Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

GARKUWA CE Complete Hausa Novel Document by GARKUWA CE


GARKUWA CE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 64275



GARKUWA CE

Reading Time: 5 Hours

Added On: 23, Jun 2024

Author: Maman Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 356.05 kb

File Type: txt

Views: 391+

Download: 492+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301
[7/17, 10:43] Washa: 💎💦💎
💝


GARKUWA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W💝


💎MMN USWAN.💎


Dedicated to sweet sis mardiya ka'oje


happy Sallah to all Muslims Sisters and brothers In Islam.

May Allah protect us and accept our Ibada Ameen ya Allah.


Bissmillahi Rahmani Rahim


1

"Zahra xan sha ruwa Zahra.

"Zahra ruwa Zahra.

"Da sauri Zahra taxo tana cewa baffa!!!!! Baffa me kake bukata baffa?

"Baffa yasake cewa ruwa.

"Duk da haka Zahra bata jiba saida ta kara kunninta kusa da bakin baffa snn taji abinda yake fadi.

"Baffa yana mgnr ne cikin yanayi na karayar harshe.

"Da alamu dai lokaci yake jira.

"A guje Zahra taje ta dibo ruwa a randar dake sakarkari ta dawo.

"Tallafowa baffa kai tai yadin dago snn ta dauki kwanin shan ruwan ta bashi.

"yana sha yai wani irin ajiyar zuciya, gaba daya idanusa duk sunyi sama wayarsa ta karye.

"Me dashi Zahra tai ya kwanta.

"Yana kwaciya tai wani irin nushi.

"Snn ya kamo hannu Zahra da karfi ya rike, Baffa yana mgnr ne cikin wani irin yanayi.

"Zahra na gani haka tafara kwalla.

"Baffa yace Zahra banida abinda da xancewa ubangiji sai godiya.

"Daya azurtani dake, Zahra inaso ki kasance yarinya me hakuri da juriya duk yanayin da kika tsinci kanki.

"Zahra ki kasance me biyyaya ga nagaba dake.

"Zahra duk abinda zakiyi kiji tsoron Allah.

"Ni tawa taxo karke, Zahra kiyi hakuri da rayuwa.

"Kada kibiyewa zugun mutani kice zaki bijirewa hajjo.

"Hajjo tamkar uwa take a gunki.


"Zahra inaso kiwa hajjo biyayya ki dauketa tamkar itace uwa mahaifiyarki zahra.

"Kinji ko Zahra.

"Zahra ta fashe da wani irin kuka tana fadin naji baffa, Baffa in Allah ya yarda xaka tashi.

"Baffa cuta ba mutuwa bane baffa.

"Baffa kada katafi ka barni baffa, Baffa banida kowa saikai baffa.

"Baffa kaine gatana baffa, baffa kada kaimin haka baffa.

"Baffa yace zahra ina Hajjo?

"Zahra tace Hajjo na gidan mai gari.

"Baffa yace ruga ki kirami ita.

"Da sauri Zahra ta mike hade da cewa to Baffa.

"Ko takalmi Zahra bata tsaya sawa ba a guje ta ruga xuwa gidan mai gari.

"Ko sallama Zahra batai ba haka ta amka kasu tana cewa ina kizo.

"Gani Zahra da tai a birkice,wani irin tsaki tai hade da cewa to bakar agunguma me kuma ya faru?

"Jin haka jikin Zahra yai sanyi, a sanyaye take mgnr tace baffa ne yace kizo.

"Hajjo tace me zanmasa kuma?

"Babu dama aga mutum yafita shan'iska, Sankace tawa uwar yake tsinanamin.

"Haule kawar Hajjo tai wani irin shewa hade da cewa mutuniyata kenan baki da dama fa.

"Idan banda abinki mutumi da yake fama da kansa me kikeso yai maki?

"Murmushi Hajjo tai snn tace idan banda abinki Haule raifa dangi goro.

"Haule tace kinada gaskiya mutuniyata.

"Juyowa Hajjo tai hade da dakawa Zahra tsawa tana cewa bacemin a gaba kibagu.

"A sanyaye Zahra ta juya...

"Da sauri Haule tace aa ba haka xa'ai ba.

"Jeki kice tana xuwa.

"Ko tankawa Zahra batai ba, haka tafita tabar gidan.

"Zahra na fita su Hajjo da Haule sukai shewa hade da tafawa.

"Zahra na komawa gida ta sami baffa yana faman mutsuke3.

"Da sauri ta karisa gunsa hade da cewa Baffa jikin ne?

"Baffa Baffa Baffa.

"Wayyo Allah Baffa na, Baffana kada ka tafi ka barni.

"Baffa idan katafi ka barni mutuwa zanyi Baffa.

"Baffa sai faman hasa2 yakeyi.

"Zahra na gani haka dagosa tai ta rungume duk tana yine tana kuka.

"Baffa sai salati, salati yakeyi babu kabkabtawa har yacika.

"Yana cikawa Hajjo na sallama.

"Gani ya daina shure2 ne kuma wayarsa ya karye idanu na kallon sama baki a bude.

"Wani irin ihu Zahra tasa, Tana fadin nashiga uku na lalace.

"Shikenan tawa ta kare.

"Baffa katafi ka barni, yadda innata ta tafi ta barni.

"Jin haka yasa Hajjo ta kariso da sauri.

"Gani Baffa bayako shurawa yasa sa wata uwar ihu tana fadin shikenan Haruna, Haruna lokaci yayi Allah ya jikanka yasa ka huta yasa iyakacin jinyar kenan.

"Shinfidashi sukai ita da Zahra.

"Nan da nan bada bata lokaci ba akai masa sutura aka kaisa makwancisa.

"Zahra babu abinda takeyi sae kuka, ko abinci ma bata iya ciba sbd kuka.

"Maryama kawar Zahra tai lailaishi har tagaji.

"Yar'uwar mmnta duk sunxo daga ruga.

"Maryama da yar'uwan mmn Zahra tare suke zaune har akai addu'ar uku.

"Bayan addu'ar uku ne yar'uwar mmn Zahra sukace abasu Zahra sutafi tare.

"Malam Habu kanin malam Haruna yace baza'a basu ba.

"Daya daga cikinsu itace uwarsu daya ubansu daya da mmn Zahra tace dan Allah abata Zahra sbd ita kadai take gani a matsayin yar'uwanta.

"Malam Habu shima yace ita kadai yake gani a matsayin dan'uwarsa.

"Dan Allah yanaso su barta a hannunsa.

"Kanwar mmn Zahra tace ba naki taka bane wlh ina gujewa yarinyar ga shiga wani haline.

"Sbd Hajjo ba imanine da'ita ba.

"Tun ubanta nan ma ya aka kare banle bayanan.

"Shiru malam Habu yai sbd yasan halin Hajjo sarai ba imanine da'ita ba.

"Zata iya jefa Zahra cikin kowani halin.

"Amma kuma idan har yabari suka tafi da'ita bazata samu wani ilimin kirkiba.

"Sbd ba zaune suke gu daya ba.

"Dayan matar dake gefene tace malam Habu kana jina kuwa?

"Malam Habu yace ina jinki.

"Ni dai dan Allah kubarmi Zahra a hannuna, in Allah ya yarda babu abinda zai sameta.

"Kuma nayi maku alkawarin lokaci lokaci zan rinka kawo Zahra kuna gaisawa.

"Jin haka kanwar mmn Zahra kuka tasa tana fadin Allah ya jikanki zainaba, Allah yasa kin huta.

"Itama zahra kuka takai sosae.

"Maryama dake gefenta sai faman lailashinta takeyi.

"Bayan la'asar suka tafi gida.

"Zahra da maryama sukai masu rakiya har bakin rafi.

"Kudi masu yawa suka bawa Zahra snn sukai sallama suka tafi.

"Zahra kuka tai sosae, suma haka.

"Maryama ne ta riko mata hannu suka koma gida.





Mmn uswan ce
[7/17, 10:43] Washa: 💎💦💎
💝


GARKUWATA
(RELIANCE)


FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.💝


MMN USWAN


Didecated to sweet Sis mardiya ka'oje


2


"Bayan addu'ar bakwai, Akaxo rabon g'ado.

"Ga malam Habu da kanwar mmn Zahra da mai gari da ita kanta Zahra sai Hajjo.

"Limami mai rabo g'adon saida ya fara da addu'a snn yace a fito da abinda mamaci ya bari.

"A lokacin ne Hajjo tace tana da mgn.

"Duk jama'ar dake gun sukace bissmillah.

"Hajjo tasa kuka tana f'adin dama tun lokacin da Haruna ke raye yasan da mgnr,Har cewa yai xai sanar dakai amma...

"Da sauri malam Habu yace wahhh????? niii??

"Hajjo tace eh.

"Malam Habu yace ina jinki.

"Hajjo taci gaba da cewa lokacin da zai kara gini d'akunan ga harda kudina a ciki...

"Da sauri malam Habu yace karya aradun Allah karya kike.

"Babu wani kudin ki a ciki.

"Kuka Hajjo taci gaba dayi, tana cewa kungani ko.

"Dama nasan xa'ai haka sbd lokacin na hanashi kudin yacemi babu damuwa xai sanar dakai.

"Malam Habu yace yasin karya ne.

"Hajjo na h'ada ido da mai gari suka kashewa juna ido.

"A lokacin ne mai gari yace tunda kaga hakan da gaske ne.

"Malam Habu yace karyane wlh.

"Saida malam yai gwaran murya snn yace to mudai yanxu bamuda abinda da xamuce a cikin wannan al'amari sbd babu Haruna inda yana rayene komai xaixo da sauki.

"Kanwar mmn Zahra tace gaskiya ne.

"Snn yaci gaba da cewa shidai a rayuwa duk abinda xakai kasa tsoron Allah ya ciki.

"Duk abinda xaka aikata yazama ka shirya ta cikin turban gaskiya.

"Tunda haka tace kai malam Habu me kagani?

"Malam Habu yace kwaran kwatsan aradun Allah karya takeyi.

"Sbd tunda nake da d'an uwana babu abinda yake boyemi,duk abinda zai aikata sai munyi shawara a tsakanimu.

"Kuma har Allah ya dauki ransa be taba sanar d'ani akwai wata mgnr kudi daya amsa a gunki ba.

"Hajjo tace to tunda haka kace babu damuwa, Ni dama gani nai yanada kyau a saukewa mamaci nawin dake kansa.

"Amma tunda haka kace babu damuwa na hakura.

"Ta karisa mgnr ne da mikewa xata bar gun....

"Da sauri malam yace aa Hajjo baxa'ai haka b, dawo ki zauna.

"Hajjo tace aa malam na hakura kawai.

"Mai gari yace kedai dawo akace ko.

"Snn ta dawo ta xauna.

"Malam yace kai malam Habu inaso na roki wani alfarma a gunka.

"Malam Habu yace ina sauraranka.

"Sai malam yaci gaba da cewa dan Allah dan annabi inaso hakuri abata hakkin ta tunda bata yafeba.

"Shifa bashi da kake gani komai kankantarsa yana hana kwanciyar kabari.

"Koda dukka tace natane gara a bata a huta??????

"Malam Habu da sauri yace minkace?????

"Malam yasake memeta masa.

"Da sauri yace wlh Allah kwaran kwatsan bata i'sa ba, saidai bayan raina.

"Gani hakan malam yace dakata bafa cewa nai abata dukka ba.

"Malam Habu da yaga hausan ta gagareshi juyawa yai harshe fullaci.

"Inda yake shiga ba nan yake fita ba.

"Dukkansu shiru sukai har saida ya numfasa snn malam tace haba malam Habu da iliminka da wayewarka shine kake haka.

"A wata tunanin koda duk dukiyar marigayine Hajjo tace nata xaka bata sbd soyayyyar dake tsakaniku.

"Amma har katsaya kaya gardama da'ita.

"Me akai akai abin duniya?

"Kada fa kamance wanda ya tare yanajin so haka ya tafi...


Read / Download GARKUWA CE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album