Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

NAJEEB Complete Hausa Novel Document by NAJEEB


NAJEEB

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 184026



NAJEEB

Reading Time: 15 Hours

Added On: 06, Feb 2025

Author: Maryam Alhassan Dan Iya (Maryam Obam) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08060860886

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 998.33 kb

File Type: txt

Views: 440+

Download: 1533+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE1*








*ASSALAMU'ALAIKUM*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN 'KAI, TSARKI YA TABBATA GA ALLAH UBAN GIJIN TALIKAI WANDA YA SAKE BANI DAMAN SAKE RUBUTA WANNAN LABARIN, YANDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN GAMA LAFIYA🙏*


*WARNING*
~BAN SON KORAFI, WANDA YAGA BAZAI IYABA YA BARI, SHI RAYUWA BABU DOLE, BAZAN D'AUKI ZAGIN DA AKAMUN AKAN NOVEL DIN *BARIKI NA FITO* BA NOVEL D'INA KYAUTA NE, AMMA WLH IDAN AKA ZAGENI ZAI KOMA NA KUD'I, NASAN REAL FAN'S D'INA WILL COME AND PAY, FAKE ONE KUMA NASAN BAZASU ZOBA, SO PLZ A KIYAYE, IN KAGA BAI MAKA BA, JUST LEAVE IT, SANNAN WANNAN LABARIN ZAIZO DA WANI SALO, KAWAI KU BIYONI NA RIGA NA TSARA LABARIN~




*LONDON*
Airport wani jirgi ne mai cin mutane 500, ya sauka airport inda mutane suka fara fitowa, yayin da masu taransu suke tsaye suna jiransu, haka har suka gama fita daka cikin jirgin.

Wani Guy ne fari Mai cikar zati ga kyau ga kwarjini ya fito daka cikin jirgin sanye da farin kaya, wanda zai baka tabbacin cewa shi pilot ne.

Mi'ka yayi tare da kallon gefenshi inda ya fara tafiya lokaci d'aya, wani d'aki ya nufa inda Nan ne aka tanadar ma matuka jirgin in sunzo zasu dinga hutawa, d'akuna ne a jere sunkai guda Goma, shiga yayi yana shiga yayi toilet.

Jim kad'an sai gashi ya fito alaman yayi wanka yana goge kanshi da towel, wayanshi ne ya fara ruri d'auka yayi yaga Monica, d'an tsaki yaja tare da danna wayar yace nazo, just coming, yana fad'in haka ya kashe wayan ba tare da yaji Mai zata fad'a mishi ba.

Ko 30mnt da Gama wayan baiyi ba aka fara mishi nocking, daka shi sai boxer a jikinshi, babu ko riga, haka ya tashi ya bud'e kofar, ganin Monica ce yasa ya kura mata ido ganin irin shigar da tayi wanda gaba d'aya half naked, d'an tsaki yayi domin duk da Monica Tana biya mishi bukata baya son tana irin wannan dressing din, dan yana da kishi, uwa uba bazai so ramin daya shiga ba wani ya shiga, shi kaf y'an matanshi sun San halinshi, shi zai iyayin komai a gabanki amma ke baki isa kiyi ba, domin yasha fad'a shi mata bai d'aukesu bakin komai ba, face Abun hutawa, sannan tunda yana da kud'i zai iya harka dako wace mace, ba tare da damuwa ba, sai yasa har yau ya kasa aure tunda yana samun abunda namijin auren ke samu a cewar shi....

Hugging d'inshi Monica tayi wanda yasa dole ya dawo daka duniyar tunanin daya afka.

D'an tureta yayi tare da fad'in just go away.

Tsayawa tayi sororo Tana kallonshi, cikin harshen turanci Wanda bata iya fad'in sunanshi Sosai ba, tace najub what happen?

Kallonta yayi shima cikin harshen turancin yake mata magana, yace nace ki tafi

Sanin halinshi sarai yasa ta juya, domin tasan ko tafi kud'a naci tunda yace mata ta tafi dagaske yakeyi, komai zatayi bazai saurareta ba, tayi nisa Sosai ta tsaya tana tunani, lokaci d'aya ta kalli dressing d'inta, kaita dafe alaman ta kwafsa.

Shiko rufe kofarshi yayi domin bacci yakeji Sosai, dama yaso tayi massaging d'inshi ne, but ta bata mishi rai, dole ya kwanta bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi.

Waye wannan guy din?

Ku biyoni nan gaba kad'an za kuji ko Waye.






*NIGERIA*
Tafiya take tana sauri daka ganin alama tana cikin farin ciki Sosai, domin kallo d'aya zaka mata ka gane irin farin cikin da take ciki, wani Gida ta shiga, cikin sauri, a tsakar Gida ta iske umminta da kakarta wacce take kira da granny, tace ummi ummi ko sallama batayi ba, tace ummi kalla naci jamb d'ina, na samu 198 wayyo dad'i naci jamb.

Granny tace Dallah Rufamin baki, kin shigo ko sallama babu, kina wani fad'in kinci Janus ne ko me kike fad'a oho.

Dariya ibtisam ta saki tare da fad'in ba Janus bane jamb nace.

Granny ta tabe baki tare da fad'in koma dai miye, ni bason wannan karatun nake ba, shima Umar d'in, na rasa mai yasa yake biye miki, in banda iya shege ace yarinya takai shekara Goma sha bakwai ace tana gida har yanzu ba'a maganan aure sai wani karatu, ta k'arasa maganan tare da tsuke baki.

ita dai ummi bata ce musu komai ba, dan inda sabo ta saba, sannan yanzu inta tofa wani abu, Indai granny ce da ibtisam ba'a shiga tsakaninsu.

Ibtisam tace gaskiya granny ki daina min irin haka, yanzu na samu dakyar abba ya yarda amma kina son rusa mun komai, shi auran ba lokaci bane, rungumo granny d'in tayi sannan taci gaba da fad'in, Kinga ina gama karatu sai aure, nan da shekara hud'u.

Granny tace shekara hud'u? Kuka ta saki tana fad'in Wlh bazan yihu ba, har sai kin k'ara shekara hud'u a gida, yanzu kina 17, sai kin Kai 21 sannan zaki aure, sai kin gama tsofewa a gida, bari Umar d'in yazo, shike d'aure miki gindi

Ibtisam tace wayyo Allah na shiga uku, gaskiya granny kina son samun hawan jini.

Granny Tana d'an share kwallanta Tana fad'in, Aini kin samun, yanzu ace aure sai nan da shekara hud'u, inna mutu banga auranki bafa? Shima gashi wannan shegen miskilin ya'ki aure, shikenan jikokin nawa bazan ga y'ay'an suba, amma Nasan maganin ku daka ke har shi Wlh.

Ibtisam tashi tayi domin jin an kira miskili tasan wa granny ke nufi, domin a duniya babu wanda ta tsana sai shi, dan ita ta tsani mutum Mai girman kai.

Ummi dai bata tanka musu ba, wani abun ma in sukayi dariya suke bata, granny na matukar son ibtisam domin sunanta aka saka mata, Amina, kuma wannan fad'an da granny take tayi koda tayi ma mahaifin ibtisam magana ya hanata, tana ganin ibtisam ta Fara kuka da fushi zata ce a barta, domin bata san ganin jikar tata kuma takwarar tata cikin damuwa ko kad'an.

Ibtisam abinci ta Fara ci tana fad'in, yanzu Idan na zama wata babba a gwamnati inna Gama karatu, ai sai kinfi kowa jin dad'i.

Granny tsuke baki tayi tana fad'in Kedai kika Sani, aure dai shine darajan mace.

Ummi tace ni maza ki gama cin abinci kije min kasuwa.

Granny ta kalli ummi tace yanzu da tsohon ranan nan zaki aikata kasuwa? Ki bari rana ta fad'i.

Ummi tace ai gwara taje ta dawo da wuri, kar muyi daren girki.

Granny tace koma dai miye sai rana ta fad'i, yanzu inta Fita cikin rana ta kwaso ciwon kai ai baki da Asara..

Jin haka yasa ummi ta tsuke bakinta tare dayin shuru, domin tasan halin granny sarai Indai akan ibtisam ne

Bayan ibtisam ta kammala cin abinci, ta tashi ta nufi Ummi tare da fad'in mai zan siyo?

Kafin ummi tayi magana, caraf granny ta amshe da fad'in, oh Ina cewa ki bari rana ya fad'i kina fad'in mai zaki siyo koh? Wlh Idan kika dawo kina kanki na ciwo ko kallonki banyi.

Ibtisam tace dama zance miki kaina na ciwo ne? Kona fad'a Aiba ciremin za kiyi ba.

Granny tace toh shikenan ke kika sani tare da tashi tana fad'in bari in rakaki in wasa kafa.

Da sauri ibtisam tace babu inda zaki bini, wajan da zani cikin minti talatin in dawo, in Naje dake Ai sai nayi awa uku, gwara Kima zauna .

Granny tace ah, lallai naga dai k'afa tace, bata wata ba, kuma Wlh saina biki, kallon ummi tayi da take ta faman musu dariya, tace maza ki fad'a mata abunda zata siyo muje mu dawo.

Nan ummi ta fad'ama ibtisam abubuwan da take bukata.

Babu yanda ibtisam batayi ba, amma granny tace Wlh tare zasu, haka suka fita, ibtisam tana mitar inta fad'in mata a kasuwa bazata iya d'aukanta ba.

Granny tace ke kika sani, in Kinga dama inna fad'i ki wuce ki barni a nan, a haka kike son zuwa karatu, a gaban mu, Ina fad'a kina fad'a, ni Wlh kunya nake ji, sai inga kaman ana nunani ace muna da katuwar budurwa y'ar shekara Goma sha bakwai a matsayinmu na Fulani ace ba muyi mata aure ba.

Ibtisam dariya ta saki tare da fad'in, ai sai kiyi tajin kunyar, ai bance ki fito tare dani ba.

Granny tace ah lallai, ni Kinga yi gaba inyi baya, dan gaskiya ji nake kaman ana nunani

Ibtisam tace Aiko tare zamu jera Wlh,wa yace ki biyoni? Ai ban saki ba.

Granny tamke fuska tayi, ita a dole ranta ya baci, Hhhhh kunji tsohuwa da karfin hali.

Tafiya suke har suka k'arasa kasuwa,
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download NAJEEB

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album