Join Our WhatsApp Group

BADAKALA Complete Hausa Novel Document by BADAKALA


BADAKALA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 325986



BADAKALA

Reading Time: 27 Hours

Added On: 08, Apr 2023

Author: Samira Harouna ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 1.76 mb

File Type: txt

Views: 2726+

Download: 3245+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 06/12/2019 à 14:41 - Les messages envoyés dans cette discussion et les appels sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations.
18/05/2020 à 13:43 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin gaske*


*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦


*Labarin nan ya faru a gaske, sai dai a wurare daban daban, amma na canza garuruwa da sunaye, domin tak'aitawa kar gidajen suyi yawa yasa zan had'a labarin a gida d'aya.*

*Nagode da gudummuwarku gareki*


_Bismillahir rahamanir rahim_

_1_


Kamar saukar aradu tsohuwar nan ta d'aga hannu ta gaure matashin saurayin dake gabanta da mari, cikin d'aga murya da b'acin rai ta nuna shi da yatsa tana fad'in "Wallahi ko zaka mutu ba zan tab'a bari ka auri karuwar nan ba, *Junaid* ko ubanka dana haifa bai isa nace ga yanda za ayi ba yace a'a bare kuma kai daya haifa, in zaka auri wacce na zab'a maka ka aura, in kuma ba haka ba to ka sani zaka mutu a matsayin wanda bai b'ata aure ba har abada."

A hankali ya d'ago daga sunkuyar da kan da yayi tare da d'auke hannunshi akan kumcinshi ya kalleta, kyakyawa ne sosai wanda ya had'a komai da komai, abun mamaki kuma shine wasu matasan guda biyu dake tsaye daga bayanshi wanda suke matuk'ar kama, sai dai kaman wad'ancen matasan tafi k'azanta matuk'a da alama ma 'yan biyu ne, cikin ladabi yace "Hajia kiyi hak'uri idan abinda zan fad'a zai b'ata miki rai, amma a gaskiya ina son *Maryama* kuma ita nake so na aura, Hajia munyi iya k'ok'arin mu wajen yi miki biyayya, mun bar abinda muke so saboda ke, na zama malamin makaranta ba dan raina na son haka ba, amma a gaskiya yanzu abune da zaiyi wahala, dan magana ce ta aure, rayuwa ce da ake saka rai idan har anyi to sai mutuwa ce zata raba, kenan taya zamu yarda mu auri wanda ranmu baya so? A gaskiya ni dai ba zan iya ba, kuma iyayena sun amince na aure ta haka ma Alhaji ya amince."

Wuyan rigarshi ta finciko ta tilasta mishi kallon fuskarta tace "Junaid ni kake kallo kake fad'awa wannan maganar, to ka sani ni ce shugabar gidan nan sai abinda nake so akeyi, daga kai har uban naka zan iya tsine muku albarka idan kuka ce wannan yarinyar zaku shigo min da ita a cikin gidan."

Sakin rigarshi tayi har saida yayi baya amma ya tsaya cak yana kallonta, gyara tsayuwarshi yayi yace "Shikenan, tunda haka kika ce ni zan bar gidan nan naje can na auri wacce raina yake so, kuma wallahi..."

Bai k'arasa ba mahaifiyarshi *Zeinabu* ta d'auke shi da wani sabon marin tana fad'in "Kayi mana shiru anan."

Sake dafe kunci yayi yana kallonta da mamaki, ita ma kallonshi tayi duk da tana goyon bayan wacce yake so ya aura, amma dole tayi haka saboda k'arshe abin kanta zai koma, da yatsa ta nuna mishi k'ofar fita tace "B'ace min da gani, kuma kar na sake jin motsinka a gidan nan idan bani na neme ka ba."

Ya juya zai fita wata kyakyawar tsohuwa wacce fuskarta ke d'auke da tsaga wacce ake caccakawa sai tayi bak'i ga kumatu da kuma gefen bakinta, cike da dattako tace "Kai Junaid, zo nan, ba kamata yayi ya fita ba, mafita ya kamata a samu a game da matsalarshi, ba wai mu barshi haka ba."

Mahaifin Junaid d'in wanda suma na gani su biyu duk kamarsu d'aya, kuma abin sha'awar ba zaka ce sun haifi kamar wannan zargadan zargadan matasan ba saboda yanda suke tsaye da kyau zaune da kyau, saidai mahaifin Junaid d'in jikinshi yafi murd'ewa kasancewarshi *soja* a cikin sojojin ma *colonel* ne, kamar baya son magana saboda yanda yayi maganar yace "Ku barshi ya tafi kawai tunda saiya mana rashin kunya ne zamu yarda da k'udirinshi." *colonel Hussein Suley Hassan Gaga* kenan wanda ko wajen aiki akafi kiranshi da Hassan Gaga.

Mai kama dashi ne sak mai sunan *Hassan* wanda shine babba yace "A'a d'an uwa ba ayi haka ba, ya kamata a tattauna a tsanake dan duk yanzu kowa zuciyarshi tafasa take."

A harzuk'e kyakyawar tsohuwar nan wacce kallo d'aya zaka mata kasan asalin buzuwa ce tace "Babu wani tattaunawa da za ayi game da maganar nan, na gama magana dan haka babu buk'atar sake taso da ita, ba zai tab'a auro karuwa ya kawomin a cikin zuri'a ba."

Tana fad'in haka ta wuce zuwa inda zai sadata da nata d'akin baccin kasancewarsu a babban falon gidan, sai lokacin kad'ai wani santalelen tsoho dake zaune yana kallon kowa ya bita da kallo da wani murmushi a fuskarshi, uwayen ma duk barin wurin sukayi rai a jagule, tsohon kad'ai ya rage sai matasan nan guda hud'u, Junaid ne ya juya zai fita tsohon yace "Junaid, kaje ka ci gaba da k'ok'arin samun yardar Maryama, zaka aureta, wannan alk'awari na ne gareka, kaji ko?"

Da murmushi a fuskarshi yace "Nagode Alhaji, Allah ya saka da alkairi."

Juyawa yayi ya kalli yan uwanshi, cikin farin ciki biyu suka rumgume shi sai d'aya da yace "Ko ba komai zakayi bacci cikin farin ciki, nima Allah yasa ta amince da zab'i na."

Murmushi sukayi sosai sai Junaid d'aya rad'a mishi a kunne "Ai kai ahalinta ce kake so, zata amince da gudu ma, idan bata amince ba ka mata bore irin nawa."

Dariya suka sake sakawa sai d'aya daga ciki daya juya ya kalli wanda ke zaune yana latsa wayarshi alamar shi duk matsalolin nan ko a kwalar rigarshi, girgiza kai mai matuk'ar kama da shi yayi yace "Yanzu yaya *Ammar* kai ko ka tayashi farin ciki ma."

Tabbas saurayin da gani kasan akwai shan k'amshi da d'acin rai da kuma miskilanci, dan ido kawai ya zuba mishi ya kalleshi take kuma ya d'auke ya ci gaba da abinda yake, d'aya saurayin ne yace "Kunga barshi da halinshi, watak'ila allurar sojojin ce ta motsa."

Yana fad'a sai kawai suka kwashe da dariya harda Alhaji dake shirin tashi, wannan kuma abun shi ya tunzura Ammar ya ji kamar ya rufe su da duka, tunda iskanci ne suke mishi, sunfi kowa sanin baya da buri a duniya daya wuce ya ganshi a matsayin soja mai kare k'asar shi, amma tsohuwar can ta bakinshi ta hanashi cika burinshi, ta tilasta mishi zama likita abinda sam baya birgeshi ma a tsarinshi, amma sun samu abin tsokanarshi da shi dan sunga yana mutuwar son zama sojan har yanzu, hararan daya musu da jajayen idonshi yasa su shiru sai *Amar* wanda shine tagwaicin haihuwarshi yace "Kunga mu bar gidan nan dan ran sojawa ya fara b'acewa, yanzu ne allurar zata motsa a huce kanmu."

Nan ma wata dariyar suka saka wacce tasa shi tashi da hanzari ya bi bayansu, ai da gudu dukansu suka fita kamar yara k'anana, rige-rigen fita sukeyi a bakin k'ofa hakan yasa yayi nasarar rik'o rigar *Jibril* wanda yake jika ne ga k'anwar kakansu *Husseina*, duk da kasancewar Jibril namiji saida idonshi sukayi ja kamar zaiyi kuka saboda wata matsa daya mishi a ciki ya had'a da fatar jikinshi, k'ara ya saki ya kalli su Amar da har sun kai k'ofar gida cikin muryar wahala yace "Kai dan ubanku ku zo ku taimaka min, ba tare mukayi tsokanar ba."

Dariya Amar harda yin zaune k'ofar gidan yana rik'e ciki saboda ya ga k'eta, Ammar kam sosai yake sake matse mishi fata yana fad'in "Gobe ka sake min iskanci?"

"A'a wallahi, daga yau gaisuwa ce tsakaninmu da kai, kayi hak'uri dan Allah yaya Ammar."

Jinjina kai Ammar yayi yace "Oho, kenan yanzu ka tuna da nine yayanka ko? D'an iska kawai gobe ka k'ara." Ya fad'a yana tura shi, Junaid na ganin haka ya haura ta kan Amar dake zaune yana dariya ya fita a gidan, dukansu baya suka rufa mishi shi kuma Ammar ya juyo ya dawo ciki.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Alhaji na tashi daga nan d'akin baccin tsohuwar nan ya shiga, zaune ya sameta cikin tsananin damuwa, sam bata san ya shigo ba har saida yace " Duk wannan damuwar akan maganar auren ce?"

Da sauri ta kalleshi, tana ganinshi ta ja k'aramin tsaki ta sake kawar da kanta, shi kam ko a jikinshi dan ya ga fiye da haka ya kuma yi hak'urin fiye da haka, dan haka ya d'ora da " *Zeeya'atu*, tsawon shekaru hamsin da bakwai da aurenmu, na saka miki ido kina juya yaran nan yanda kike so, dayawa daga cikinsu suna rayuwa babu farin ciki saboda kin tauyesu ta wani fannin, hatta aikin da sukeyi duk ke ce kika zab'a musu shi haka ma matan da suka zama uwayen yayansu, akwai wanda kina kallonshi zaki san baya farin ciki da zab'in naki , amma saboda biyayya sun hak'ura suna yi, to ya kamata ki sani zmanin yayan da kika haifa da zamanin yayan da suka haifa ma'ana jikokinki ba d'aya bane, yanzu ba'a tirsasa yaro yayi abinda baya so, nasan kin fara fahimtar hakan daga yanda Junaid ya miki magana yanzun nan, da wannan nake shawartarki da ki janye wannan kud'irin na cewa ba zai auri yarinyar nan ba, dan na mishi alk'awarin zai aureta kuma babu abinda zai hana hakan."

Har ya juya zai fita ta mik'e tace "Wallahi baka isa ba, indai ina numfashi a doron duniyar nan Junaid ba zai tab'a auren yarinyar dake yawon ta zubar ba, ba dai a dangina ba, sannan da kake maganar babu mai farin ciki a ciki amma ai suna zaune lafiya."

Juyowa yayi yace "Babu wanda yasan abinda ke b'oye cikin duhu, ki zuba ido zakiga auren Junaid da Maryama, tunda Allah bai haramta mishi ba mu ba zamu hana mishi ba, indai har zatayi tuban gaske to wannan ba matsala bane."

Cike da rainin wayo tace "Idan ya aureta ya shigo da ita cikin gidan nan harta haifa mishi 'ya'ya, ya'yan wa zamu kirasu? Kana so ace ai uwarsu tsohuwar karuwa ce suma kamar yanda Jibril ya kasance jika ga tsohuwar karuwa?"

Da k'arfi ya juyo ya k'ura mata ido, zuciyarshi ce ke bugawa da k'arfi yana ji kamar ya mata bugun mutuwa, saidai kuma abinda baiyi da k'uruciya ba shiyasa ba zai iya yi yanzu ba, haka ma baya so yayi magana ta hanyar bankad'o sirrin da yake ta rik'o a ranshi tsawon wannan shekarun, murmushi ya mata yace "Hum! Tabbas ba k'arya kika fad'a ba, ki sani nata karuwancin ne ya fito fili, na wasu kuma bai fito ba watak'ila talala ubangiji ya musu su gama gurza rashin mutumcinsu."

Yana fad'a ya sa kai ya fita dan fad'an su ba k'arewa yake ba, shiru tayi tare da tunanin me yake nufi da abinda ya fad'a, ta jima a haka tana wannan tunanin kafin ta d'auki gabjejiyar wayarta ta dannawa Amar kira, dan daga kallon kayan dake jikinta da yanayin shigarta da kwalliyar fuskarta zaka san tsohuwar wayayya ce ta gidan gaba, yana d'auka cikin sanyin murya tace "Jikalle kana ina? Ka fita?"

Cikin gatsali yace "Me kike so kuma yanzu? Ni bana gida."

Murmushi tayi har saida yaji sautinsa tace "Jikalle kuma guduna kake yanzu? Me ya sa kake haka?"

Cike da k'aguwa yace "Kinga Hajia, ni na fad'a miki bana gida, sai anjima."

Kashe wayar yayi ita kuma ta aje gefe tana kallon wayar tace "Allah yasa ba wajen wata shed'aniya kaje ba, amma idan ma da wani abu zan gano koma menene."

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Jibril ma yana fita bai jima ba ya dawo gida, fitowa yayi daga motarshi mai shegen kyau da tsada, cikin falon ya tunkara ya bi ta inda zai sadashi da d'akin baccin kakarshi, saman bene ya kalla inda hayaniyar yara ke tashi sunata wasa da guje guje, yana kusa da kaiwa ya tsaya cak saboda tuna wani abu daya riga ya zamar masa jiki, a hankali ya rintse idonshi yana kallon fuskar a hoton k'wak'walwarshi tare da tuna wasu maganganu da suke gigita tunaninshi, duk da idonshi rufe suke amma saida hawaye suke zubo mishi saboda tuna wasu maganganu na k'arshe da macen take cewa " *Idan fa ciki ya shiga jikina sakamakon hakan? Ya kake so nayi? Wai kai baka da imani ne?*"

Da sauri ya bud'a ido ya goge hawayenshi ya d'aga kai ya kalli sama yace "Allah ka kareta a duk inda take, Allah kasa bata samu ciki ba a dalilin wauta da mahaukaciyar sha'awata ta k'uruciya."

K'asa yayi da kanshi tare da fad'i a zuciyarshi "Ameen." Cikin sanyin jiki ya k'arasa k'ofar d'akin yayi sallama, amsa sallamar akayi daga cikin d'akin kuma harda muryar mahaifiyarshi, shiga yayi ya samu wuri ya zauna kusa da kakarshi yana fad'in "Mama sanunku, hira kuke ke da yar tsohuwa?"

Dukanshi Husseina tayi tace "Ubanka ne tsohon, ni matsa can ka bani wuri."

K'ara lafewa yayi a jikinta yace "Ina zan matsa ni da na zo miki da muhimmiyar magana."

Mahaifiyarshi mai sunan *Soueba* ce tace "A k'alla ka d'auki sama da wata d'aya kana fad'a min zamuyi magana amma ka kasa nutsuwa ka fad'a min."

Sosa kanshi yayi yace "Mama yau dai zan fad'a muku tunda na samu k'arfin gwiwa daga abinda Junaid yayi yau."

Zaro ido tayi tace "Kai duba ka kiyaye ni wallahi, kai ma rashin kunyar zakawa mutane? To babu ruwa na ni dai, Mama ku zama shaidata."

Murmushi Husseina tayi tace "To ki barshi ya fad'a mana muji me yake tafe da shi, fad'i ina jinka."

Kallonsu yayi dukansu yana murmushi kafin yace "Ni fa dama ina so na fad'a muku ne nima na samu matar aure."

Dogon tsaki Soueba tayi tace "Aikin banza, dama wannan maganar ce zaka fad'a."

Husseina ma dariya tayi tace "Wannan wacece haka zata kwashe min wannan rigimamman mijin?"

Nan ma k'asa yayi da kai cikin kunya ya kalli kakarshi ya jawo kanta yace "Zo na fad'a miki a kunne."

Cikin kunne ya rad'a mata ita kuma ta bud'e baki tace "Iyeee, to kai ai duk gida ne, ah gaskiya nayi farin ciki da jin hakan."

Soueba ta kalla tace "Kinji fa ke, tuwo na mai na za ayi, dan yace dai *Amna* (kamar k'anwa take gareshi saboda mahaifinta da mahaifinshi yayan wa ne da k'anwa, ma'ana ita jikar alhaji ce daya haifi ubanta, shi kuma jikan Husseina ne wacce suke ciki d'aya da alhajin) yake so."

Tashi yayi ya fita wai shi kunya yake ji, ita kanta Soueba taji dad'i daya kasance Amna ce yake so ba 'yar uwar haihuwarta ba *Hamna*, duk da ciki d'aya suka rayu kuma uwa d'aya ta haifesu, amma...


Read / Download BADAKALA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album