Join Our WhatsApp Group

AKAN SOCIAL MEDIA Complete Hausa Novel Document by AKAN SOCIAL MEDIA


AKAN SOCIAL MEDIA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8395AKAN SOCIAL MEDIA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 25, Nov 2023

Author: Kausar M Hassan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 48.87 kb

File Type: txt

Views: 454+

Download: 100+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [1/6, 6:20 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA (YANAR GIZO)🕸```


```©Kausar M Hassan```


Page 1 to 10.


Bismillahi Rahmani Raheem!

Masoyana Ina baku hakuri akan rashin zuwan littafin *MUGU BAI DA KAMA*. Wannan ya farune saboda bayanai da nake tattarawa akai. Kapin zuwanshi ina maku sallama da wannan takaitaccen littafin nawa mai suna Akan social media (yanar gizo)


K'arar sakon daya shigo a wayantane yasata yin firgigit ta miqe dga zaune da take ta d'auki wayanta, sunan da tai saving dashi na "My one" ya fitah akai. Wani d'an karamin tsaki taja saboda wasu guntayen hawayen da suka zuba mata a fuska. Kanta ta kifah akan guiwowinta ta fara shiesiehkar kuka.
Dea2 wannan lokacin wata yar matashiyar mata ta shigo gidan, baqa mai matsakaicin tsaye, mai kyau da itah.
"Keko fadila mai yasa ki cikin wannan yanayin? Tun d'azun naketa rafka sallama gaki zaune kin kasa amsawa"?
Hawayenta ta share ta d'aga idanunta ta dubietah, cikin muryar kuka mai d'auke da nadama ta furta
"Farry ina cikin hatsarin ruwa, na shiga ukki na lalace"
Zaunawa farry tai ta dubeta cike da d'umbin damuwa
"Ke kuwa fadila mai yasa? Dan Allah ki deana fad'ar haka, kisani fa cewan komai na Allah ne, kuma duk abunda ya sameki Allah ya kamata ki miqawa ai"
Hawayenta ta k'ara shareware, ta dubie farry
"Farry na cuci kaina, naci amanar mijina da iyayena da kuma rayuwata gabad'aya"

Hannunta farry ta kama
"Look! Fadila idan bazaki fad'amin damuwarki ba billahil azim tafiyana zanyi"

Idanunta ta saukar kasa tare da tashi tsaye ta juya bayanta
"Farry, tun kapin inyi aure ina chatting da wani mai suna Adnan"
Farry ta tari numfashinta
"Adnan dai wanda nasani"
"Eh shi farry, tun muna chatting a 2go, facebook, muka dawo whtsapp, hr muka fara imo dga nan sai video call farry"
Dakatawa fadila tai tacigaba da cewa
"Adnan ya kasance abokin firata a online idan banga adnan ba bana iya yin komai, ya kasance ya fara jan ra'ayina muna video call, haka adnan zaisani in cire kayana tas shima ya cire nashi muna video call, babu abunda muke fad'a inba maganganun batsa ba"
Kuka yaci karfinta ta dakata ta cigaba da cewa
"Farry, tun banyi aure ba gashi ynxn nayi aure har na shekara d'ayah, amma na kasa deanawa. Duk ranar da banyi video call da adnan ba, farry ji nake kamar zan mutu. D'aki nake shigiewa inyita kuka har garin Allah ya waye, gani da miji amma bana bari muna kwana a daki d'ayah, wayata ko ina security code ne da itah"
Komawa tai ta zanah ta maida kallonta ga farry data saki baki take kallonta
"Farry bazan iyaba, dan Allah ki taimakeni inaso in deana, dan Allah"
Hannunta farry ta rike da itama d'in kukan takeyi
"Fadila! Dan Allah kicemin mafarki nakeyi ne ba gaske neba"
"Wallahi farida iyakar gskyr kenan, ki taimakeni dan Allah"...

**************
"Rashida"
D'agowa tai ta dubie mai kiran nata
Cikin murya ta fitsara ta amsa da
"Yes! Akuy damuwane"?

D'an murmushi mai kiran nata yayi
"Tun d'azun nake binki fa tundga makaranta kinsani kuma kin ganni amma kin fito kin kyaleni"
Daria rasheeda ta kyalkyale dashi ta kalleshi tundaga sama har kasa
"Chabb! Wallahi bazan aureka ba, kai bara kaji bana sonka ma, dubeka fa ko kyau bakada, yar motar nan ta hawa ma bakadashi. Ni mai kyau nakeso mai kud'i mai kuma motah ehe"

Tsaki rashida taja masa ta wuce ta gabanshi ta shigie gida ta maida kopa ta kulle...

```®Kausar Luv💞```
[1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸
(YANAR GIZO)```

```©Kausar M Hassan```


Page 11 to 20


Kai ya girgizah saurayin mai suna sani ya kama hanya ya wuce gida abunshi.


*Fadila*
Hannunta farry ta rike gam da jikinta ya hau rawa
"Kinga ki kwantar da hnklinki dan Allah, ynxn ina sauri buh in shaa Allah zan dawo sea muyi magana, kada ki fad'awa kowa"
Kai ta d'aga mata tare da share hawayenta, farry ta tashi ta fice dga gidan. Yayinda wayan fadila ya qara hawa ruri, again dai text msg ne dga adnan, hannu ta zura kamar ta d'auka kamar kada ta d'auka, jikinta ya hau rawa, tana d'auka yana kiranta a wayah.
Ilaharin hnklinta gaba d'aya ya tashi saboda tsabar firgici, da sauri ta kifa wayan kasa ta juya bayanta ta cigaba da hawayenta.********
Dea2 misalin karfe 2 na wannan rana, zaune take akan kujera wayarta na a hannunta tana cikin wani group mai suna
"Girke2 da kwalliya"
posting akai dea2 lokacin akan yanda mace zata rika gyara jikinta da kamshi kala2, da kuma wasu dabarun girki.
Sallaman da tajine yasata d'aga idanuwanta ta duba mai yin sallaman
Ganinshi da tai yasa ta d'an gyara zamanta tare da rufe datan wayanta ta maida kallonta gareshi
"Sannu da zuwa mijina, abun alfaharina, awa d'aya idan nai banganka ba ji nake kamar anshare wasu shekaru masu tarin yawa"
D'an murmushi ya sakar mata a fuska
"Matata rabin raina kenan, kisani cewan kece mallakin zuciyata, dake nake alfahari a kodayaushe"
Murmushi tai masa
"Bara in kawo maka abunci"
Tashi tai ta miqe zuwa kitchen yayinda ya d'auki wayanta ya shiga whtsapp d'inta ya fara dubawa, dae2 lokacin ta dawo ta ajiye masa abuncin akan carpet ta bud'e kolan ta fara zuba masa, towun shinkafa da miyan ganye.
"Wato dama nan ake koya maku girki da kwalliya ko"?
Murmushi tai masa
"To kadea gani, groups d'inne ynxn kowanne da nashi fa'idah, ka manta na fad'amaka cewan har wani group ke garemu mai suna Matambayi baya 6ata? Gskya sunayin posting mai ma'ana kuma ynda kasan makaranta haka ake tafiyar dashi"
Ido ya kanne matah
"Kai salmana, nidea ngdewa dya had'ani da matar kirki, ynx dea a bani abunci inci sea inyi wanka dan ynxn sea kuma wata safiyar nida fitah"
Murmushi salma tai
"Yes sir angama"


A wannan gida rayuwa suke cikin jin dad'i wal2 da kirkiza, basuda wata damuwa, saboda a cikinsu kowanne yana kula da hakkin d'an uwanshi a bisa gskya.


```Fadila```

Karfe 9pm dea agogo ya buga, fadila ce zaune a falonta tana kallon TV, ta baya taji an rungumeta sosai. Cikin sanyin murya ta furta
"Haba zaid dan Allah, meye haka ne"?
Murmushi yay
"Fadila wea dan Allah halan ba auren soyayya mukai ba? Ki duba kigah yau shekara d'aya kenan da aurenmu amma kin kasa sakin jiki dani, a kullum kina d'aukata kamar wani baqo"
Fuska ta d'an saki kad'an
"Em am wallahi zaid ba haka bane, kawea bana jin dadin jikina ne"
Da sauri ya juyu ta bayanta ya fuskanceta
"Fadila mai ke damunki? Sannu kinji taso muje ki kwanta naga kamar jikinki da zafi"
Wayarta ta d'auka zaid ya rika hannunta ya shiga da ita d'aki, ya kwantar da ita akan gado, bargo yasa ya rufeta, ya kashe mata wutar d'akin ya fitoh.
Fitarsa baifi minti 10 ba ta tashi ta kunna light d'in d'akin sakamakon kiran da adnan ke matah. D'akin ta maida ta rufe da sakata.
D'auka tai tare da zaunawa kan gado. Yana kallonta tana kallonshi. Adnan ya fara magana
"Fadila! My one, talk to me plzz"
Kallonshi tai
"Adnan dan Allah ka fitah rayuwata ka kyaleni nifa ynx matar aure ce"

Murmushi adnan yay
"Fadila nasani mana, amma kema ai kinsan ina sonki sosai, dan Allah ki deana wannan maganar, ynxn dea inaso ne kimin kiss"
Kallonshi ta karayi da hawayen dake zuba a fuskanta
"Adnan plzzz dan Allah ka kyaleni"

Fuskarshi wasai ta nuna alamun damuwa
"Baby dan Allah ki deana kuka, idan kina kuka ji nake kamar jinina ne ke fitah dan Allah, look, zo inyi hugging d'inki"

Kalamai adnan ya rika ratsawa fadila wanda har yasata ta kara aikata wannan aiki.```Rashida```
Wayarta ce a hannunta, tayi zugum tana kallon group d'in da take ciki mai suna
"Novels world"
Typing ta d'anyi kad'an
"Ummi Aisha muna jira pls a cigaba da sanadin gata"
Bayan kamar minti 3 da faruwar haka sea gashi anyi posting page 30 to 35. D'an Murmushi tai ta rubuta
"Tnx" ta aika ta gyara zamnta ta fara karantawa, bayan ta kammala wannan episode d'in tai murmushi, a cikin zuciyarta ta furta
"Bazanyi aure ba sea mai kyau kamar Haydar d'in cikin littafin Khaleesat na maman shakur, gashi na kamu da soyayyar Anas (blue eyes) gashi ina son mai kud'i kamar barraq.
Fuskarta ta yamutsie
"Mtsww ya Allah ka cika min burina ta furta a fili, ta cigaba da chatting d'inta.

```salma```
Addu'ah sukai tare da kwantawa akan gado d'aya laqamie da juna.


```Rashida
Salma
Fadila```

Ya rayuwa zata cigaba da kasancewa a wad'an nan gidaje"?

```®Kausar Luv💞
[1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIL MEDIA🕸
(YANAR GIZO)```


```©kausar M Hassan```Page 21 to 30

Washe garin ranar da asuba, salma ce ta farka dga bacci, kasancewar yau sun d'an makara ne yasa ta tashi mijinta mai suna bilal
"Yaa Bilal ka tashi zamu makara bamuyi sallah ba, tashi yay suka d'unguma zuwa toilet, yayinda sukai alwala suka dawo d'akin dmn yin sallar asuba.


```Rashida```
Tashi tai dga kwanciyar da tai, tai miqa dea2 lokacin an kammala sallar asuba, bayi ta shiga tai alwala ta fitoh tai sallah kapin nan ta koma bacci.


```Fadila```
Kayanta ta tattara gefe tana mai jin haushin kantah, ta tashi ta shiga toilet tai wanka har guda 2 kapin nan ta fitoh ta chnza kayan jikinta ta maida gabanta gabas tai sallan asuba, ta tsaya tana rokon Allah akan ya shiryata ya kuma sa ta daena wannan mummunar d'abi'ar.
Dea2 lokacin zaid ya kwankwasa kopar d'akin, hannu tasa a fuskanta tai maza ta mike ta d'an kimtsa gadon kapin nan ta duso kopan ta bud'e. Kallonta ya tsaya yanayi akan kopar
"Fadila y jikin? Hope dea ynxn kinji sauki ko"?
Murmushi tai masa
"Alhmdlh zaid naji sauki, ynxn dea muje in had'amana breakfast"
Murmushi yay ya rungumeta
"To ki bani hot kiss sea muje in taimaka maki"
Matsawa tai tare da furta
"Plzz zaid, ka barni mana"
Murmushi yay
"OK matar laushi, less feeling less emotional, muje"

Haka suka kama hanya tana gaba yana bayanta har suka isa kitchen, tare da taimakawarshi ta kammala had'a masu breakfast d'in.


```Salma```
Kusan karfe bakwai na safe ta kammala had'a masu breakfast d'insu, indomie ta dafa masu, akasa ta dire farantin sukayi basmallah suka fara cin abuncin, suna fira irinta masoya wasa da daria.


```Rashida```

Bayan ta kammala karyawa ta shirya tsaf cikin uniform d'inta ta kama hanyar zuwa makarantar islamiyya kasancewar bana ta kammala secondary. Kasancewar dga gidansu zuwa makarantar akuy yar tazara.
Ta kusa isa a mkrnta taji ana yimata horn, juyawan da zatai ta hangi wani santalelen saurayi a cikin mota, batasan sanda tai wata irin murmushi ba
Saurayin saukowa yay dga motan
"Yan mata sannu ko"?
Fuska ta d'an gimtsie
"Yauw, sannu"
"Plz idan bazaki damuba ni sunana abdulmaleek, amma ana kirana da abdul, zanso ki bani lokacinki, dan wallahi kin burgeni kuma ni bada wasa nazo ba da maganar aure nake tafie"

Kallonshi tai tare da k'arewa motarshi kallo
"Tohm yxn dea kaga makaranta zan tafie"
"Ba damuwa, mss...??
"Rashida"
"Yauwa rashida, plzz ki bani number d'inki zuwa idan kin dawo sea muyi magana ko"?
Fadamashi lambarta tayi shi kuwa ya d'au katuwar wayarshi fara tas ya fara rubutawa akai, bayan ya kammala yay saving ya danna kira.
Vibration wayanta dake cikin jaka ya farayi
"Yauwa ta shigo"
Juyawa yay zuwa motanshi ya shiga
"Zuwa karfe 1 zan kiraki nasan kin zama available, ki kula da kanki rash, I love u"
Wucewa yay abunshi yayinda rashida tai tsaye tana jin kamar mafarki takeyi.
"Yeeeeh! Abun kamar a novel wallahi, mai kyau mai kud'i yana son yar talakawah, yeeeee! Burina ya cika. Zan wataya inyi walkiya kan daula.
Anya kuwa rashida rayuwar novel d'aya take data zahiri kuwah? Inji kausar. Zamu gani dea.

```®Kausar Luv💞```
[1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸
(YANAR GIZO)```

*Page 31 to 40*

```Rashida```

Karfe d'aya na rana, kira ya shigo a wayan rashida, murmushi tayi, ta d'auka tare da karawa a kunne
"Assalamu alaikum"
Abdul yay sallama
"Amin alaika salam, gskya kam kana da cika alkawari"

D'an murmushi yay
"Gskyne amma kinsan abubuwa suna zuwa haka ai, yxn dea kimin misalin gidanku idan na tashi zuwa karfe 7 na dare zanzo in shaa Allah"
Fari da ido tai kaman wanda ke ganinta ta fara yimasa bayani
"Well! Nagane sea kinganni"
Haka sukai sallama rashida dake zaune ta fitah wajen tsakar gidansu
"Innah!!!"
"Ke lapiya kike kwala min kira haka"?
Ajiyan zuciya ta sauke
"Inna kinsan na ta6a karanta maki labarin littafin martaba ta na ummi aisha ko"?
Kai ta d'aga tare dayimata wani irin kallo
"To inna abun kamar haka, yau na had'u da wani handsome, zuwa darema yace yana nan zuwa, shiyasa kiga inna na dage na iya abunci kala2 saboda tsaro"
Murmushi innah tayi tare da cewa
"Allah ya kyauta"


```Fadila```
Bayan tayi wanka tayi sallah ta d'an kishiengid'a kanta akan gefen kujerah.
Ji tai gabad'aya batajin dad'in jikinta, wayanta ta d'auka kaman zatai kirah, sai kuma ta koma ta ajiye, bayan kmr minti 2 haka ta k'ara d'auka ta danna kiran number d'in adnan. Video call.
Murmushi yay
"Kyakyawa ykk? U miss me"?
Kai ta d'aga masa
"Yes! Adnan plz mai yasa bazaka fitah rayuwana ba"?

Ido ya kanne mata
"Ni adnan in rabu dake fadila kema kinsan abune wanda ba xai taba yuwu ba, just relax ki cigaba da kulamin da kanki kinji"

Hawaye suka zuba mata a fuska
"Adnan kasan cewa zamu mutu kuma zamu koma ga mahallicin mu, abunda muka aikata dashi Allah zai mana hisabi, mai yasa bazamu deana ba"

Tsuke bakinshi yay
"To dga yau kada ki kara kirana a waya, zan goge number d'inki a cikin wayana in koma gogeki a cikin zuciyata da kuma rayuwata"

Jin kalamanshi da fadila tai yasata cikin tashin hankli, stammering ta fara yi, kapin ta bud'e baki ta bashi amsa ya kashe wayan tare dayin tsaki.
Ido tabi wayan dashi da idanunta da suka chanza kala, take ta maida kiran nashi, har sau 3 kiran na shiga yana tsunkewa bai d'auka ba. Jikinta ya hau rawa gabad'aya ta fita hayyacinta,...


Read / Download AKAN SOCIAL MEDIA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album