da sauri ta dauro alwala ta gabatar da sallar magribanta sannan ta hada su da isha, ita a tsammaninta kafun ta idar da sallahr zataji shigowar gogan nata, amma shiru kake ji kaman maye yaci shirwa
Take ta fara neman wayanta dan tama manta ina ta ajiye shi take ta shi taje tahau duba kan gado, amma bata ganta ba taje bandaki inda ta dauro alwala amma sai wayan nan tace mata dauke ni ta tafi kitching ta fara bude-buden kwanuka sai dai nan din ma shiru babu labari bakin ciki ya cikata ta juya zata tafi daki daga kitching sai kawai taji wakar (Mai Gadon Zinari) Na tashi A Falonta akan dinning table, Nan take sai ta tuno ashe daga kan dinning din tayi bandaki dan dauro alwala, Kafun ta isa ma wayar ta katse tana zuwa da gudu hannunta na bari ta dauko wayarta tana duba sai taga missed call wanda take tsammanin ne, Dan MAI SANYI NA tagani kawai sai ta kira wayar tana fara ringing ya daga yana dagawa sai yaji ta fara masa kuka irin na sakalcin nan mai kashe jikin duk da namiji mai saurarensa.
Sai yace: Dakata sarkin kuka kiyi hakuri! kiyi hakuri, kin san yanzu haka ina ina ? tambayar da taji ya jefo mata kenam.
Take cikin muryar sakalci tace masa: Nikam ban sani ba, tunda bazaka dawo ba!
Yace: haba!! Yanzu haka ina kofar gidanki jira nake kizo ki bude min, amma dan allah kibar kuka saboda tare da abokina Musa nake ?
Bata bari ya gama rufe bakin saba ta ruga da gudu bakin kofa tana zuwa cikin dauki ta bude kofar ina shigowa gidan bata bari ya kara saba ta daka wani uban tsalle ta rungume shi ta fara masa kuka.
Tana ce masa: yanzu ne karfe biyar din naka tayi ko ?
Duk abun da takeyi ta ma manta da akwai wani abokinsa agun shi kuma musa tsayawa yayi yana kallonsu da yaga abun bana kare bane, sai yace: Abokina nikam Bari na tafi kar amin tarar letti tunda naga abun naku bana kare bane.
Take Sai jameela taji wani uban kunya ya kamata ta sake sulaiman a hankali Cikin jin kunya ta juya tace: Malam musa ina wuni ?
Yace: Lafiya.
Bai kara ce mata komai ba daga nan
KASH MU HADU A PAGE 002



&& AUREN WUCIN GADI &&
l ������ Page 002 ������
Na
�Usman Umar Gombe &&
(Babangida Ustazu)&&
Call/WhatsApp
08137017208
Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Kawa Ta Gari
FATYN MAMAN FATY '''
(Ceceniya Bayan Tike Gombe)
#ToDayIsMyBirthDay @21
Tun lokacin data hadu da sulaiman to tare take ganin su da musa, tana jin kunyar musa sosai saboda mutum ne kamili mai addini da son sada zumunci dan haka tun kafun ta auri sulaiman take matukar jin kunyar abokin nasa.
sulaiman yaga shirun nan bana kare bane sai yace: Idan kun gama jugum-jugum din sai mu shiga ko ?
Nan take ta karbi Jakar mijin natan wanda yake hannun abokin nasa suna shiga ciki tace yanzu kam sai ka shiga kayi wanka ka fito kazo kaga irin tarbar dana maka, daga nan kuma sai ka bani tsaraba na.
Yace: to zumudi naji, Aboki na kaje ka zauna ta baka labarin mai ta dafa mana.
Musa Yace: A'a Ni a Suwa ? Nama Isa kadai kawai kaje ka fito nima na samu na tafi dan kar amin taran latti a gida.
Sulaiman yace: Ka ganka ko ka fara ko ? Nikam ko ka dawo Mijin tace ne Sai abun da maman Sajjad tace maka shi zakayi ?
Musa Yace: Mijin kan tace nema!
Dukka sai kuka fashe da dariya, sai sulaiman ya ruga da sauri ya shiga bayan gida dan ya watsa ruwa.
Sai jameela tace: malam sai muje dinning table ko ?
Sai yace: inje in miki meye ?
Tace: Ah abun da yace na fada maka mana!
Zama yayi a kujerar Falon Yace cikin barkwanci: Dan allah ki rabu da wannan mai zafin naki ?
Tace: A'a Kul! shi mai sanyi nane bai mai zafi ba! Ai Allah ya raba mu da zafi kona wutan duniya yane, balle konan zuciya.
Yace: To! Ameen tunda dokin mai magana yafi gudu!
Tace: Babu wani!
Suna cikin surutun sai taga ya fito tace muje ka canja kaya ko dan na tanada maka kayan sawa na musamman daman.
Baima kula ta yace: Aboki na ta cikaka da cakwaikwaiwa ko ?
Musa yace: nidai ban fada ba!
Tashi tayi ta rike hannun sa ta jashi daki suna dariya suka bar, malam musa a falo, cikin abun da bai wuce minti biyar ba, sai gasu sun fito tare.
Ganin hakan yasa musa yace: Gwanda na tashi na tafi naga kamar na hana ku shan iska ?
Cikin dariya sulaiman yace: koma wani irin iska ne tare dakai zamu sha ta ?
Cikin bude baki yace: na isa ma ? wane ni ?
Ana cikin haka sai musa yace: Aboki ba muyi sallah ba ko ?
Sai sulaiman yace: eh mana ai duk kaika jawo, tun da kaine ustaz gashi kuma ma har anyi sallahr isha kuma ko magriba bamu yi ba!

Sai Musa Yace: A to ba komai sai mu hada su muyi su!

Sai a daidai wannan gabar jameela tasa baki tace: Amma malam hakan ba laifi bane ?

Sai Musa yace: Eh mana ba laifi bane ana iya hada sallah dan annabi S.A.W.A shima ya hada sallah a wasu hadisai.



ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJEN MASU BIBIYAN RUBUTU NA INA MUKU FATAN ALKHAIRI BISA SHAWARWARINKU NA ZABI NA CANJAWA WANNAN LABARIN SUNA DAGA AUREN MUTUA ZUWA AUREN WUCIN GADI SABODA DUKKA ALAQAR SU DAYA NE



Cikin mamaki tace: af to ai ance, wai bakyau hada sallah sai aguri hudu sune: Idan ana ruwan sama, ko idan mutum yana tafiya, dadai sauransu.

Musa cikin fara'a yace: mata eh annabi s.a.w.a ya hada sallah a koma bayan wadannan lokuta akwai hadisai daban-dabam da suka karfafi hakan Domin lokaci azahar da la'asar lokaci kusan daya haka nan magriba da isha.

Sulaiman yace: kafun ku gama
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AUREN WUCIN GADI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album