Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

ANTI ROMANCE Complete Hausa Novel Document by ANTI ROMANCE


ANTI ROMANCE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12146



ANTI ROMANCE

Reading Time: 1 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Oum Aphnan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09065990265

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 67.56 kb

File Type: txt

Views: 2841+

Download: 1497+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [2/10, 11:15 PM] Chuchu👻: ANTI-ROMANCE
Oum Aphnan
Page B

1.Akan Dadirona
2.Auren Sha'awa
3.Abu Uku
4.Bagidajiya
5.Bariki Gadona
6.Bad biya
7.Banana Island
8.Gwauro
9.Gidan Daɗi
10.Hariji
11.Indo Maƙata
12.Jarababben Namiji
13.Jinin Sarauta
14.Laylerh
15.Namiji kishi
16.Qasaitattun Mata
17.Ramuwar gayya
18.Rayuwar Afredarh
19.Sugar Mummies
20.Sinadarin Ma'aurata
21.Yaron Gidana
22.Ƴan Lesbians
Chat or call via
09065990265

Warning!!
Duk wacce ba matar aure bace ba,kar ta kuskura ta karanta mun ,in kin karanta ban yafe ba.
___________
Jabi Motor Pack,Abuja.
A hargitse Dije ta dirko daga commercial bus ɗin da ya ɗauko su daga Yobe state zuwa Abuja. Wani wawan miƙa tayi ,ta yayibo Zanin ta dake ƙoƙarin ɓallewa a tasha ,tayi azaman ɗaureshi gam da igiyar baya. Cike da tarin gajiya ta zura da gudu wajen Boot din motar da ake ta sauke kayan passengers. Da hayaniya na ballagazan mata ta fara yiwa kondosta din Cara a Kai.
“Hankali, inada kayan fashewa a kayana don kwarankwatsa tallatsa suka fashe bani daukan Hasara ,wallahi sai ka biya Ni kudina kobo na bayi ciwon kayi.”
Kallon sama da ƙasa ya bita dashi ,kana ya janyo tsohon gari yai zafinta ya ajiye mata a gefen Ghana must go dinta Wanda tsabagen tsufa zip din ya ɓaci aka sa zare da allura aka ɗinke. Saida ya tara mata kayanta ƙulli uku guri guda sannan ne ya magantu
“Ga kayanki nan sai abi wani sarkin,Laluwa masifa! Daga Yobe zuwa Abuja nasha Panadol guda shidda amma ciwon kai yaƙi sauka mun saboda bala'inki”
“Oho dai bani bari in cutu ,ciwo kuma dama can da guntun ciwonka ba sanadiyyar Dije ba ,ahaaa” ta kare magana tana dukan cinyoyinta da tafikan hannayenta irin na fitinannun matan nan.
Horn taji anyi motar tana neman yin reverse ,aikuwa ta zunduma Ihu “Wayyo Allah zasu gudu mun da ɗiya...”
A tsorace drivern ya take burki “Na shiga uku kai udi,idan bakayi ka sallami yarinyar nan ba zata iya ja a ƙona mu a garin Abuja”
“Nafi karfin ka ganni kace mun yarinya,Shekaru na ashirin da hudu ,haba ai duk wanda yakai shekaru ashirin da ɗoriya ya wuce yaro ,bare kuma gani da zangareriyar budurwar yarinya er shekara bakwai ”
Banza Driver din yayi mata ya yayibo wata tsohuwar malfa dake gefensa ya soma doka ma Naja a gefen ƙafarta ,hum a gigice Naja ta farka daga kan dandankan pillow din dake kan injin motar ,wanda idan injin ya dau zafi ake baiwa fasinjoji su daura akai sannan su zauna.
“Wai waye ...wai waye?"
“Sauka ki bani waje gayyar jarababbu ...fita!”

Ai a karce ta fito daga motar taje ta ƙanƙame kafar Dije “Wayyo mama,wayyo mama” ballara ma drivern harara tayi gamida murguɗa masa baki

“Bar Hegu ,Allah zai gama ku da gamanku” Da sauri ta kinkimi kayan ta ta Aza katon akai ,ta rike dayan a hannu ta daura ma Naja mara nauyin sosai a kanta.

“Muje kinji ƴar Maman ta ,yau a gidan tsohonki zaki kwana,koma ina ya maƙale zai fito ne,ɗan Asara!!!”(Kash kunji wani irin zagi?)
Da Kafa ta soma takawa suna tunkarar cikin gari dukda batasan inda ta nufa ba,sunyi tafiyar kusan awa biyu daga nan naja ta fara kuka
“Mama na ,na gaji”
“Allah sarki ƴar leleh zo in goyeki ” haka ta cire mayafin kanta tayi mata majanyi ta goyeta ram ,suka cigaba da Tafiya.
3.30pm
An fara kiraye kirayen Sallar La'asar ,a nan ne Naja ta soma zillo a bayanta.
Aikuwa Dije ta dauki bahaguwar hannunta ta maka mata a ɗuwawu .
”Zauna !!! Kadani kike son yi ,ko ƙaƙa?,Da wanne zanji ga goyonki ga kaya niƙi niƙi?”
“To Ni sauke Ni ,ki sauke Ni nace kinsa mutane nata kallon mu Ni ba yarinya bace ba da zaki rangaɗa Ni a baya”

“Ohoooo ,Yanzu ne kikasan da hakan?To aikuwa kafafuwar ki zasu gurzu a kwaltan garin nan ,uhum uhum muje zuwa debi kaya budurwa,Yo dole kice mun ke ba yarinya bace ba tunda kin huta a bayana ,kin manta dazu kika gama mun kuka ke kin gaji”

Zumɓuro baki Naja tayi “To mama yanzu ina zamu?”
Fiƙi Fiƙi da ido tayi “Sau nawa zan faɗa maki gidan babanki?”
“To kinsan Gidan ne?"
“Af na manta bari to in ɗauko adreshin muyi tambaya ko ma dace?”Leman wata mata suka nufa da sauri dake gefen Titi tana gasa plantain da miya na saidawa.
“Assalamu Alaikum ,baiwar Allah don Allah tambaya muke”
Fuskarta fururu da tokar gawayin da ta rura ta ɗago ta kalleta
“Wa'alaikumussalam ,Allah yasa na sani”
Miƙa mata takardan dake dauke da adreshin gidan Baban Naja tayi “Don Allah nan gidan nike nema”

Zuru matar tayi tana kallon takardan adreshin,Wannan fa unguwar gawurtattun masu kudi ne ,can ASOKORO me ya haɗa wannan matar mai zubin mahaukata da wannan unguwar?

“Anya kuwa?...” kafin matar tayi magana tayi karaf ta takatseta
“Baba ki taimakeni ,Sunanshi Ɗan lami,Abokansa kuma na kiransa da makil jaksin”
Kunshe dariya matar tayi a ranta tace aikuwa lallai ƴan ƙauyen nan sun sama bahaguwar kwatance kuma zasu kare da kwanan karkashin gada.
“Kina ji? Wannan unguwa ne mai nisa fa ,sai kun hau Taxi zai kaiku”
Amsar Takardan tayi ,gamida yin mata Godiya ta koma can gefen Titin ta fara miƙa hannu tana tsaida ababen Hawan.
Sun sha bakar wahala kafin su samu wani ɗan kabo_kabon da ya kwashe su .Tafiya kaɗan Daga nan barci mai nauyi yayi awon gaba dasu,mai kunshe da tarin gajiya.
Subhanallah,Me golf Saida ya kusa karade unguwarnin Abuja ,amma bai ji pasinjojinsa since ‘Akwai nan ’ ba ,Da dai yaga Tankin mai dinsa na masa warning ya kusa ƙarewa nan yaja tunga ya tsaya
“Hajiya...Malama Ki tashi mana wannan wata irin bagidajiya na dauko a mota na?” malau tayi da ido cikin barci tace
“Har an kawo gidan ɗan lamin?”

Sakin baki yayi cikin mamaki wai gidan ɗan lami ,anya banyi wauta ba kuwa? Tsaki yaja ya kashe motar a kufule ya fito waje ya wangale back seat din ya fizgo Naja zuwa kasa ai a guje Dije ta fito tana gyara daurin zani
“A'ah malam karka ɓalla mun haƙarƙarin yarinya mana ”
“Sallame Ni intafi"

“Ai bamu kawo inda zamuje ba”
“Ke wata kalar halitta ne wai? Ni nasan inda zakije ne?"
“Haba sau dubu nawa zance maka gidan dan lami,ba gayinan a jikin takardan da na baka ba,ka duba mana”
Wuwwurgo idanuwa waje yayi
“Ni kika ba takarda,aah ki binciki takardanki”
Wani ihu da kururuwa ta buga kamar ƴar farauta “Durun uwa salatin Arna,ai wallahi saidai muyi kare jini biri jini dan bamu takardan mu ko malamin su..."

Ai Driver na ganin tana neman Kwanto masa kura ya falfala da gudu wajen motarsa ,kafin ta ƙaraso yaci taya a karce.
Waigawa tayi ta kalli Naja “Ko ke naba ki riƙe?” kamar wawiya Naja ta Girgiza kai .maimakon ta bata amsa sai ma bin bayan motan Naja tayi a karce tana kururuwan “Wayyo Allah jakukunan mu”
Ɗaura Hannu aka Dije tayi “Wayyo Allah mun shiga uku ya gudu mana da kayanmu!”
Can wajen da ake tara bola sukaje suka zauna kowannensu ya rafka uban tagumi
“Mamana Yunwa nike ji”
“Zo gani nima abinci ne cinye Ni ki huta,duk ke kika ja mana wannan bala'in”
Kuka Naja ta fashe dashi mai sauti ,a take hankalin Dije ya dugunzuma
“Ihaƙuri kinji ,Ihaƙuri ina zuwa ,zauna anan kin ji karki je ko ina ,kowa ya kiraki karki je ,bari inje in Nemo maki abinci ,ko Bara ne sai inyi ,ki shiru kinji yarinya ta”

Shiru Naja tayi tana goge hawaye ,itakuma Dije ta shuri takalmarta ta nutsa cikin layukan masu kuɗi ,saida tayi nesa ta kusa ɓace ma ganin Naja,kana ta ɗaga murya

“Naja kar kije ko'ina kinji?”
Yamutsa Fuska naja tayi cike da gundura “Kash! Mama naji ”
***
Ta kwashe kusan mintuna 30 tana tafiya amma ba gida daya da ta gani a buɗe ko'ina tsit babu ko mutum daya da yake tafiya a kafa ,wannan yasa tsoro ya fara kamata karma dai a biyo bayana a jefani a buhu ake a fille mun kai,kafin tayi wani yunkuri taji gari yana walƙiya ana buga tsawa daga nan kuma kan kace mene ,ruwa ya goce. Daura hannu aka Dije tayi cikin matsanancin tashin hankali.

“Wayyo Allah na wannan wani irin iftilai muka riski kanmu a ciki daga wannan sai wannan?...” haka ta runtuma da gudu “Wayyo ƴata wayyo ruwa...” tana gudu ruwan na tsagaitawa

“Hum wannan Habuja! Ga dukkan alamu ma ,ba ko'ina ake masu ruwan ba,Allah mai iko ,mai kudi abokin harka!!”
***
Cikin ɓacin rai ,Sajeedah ta fito daga shopping Mall din hannunta rike da jakkar kayan kwalam din da ta siyo ,sai faman masifa take .
“Tir! Sam wannan basu iya business ba ,In kun sake ganin ƙafata kuyi mun duk abunda kuka so... Nonsense”

Wani Bangaza sukayi wa Juna ita da Dije da ta kwaso a guje ta ƙasan layin tana kururuwan kiran Naja, taje inda ta barta bata ganta ba.

Wani tsawa Sajida ta daka mata “Keeey ! What the hell?” ɗagowa tayi suka kalli juna ,cikin ɓacin rai Sajida taja tsaki “Mts Lunatic,shift for road, Nonsense!” ta buɗe motarta dake gefen hanya ta fada ciki da azama ta wulla tarkacen da ta siyo a back seat ,ta bawa motar wuta

Caɓe Baki...


Read / Download ANTI ROMANCE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album