Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

TARAR ARADU Book 1 Complete Hausa Novel Document by TARAR ARADU Book 1


TARAR ARADU Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12377



TARAR ARADU Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 04, Jul 2024

Author: Umar Lawan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 72.62 kb

File Type: txt

Views: 763+

Download: 261+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: TARAR ARADU DAKA
Littafi na daya 1
Na Umar Lawan
Typing:- Shuraih Usman
.
DANDANO daga cikin littafin
••••••••••••••••••••••••••••••••
Umar ya shiga gararin rayuwa
Inda ya rasa kwanciyar hankali
Sakamakon soyayya da
Yarinya mai suna Farida.
Wacce akan tane mutane uku
Suka rasa rayukansu,
Akokarin neman aurenta.kuma
Shima an gargadeshi
Amma yace yaji yagani
Kuma YATARI ARADU DA KA
Saboda fadin kai
Koya zata kasance kubiyoni acikin wannan littafi mai suna
TARAR ARADU
KunasooooTARAR. ARADU
Littafina daya 1
Na Umar Lawan
Page 1
Typing & posted by Shuraih 99%
.

Na yayi mo takarduna bayan na cika tumbina da
waina.nan da nan nafara angizo babur dina Vespa
zabuwa .zuciyata na mai dari darin dadewar da zan yi ina
bugu kafin ta tashi.
Bayan dana hada waya sakamakon gidan makullin
(ignition)da ya dade da lalacewa.
Abin mamaki yau bugu shabiyar kawai nayi ta tashi .anan
da nan wata kara ta cika wajan kamar an kunna injin
markade sabon washi, saudadama idan ina sabis acikin
gida in har na tasheta yara kanyi sallama ."Ga markade".
Ni kaina duk sanda ta tashi nakan toshe kunnena .
Lokacin kwanciyar zafi yan unguwar mu har basa so nayo
dare .
Darana kuwa matan aure basa son wuce wata wai nakan
tayar masu rigimammun 'yayansu daga barci,kuma na
kan hansu bin sallar jam'I.
Dama gababur babu gudu,kuma nakara kasheshi da kaya
.
Domin kuwa idan nabudema wajen adana kayayyakinsa ,
babu komai illa tulin fulogi wanda nikain nasan suna
ragemin gudu.
Amma inkaduba body ,mai motama sai yayi zaton zan iya
wuceshi har yagaza kamoni.
Nan da nan na dare sama mukafara kokoyi da giya na
dade ina shammatarta kafin tafada .
Aifa shigar giyar kedawuya na murdashi sai tyafiya ,kar
kaso kaga yanda nake doro ina kwambarewa .
Kullum nahau haka nake fankama naketakama kamar
sarki akan doki.
Idan na raina majalisama ko sallama banayi ahaka naita
wuta har makarantar dangiwa commercial secondry
school.
Inda anan nake koyarwa amatsayin malamin English.
Da malam sule mai gadi muka fara gaisawa "har an fito"
"Allah yayi"
Nabashi amsa .
Nakafe babur dina a inda aka tanada domin yin fakin.
@mr:-Shuraih 99%
Na nufi ofishin principle. Ko ba'a fada maka sunansa ba
zaka iya ganewa da kanka.
Domin kuwa yafi dacewa da malam Abba .akwai kwazon
aiki akwai kuma mugun son kudi na gaisheshi muka
kuma taba yar hira wadda zolaya acikinta tafi yawa .
Da fitowata na nufi wani abokin aikina kabir sabi'u. Muka
caccake na dubeshi "naga sai kyalli kake kodai kanasan ka
angoncene ban saniba?"
Yayi dariya" kaifa tsiyarka kenan baka kyale mutum haka"
Muka zauna na shiga dube dube wani lokacin har nakan
mike tsaye "wai kai me kake dubawane"
Na dawo na zauna bayan na gaza hango abin danake
nema "don Allah bakaga shigowar farida ba ?"
Na tambayeshi . Ya tintsire da dariya . "Kai mallam tunda
farida tafara aiki anan naga sai wani kankajeri Kake kana
kara kwalliya ,kodai da watane akasa?"Nace babu komai ,
don mutum ya tambayi abokin aikinsasai yazama laifi"
Ya girgiza kai
"To me isa baka tambayar su hafiz?
Kosu ba abokan aikin kabane"?
Na gyara takarduna sa'arda nake cewa
"Kaga mungama hirar ne ban tambayekasuba"
"To shikenan tunda boye-boye kake ,amma indai kuka
shirya kanku kayi sa'ar mata UMAR"
Bancemasa komaiba ,duk dacewa maganar tasa ta
kayatar dani . Bada jimawa ba na hangota tana shigowa
tana rungume da jakar takardunta .
Mace ce mai matukar tsari da kyau tana da yawan kuya
da kulawa da Addini,kai ni tunda nakke ban taba ganin
kamartaba .
Na mike tsaye kabir yabini da kallo
"To mallam ka hangota zaka gujeni ko?"
Na harareshi
"Ai kaine kake yimin wulakanci,ba gara na tafi inda inda
za'a karramani ba " ban tsaya wata wata ba nanufi inda
take da ganina ta fara murmushi ,
Murmushin da kullum in tayimin sai nadan rikice .
Na dubeta cikin sarkewar murya
"Ina kwana hajiya farida "
"Lafiya lau umar"
Tra amsa cikin daddar muryarta
To be conti......
Via:- mr:- Shuraih 99%
TARAR ARADU
Littafi na daya 1
Na Umar Lawan
Page 2
Typing and posted by Shuraih 99%
.
.
"Yau narigaki zuwa "
Nace da ita tadan kwatar da kanta
"Nadan ragewa mummy aikine saboda batajin dadi"
Ashsha Allah ya sauwake"
Nadan gyara tsayuwata "don Allah farida idan an tashi
tara ina son magana dake'
Ta kalleni da fararen idanunta sa'ar da take cewa
"Lafya dai ko umar"
Na kauda kaina domin bana jurewa kuramata ido saboda
wani kwarjini da take dashi.
"Lafya kalau akan dai maganar nan ne"
Ta sun kuyuyar da kanta kas daga bisani ta dago
"To Allah ya kaimu"
Muka juya muka tafi.
@mr:-Shuraih 99%
Tunda farida tafara aiki amakarantarnan Allah yasanya
min tsabar kaunarta , nayi kokari in yakice amma ina.
Abin yaki yiwuwa .
Wannan yasa nafara yi mata isharori amma tayi biris
kmar bta gane ba , ga misali nasha sai mata sabulai da
mayuka .
Amma sai dai tayi godiya ta kuma bini da Addu'ar Allah
yabar mutunci.
Wannan yasa nafito fili na shai da mata amma sai tace na
saurara zata tun tubeni .
Kuma shiru kakeji haryanzu taki tuntubata .
Dana tina mata saita kama noke-noke shine yau nayi
kunar bakin wake domin nasan wacce akeciki.
Ana tashi tara na nemi karkashin wata bishiya na hakimce
can jimawa sai ga farida tana isowa
"Mai yafaru ne umar?"
Ta tambayeni bayan data zauna ,nakara jingina sosai
ajikin kujerar danake kai.
Sannan na dubeta na fara dacewa
"Wai dan Allah farida mai yasa har yanzu kika ki bani
cikakkiyar amsa ?
Nidai idan kina ganin babu dama gwanda ki gayamun
insan yanda nayi.mai makon ki kyaleni kullum ina
azabtuwa da tsabar sonki, kuma ina hada ki da Allah ki
shaudamin hakikanin gaskiya "
Na dade ina sauraronta taki tace uffan .sai kawai ta
tokare habarta da hannu,
Babu tsammani kuma sai naga tafara kwalla .
Hakan ya rikitani ,cikin rudewa na fara cewa
"Maganata rai ya bata miki"
Don Allah kiyi hhakuri"
Batace komai ba taci gba da kukanta kawai
"Don Allah farida kiyi hakuri bazan sake tambayarkiba"
Ta girgiza kai lokacin da take share hawaye "umar ba
tambayr kabane ta bata min rai illa iyala wani al'amari
dabam , zan amsamaka tambayarka umar,amma saidai
in antashi kasameni agida "
Nadubeta
"Inane gidanku
Tadanyi jim sannan tacigaba 'goron dutse bayan gidan
isiyaka rabi'u gida mai kallon kudu, na biyu ahannun
dama"
*** *** ** ** ** ***
Dayin sallar la'asar na shiga wankka , nadade ina shekawa
domin kuwa awa guda na karar cur, nakarar da ruwa ya
kai jarka uku, ba'a batun sabulu wanda nakarar da fakiti
guda badon komaiba sai don na kara haske.
Aranan sabon man shafawa nasiyo saboda ji nayi nawa
nada yana wari, alhalin kuma dukranda nashafashi har
tambata ake wannan wane maine?.
Saoda tsabar kamshi, na bude kwaba nayi ta zaro kaya
ina ajiyewa gefe guda ,har nazo kan na cin yewar
,dukranda na sanyasu ka tabbatar zani muhimmiyar
ungwa ko kayataccen fati.
Nan da nan nafara jikasu da tirarena.
Na makala farin gilkashi.
Ban nufi ko'inaba sai gindin dressin mirror don duba
haduwar tawa,
Hakika nafito kamar yadda nayi tsammani, nakalli
takalmana cali-cali wayanda tuni na baiwa shushaina ya
wankeminsu harda karin kudi nayimasa domin yayi mani
wanki na musamman nan danan na zura kafata nafara
takawa cikin takama ,
Kai kace wani dokin dan sarki,
@mr Shuraih 99%
Na kulle shagon nanufi cikin gida anan na sami matar
yayana tana kokarin dora girki.
"Kai umar ina zakne haka kaci kwalliya ?"
Nagoge fuskata da hankici
"Wallahi zani unguwne ,yaya kika ganni,nafito?"
Ta kalleni daga sama har kasa
"Wallahi ka fito"
Kaga yanda kake kyalli kamar sabon kwabo"
Wata dariya ta kwacemin .
"Toh madalla dama haka nakesopn ji"
"Zanyi miki karin kudin cefane tunda kin yaba "
Tayi shewa .
"To mai gida, godiya nake,ince dai ba kishiya zakayiminba
ko?"
Na duba agogona
"Ke dai wallahi kin cika tsoron kishiya kimin Addu'a Allah
yabada sa'a"
Ta kwantar da kai
"To Allah ya taimaka "
"Amin"
Nafito nabarta .
Raina yabaci yayinda na iso soro,baodn komaiba sai don
bata min lokacin da mashin zaiyi.
Na turashi har muka zo waje.
Nakafeshi nafara bugawa nayi tayi amma ina ko amsawa
bayayi kamar wanda na cika tankinsa da ruwa .
Yara kuwa sukazo suka yanyameni,kullum haka sukemin
in har nazo fita da yamma ,sukanyi ta dariya sa'arda nake
bugawa.
Wani lokaci nakanji kaman nasa duka amma sai na daure
na rabu dasu.
Har ina shirin hakura sai naji yafara amsawa.
Wannan yasa nacigaba banfi bugu ashirin ba kuwa
yatashi.
Yara suka kaure da shewa ye !yatashi yatashi!
Nan fa suka da baya yayinda suka ga dare,badon komai
ba saidon sun san in yayi wata zabura zai iya bi takan
yaro.
Raina yakara baci dana tuna yadda zanyi fama da giya
,amma cikin ikon Allah murdawata sau uku sai fada, na
murza totur sai tafiya ahaka na ringa tuki cikin hkima da
dabara.wai ance inkana da abin hawa dolene kazama
makaryaci saboda takurawar yan aro mai zuwa yau
dabam mai zuwa gobe dabam.
To nidai nakaryata domin kuwa babur dina saudaya wani
abokin aikina yataba aronsa da uzurin gaggawa ya
kamashi,daga ranar shima bai kara araba.
CABDI WANNAN BABUR KO WAHALA DA RAI
Zamu cigaba anjima
By @mr:- Shuraih 99%TARAR ARADU

Littafina daya (1)

Written:- shuraih 99%
Page 3

Adai dai junnction din bariki yellow fifi ya tsaida mu.
Raina yabaci domin kuwa shine abin dana tsana sakamakon rashin wadataccen burki,nayi iya yina domin ya tsaya amma ina ,har nakaiwa yellow fifan sura .yayi tsalle gefe guda .
Da kyar babur din ya tsaya bayan daya tungudi ginin express, na juyo domin bawa yallaban hakuri, sai naga ashe bai dauka da zafiba ,daomin ma dan unguwar ne.
Ba'ajima ba akabamu hannu nafara kokarin sa giya ina takawa da kafa da kyar na samu ta shiga,
Wata rana ma kin shiga takeyi sai nagaji da shan zagi da horn daga masu ababen hawa .
Kai har akwai kwandastan daya taba rankwashina wai tare musu hanya .
Haka naci gaba da taifya rakakai raka kai kamar wanda yake tafiya akan jaki, sauda yawa mai
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download TARAR ARADU Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album