Join Our WhatsApp Group

ZAYYANA Complete Hausa Novel Document by ZAYYANA


ZAYYANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29884



ZAYYANA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 167.27 kb

File Type: txt

Views: 576+

Download: 233+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ZAYYANA 1 and 2
Littafin Nazir Adam salih
(c) Nazir Adam Salih
Created and design by :- Shuraih Usman
.
Daga Nazir Adam Salih
1- Kibiyar Ajali
2- Me Yafi Kudi ?
3- Ta Leko Ta Koma
4- Birnin Sarauniya
5- Naira Da Kwabo
6- Aci Bulus
7- Mutuwar Kasko
8- Alakakai
9- Wa Na Kama ?
10- Hindu
11- Ruhina
12- Dare Da Rana
13- Karya Linzamin Shaidan
14- Cuta Ta Dau Cuta
15- Iska Mai Kada Ruwa
16- Bindigar Kwali
17- Damisar Takarda
18- Aziza
19- Tsohon Alkawari
20- Kai Da Jini
21- Aljani Ya Taka Wuta
22- Sai Mutuwa
23- Kudi Da Maciji
24- Kisan Boko
25- Kura Da Kan Rago
26- Murmushin Alkawari
27- Zayyana.
.
DON Halima Umar Tudun Maliki.
.
ZAYYANA
Copyright (c) Nazir Adam Salih 2008
.
Hakkin Mallaka (H) Nazir Adam Salih 2008
.
TARIHIN DAB'INSA
An Fara Bugashi A Kamfanin KAMNAS PUBLISHERS
Dakata Kano A Shekarar 2008.
.
GARGADI
Ba'a Yarda Wata Qungiya Ba Ko Wani Mutum Ya Juyi
Wani Bangare Na Wannan Littafi Ba Ta Hanyar Wasan
Kwaikwayon Majigi Ko Kuma Wani Abu Daban Saida
Izinin Marubucin.
.
ADIRESHI
Abubakar Sadik Islamiyya Dakata Kano
Akwatin Waya 4792.
.
ZAYYANA
Nazir Adam Salih (NAS)
.
FADILA
Wata dankareriyar mota jeep baka kirin kirar
kamfanin marsandi tayi fakin akusa da wani
munafikin lungu dake wata unguwa acikin birnin
Kano.
Ga wanda ke tsaye awaje bazai iya ganin wanda ke
cikin motar ba domin gilasan motar masu duhu ne
sosai anyi musu dare jim kadan da tsayawar wannan
mota sai kofar gidan gaba ta motar ta bude ahankali
sannan aka zuro wata santaleliyar kafa kyakkyawa
fara sol da ita kamar kafar balarabiya daga cikin
motar sannu ahankali takalmi mai tsini wanda ke
dauke da santaleliyar kafar ya sauka acikin cabin
ruwan saman da ake ta makawa kamar da bakin
kwarya tun da garin Allah ya waye.
Duk da yake ana kiran Sallahr Azahar ruwan yadan
tsagaita amma har izuwa yanzu karfe uku na rana
yayyafar kananan kwayoyin ruwan basu daina sauka
akan doron kasa ba.
Kofar motar ta dada budewa sosai sannan sai wata
kyakkyawar halitta doguwa tafito daga cikin motar
Zuwat.
Tana rausaya kamar macijiyar data fasa kai
kyakkyawa ce ta gaske ga duk wanda yasan me ake
cewa KYAU haka nan kamar yadda kafafunta suke
haka nan ma sauran jikinta yake fari sol kamar
balarabiya me yiwuwa kuma ga wanda baiyi yawon
duniya ba ya iya kuskurenta amatsayin shuwa arab,
to amma agaskiyar al'amari iyayenta fulani ne gaba
da baya.
Kyakkyawar halittar tayi tsaye bakin kofar motar tana
duban ciki lokaci guda kuma ta gyara dan yalolon
gyalen dake dafe akanta kana ta dada jan
damammiyar rigar silikin dake jikinta kasa sannan
daga karshe saita zato wata farar lema daga cikin
motar ta budeta akanta domin ta kare yayyafar ruwan
dake zuba haryanzu akan doron kasa kyakkyawar ta
dada gyarawa lemar tsayuwa a saman kanta sannan
saita dubi wasu kyawawan yan mata su hudu dake
cikin motar suma farare sol dasu kamar ya'yan
larabawa fuskarta a murtuke amma kyawunta ya
karu.
Ku zauna anan kuyi jirana kada ku sake naga wata
shegiya acikinku ta biyoni saura kuma ku koma gida
ku fadawa mama munzo nan sainaci uban yarinya.
Tana gama fadin haka saita rufe kofar motar da karfi
a fusace sannan ta nufi munafikin lungun cikin sauri.
.
Sunan wannan kyakkyawa FADILA
kuma adaidai wannan lokaci data nufi wannan
munafikin lungu cikin sauri sa'o'i ashirin da uku kacal
suka rage adaura mata a aure da sahibinta FAISAL.
Mutumin da take kauna fiyeda kowa aduk fadin
duniya zakuma ta iya tsallake maganar kowa domin
ta farantawa faisal hakanan Fadila na iya bata ran ko
wane in dai zai taba mata Faisal watanni tara da suka
gabata watarana da yamma suna hira akatuwar
farfajiyar gidansu Fadila acikin motar faisal sai faisal
din ya kalli hannun fadila yaga duk an zane shi da
kunshin zamani wasu irin surori ne na furanni da
siraran ciyayi kamar na bakin kogi masu kyawun
gaske. bakin zanen yayi matukar fitowa akan fararen
hannun Fadil.
Kai amma yau kin kara kyau Fadilata
Faisal yace yana kallon bakin zanen dake hannunta
Fadila ta lumshe idanuwa cikin farin ciki wani irin
sassanyan dadi ya mamayi zuciyarta jin cewa ta
farantwa Faisal
Allah ko? To nagode tace tana wani farfarar da idanu
Faisal ya mika hannunsa zai taba hannunta cikin sauri
ta dauke hannunta cikin dariya tace Menene?
Da Allah kawo hannunki na gani a ina akayi miki
wannan zanen kunshin mai kyau haka?
Cikin murmushi fadila ta mika masa hannunta ya rike
yana kallon zanen kunshin
Wata mata ce take.... Yi mana Fadila tayi masa karya
domin abinda faisal bai sani ba shine wani katon dan
daudu ne wai shi AMARA yakeyi musu wannan zanen
kunshin da ace Faisal yasan gaskiyar al'amarin da ace
yasan cewa zanen ya kamane tun daga kan kafafunta
da hannuunta har zuwa kan cinyoyinta sannan daga
kan cibiyarta zuwa kirjinta da wuyanta
da babu abinda zai hana zuciyarsa bugawa domin
yana tsananin kishin fadila wannan ce ma tasa tun da
yake zuwa hira gurinta bai taba zuwa da aboki ba sai
sau daya shima daga nan bai kara ba domin ya
fahimci tun da sukazo idanun abokin akan Fadila
yake.
To My Faisal tace gamida hadawa da turanci
dan haka ayanzu da fadila ta nufi munafikin lungun
gidan dan daudun ta nufa domin ya zane ta da
furanni tun daga sama har kasa domin burinta shine
ta ruda faisal adaren amarcinsu na farko ashe kuwa
bata sani ba wannan kunshin ba karamin Rudashin
zaiyi ba.
.
Sannu ahankali fadila ta kawo izuwa kofar wani gida
wanda shi kadai ne acikin lungun tayi mamaki sa'ar
dataji kamar gidan shiru bata jiyo hayaniyar mata ba.
Tayi sa'a yau ba layi tace cikin zuciyarta abinda
daman take tsoro kenan domin Allah Allah take yi
tazo agama mata ta koma gida kada ta dade
mahaifiyarta ta tambayeta inda taje.
Tuni mahaifiyarta tayi tofin Allah tsine da wannan
kunshin
kada in sake ganin kinyi wannan sakarcin shashashar
banza shashashar wofi in banda wauta irin ta ya'yan
zamani yaushe zanje gaban wani kato in bude masa
cinyoyina da kirjina wai yayi min zanen kunshi kada ki
karayi babu kyau ko macece yar uwarki bai kamata
taga tsaraicinki ba ballantana wani katon banza
munafikin dan daudu idan kika sake yin wannan
kunshin Fadila to wallahi bada yawuna ba
Fadila ta tura baki gaba kamar tsuntsuwa tana
gunguni tundaga.
wannan rana bata karayin wannan
kunshi ba sai awannan rana tafito yiwa Faisal dinta
kunshin da yake so ta riga ta kuduri aniyar ko
mahaifiyarta bata amince ba sai tayi wannan kunshin
tunda faisal dinta yana so.
.
Fadila ta shiga farfajiyar gidan sannan kai tsaye ta
wuce wani falo inda anan ne tasan mata ke taruwa su
jira kafin azo kansu duk wacce akazo kanta saita bi
dan daudun abaya su shiga wani dan daki inda anan
ne zata tube ya zaneta tun daga sama har kasa.
Salamu alaikum kwan kwan fadila ta kuma cewa shiru
ba'a amsa ba me yiwuwa ya fita sayen sinadaran
kunshin ne Fadila tace aranta domin tariga ta sani
wata sa'ar ana cikin kunshin sinadarin ke karewa sai
AMARA yafita ya sayo musamman lokaci irin na bikin
sallah, dan haka sai fadila ta nemo kujera daya ta
zauna sannan ta dauko daya daga cikin mujallun
kasashen turai dake warwatse akan wani tebur dake
tsakiyar dakin ta fara karantawa domin ta raka lokaci
kafin Amara ya dawo
.
Adaidai wannan lokacin ne wata sassanyar iska mai
sanyin gaske ta fara ratsowa cikin dakin nan da nan
fadila taji jikinta ya dauki rawa domin sanyin iskar
cikin bargonta yake shiga ko kusa ko alama iskar
batayi kama da iskar damuna ba jikinta na rawa
fadila ta dago kai daga kan Mujallar da take
karantawa ta dubi kofar falon inda take tsammanin
tanan iskar ke fitowa ga mamakinta sai taga duk da
wannan sassanyar iskar mai karfi dake shigowa
labulayen taga da kofar falon basa motsi kai hatta
takardar mujallar dake hannunta bata motsi gashi
kuma haryanzu iskar na kadawa.
.
MAMA
Karfe uku da minti goma daidai wata tsohuwar tasi ta
nufi munafikin lungun tana tafiya tana kara rukukuku
kamar tsohon keken shanu tana tafiya tana bulbular
da farin hayaki kamar jirgin kasa.
Kai wannan wace irin mota ce anya kuwa ba kamawa
tayi da wuta ba? Wata doguwar mata dake zaune
abayan motar ce take fadawa direban
ba'a bakinki nafara jin hakan ba 'Yan mata sau uku
kenan yau ana cewa in tsaya in kashe wuta basu san
ba motarce ahaka so nake idan kin sauka na wuce
gurin gyara direban yace dan tsatstsama ne
busashshe mai tarin gashin baki kamar ciyawar bakin
kogi sanye da doguwar riga da hula amma samanta
ya cizge kamar bera ya gwagwiya saboda yawan
shekarunta a duniya.
Ni wannan mota da nasan haka take da wallahi ban
shiga ba ga tsada ga babu sauri ga kuma shegen
hayaki.
Direban ya shafi gashin bakinsa sannan ya juyo da
kansa ya dubeta.
In banda tsohuwar motace yaya zan dauko ki shata
tun daga Na'ibawa har nan a naira tamanin kema
dama ai san banza ne yasa kika tsayar dani.
Kaga juya can ka isheni da surutu lura da gabanka
Wallahi ga kwanan nan agabanka Matar tace dashi
cikin Karaji.
Direban ya juya da sauri adaidai lokacin ne to ya
hangi katuwar Jeep din baka agabansa.
Saukeni anan matar tace.
Dan tsatstsaman direban ya daddage ya taka birki
yana ciccije baki dakyar gamida kama sandar giya ya
samu ya tsayar da motar adab da gindin Jeep din.
Yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi matar da murmushi
yace.
Dana bugawa danyen kwannan dake gabana ai da
zurawa zanyi aguje na barki acikin tsohuwar motar
nan.
Matar ta harare shi sannan ta zaro naira dari ta
dungura masa a kasan hanci
gashi nan ka rike sauran chanjin ashirin din ka cika
ka sayi sabon inji.
Kafin direban ya sami damar mayar da martani tuni
har matar ta bude kofar ta fice abinta.
Shegiya Kilaki direban yace yana kallon bayanta.
Cikin sauri doguwar matar ta nufi cikin munafukin
lungu tana tafiya tana girgiza bangarorin jikinta
kamar wata bishiyar kanya lokacin iskar hunturun
sanyi doguwar matar farace amma farin dan kanti ne
baza a iya kiranta kyakkyawa ba amma tana da
daukar hankali Allah ya hore mata kyan kirar jiki
wanda ke tattare da wani mayen karfe mai karfin
gaske wanda ke fizgo hankalin mazaje izuwa gareta
musamman wadanda shaidan yafi karfin zuciyarsu.
Wannan doguwar mata mai kyakkyawar jiki
ma'abocin sinadaran mayen karfe sunanta MAMA
akalla dai hakanan yan uwanta karuwai yan duniya
suke kiranta a bariki to amma wani tsohon dan bariki
wanda ya dade da saninta tun tana karama a
mahaifarta GOMBE ya taba cewa da Babbar kawarta
BEBI.
Wai kinsan sunan kawarki kuwa na gaskiya
Bebi ta girgiza kai menene sunanta na gaskiyar
ZULAIHAT
Uhm bebi tace dashi a yatsine
wannan kai ta shafa tsohon munafiki meye na fada
min sunanta na gaskiya kuda bakwa rabuwa da
munafurci.
.
Ayanzu haka da mama tashigo layin tana rausaya sai
ka kira sunanta Zulaiha akalla sau hudu kafin ta iya
tunawa ma da sunan ne domin rabon da akirata da
wannan suna tun tana garinsu Gombe yau kusan
shekaru shida kenan da suka gabata.
Zulaihat ko kuma Mama yar gidan wani tsohon
direban jirgin kasa ce wanda Allah yayiwa rasuwa tun
tana karama Mahaifiyarta talatu tsohuwar yar duniya
ce tana yawonta suka hadu da mahaifin mama a
tashar jirgin kasa dake garin GURU sa'ar daya tsaya
sauke fasinjojin jirgin kasan basufi wata biyu da fara
harkar bariki ba suka auri juna sa'ar da mahaifin
mama yakai mahaifiyarta Gombe jama'a.......
jama'a sunyi mamaki da akace dasu karuwa ce ya
auro akayita surutu wasu sukace wai asiri tayi masa
ya aureta wasu ko sukace a'a wai cikin shege sukayi
dan haka suka auri juna abinda jama'a basu sani ba
shine dalilin auren mahaifan ma dalilai ne masu
sauki na farko dai mahaifin mama ya auri
mahaifiyarta ne saboda kyawun jikinta kuma bazai iya
ganin kowane namiji yana mu'amala da ita ba itako
mahaifiyar mama ta auri mahaifinta ne saboda ta
fahimci akaluum kwanan duniya baya rasa kudin
kashewa ya sai musu tsire suci kasu su sha nono ya
kuma dinka mata duk irin suturar da take so.
.
Mutuwar mahaifin mama keda wuya sai ungulu ta
koma gidanta na tsamiya to saidai kuma awannan
lokacin tsohuwar ungulun tsufa ya risketa batareda ta
sani ba dan haka sa'ar da mahaifiyar mama ta dawo
barikin ma babu riba domin babu mai kulata sai
dattijan banza wadanda dayawansu matsiyata ne
wadanda suka dorawa kansu masifa
sa'ar da mama takai shekara goma sha tara sai tabi
sahun mahaifiyarta domin abinda ta gani kenan
tanayi nan da nan sai bakar kasuwa ta bude mata
ba'afi shekara guda ba ta baro Gombe zuwa kano to
saidai kuma tazo arashin sa'a domin tazo ne alokacin
da aka kaddamar da shari'ar musulunci a kano
karuwanci ya zama babu riba in ma za'a yi saidai a
boye sannu ahankali shekaru hudu suka shude mama
tana kano to saidai abubuwa sunja da baya matuka
domin mama ta lura duk da kyawun jiki irin nata ta
sami wadanda suka damata suka shanye hakanan
saita fahimci kamar karuwan ma anfi son farare dan
haka sai mama ta fara bilicin nan da nan ta kwaile ta
koma fara jajuz duk da wannan ungulu da kan zabo
da mama tayi hakanta bai cimma ruwa ba domin
haryanzu a cikin kawayenta ita kadaice bata da motar
hawa ana cikin wannan haline to kwatsam rannan da
rana sai babbar kawarta dake abuja wai ita Bebi ta
bugo mata waya.
Hello kawata kina ina.
Maza ki hada naki ya naki ki taho nan abuja muci
karenmu babu babbaka babu wanda zai
tsangwamemu da zancen shari'a kinga daga zuwana
har wani dan majalisa yabani mota
Ke ki bari don Allah. Mama tace cikin kaduwa.
Wallahi kuwa kawata ai kema kina kan hanya kuma
mota kamar kin samu domin jiya muna tare dasu
wani honorabil abokinsa yaganki a hotunan da muka
dauka aruwan tiga yace lallai saina kawo masa ke.....
Saboda haka duk abinda kikeyi saiki bari ki taho abuja
amma fa sai kin gyara jikinki da kyau kizo musu a
hade.
Wannan kalma ta karshe ita tasa mata shigowa
munafukin lungun cikin sauri domin tazo Amara ya
zaneta tun daga sama har kasa irin yadda zata ruda
honorabil din da kawarta Bebi zata hadata dashi.
Gobe har wahaka na rabu da wannan jaraba anbi an
hanamu rawar gaban hantsi da wata shari'a sai inga
uban da zai bimu abuja ya hanamu abinda muke so
Mama tace aranta sa'ar data karaso farfajiyar gidan
Amara dan daudu mai zanen kunshin zamani.
.
Sannunki mama tace da fadila ayatsine sa'ar data
shigo falon mama taja kujera ta zauna sannan ta kalli
kyakkyawar surar fadila nan da nan saita sami kanta
tana mai fatan inama itace Fadila Da ko babu kunshi
sai na sace zuciyar honorabil. Mama tace cikin
zuciyarta.
Yana ciki ne? Mama ta tambayi Fadila
nima ban same shi ba inajin dai kasuwa yatafi sayen
kayan hadi fadila tace bakinta na rawar sanyi.
Baiwar Allah lafiya naga kina rawar sanyi? Naga
kamar ai zafi akeyi ko?
Mama ta girgiza kai aini da'ace da fanka ma kunnawa
zanyi mama na rufe bakinta sai taji sanyin ya soki
cikin kashinta.
Kai Wallahi nima nafara ji wannan wanwe irin sanyi
ne?
.
FARIDA.
Da wani dattijo da wata budurwa yar makaranta suka
shigo munafukin lungun cikin wata mota honda kirar
Ali dari tara da casa'in da takwas dattijon shike jan
motar budurwar na zaune abaya da yan littattafanta
da takardu agefenta akan kujerar motar jakarta ajje
akan cinyarta. Dattijon direban yayi fakin akusa da
katuwar jeep din sannan ya dubi budurwar da tun
tana yar kankanuwa yake tuka takata a mota direban
gidansune.
Ko ba nan bane lungun da kike fada?
Nan ne budurwar tace da dattijon
to saidai fa na jiraki anan kinga mota bazata iya shiga
lungun ba kuma dan Allah kiyi sauri kinga ina mayar
dake zan koma dauko yan uwanki.
Budurwar ta bude kofar motar lokaci guda kuma tana
kokarin bude jakarta.
Dan Allah idan munje gida kada kace munzo nan kaji
BABA ALI
Dattijon ya dubeta cikin mamaki
me zakiyi anan din?
Kunshi ne za'ayi min ka gane to amma hajiya bata so
na tafi ko ina indai yayi nesa da gida to ni kuma
agaskiya irin wannan kunshin sai anan kawai za'a
iyamin irin shi.
Zaki dade kenan Baba ali yace yana dubanta cikin
damuwa
Gaskiya zan dade tun da idan da akwai layi ma dole
saina jira.
A'a kinsan bazata yiyu ba idan muka koma gida
amakare banje dauko yan uwanki ba me kike
tsammanin zan fadawa Hajiya?
Budurwar ta dubeshi cikin damuwa
haba baba ali kaifa nawa ne kasan ai bama haka
dakai nasan bazaka rasa abinda zaka fadawa hajiya
ba ta danyi shiru sannan saitaci gaba dacewa cikin
sauri
kokuma me zai hana kaje yanzu ka dauko su salima
din ka mayar dasu gida nasan kafin kadawo ko...


Read / Download ZAYYANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album