Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KADDARA CE Complete Hausa Novel Document by KADDARA CE


KADDARA CE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38906



KADDARA CE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 07, Jul 2024

Author: Salma Ahmad Isah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08130172702

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 201.53 kb

File Type: txt

Views: 668+

Download: 495+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: *ƘADDARA CE!*

_(Destiny unfolds with a heavy heart)_

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

•••
Assalamu alaikum jama'a.

Barkan mu da wannan lokaci. Sannun mu da sake saduwa da ku a sabon littafina me taken ƘADDARA CE!.

To, kamar littafin HASKE, shi ma wannan paid book ne. A kan ₦300 kacal. Amma kafin nan ina ɗauke da free pages har guda 10.

To sai ku gyara zama, domin karɓar wannan da zafinsa. Kamar dai yanda kuka saba karɓar duk wani rubutu nawa.

*⚠️ Ban yarda da wani/wata. Ya sarrafa min littafi ta ko wace hanya ba tare da izinina ba. Saboda yin hakan, babban kuskure ne. Da fatan za mu kiyaye, a bi doka a zauna lafiya.*

Na sadaukar da wannan littafin zuwa ga duk wata 'ya mace dake fama da cutar sickler...

•Gaisuwa zuwa ga Khadeeja Candy, Hadiza D Auta, Sadi Sakhna, Nainerh KD, Fatima Ahmad Isah da kuma Amina Ahmad Isah. Allah ya kare min ku a duk inda kuke.•

*SHIMFIƊA...*

KADDARA!

Shin me cece ita?.

KADDARA na ɗaya daga cikin hukuncin Allah da ya kan zartar a kan bayinsa tun yayin hallita.

KADDARA tamkar zagayen zobe take, wanda ɗan adam ke rayuwa a tsakiyarsa.

Duk wani abu da ya samu bawa tun daga ranar haihuwarsa zuwa ga ranar da zai koma ga mahallicinsa sunansa KADDARA.

KADDARAr ko wani bawa na rubuce ne tun kafin ya iso zuwa duniya.

Kowa da ka ga yana rayuwa a doron duniya yana yin ta ne a doron KADDARA.

KADDARA na ɗaya daga cikin manya manyan siffoffin Allah subhanahu wata'ala.

Domin duk abin da ya samu bawa a rayuwa muƙaddari ne daga wurinsa. Wa lau me kyau, ko akasinsa.

بسم الله الرحمن الرحيم

*01*

*Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.*

*Da misalin 08:20 na dare.*

Matashiyar yarinya ce tafe a gefen hanya. Hannunta na dama riƙe da farin bokitin fenti. Yanyin yanda doguwar rigar atamfar robar da take sanye da ita ke mannewa a jikinta zai sa ka fahimci cewa ana cikin yanayin hunturu ne.

A hankali take ɗingisa ƙafarta ta hagu wadda daga gani bata da lafiya tun asali. A kallo ɗaya da za ka mata za ka san cewa tana ɗauke da ciwon sickler. Saboda kalar idonta da yake yalo. Da cikinta da ya tashi kamar na me jaririn ciki. Da kuma yanda yanayin jikinta yake nuna cewa tana da sickler.

Damuwa ce kwance a kan allon fuskarta dake nuna nau'in jinyar da take fama da ita. Kuma damuwar tata ta samo asali ne sakamakon wani da ya karɓi kunun ɗari biyu a wurinta ya sha. Ya tashi ya tafi ba tare da ya bata kuɗi ba.

Ba wai wannan ne ya jefata cikin damuwa ba. Fargaba take na yanda za su kwashe da matar babanta Auwwa. Saboda kunun nata ne, ita ce take mata shi dan ta je ta siyar ta kawo mata kuɗi. Kuma a kullum cikin gargaɗarta take kan kada ta kuskura ta bada bashi ko da kuwa kunun zai yi jangwaɓo ne.

Jiki a sanyaye ta dakata a ƙofar gidansu na masu ƙaramin ƙarfi. Ta ɗaga kai ta kalli gidan tana jin yanda iskar da ake a garin take shiga har cikin ƙasusuwan jikinta da ba su da ƙwari. Ga kuma yanda ƙafarta ta hagu ke mata ciwo tun a safiyar yau da ta tashi. Kasancewar lokacin sanyi shi ne lokacin da ciwon sickler ya fi zaɓar ya dinga tashi a-kai-a-kai.

Yawu ta haɗiye a sanda ta hasaso irin azabar dake jiranta a cikin gidan. Ko da rantsuwa za ta yi ba za ta yi kaffara ba kan cewar yau sai ta yabawa aya zaƙinta. Dan Auwwa ba ƙyaleta za ta yi ba.

Cikin saddaƙarwa da sallamawa rayuwa ta shiga gidan, bakinta ɗauke da sallama. A tsakiyar gidan ta ci birki. Sakamakon arba da Auwwa da ta yi, zaune a tsakar gida tana firfita murhu. Wutar dake cikin murhun ta kalla. Sannan ta faɗawa kanta cewar sai an ɗana mata wannan wutar a fatar jikinta.

Saboda tsabar Auwwa muguwa ce. Ba ta hukuntata da komai sai da wuta. Hantar cikinta ce ta kaɗa, a sanda hankalin Auwwan ya kai kanta. Wata uwar harara ta watsa mata tana faɗin.

“Kunu ya ƙare yau?”

Cikin fargaba ta gyaɗa kanta tana aje bokitin hannunta a tsorace. Auwwa ta harerata tana faɗin.

“Miƙo min kuɗin nan na lissafa shi.”

A hankali ta matsa kusa da Auwwan tana jin ƙamshin azabar da za'a mata na kusantota. Ta tsugguna a ƙasa. Sannan ta sa hannu ta ciro cinikin da ta yi a cikin jaka. Ta miƙawa Auwwan tana jin ƙwallar azabar da ba'a mata ba na cika idonta.

Auwwa ta karɓi kuɗin. Sannan ta shiga lissafawa. Har zuwa lokacin matashiyar na tsugunne tana sauraron hukuncinta. Cike da masifa Auwwa tace.

“Ina kika kai ɗari biyu?”

Matashiryar da ƙwallar idonta ta fara zubowa ta ɗaga kai ta kalli Auwwa. Sannan ta girgiza kanta tana faɗin.

“Salisu osi ne ya karɓi kunun na ɗari biyu ya sha. Da zai tafi nace ya bani kuɗin... Shi ne yace... Ya ce wai sai gobe zai bada, yanzu babu canji a wurinsa!...”

Ba ta kai ga rufe bakinta ba wani mari me ƙarfi ya sauƙa a kan kuncinta. Ta fashe da kuka tana dafe wurin. Cikin ƙanƙace ido Auwwa tace.

“Maimuna sau nawa nake ja miki kunne kan bada kayana bashi?. Saboda irin wannan ya sa sai na auna kununa ko na nawa ne, sannan nake baki ki fita da shi... Amma sai da kika ha'ince ni. To ba ki sha ba!”

Auwwa ta kai ƙarshe tana rarumar bakin wutar dake cikin murhu, sannan ta kamo hannun Maimuna ta ɗora mata shi a kan tafin hannunta. Haka ta dinga ƙwalla ihu tana kuka tana faɗin ba za ta sake ba. Amma Auwwa bata ƙyaleta ba sai da ta tabbatar da ta ɗauke mata fatar tsintsiyar hannun sannan ta saketa.

“Gobe ma ki sake bawa wani bashin kayana kin ji?... Kuma ki zo ki zauna ki kaɗa min miya”

Cike da jin raɗaɗin da hannunta yake mata. Maimuna ta gyaɗa kai. Tana jin yanda fatar wurin da Auwwa ta ɗora mata wuta ke tashi. Auwwa ta miƙe daga kan kujerar da take zaune. Sannan ta shige ɗakinta.

Yayin da ita kuma Maimuna ta ja jikinta ta zauna a kan kujerar tana kukan da ya zama abokin rayuwarta tun tasowarta. Saboda a rayuwa ba ta jin tana haura sati ɗaya ba tare da ta yi kuka ba tun da ta zo duniya kuwa.

Iyaye su ne bango kuma abin jinginar 'ya'yansu masu rauni. Ita bata ta so ta ga iyayenta a raye ba. A lokacin haihuwarta mahaifiyarta ta rasu. Kasancewar mahaifinta direban tirela ne ya sa lokacin da aka haifeta yana garin Lagos. Labarin samun ƙaruwa tare da rashin da aka masa lokaci guda ya sa ya ɗauko motarsa domin dawowa gida.

Sai dai kuma cikin nufin Allah sai ya gamu da haɗari a hanyarsa ta Kano zuwa Haɗejia. Hakan ya sa ta taso a wurin matar babanta ta farko wato Hauwa, wanda ake kira da Auwwa. Duk da kakarta ta wurin uba tama da rai, amma haka aka barta a wurin Auwwa tana gasa mata aya a hannu tun tana ƙarama.

Da Allah ya so jarrabarta sai ya sa ta taso da cutar sickler wanda aka haifeta da ita. Ita kuma cutar sickler cuta ce da take buƙatar kulawa da kuma bin doka da ƙa'idojin da cutar bata so. Amma sai ga shi ta taso a hannun matar da bata sonta, ballantana har ta bata wata kulawa da me cuta irin tata ke buƙata.

Hakan ya sa cutar ta kassarata sosai. Dan babu ta yanda za ayi ka ganta ka kasa sanin cewa tana da sickler. A hankali ta share ƙwallar da ta gama ɓata mata fuska. Sannan ta kai hannunta na dama ta ɗauki ledar kukar da ta siyo ɗazu kafin ta tafi tallar kunu.

Ta yi amfani da hannunta na hagu da yake zugo ta kunce laidar. Sannan ta saka ludayi a cikin miyar, ta shiga kaɗa miyar da ta san bata isa cinta ba a yau. Dan tun tana ƙarama ta saba da horon yunwa. Shi ya sa kullum take ƙarewa kamar tsinken kwakwa.

Sai da ta gama haɗa miyar, sannan ta sauƙe tukunyar. Ta faɗawa Auwwa cewar ta gama haɗa miyar. Auwwa tace mata to ta kashe wutar, dan kada ta mata asarar ice. Duk da ita ta so ta zauna ta ɗan ji ɗumin wutar haka ta kashe. Sannan ta koma ɗan ƙaramin ɗakin da yake a matsayin nata.

Ta ɗauko ledar magungunanta da kawunta ƙanin mahaifinta kan sai mata idan dama ta samu. Ta ɗauki palludrine da folic acid. Magunguna biyu da sukafi sauƙin kuɗi na masu sickler. Ita palludrine aikinta shi ne sace sefar cikin me sickler.

Abinda ya kan kawowa masu ciwon sickler ƙaton ciki shi ne kumburar sefa. Kuma ita ce takan jawowa masu sickler...


Read / Download KADDARA CE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album