Join Our WhatsApp Group

TAFIYAR DARE Complete Hausa Novel Document by TAFIYAR DARE


TAFIYAR DARE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23391



TAFIYAR DARE

Reading Time: 1 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Abdul King Article ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 124.59 kb

File Type: txt

Views: 681+

Download: 206+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: TAFIYAR DARE
MAYYUN JINI
Na Abdul King Article
Ebook created by Shuraih Usman
Ebook publish by http://www.hausaebooks.cf
TAFIYAR DARE 2
MAYYUN JINI
AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE
EPISODE 1
PAGE 1
Dare mahutar bawa, idan lokacin ka yayi dole a tareka,
dare mahutar bawa, idan kazo dolene komi ya samu
akasi. Dare mahutar bawa, duk wanda bai zauna wuri
daya ba to bayada banbanci da matacce.
Wannan magana haka take ba tantama, nasan dolene
kayi mamaki yadda na fadi wadannan zantuttuka masu
rudani da tafarfasa zuciya. Amma wannan ya farune
sanadiyar wani bakin al amari daya taba faruwa a gareni
shekaru da yawa, wannan al amari ya farune a cikin dare
kuma ya kare a cikin dare. Sanadiyar hakane naga ya
kamata in bayyana kadan daga faruwar wannan abu ba
don komi ba sai dai domin kaima ka kiyayi dare domin
gudun watarana.
Sunana anisa, amma akan kirani da baby, a wannan
lokaci ba abunda na rasa na jin dadi daga gidanmu
domin abbana ya tanadar min duk wani abu na jin dadi
da annashuwa, amma kuma duk da hakan ko kadan ban
damu ba. Babban abunda ke batamin rai shine abba baya
bari na fita ko kofar gida, idan kaga na fita to makaranta
zanje domin duk wani abu da ake bukata akwai masu
aiki. Saboda haka su ake sawa aikace aikacen gida.
Inada waya babba ipone x, sai kuma laptop dita HP, kai in
takaicemaka labari harda mota tawa inada amma ko
kadan bana moriyarta sanadiyar bana yawo, daga
makaranta sai makaranta, kai ko biki idan zan fita sai
abba yayi min nasiha cewa in kiyaye, wannan abu na
mutukar batamin rai sai dai ba yadda xanyi, a duk lokacin
danaga kawayena suna sharholiyarsu abun kan mutukar
burgeni, sai naji dama ace inada wannan damar ai da
shikenan.
Bako shakka uwaye sun cancanci yabo, godiya, karamci,
da kuma girmamawa. Duk wanda bai girmama uwayensa
ba to yayi asara tun a nan duniya. Duk abunda abbana ke
horar dani gaskiyane, ni a tunani na yana cutar dani
amma daga baya sai na gano ba haka ba. Bako shakka
abba na mutukar sona so na hakika son da duk wata ya
mace zataso ace abbanata na mata. Na gano hakan ne
sanadiya wata tafiya data kama mu a cikin dare nida
kawayena. Saboda haka bari in baka labarin wannan
tafiya da kuma makasudinta.
PAGE 2
Anisa ce ke zaune cikin wani katafaren falo cikin jin dadi,
fuskarata cike take da annashuwa da walwala. Kai da gani
kasan diyar masu hali ce tun daganin shigar ta. Dan
lemon tane exotic a kusa da ita sai wani cup na glass rike
da hannunta, idan tadan kurba lemon sai ta fincike wani
cake dake kunshe a cikin wata leda. Idanunta ko kyaftawa
basayi sanadiyar ta kurawa tv idanu sai kyalkyatar dariya
take kai kace mahaukaciya.
" Laaaaa, shegiya baby hala miye kikeci haka kina dariya
sai kace aJmaryar da za a kai gobe? "
Anan anisa ta daga ido sai tayi arba da kawarta. A guje ta
sheko suka rungume juna cikin murna. " Amma zee
bakida kirki ko kadan,wai ace kinyi graduating amma ko
flashing ba za ayimuna ba." Haka anisa ta fada tare da
jawota.
" Haba kawata kiyi hakuri mana, ai da kin san abundan ya
faru da bakice haka ba." Cewar zee tana murmushi.
Anan anisa ta wani karkada idanu tare da yi mata kallon
uku saura kwata. " Humm, dama haka kike, ai dama
nasan dole ki manta damu tunda kin samu kawaye a can
ko. Mutuniyar banza." Anan anisa ta fita falon. Bata jima
ba sai gata ta dawo da wani cup. " Yauwa, bari na zuba
miki lemon kema kisha ko kyaji gardi." Anan anisa ta
zuba mata lemon ta bata. " Saura kuma kice mun bazaki
shaba."
" Au, har na isa." Inji zee bayan ta karbi lemon. " Kedai
kinason exotic, ni kodan bai yimun ba, balantana yanzu
fa akwai drinks na yayi amma ke kullum ancient ce.
Bakauya kawai."
" Iyee, kina nufin ni bakauya ce?" Anisa ta tambaya.
" Tab, to ke a tsammaninki yar birni ce? Mai bleaching da
garin kwaki irinki." zee ta bata amsa.
Dariya sukayi tare da kallon juna suna taba hannu. " Keda
ko waya bakida, amma ni kike cema bakauya." Anisa ta
fada cikin wasa.
" E naji dai, ai waya nice banso samu ba, kema kin san
ruwa ba sa an kwando bane, zan iya sa samarina su siya
min duk wadda nakeso." Inji zee cikin daga murya.
" Samari kuma? Yaushe kika fara bin maza ban sani ba?"
Inji anisa.
" Au, dama baki sani ba? Ai karuwace kike kawance da
ita." Xee ta fada cikin bakar magana.
PAGE 3
" A a ni dai kada ki kaini inda yan kuda ke salati, nifa ba
haka nake nufi ba. " Anisa ta fada cikin lallashi.
" Ko ma me kike nufi ke acciki, nidai nasan duk yadda
goma ta lallace tafi biyar albarka. Ke da kike daure sai
kace tunkiyar masar. Idan ba tsoro ba mutum ya fita
mana, kinzo kin hakince cikin gida bakya ko tunanin aure,
ko kina nufin samarin a cikin gida zasu ganki suce
sunaso?"
" Kema fa kin san ba laifi na bane laifin abba ne." inji
anisa.
" To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita,
aiko yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da
shekaru kadan zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki
bola tunda kinyi wari." Haka zee ta fada tana hamma.
Cikin rashin tsammani ta banko wata tusa mai shegen
doyi ji kake buuuuuuuummmmm.
" Haba zee bagirman kibane, yanzu fa da ace su al-ameen
na nan da sunyi dariya." Cewar anisa bayan ta toshe
hancinta.
" Wai har kin sa gabana ya fadi, hala ina suka jene?" Zee
ta tambaya.
" Tare suka fita da abba, inaga harda mumy ta bisu wai
zasuje kasuwa." Anisa ta bata amsa.
" Kice ke kadaice a gidan yau?" Zee ta fada.
To kafin anisa ta bata amsa sai ga wata tusa wadda tafi ta
farko kara da wari. Anan zee ta mike da sauri." Wayyo
cikina, inaga exotic din nan da kiban ya bata mun ciki.
Nifa zawo nakejiiii." Anan zee ta nufi toiltet a guje. Anisa
ce ta danyi dariya saboda kallon data yiwa zee a lokacin
da take gudun. Wato kayan data sa ne suka matseta sosai
yadda gudun take amma ana ganin kome na siffar jikinta.
Anan anisa ta kara fanka domin warin yadan rage. To
bayan ta zauna ne sai tunanin maganar zee ta taso mata.
To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita, aiko
yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da shekaru
kadan zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki bola
tunda kinyi wari.
Bako shakka abunda zee ta fada gaskiyane fa, to yanzu
idan na cigaba da zama a nan to yaushe zanyi aure, burin
kowace ya mace shine tayi aure ta kuma haifafa. To
amma ni ko kadan banada wannan gatan. To yanzu yama
za ayi samari su ganni suji na burgesu idan ban fita ba?
Bako shakka dolene na dauki mataki sosai game da
wannan al amari. Anan tunanin anisa ya yanke sanadiyar
fitowar zee daga toilet.
PAGE 4
" Wai, har naji dan sauki." Cewar zee bayan ta kishingida
kan kujera.
" Duk kin cika mana wuri da shegen doyi." Inji anisa cikin
wasa.
" Ai ba laifina bane, ai dana sani da ban sha ba." Inji zee.
Anan ta mike ta dauki jakarta." Bari na koma gida
magriba ta kusa."
" Tun yanzu zaki fita?" Anisa ta tambaya.
" Hmmm, ni dai sai anjima kada ki bata min lokaci, gashi
ba yawo kikeyi ba balantana nace ki rakani." Haka zee ta
fada kafin ta fita.
Anisa binta tayi da kallo cikin zurfin tunani na wannan
maganar data yi mata. Haka zee ta fita cikin rangwada kai
kace jikinta ba jini da tsoka bane. To a wannan lokaci
tunanin anisa ya zurfafa har takai ta kashe tv saboda ji
take kamar ana damunta. Gaskiya dole na dauki mataki
akan wannan al amari, abu har yakai an fara yimin gori
akan rashin fita. Gashi kuma na girma amma har yanzu
ace banada yancin kaina. Haka dai anisa ta cigaba da
tunani daga nan kuma sai ta koma dakinta domin ta dan
yi bacci.
Kida ne ke tashi mutane sai rawa akeyi kowa ya kama
gwaninsa, maza da mata an cankude sai bushasha akeyi.
Anisa ce ke tafiya tana waige waige a cikin filin rawan. A
haka ne tayi kicibis da wata budurwa tsaye. " Yauwa,
dama ke nake jira." Haka yarinyar ta fada kafin daga
bisani ta dauko yuka da zimmar yanka ta. Anisa ce ta
kwala uban ihu daga nan ta farka firgigit. Ashe mafarki ne
takeyi. To a wannan lokaci mumy ce ta shigo taga lafiya.
Anan anisa ta fada jikinta tsorace.
" Me ya faru haka kike wannan ihu sai kace mahaukaciya,
to fa kada ince dai mafarkin ne kika karayi?" Mumy ta
fada bayan ta rungume ta."
" E wallahi mumy, a wannan karon dakyar nasha da ta
sokamin yuka." Anisa ta fada a tsorace.
" Kinga abunda nake fada miki ko? Idan akayi la asar ba a
bacci amma kinki. Ko yaushe sai kice wai yafi karfinki."
Mumy ta fada bayan ta tayar da ita." To yanzu sai kije kiyi
salla ga a can ana magrib."
PAGE 5
Da misalin karfe 8:30 PM ne su anisa suka nufi dinning
table domin daukar dinner. A wannan lokaci kowanensu
yayi sallar isha i. Al ameen ne da husna suka fara zaunawa
saman kujerun. Abunka da yara basa ko bari sauran jama
ar su karaso domin aci abincin tare. Cikin gaggawa suka
fara tura loma suna kyakkyatar dariya.
To bayan kowa ya zauna ne sai aka fara cin abincin tare. "
Nifa wannan mafarki na anisa kan mutukar ban mamaki
domin ban taba jin wanda ya taba yin irinsa ba. Kuma
ace abu ya kici yaki cinyewa." Haka daddy ya fada yana
kallonsu daya bayan daya.
" Hmm, kai dai bari, ai abu ya tsananta yanzu. Tunda har
da fizge fizge take yi idan tana bacci." Haka mumy ta fada
tana kallon anisa.
" Haba mumy fizge fizge fa kikace." Anisa ta fada cikin
rashin jin dadi.
" E to zan miki karyane?" Mumy ta tambayeta.
" Yanzu dai ya isa sai ku saurara muci abinci." Daddy ya
tsawatar.
A haka dai suka cigaba da cin abincin, to bayan sun
kammala ne kowa ya nufi dakinsa domin ya sarara. Haka
anisa ta shiga dakin cikin rashin jin dadi. A yau dai jikinta
ba karfi sai kace wadda aka zane. Laptop da dauko da
nufin kallo kuma saita ajiyeta gefe saboda tunanin daya
dameta. Tana cikin hakane sai ga husna ta shigo aguje
rike da littafinta na islamiya ( MUKARRAT TAUHID)
" Shegiya har kin ban tsoro, wai uban me ya kawoki dakin
nan?" Anisa ta fada cikin jin haushi.
" Wayyo sorry baby, wani fa assignment ne aka bamu
kuma gobe akeso mu bayar." Husna ta fada cikin
tausayawa.
" Ina fatan dai english ne?" Anisa ta tambaya.
" A a, amma duba ki gani."
Anan husna ta miko littafin. Anisa na kallon littafin
gabanta ya fafi. " Kwal uba." Ta fada da karfi tana kallon
husna. Anan ta fara tunani yadda zata bulloma al amarin
domin ko kur ani daga shekara sai shekata take karatunsa
a lokacin azumi. Gashi kuma bataso ace bata iya ba.
PAGE 6
" Baby ya naga kinyi shiru?" husna ta tambaya cikin
natsuwa.
" E ina dan tunani ne ai kema kin san cewa wannan littafi
na dade da kammala shi. Yanzu bari na biya miki."
Anan anisa ta rika mukarrat tauhid ba tare da sanin abun
cewa ba. Ita kuwa husna kallonta take tana saurare taji
me zatace.
" An karbo daga.... Ummm......" Muryar anisa ta fara rawa.
" Laaaaaa, bafa hadisi bane ji yadda take....." Husna ta
fada cikin dariya.
" Ke ubanwa kikewa dariya?" Anisa tasha toka.
Anan husna tasha jinin jikinta domin tasan data motsa
zataji masga.
" Wane wurine za a biya miki?" Anisa ta tambaya.
Anan husna ta buda mata dai dai shafin da takeso ta
karanta mata. Cikin rashin tsammani sai sukaji an banko
kofar da karfi. Juyawa sukayi da nufin ganin ko waye. Ai
kuwa ba kowa ceba in banda halina wato kawar anisa.
" Me kuke karatu haka?" Ta fada tana taku dai dai. Basu
amsa mata iyaka dai sun bita da murmushi har ta karaso
wurinsa. To anan suka taba hannu cikin jin dadi. Batayi
wata wata ba ta fizge littafin tana dubansa. " Anisa,
yaushe kika zama ta kwarai, wai kece da wanan littafi
kuwa?" Halina ta tambaya cikin mamaki.
" Hmm, ai kema kin sani ba saina fadaba. Nifa rabona da
arabic tun..... " Anan anisa tayi shiru bata iyar ba don
kada husna ta gane halin da ake ciki na cewa bata iya
karatun ba. " To yanzu tun da Allah ya kawoki ai shi kenan
kin hutar dani sai ki fada mata." Cewar anisa cikin
murmushi.
Kasancewar halina mai ilimin addini ce, cikin kankanin
lokaci ta karbi littafin ta fashema husna shi har saida ta
fahimci abunda ake magana akai. Daga nan kuma ta
taimaka mata wurin amsa assignment din da aka bata.
Anan husna ta karbi littafinta ta nufi waje bayan tayi
godiya. Wannan abu da halina tayi ya mutukar burge
anisa domin tasan cewa idan da bata zoba. Tofa yau da
kunya ta kasheta.
PAGE 7
" Amma fa kawata kin ceceni, yau inaga da baki zoba da
sunana gawa." Anisa ta fada cikin dariya.
" Au wai kina nufin bazaki iya karanta wannan littafin na
yara ba?" Inji halina.
" Wai na yara! Kajita da wata magana." Anisa ta fada tana
kallonta.
" Wai ya akayi kikasan ina nan?" Anisa ta tambaya.
" Daga shigowata na iske su mumy a falo, to bayan mun
gaisa ne saita fadamin cewa kina nan daki." Halina ta
amsa.
" Gaskiya ilimin addini yayi, yanzu ke halina bakida
matsala ko kadan."
" Haba wa? Ni har ilimi gareni, ai idan kikaga wasu sai kin
rike baki."
Anan su anisa sukayi tadi har saida dare ya raba sannan
sukayi sallama halina ta koma gida.
Tunda kulu kulun safiya anisa ta farka domin yau akwai al
amurran da takeso ta gabatar, a haka ta shirya jikinta
tsaf, daga nan ta dauko wayarta ta fara wasa. Da misalin
karfe 8:30 AM, sai ta farajin ana kwankwasa kofar
dakinta. Bai jira an budeba kai tsaye ya shigo.
" Anisa, wai kece a farke?"
" E mana daddy tun dazu fa na tashi."
" Tab, kina nufin har kinyi sallah?"
" E mana tun dazu."
" Mamaki, Keda bakya asuba sai karfe goma sha biyu na
rana amma yau har kin samu asuba. To Allah yayi miki
abarka yata." Anan ya juya ya fita.
Da misalin karfe 11:30 AM, anisa ta fito da makullin
motarta, a yau fa cikin jin dadi take saboda tafiyar da
zatayi. Rabonta data fito waje har ta manta. Gate man ne
ya mayar da kofar bayan ta fita da motar. To anan ta
nausa aguje ba sassauci. A haka ta miki hanya duma na
tashi a hankali yadda ita kadai keji. Bayan tayi tafiya mai
dan nisa sai ta cimma wani makeken gida. Sau biyu kawai
tayi oda aka bude mata gate din. Ciki ta nausa kai da gani
kasan cewa ba bakuwar gidan bace.
" Hajiya sannuki da zuwa." Anan mai gadi ya sheko a guje
wurinta.
" Yauwa barka, ina fatan dai tana ciki.?" Anisa ta tambaya.
" Gaskiya batanan, amma taban wannan takardar cewa
idan kinzo in baki."
PAGE 8
Anan anisa ta karbi takardar tana karantawa, " Ai kuwa
daka fadamin da bazan shigo ciki ba, kaga yanzu aiki ya
sameni wai ba a nan zamu hadu ba." Haka anisa ta fada
cikin rashin jin dadi domin ji take kamar duk ta wahala.
" Hajiya ayi hakuri, anan na tafka babban kuskure." Haka
mai gadi ya bata hakuri. Daga nan kuma ya bude gate din
ta fita. To bayan ta fita ne saita nufi inda zata hadu da
kawarta. Anan taci taya sai banka wuta take. Bata tsaya
koina ba sai kusa ga wani restaurant. Aiko tsayawarta
keda wuya sai taji an shigo cikin motar. Tana dubawa sai
tayi arba da zee. Wato kawarta.
" Tun dazu fa nake jiranki amma sai yanzu." Zee ta fada
cikin murmushi
" Yanxu...


Read / Download TAFIYAR DARE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album