Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ASHE KE CE Complete Hausa Novel Document by ASHE KE CE


ASHE KE CE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 81592



ASHE KE CE

Reading Time: 6 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Deeja One Love ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 455.71 kb

File Type: txt

Views: 1074+

Download: 1253+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: ๏ปฟCompiled By Deeja 0ne Love




๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)




*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*





*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated to
Maryam khamis*
*ALHAMDULILLAHI ALA NI'IMATIHI, ALLAZIY MANNA ALAINA*


*ina taya daukacin musulmai na duniya baki daya murnar yin idil fidr*


Yan kasa ta nigeria dafatan anyi sallah lafiya, allah yasa haka ameen.


*Zazzagawa bayin Allah,na gaishe daku ku din na daban ne a duk inda nake zan amsa da nidin bazazzagiya ce,so proudly zage-zagi*.

Kungiya mai albarka, kece sama dasu, a cikin su kin zama zara,suna sukar ki kina kara haskakawa, makiyan ki fadawan ki,kinfi karfin su sai dai idanu, kin zarce sa'a

*_GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION _*.

Big bro angon katifa da filo babban yaya mai ji damu *UMAR DALHAT*fatan anyi sallah lafiya.


*yan uwana marubuta a kungiyar*:-
Nabeelert
Feenert(matar soja)
Dr fatee
Harira(yar fillo)
Khadeejert haidar(namesy tawa)
Ameeshert
Zinariya
Ummu noor
Ummee yusuf
Maman ashefat
Maman mamy
Princess
Da sauran wa'inda ban ambato ba ga bayan sallah yayi allah ya kawo mu, dafatan za'a faso da karfin allah.



*Masoyana dake fadin kowacce jaha a nigeria ina muku fatan alkairi*.

Ammatul mannan
Shamsiyya m magaji
A'eesha adam(daughter)
Maryam musa1
Hanane mohammad
Ramlat
Maryam musa
Zulaihat sani
Mustapha marakisiyya
Abuakar ahmad
Starboy umar
*Members of*:-
Hafsat hausa novels(Hยฒ)
Dandalin littafan jarumai and hausa novels
Hausa novels ayau
Aunty fatee hausa novels
Da duk wanda ban ambata ba ku sani duka ina yin ku kamar yadda kuke yi na.



*Yan uwana marubuta*
*Deejency* ina miko gaisuwa ta
*Mamuh gee* ina ganin girman ki har gobe
*Bashier sufyein(sarduna)*banga kayan sallah na ba ๐Ÿ˜.

*Bismillahir rahmanir rahim*
001-002

Daidai murtala muhammad way titi daya dauke hanya yayi kudu,motatoci ne gasu nan babu iyaka a tsaye kowa ya San yanayin cinko son kano.



Wata mota ash colour high lander wacce take jerin motocin dake tsaye suna jiran traffic,wata matashiyar mace na hango wacce daka ganta kasan hutu ya ratsa ta.


Agogon kamfanin rolex dake daure a farin hannun ta ta kalla,Dan karamin tsaki taja,ta San yanzu baby na can na jiran ta.



Yana nuna green ta figi motar da gudu,wayar ta samsug galaxy S8 ta fara ringing,ko kallon wayar bata yi ba.




Dai dai bakin get din,dalibai ne da yawa kowa yana harkar gaban shi,masu trekking nayi masu jiran a zo a dauke su suma suna zaune.



Cikin sauri ta bude motar ta fito,subhanallah kyakkyawa ce to d extend,doguwa ce tana da jiki dai dai Wanda baza'a ce mai kiba ba kuma ita ba siririya bace,tana da manyan idanu grey colour,Wanda ta boye su cikin goggle hancin ta dogo,hakoran ta farare tas yayin da pink lips din ta suka adana su ta ciki,dogayen yatsun ta ta dago ta rataya swag din ta,cikin ta sanye da doguwar riga light yellow da brown kanta ta yane da mayafi light yellow.



Cikin tafiyar kasaita da tsananin yanga ta fara takawa,gaban makarantar ta karasa.


Wani farin yaro wanda bazai wuce 7yrs ba ta riko hannun shi,murmushi tayi Wanda gefen kumatun ta ya lotsa a hankali ta bude baki tace"haba baby baka ganni bane come and hug me mana".



Juya baya yayi,cikin sauri ta janyo shi tace"oya come and see something",kwace hannun shi yayi ya cuno baki yace"please leave me alone",manyan idanun ta me kama da na mage ta zaro tace"to baby yau kuma fitina kake ji kenan".



Jakar shi ya amsa a hannun wani yaro kamar shi ya wuce cikin mota,a sanyaye ta mike ta bi bayan shi,ganin ya shiga baya yasa ta daure fuska tace"dawo gaba",banza yayi da ita.


Daka mishi tsawa tayi tace"ba da kai nake ba oya dawo gaba",jikin shi har rawa yake yi wajen dawowa".



Tunda suka fara tafiya babu wanda yace da kowa komi,dai dai haske shoprite tayi parking,kallon shi tayi kafin tace"baby am sorry na taho traffic ya tsayar dani",tabe fuska yayi yace"ai nayi ta jiran ki baki zo ba",hannun shi ta rike tace"yanzu jira ni na shiga wannan shoprite din yanzu zan dawo.



Jinjina kai yayi yace"a dawo lafiya,"murmushi ta Mayar mishi kafin ta bude mota ta fita.



Tana shiga ta mai da goggle din ta fuska ta ja basket,duk inda ta gifta maza bin ta da idanu suke yi,hakan be dame ta ba kamar ta saba da hakan ne.



Siyayyar ta take hankalin ta kwance,har ta fito wani ya biyo ta,cikin sauri yace"assalamu alaikum,madam zan sami lambarki?inji ogana.




Watsa mishi idanun ta tayi,cikin sauri ya sauke kan shi kasa,murmushin gefen baki tayi tace"kaje ka cewa ogan ka ni ba'a mini aike yana son lamba ta yazo da kan shi",tana gama fadin haka ta bude motar ta ta shiga ta figa da gudu ta bar shi tsaye.




Cikin sauri ya koma cikin shoprite din,mutumi ne wanda yake babba Dan dattijo ne ga body guard za gaye da shi,tashi yayi a zafafe bayan wanda ya aika ya dawo mishi da sakon data bashi,cikin huci yace"ita yar gidan uban waye da zata wulakanta ni dan haka skype ka binciko mini waye uban ta a garin nan.


Wanda aka Kira da Skype ya amsa da"an gama yallabai",wuce wa yayi cikin sauri,masu daukar jaka nayi masu daukar phones suka kwashe sannan suka bishi.



Tuki take cikin natsuwa har ta iso zoo road,a dai dai bakin wani katon gida ta tsaya horn tayi,mai gadi cikin girmama wa ya bude Mata get din,parking lot tayi parking, a tare suka bude kofar suka fito.



Jakar hannun shi ta amsa sannan ta rike mishi hannu suka shiga ciki.



Wow gida ne babba Wanda ya amsa sunan gida,wani hadadden falo ne wanda aka kawata shi da kayan more rayuwa.



Amina!Ameena!!Ameena!!!ta kwala mata Kira,wata yar shekara 17 ta fito cikin sauri,kallon ta tayi tace"baby ya dawo a kai mishi abinci",jiki na rawa ta amsa da to.


Ameena ta kuma cewa"aunty ke ba zaki ci abincin bane?",kamar baza ta amsa ba tace"eh na koshi",daga haka ta juya ta tafi.



Wani kofa ta bude,wani falon ne sai dai wannan be kai wancan girma ba,komai milk da brown ne,a hankali ta isa gaban center table din wayar ta da key ta ajiye,wata kofar ta sake budewa,hadadden bedroom ne white and pink komai na ciki,rigar jikin ta ta cire ta shige bathroom.



Wanka tayi sannan ta fito,simple make up tayi,wata doguwar riga ta saka armless peach colour,farin mayafi ta yane kan ta dashi jikin ta sai tashin kamshin laylatus-Sahara yake yi.




Cikin takun ta ta nufo Falon ta,kan center table taje ta dau wayar ta,main palour ta nufa tana tafe tana yin waya.



Cikin muryar ta mai kama da busar sarewa tayi sallama.



A ta can bangaren aka amsa,tace"yadai beelert mai ya faru naga kiran ki lokacin ina driving ne",



Beelert tace"cat eyes feenert tace"anjima mu hadu a 021 saffah 20:009,"murmushi tayi tace"ok sai na zo din akwai new story kenan",eh i think so gaskiya"beelert ta bata amsa",cikin sanyin murya tace"okay.




Kashe wayar tayi kafin ta zauna,Ameena ta kwalawa Kira,cikin sauri ta karaso,tace"ina baby yake?"cikin sauri ta bata amsa da "da yana dakin shi",mikewa tayi tace"jeki cigaba da abinda kike yi.




Tura kofar tayi ta shiga,a zaune ta same shi yana game a tablet din shi,gefen shi ta zauna sannan tace"baby kaci abinci?,daga Mata kai kawai yayi ya cigaba da abinda yake yi.



Shiru dakin yayi kafin tace"baby wai me yake faruwa ne da yanzu kwata kwata baka da farin cikin da?,a Dan karkace ya kalle ta kan ya juyar da kai cikin sanyin murya yace"baby ai yanzu baki damu Dani ba kamar da",da mamaki tace"bangane ba me nake maka Wanda yanzu bana maka?".




Hawaye ya goge yace"da baki fita ki barni yanzu kuwa kina fita,a da kikan tsaya kiji meye damuwa ta yanzu kuma bakiyi yaya na kwana me naci duka basu da meki ba kamar dai kin daina sona yanzu",cikin sauri ta riko hannun shi tace"har yanzu ina son ka mana baby wa nake dashi bayan kai",girgiza kai yayi yace"baby kina da mum feenert da mum beelert da sauran mazan da kike yawo dasu,"tsawa ta daka mishi tace"baka da hankali ne ni kake zargi baby?",mikewa yayi yace"kin gani da baki yi mini tsawa but yanzu kina yi mini kawai kije nidai abu daya na San zan gaya miki shine kiji tsoron Allah",yana gama fadin haka ya mike ya shiga bathroom.




Ai galala ta tsaya tana juya maganar shi wato taji taji tsoron allah ma,yaro sai kace wani babba,girgiza kai kawai tayi ta fita.


Falon ta ta koma gaban wani karamin frame ta karasa,hoton kyawawan yan Mata ne guda biyu da check a jikin su alamun a makarantar boarding aka dauke shi,fuskar daya duk gari ta Dan bata rai Dan rigar ta ma ajike take,ita kuma wacce tafi waccan kyau ta nuna ta tana dariya.




Shafa wacce take da gari a fuska tayi tana murmushi,hawaye ya ziraro Mata.


_Ga yarona nan
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ASHE KE CE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album