Join Our WhatsApp Group

BABANA DA MIJINA Complete Hausa Novel Document by BABANA DA MIJINA


BABANA DA MIJINA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12494



BABANA DA MIJINA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: fertymerh xarah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 810 732 0127

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 69.55 kb

File Type: txt

Views: 964+

Download: 188+

Last download: 1 day ago

Description/Story: BABANA DA MIJINA
Fertymah zarah
Ebook creator:- Shuraih Usman

Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya
saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com
Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download
it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at
www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading

Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga
wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group
a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan
wannan nombar 08170707521
Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan
adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah
muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu

Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a
whattsap asha karatu lafiya

Hakkin mallaka (m) fertymarh Xarah

[2/28, 7:43 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

1

Agogon alarm dake manne a bangon falon ya buga qarfe ďaya dai dai na dare,

Ta ďauke kanta daga kallon agogon ta maida jikin TV tana kallon aljaxeera....

Xaune take akan sofa tana sanye cikin rigar barci mai tsantsi fara sol,

Ba wata muguwar kyakkyawa bace can, tana da kyau dai dai nata sai dai kuma mace ce Mai aji na
qarshe,

Akan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haifeta da Ita tayi mata kyau kasancewarta farar
mace

daga nan xaune taji tsayuwar motar mahaifinta, idan da sabo ta saba da wannan hali na mahaifinta
da mijinta na fitar dare ko dawowar dare, gwanda mahaifinta ďan siyasa ne shine mataimakin
gwamnan birnin kebbi, sukanyi meeting ďin dare akai akai wataran ma a gidan sukan taru suyi tana
jiyo hayaniyar su daga nata gidan,

Bai jima da tsayuwa ba taji ya shige sashensa, tayi hamma haďe da yin miqa cikin wani irin yanayi
na barci dai dai lokacin daya shigo falon da qatuwar kwallo a hannunsa,

Ko kaďan bai raxana da ganin matar tasa a Wannan lokacin tana xaman jiransa ba Co's ta saba,

ta xuba masa idanuwa tana kallonsa cikin wani irin yanayi fuskarta ba walwala, ya cillar da
Kwallon dake hannunsa haďe da xare socks ďin qafarsa duk Idanunsa akan ta

har ya gama cirewa yayi sassanyar ajiyar xuciya, duk hankalinsa da attention ďin sa yana kanta, ya
sami kansa da ruďewa, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idonta Wanda ba duk mata Allah
ya mallakawa ba, ya nufeta cikin wata irin tafiya ta izza cike da taqama ya xauna a kusa da ita haďe
da ďora hannunsa akan nata hannu,

Kiyi haquri Iman kamar yanda kike a kullum wasan kwallo wani abu ne d.... yayi shiru sakamakon
wani kallo da tayi masa,

A iya sanina wasan kwallo anayinsa ne da rana ko da safe amma ku bansan wane irin Wasa ne naku
da sai dare kukeyinsa ba,

Ya tsura mata ido,
Iman baki yarda dani bane, ko kina xargina?

Ba xargi a nan illah gsky nake son ka gayamin, bayan albashinka na banki kana nufin duk wannan
dukiyar daka tara duk akan kwallo ne ? Ya gyada kansa

Kwarai Kuwa, kije ki tambaya kiji duk ďan kwallo na asali Mai fita waje yana ball ba qaramin kuďi
suke samu ba, ki yarda dani Mai sunan mamana bani da wani mugun hali Wanda xai cutar dake,
tayi shiru kawai idanunta sun kawo kwalla ta kasa yarda da mijinta da mahaifinta, tsakanin *babana
da mijina* baxan ce ga Wanda yafi wani so na da kula dani ba, ga kuďi har batason ganin su
kasancewar tana xargin masu su, ta goge hawayen fuskarta, yana kallonta cike da so da tausayinta
yana jinta har cikin ransa shi kansa baisan wane irin so yake wa Fatima ba, ya riqo tafin fuskarta
haďe da sanya yatsansa yana share hawayen fuskarta,

Babban tashin hankalina shine naganki cikin damuwa, har sai yaushe xaki yarda dani Iman, idan
baki yarda dani ba Waye xai yarda dani, wallahi ni ďan kwallo ne kidaina xargina,

taja numfashi haďe da Sakin malalacin murmushi tana kallonsa

na yarda da kai mijina, amma Ina so ka kiyaye kayi a hankali da duniya ka Kuma ji tsoron Allah,
jikinsa yayi sanyi

Yace Insha Allah Iman, ya riqa hannunta suka tashi da kansa yaje ya kashe tv da komai, tana tsaye
sarqe da hannayenta a qirjinta tana kallonsa cikin so da qauna, ya juyo yana kallonta
'let's go... ta juya yabi bayanta, har suka hau step ba mai mgn a cikinsu kowa da saqe saqen
xuciyarsa,

ďakin qanwarta Fauxiya ta nufa ta buďe dakin a hankali ta shiga, ta same ta tayi barci sosai ďakin
ya ďauki sanyin a.c ta qudundune guri ďaya da alama tana jin sanyi sosai,ta juya tana kallon sa,

'you see Fauxiya bata jin magana duk ynda nayi da ita akan shan sanyinnan bataji,

Ahmed yaje ya kashe a.c ďin kana ya ďauki blanket ya lulluba mata bayan ya gyara mata kwanciya,
ta matsa ta gefenta ta xauna, addua tayi mata kafin su bar ďakin,

Kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka, yana shirin barci ta shigo da coffee a hannunta, ya karba yana
kallonta da murmushi,
'thank you wify ,tayi murmushi ta xauna bakin gado tana kallonsa,

Yana gama shan coffee ďin ya juyo ya sumbaceta a goshi yana fadin gudnyt, kafin tayi mgn har ya
faďa Kan gado ya kwanta, ta bisa da ido cikin tausayin kanta hawaye suka xubo mata,

Wannan wace irin rayuwace, wane irin aure ne wannan, am a doctor, mijina yana aikin banki, idan
ya fita tun da safe baxan qara sa shi a ido ba sai 6pm da yayi wanka yaci abinci ya fice sai 1 ko 2am
wataran ma sai da safe take ganinsa ya dawo wai yaje training ďin kwallo,

Yau satinta biyu rabonta dashi tana buqatar mijinta tana da haqqi akansa bai damu ba saboda ita
tana da buqata sosai ba Kamar shi ba ko xasuyi wata a hakan baxai damu ba,

A matsayina na matarshi abokiyar rayuwar sa bashi da lokacin da xai xauna dani and sai dai kullum
idan nayi masa Mgnr fitar dare yace bana yi masa uxuri da yawan ayyukan dake gabansa a banki,
da dare Kuwa xaije training na kwallo,

Ban rasa ci ba ban rasa sha da sutura ba amma na rasa kulawa da soyayyar mijina abin tambaya
anan shi wannan shine ginshiqin auren, am not satisfied with my husband, bama Wannan ba rashin
xamansa gida...

Babana ďan siyasa ne shi ba mai xama bane idan baya gari yau gobe yana wata qasa, idan yana gari
shima baxaka ganshi ba sai cikin dare yake dawowa, idan taje mashi da complain na fitar mijinta sai
dai yace
'haquri xakiyi tunda koni mahaifinki kina ganin ba maxauna bane, muna meeting sosai Mai
muhimmancin acikin dare, tunda ya gayamiki wasan kwallo suke xuwa kiyi haquri ki barshi komai
lokacine, ta share hawayen ta cike da mamakin kalaman mahaifinta,

shekara biyu da rasuwar mamana, banda kowa a duniyar nan bayan *babana da mijina* sai qanwata
fauxiya, bansan wa xan kaiwa kukana ba ya share min shiyasa ko aiki naje banda tunani sai na
*babana da mijina* babu wanda baya fuskantar challenge(qalubale) a rayuwa, and is up to us to
accept such challenges mu bita da duk fuskar da rayuwa ta xo mana....

Jin shiru bata kwanta ba ya juyo yana kallonta,

'lafiya Iman, me kike tunani, ta tashi da sauri tana fadin ba komai ta nufi toilet, ta saki ruwa tana
kuka sosai yanda baxai jiyo ta ba......

*Dedicated dis buk to*
*Rabi'atu Sk Mhs*
*Sadiya Lawal bala*
*Aysher Gambo*
[2/28, 7:50 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

2

Asalin labarin......

Ahmed mutumin jihar Birnin kebbi,

Daga kallo na farko mawuyacin haline ka gane qabilar da ya fito Hausa ko Fulani, wani mutum
ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa,

Mahaifinsa malam Abubakar buba malamin islamiya ne mutum ne mai ilimin addini, haka mutanen
unguwa suna tsananin girmamashi,

Sai mahaifiyar Inna, shika dai ne ďa a gunsu, bayan rasuwar mahaifinsa suka shiga wani hali na
rashin babu, gashi qarami a lokacin primary 6,

Ba Mai taimaka masu wani sa'in ma Inna ke xuwa wankau ta sami kudin da xata ciyar dashi, shi
Kuma Ahmed a rayuwarsa yana son karatu shiyasa yake dagewa akan karatun, he is gifted tun yana
qaraminsa malamai sun San dashi,

Ahmed yayi karatunsa da taimakon mahaifiyarsa dake siyarda qarfinta dan ganin farin cikinsa,
lokacin da ya shiga babbar makaranta I mean higher institution duk qaddararta sai da ta saida ganin
ta cika masa burinsa,

Alhamdulillah ya kammala degree ďin sa lfy duk aikin dayaje nema na gwamnati bai samu ba, duk
inda yaje nema baxai samu ba, abokan karatunsa Waďanda iyayensu suke da kuďi sun fara aikin
banki saboda suna da ďaurin gindi a gwamnati wasu ma sun fita waje neman wani ilimin, shikam
degree ne iya qarfinsa yana so ya sami aiki dashi ko yayane dan ya tallafi mahaifiyarsa....

Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi an kwantar da Inna asibiti babu kudin magani Babu babban
tashin hankalinsa kamar ciwonta ulcer da kuma hypertension, duk inda ya buga bai sami kudin ba,
abokansa dake bashi aro sun daina saboda baya biya,

Ya qara komawa asibiti kai tsaye ya nufi inda likitan ya roqesa ya taimaka ya duba mahaifiyarsa
fisabilillah saboda bashi da kuďi, fafur likitan yaqi har kuka yayi wani mutumi dake xaune office
ďin shima yaxo likita ya dubashi ya dubi likitan,

Nawa ne kudin maganin,
Dubu biyar ne fa bawani yawa, kamarsa baxai iya biyawa mahaifiyarsa kudin magani ba, baxaije ya
nemi aiki ba, muma karatu mukayi muka sami aikin,

Ahmed ya dubesa, ko xaka daukeni aiki ne, ko wane irine inaso indai xaka biyani na kula da
mahaifiyata

Likitan yace bama daukar mutum aiki sai mai ilimi kai kuma baka dashi,

Ahmed yace inadashi nayi karatuna na kammala na nemi aiki ban samu ba yaciro takardunsa ya
nuna masa, likitan ya duba sosai Ahmed ya cancanci a daukesa aiki saboda matakin karatunsa
Kuma result ďin sa mai kyau ne...

Xan iya samama aiki da wannan result amma sai idan xaka iya biyan dubu hamsin, kasan aikin
gwamnati ynda yake Kuma a banxa baxaka sami aiki ba sai ka kashe kuďi....

Ruwan cikinsa na soma qugi Wanda bai sami dubu biyar na magani ba Ina xai sami dubu hamsin a
ynxu, ya karbi takardunsa ya juya ya fice yana hawaye,

dakin da aka kwantar da mahaifiyarsa ya nufa har lokacin bata farfado ba barci takeyi, qarqashin
pillow ďinta ya cusa takardun xaije ya nemo kuďi da qarfin jikinsa ya juya ya fice....

Ya fito harabar asibitin ya haďu da wannan mutumin na ďaxu ya kirasa yaje,

Sannu saurayi,
Ahmed ya qara gaida mutumin,
Na ganka kana da hankali sosai Kuma da ganinka xakayi jarumta xan baka kuďi ka taimaki
mahaifiyar ka kakuma sami na aiki indai xaka iya min aiki,

Wane aiki ne xan iya....ya faďa muryarsa na rawa

Mutumin yace ka taba riqa bindiga? Ahmed ya girgixa kansa yana kallonsa cike da mamaki,

Xaka sami kuďi sosai indai xaka iya shiga cikinmu, ni babban ďan ta'adda ne nayi irin Wannan
rayuwar taka ta talauci da haka hr na rasa iyayena, saboda rashin kuďi gurin haihuwa matata ta rasa
ranta, bansan wace irin rayuwa muke ciki a ynxu ba da masu kuďi basa taimako dan Allah, Mai
kuďi daga shi sai xuri'arsa, ďan siyasa ma haka, neman aiki ynxu baxaka samu ba sai dai su bawa
yan uwansu, shugabannin mu na Yanxu basa aiki kamar na da, shin miye laifin talaka? da haka na
nemawa kaina aiki nakewa masu kuďi fashi, inada yara biyar duk aka sami kuďi kowa Ina bashi
kason sa da haka nake gayyatar ka kashigo cikin xaka sami kuďi Kuma xakaji daďi....

da'ace mutumin ya lura da yaga xufar dake ambaliya a fuska da jikin Ahmed, yayin da gudun jini ya
Katse a jikinsa, hanjin cikinsa ya dunqule guri ďaya

ďan fashi kenan xai xama, barawo Mai daukar haqqin mutane haqqin da ba nasa ba, duk wahalar
nan da yayi wajen neman ilimi da kwalinsa sai ya qare a sata.... tor miye amfanin karatun da yayi?
Wata xuciyar tace rayuwar mahaifiyar ka fa, kana nufin karatun yafi tane?
[2/28, 7:51 PM] +234 810 732 0127: BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

3

Shiru yayi yana kallon mutumin sosai xuciyar sa sai bugawa take yayinda take ingixa sa akan ya
amincewa mutumin ya sami kudin da xai Kula da Inna, tunda yan uwansu ma sun gujesu basa
taimaka masu da komai tunda ba su da,

Baya manta sanda mahaifinsa na da rai yan uwansa kamar xasu haďiye su saboda kulawa Kuma
saboda mahaifinsa mutum ne dayasan haqqin ďan uwa yake biya masu buqatocinsu, yau gashi babu
ran mahaifinsa sun gujesu saboda basu da komai, mahaifiyarsa na kwance ba kuďi Kuma ba Wanda
xai iya xuwa ya xauna da Ita asibitin sai shi.....

Wannan dalilin ne ya Sanya Ahmed amincewa ya karbi tayin oga nas Wanda yayi matuqar jin daďi
da ya amince kai tsaye ya bashi dubu goma da address ďin inda xai same sa....

Bayan ya karbi kudin jikinsa na rawa yaje pharmacy dake nan asibitin ya siyo magani ya nufi inda
mahaifiyarsa take,

Yanda ya sameta hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya xaije ya Kira likita ta riqo rigarsa, da kyar
take iya mgn

Baxan tashi ba Ahmed, buri na bai cika ba inganka yau ka xama wani mutum da duniya xata so
kuma tayi alfahari dashi, kayi haquri da duk yanda rayuwa ta xoma, ka nemi halal, ka Kula da kyau
kada kabari ruďin duniya da abinda ke cikinta ya ci galabarka,

Hawaye yake sosai, jikinsa na rawa hankalinsa yayi matuqar tashi da maganganun mahaifiyarsa,

Baxaki mutu ynxu ba Inna sai nayi maki gata, ya banbare hannunta da kyar ya fita da gudu neman
likita,

Ko kafin su xo rai yayi halinsa, Allah ya gafartawa Inna......
*

Alhaji Abdallah mutumin xuru ne qaramar hukumar Birnin kebbi,

Babban mutum ne mai ji da kansa Wanda duniya ke damawa dashi a siyasa, shine mataimakin
gwamna a Yanxu kafin ya sami matsayin da yake a yanxu sai da yayi fafatukar duniya da shige
shige Wanda Dama a Yanxu idan mutum na neman cimma wani buri nasa yakan manta Allah ya
kauce hanya, a taqaice sai da ya bada jinin ďaya daga cikin yaransa kafin ya sami kujerar da yake
Kai a yanxu,

Ya'yan shi biyar mata biyu maxa uku sai matarsa Mami, mace mai kirki da mutunta ďan Adam..

Naxir shine babban yaron sa, sai fatyma(iman), Musa, Ismail da qaramar su Fauxiya,

Acikin yaran kaf ya fison Fatima da Fauxiya ko kaďan baya son Abinda xai tabasu, soyayyar da
yake nuna masu daban ce da ta sauran yaransa.......

Kuďin sa Kuwa baa magana, yana da dimbin tarin dukiyar da yabayarda ya'yan sa uku duka maxa,

Mutuwar su tana xowa Mami a baxata, babu ciwo babu komai xaka ga kumfa na fita bakin su daga
nan Kuma rai yayi halinsa, da haka ta fara rasa yaron ta Naxir...

Naxir ba qaramin mutum bane, a shekaru yabawa 26 har an nema masa mata, fatyma Kuwa a
lokacin ba Mgnr aure a gabanta she is 24 karatunta ta sanyawa gaba, she want to achieve the goal,
bata da buri a duniya kamar ta wayi gari yau ta ganta cikakkiyar likitar mata tana jin haushin yanda
mata ke Kai matsalolinsu da sirrin jikinsu ga likita namiji,

Sanda babansu ya fara siyasa a lokacin komai ya soma sauyawa daga rayuwar gidan na rasa babban
ďan gidan, sosai Mami ta shiga damuwa shi kansa...


Read / Download BABANA DA MIJINA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album