Join Our WhatsApp Group

MUTUWAR KASKO Complete Hausa Novel Document by MUTUWAR KASKO


MUTUWAR KASKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24201



MUTUWAR KASKO

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 133.42 kb

File Type: txt

Views: 564+

Download: 241+

Last download: 1 day ago

Description/Story: MUTUWAR KASKO-01

KASHI NA FARKO

DAYA
Na lumshe idanuna ina sauraran daddadar iska mai sanyin sanyaya zuciya dake karkada tsummar rigata mai kamar mayafin koko.
Babu alamar hadari a sararin samaniya amma duk da hakan babu zafi sakamakon sassanyar iskar marecen dake busawa wani abin ban sha'awa da karin annashuwa dake tattare da iskar shine kamshi ruwan dake tafe dashi. Alamu ne dake nuni da samuwar ruwan sama nan da dan lokaci bada dadewa ba.

Kusan rabin sa'a guda kenan ina zaune akan bencin majalisar ko dayake awani lokaci daya wuce ba majalisa bace agurin sai da na fara zaman banza sannan na kafata a tsakanin rabin sa'ar data shude amma babu ko mahaluki daya daya leko majalisar hakan ya bani mamaki ganin cewa tuni lokacin taruwar majalisar ya shude amma babu ko mutum daya da zai canza min lissafi daga daya zuwa biyu.
Na mike tsaye ahankali sannan na karkade bayan tsummar rigata farar riga ce shat da wando baki duk dayake kuwa rigar ta kode ta kode har ta sauya kala kala daga fara zuwa ruwan zuma zuma ne yiwuwa kuma ka iya kiranta launin tsanwa tsanwa. Shekarunta bazan iya tunawa ba domin kuwa Allah ne kadai kawai yasan yawan kananan yaran data girma aduniya. Abinda kawai dana sani shine da wahala yari dan shekara takwas zuwa tara yayi ikirarin girmar rigar.
Hakan shiyasa da dama yan majalisata ta masu zaman banza sukan tsokane ni da rigar.
Wani lokaci har kama rigar suke da hannunsu suce da ita wai yayata.
Bakin wandon dake jikina shine mai yar dama dama duk dayake kuwa yafara tsagewa ta gwiwa amma dai bai dade ba shekarunsa kusan biyar ina tare dashi kamar rai saboda TALAUCI.

Zaiyi wuya ka dube ni ayanzu in dai har baka dade da sani na ba ne ka iya gane ni sam Sam ko kusa ko alama banyi kama da FARISUN daka sani ada can ba.
KO ada can Daman ni ban kasance daga cikin wadatattu ba to amma abin da sauki ba kamar yanzu ba bayan zaman gidan yari danayi na yan shekaru na dauka ina fitowa na rabu da wahala kenan to ashe bahaka abin yake ba ba'a yi ma komai ba rayuwar danayi ada tafi rayuwar danayi ada can tafi tafi wacce nake yi bayan fitowata daga gidan maza nesa ba kusa ba domin ko banza ada can zan iya neman aiki a dauke ni.
Zaman danayi agidan maza saiya zama tamkar wani tabo ne Manne agoshina duk inda na shiga sai yan tsurkun unguwa suyi ta nuna ni ko wanne na fadar albarkacin bakinsa wasu da dama daga cikin masu zundena sun san bada hakkina aka kaini gidan maza ba.
to amma abin mamaki sai gashi da wanda suka san hakan da wadanda basu sani ba duk sun hadu suna fadar abin daya zo daidai da ra'ayinsu akaina to wanda bai sani ma ba fada masa akeyi ballantana kuma wanda ya sani na zama abin kyama acikin al'umma duk inda na shiga sai kaga ana jajjanye jiki.
Banga laifin su ba dole ne a kyamaci wanda duk ya aikata laifin kisan kai mutum daya ne ya bani mamaki shi ne Abokina SAGIR na tuna yadda muke dashi amma tun ranar da masifar ta fado min ban kara ganinsa ba.
Lokacin dana dawo daga fursuna ne na sami labarin wai ya sami aiki awani gidan gona ayadda kuma Naji mukamin sa babba ne. Tun da na dawo bai neme ni ba kuma Nima ban neme shi ba.
Meyiwuwa kafara tunanin duk abubuwan danake baka labari sun faru ne tsakanin sati wata ko kuma rabin shekara data fitowa ta daga fursuna idan kuma har kafara tunanin hakan to yana da kyau ka sake tunani abun da nake baka labari ya faru ne tsakanin watanni goma sha biyar shekara ta daya kenan da wata biyu da fitowa daga fursuna.
Abubuwa da dama sun faru a kaina aduk abubuwan kuma da suka faru babu wani abin farin ciki aciki saidai ko da sauki.
Me yiwuwa ka tausaya min in kaji abubuwan da suka faru na bakin ciki akaina tun daga ranar dana fito har zuwa yanzu me yiwuwa kuma ka zarge ni kasancewata ma'abocin TAURIN kai da kwadayin abin duniya...........

Abu daya da yafi bani mamaki acikin watanni goma sha biyar din nan da suka shude shine SALMA........MUTUWAR KASKO-02

Abu daya da yafi bani mamaki acikin watanni goma sha biyar din da suka shude shine SALMA.

Hakika nayi matukar mamaki domin ganin tun ranar da ta tuka motar ta ahankali tabar layin gidan mu har yau ban sake ganinta ba tun abun yana damuna har yazo ya yafara sosa zuciyata ada can na dauka Salma zata dawo ta lallabe ni amma abin mamaki sai gashi har yau din nan danake baka labari ban sake ganin ta ba.
Watanni kusan uku suka shude banga Salma ba kullum tunanin ta ne araina akullum saina tuna ranar da muka fara haduwa da ita. Inda take dafa hannayena take cewa.
BA BAZA KA FADA MIN SUNAN NAKA BA.?

Tun ina daurewa har na kasa jurewa saina fara neman ta awayance sakamakon neman dana samu daga karshe baiyi min dadi ba. Awajen maigadin gidanta na sami labarin cewa Salma ta dade da tafiya Kasar Turai acewarsa kusan watanni uku kenan da suka wuce. Wannan shi yazo daidai da ranar da mahaifina ya riga mu gidan gaskiya. Abubuwa suka taru suka cushe min ga rashin mahaifina sannan kuma ga rashin aikin da zai tallafamin wajen daukar nauyin mahaifiyata da kannena.
Tun ranar da mahaifina ya rasu ban kara tunaninta ba sai ranar da akayi sadakar bakwai sannan ne katsam ba zato ba tsammani sai tunanin ta yayi dirar ungulu cikin zuciyata. Aranar ban tashi da ko sisin kwabo ba gashi matsaloli barkatai basu kirguwa kamar tarin yashi banajin kuma zan iya magance ko da daya daga cikin su.

Alokacin ne to tunanin Salma yafado min na tuna irin kaunar dake tsakaninmu da ita na san da tana nan dole ne ta tallafa min na zargi kaina na kuma tausaya wa kaina kodayake sharewa Salma shi yafi sauki domin kwadayin abinda ke hannunta na iya jefa ni cikin masifar da ta fi wacce na sha baya don haka yanzu na jefar da salma kwallon mangwaro na huta da kuda.
Saidai kuma acan cikin wani lungu na zuciyata ana ta cewa dani shashasha ka cuci kanka da ka wulakanta ta kaki karbar soyayyar ta shin ko kasan kin karbar soyayyar tata ne yasa tabar garin shin kuma ko kasan gara kudan da kake gudu da talauci.

Ban yarda tunanin yayi tasiri azuciyata ba akullum abinda nake kokarin koyawa zuciyata shine Tawakkali da juriya akan duk abinda Allah ya kaddara akaina abin kawai dana kasa fahimta shine tunanin da nake yawan yi na salma na nufin ina kaunar ta ne ko kuwa ina kaunar abin hannunta ne?

Washagarin rana ta takwas da rasuwar mahaifina mahaifiyata ta turo kofar gida akayi kirana lokacin dana shiga cikin gida saina same ta ita da kannena yan kullikan kaya biyu A gabansu.
Lafiya? Na tambayeta
Lafiya Ƙalau Farisu sannan saita fara sharar hawaye. Hankalina yayi matukar tashi saboda ganin kukan da takeyi.
Farisu inason ka saurare ni da kyau domin ni yau in Allah ya so ban sake kwana ko ina sai a kauyenmu na dube ta sororo sannan nace da ita.
Haba ummi idan kin tafi nikuma na zauna da wa? Ki tuna fa bani da wanda yafi ku aduk fadin duniyar nan yanzu idan kuka tafi.... Yaya zanyi babu ke babu kuma ba....ba nafara kuka.
Kada ka damu Farisu Allah yana tare da kai kaidai kawai kayi ahankali kada ka sake kabi son zuciyarka sannan kuma ka guji kwadayin abinda ke hannun mutane saiku zauna dasu lafiya. Tayi shiru tana dubana sannan tace. Allah ya taimake ka yayi maka arziki Farisu saimu dawo mu zauna kamar da amma ayanzu kam kaji da kanka Allah yayi maka Jagora.

Na kasance cikin kadaici har zuwa yanzu akullum burina shine na sami abin yi domin na je kauyen mu na dawo da mahaifiyata amma abin ya faskara aduk tsawon shekara danayi na zaman banza agidan makwabcin mu ALHAJI ILYA nake karbar abincin dare da rana har da safiya nayi kokarin samun aiki koda leburanci amma daga na fara sai yan tsurku su kai labarin zamana agidan maza saikaga an kore ni babu dalili mai karfi.
Wannan shine dalilin kafa majalisata ta zaman banza akullum banida gurin zama daya wuce gurin
Anan muke tattaruwa muda mutanen tsiya dana kirki akan dole saboda abokaina sun gujeni suna yi min mummunan zato.

Farisu aka kira sunana nayi sauri na juya......MUTUWAR KASKO-03

Farisu aka kira sunana nayi sauri na juya MAMUDA ne ke kirana. Baki ne kakkaura sannan kuma sananne ne wajen zukar tabar wiwi wasu lokutan ma har yakan kora ruwan bagaja.

Farisu kanka ya tabu ne? Kake zaune anan baka san jiya yan sanda keta sunturi ko so kake su cafke ka?
Kada ka damu Mamuda komai kaga yafaru kadd......
AKA rarumi kuguna ta baya bana bukatar juyawa nasan babu mai iya wannan rikon sai yan sanda irin wannan rikon ba bakona bane na juya ahankali yan sanda biyu cun cika hannayen su da rigar Mamuda dakyar kafarsa take taba kasa Ranar a ofishin yan sanda muka kwana ana zanar mu.

Hasken ranar ya bugi fuskata nasa hannuna na kare fuskata kafin idanuwana su saba da hasken hantsin bayan da kwanaki biyu suka shude babu ko mutum daya dayazo belina sai yan sandan suka fara ligwigwita ni akan cewa dole saina fadi sunan wanda zaiyi belina BANIDA KOWA nace dasu
Mutum daya ya fado shine makwabcin mu Alhaji Ilyasu saidai bazan iya dora masa nauyin belina ba a kansa ba wahalar ciyar dani ma kawai ta ishe shi tunanin hakan shi ya sani jure duk wata wahala har suka gaji suka watso dani waje. Lokacin dana fito daga ofishin yan sandan saina bi ta gefen titin motar dake daf da ofishin yan sandan ina tafiya a mimmike kamar wanda aka jerawa tabare abaya duk bayana a kukkumbure yake. tsinannen dukan dana ci a ofishin yan sandan shi ya yi sanadiyar kukkumburar bayana.
Duk taku daya idan nayi sai naji kamar ana sukan gadon bayana da tsinin wuka.

Da farko na dauka jujjuyawar da kai na keyi tana da alaka da tsinannen dukan da akayi min to amma lokacin da na juya kaina na dubi tsallaken titin sai mukayi ido hudu da wata inyamura mai tuyar kosai cikina yayi kulululu sannan yabada wani irin sauti irin sautin da zakaji ne yayin da ka diga dan digon ruwa acikin tafasashshen mai.
Nayi sauri na juya na dubi bayana sannan nafara yan waige waige ganin cewa wasu yan mata dake kokarin tsallaka titin na kallona shiyasa ni fargabar anya kuwa basu ji karar da cikina keyi ba. Hakan shiya tabbatar min da cewa yunwa ce ke sa kaina juyawa. Sai yanzu ne na tuna da cewa yau kusan kwanana daya da wuni kenan rabona da abinci. Adaidai lokacin da wannan ke faruwa ne motar taja ahankali ta tsaya da kyar agabana. Nayi mamaki in da burki ajikin motar sannan na girgiza kaina cikin shakka. jikin motar ya dauki rawa gir gir lokacin da direban yafara kokarin budewa kai kace girgiza ta akeyi but din motar na barazanar tumbukewa daga jikin tsohuwar motar aka yi sa'a bai tumbuke ba har kuma zuwa lokacin da direban ya kashe motar (BANA BA HARKA) babu wani bangare nata da ya samu nasarar ballewa daga jikinta kamar yanda nake tsammani.
Shigo mu tafi Farisu Direban yace dani.
Makwabcin mu ne Alhaji Ilyasu.

BABI NA BIYU
Bayan yayi kokarin sa giyar motar kusan sau bakwai bai samu nasarar ba sai a cikon na tara ya dace ya taka totur din motar tayi zillo muka harba kan titi ko ina ajikin motar na kara kai kace keken shanu muka hau. Alhaji ilyasu ya juyo ahankali ya dube ni daidai lokacin da yake kokarin kaucewa wani dan Hayis.

Tun shekaran jiya muke neman ka ban samu labari ba sai dazun nan da sanyin safiya Naji wasu samari suna zancen wai yan sanda ne suka kama ka.
Bance dashi komai ba ban kuma yadda mun hada ido dashi ba na dan juya ahankali na dubi gilashin bayan motar farin hayaƙin dake fita ta cikin salansar motar ya hada dan karamin gajimare abayan mu.

Meyasa baka aiko min ba Farisu? Ya tambaye ni. Nayi shiru ban amsa tambayar ba fuskata na kallon gabana ga wanda bai sanni ba sai yayi tsammanin ko kurma yake wa magana nasa hannuna ahankali na murda majanyar gilashin motar na dan sauke shi kasa kadan domin na ba tsabtatacciyar iskar dake kadawa samun damar sanyaya fuskata wasu lokuta sai hantsin ya dan lumshe sakamakon yan gutsure gutsuren gajimaren dake giftawa ta fuskar rana.
BANJI dadin rashin aika min da bakayi ba Farisu. Domin ina ganin yadace yanzu ace mun zama kamar yan uwa ni da kai duk abunda ya same ka na sharri ko na alkhairi yana da kyau nasan dashi kamar yanda yan uwanka na jini zasu sani.

Ya danyi shiru kenan kawai sai muka ji.......MUTUWAR KASKO-04

Mun zama tamkar yan uwa nida kai duk abinda ya same ka na sharri ko na AlKhairi yana da kyau nasan dashi kamar yanda yan uwan ka na jini zasu sani.
Ya danyi shiru kamar mai tunani hannayensa biyu dafe da matukin motar ya lankwasa kan tsohuwar motar dakyar muka shiga titin (BAROON).

Lokaci yayi daya kamata ka daina zama acikin dabar nan ta mutanen banza domin hakan bai amfanar ka da komai sai sharri ka tuna fa Farisu kai dan mutunci ne iyayen ka mutanen kirki ne yan mutunci Allah ya jikan mahaifinka tun da muke dashi wani sharri bai taba shiga tsakanin mu dashi ba ina ganin ya dace kayiwa kanka fada Farisu nasan kai ba lalatacce bane kamar sauran samarin da kuke tare dasu yanayin rayuwa ne kawai ya mayar dakai haka to amma duk da hakan baikamata mutum ya saki al'amuran sa ba haka sakaka yana da kyau kayi wa kanka fada bai dace ba ka zama daya daga cikin Ma'abota mutuwar zuciya tun kana da ganiyar kuruciyar ka ba hakika idan kayi haka Farisu baka kyauta wa kanka ba ka tuna fa mahaifiyar ka da kannen ka gaba daya kai suka sawa ido Allah ne gatansu kaine gatansu da kai suka dogara to yanzu Idan ka tasamma mutuwar zuciya yaya kenan?
Me kake tsammanin sakamakon hakan zai haifar?

Kusan minti daya bai ce dani komai ba sannan ahankali saiyaci gaba da cewa inason na taimake ka Farisu amatsayina na dan uwan ka kuma makwabcin mahaifin ka saidai akayi rashin sa'a Farisu ruwa ya daki babban zakara mu ma yanzu abubuwan namu duk
BINDIGAR KWALI CE harsashin ruwa abubuwa ba kamar da suke ba basai na fada ma ba Farisu kasan da inada shi amma yanzu saidai ko a KUNDIN TARIHI
Ban tsira da komai ba sai gidana danake ciki da wannan tsohuwar motar danake dan taba kabu kabu da ita.
Yayi shiru kamar mai tunani sannan yace...


Read / Download MUTUWAR KASKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

6 months ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album