Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

HIRA DA MATATTU NA BIYU Complete Hausa Novel Document by HIRA DA MATATTU NA BIYU


HIRA DA MATATTU NA BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 4911



HIRA DA MATATTU NA BIYU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Jamila Umar Tanko ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08061225337

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 25.92 kb

File Type: txt

Views: 1666+

Download: 371+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: HIRA DA MATATTU























Jamila Umar Tanko:

JUT

Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko
Copyright: Jamila umar tanko


Wannan littafi mai suna HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne.

300 ne kacal Zaa biya
0112240731
Gt bank
Jamila umar tanko

Idan an biya a turo shaidar biya ta wannan lambar:
08061225337

Na gode


HIRA DA MATATTU .....1 (True life story)

Haqqin Mallaka: Jamila Umar Tanko
Copyright: Jamila Umar Tanko


Saudaukarwa:
Na sadaukar da wannan littafin ga matan da suka yi jahadi wajen biyayyar aure ko su na raye ko sun rasu. Allah Ya duba yaransu ya raya su akan sunna.


Gargadi:
Baa yarda wani/wata ta juya labarin ban zuwa wata Shiga ba fim ko rubutu ba tare da izinin Marubuciyar ba. Sannan ban yarda a karanta shi a you tube channel, ba tare da izinina ba.








[2/28, 5:26 PM] Jamila Umar Tanko: 1

Sharifah ta ci gaba da cewa "duk wanda ya san ni a duniya toh ya san ni tare da Shariqah dan kamar 'yan tagwaye mu ke. Mun shaqu sosai kamar yadda uwa take shakuwa da 'ya'yanta.
Bayan son Allah (S.W.A) da ManzonSa (S.A.W) daman wannan baa hada su da kowa, sannan iyaye su daban ne. Duk duniya babu abinda na fi so irin yadda na ke son Shariqah, haka itama.
Ita karamar kanwata ce ba ita take bi na ba ma, Bello ke bi na ita kuma take bin sa.
Na riga ta yin aure da dadewa, amma a kullum tana gidana, idan ma bata zo ba ni zan je gida saboda ita, kasancewar mijina ba zaunin gari ba ne, yayi min lamuni idan baya nan zan iya tafiya gida in kwana. Kusan kullum tare muke kwana shinfidarmu daya, mu na raba dare mu na hira.
Baiwar Allah ta fi ni hakuri da hangen nesa, ko da zan zazzage ta sai ta fada min gaskiya.Babu mai goyon bayana a duniya irin ta, komai girman matsalata tana tare da ni kuma ita kadai nake fadawa komai nawa.
Ko kwalliya na yi idan Shariqah ba ta ce na yi kyau ba toh ba na yarda akan na yi kyau din.
Na haifi 'yata Hamidah, na rantse da Allah bayan wahalar daukar ciki watanni tara da nakuda da shayarwa zuwa kwana arba'in ban san wahalar raino ba. Shariqah ce komai na game da kula da jaririya, duk wata kazantar jariri da zaryar zuwa asibiti ita ce.
A lokacin ina tafiya jami'a wani lokaci ma ina gida a kwance ita ke faman rainon Hamidah. Har fada ake yi da ni ina cewa idan ba za ta yi ba a bar 'yar a wajen.Mutane su cika da mamaki. Ta yaya uwar da ta haifi 'yarta zata ce haka? Saboda na san ai ba za ta iya barin 'yar ba ne shiyasa nake cika baki.
Watanni takwas kadai Halidah ta yi ta na shan nono, na yaye ta, na damqawa Shariqah suka kaura gidansu gaba daya.
Hamidah ta tashi a tunaninta Shariqah ce mahaifiyarta, ta sanni amma ta dauka ziyara kawai nake kawo musu a matsayina na 'yar uwarsu.
Hamidah ta sha laulayi na jinya kala-kala haka Shariqah ta ke wuni a layin asibiti tana jinyar ta.
Samari da dama 'yan gayu sun sha ganinta a hanya su na so, daga sun matso suka ganta da 'ya har tana kiranta mummy sai su yi kwana a zatonsu matar aure ce.
Qawayenta har tsiya suke yi mata cewa sai an yi kwalliya zaa fita unguwa kawai sai ta dauko musu 'ya tana bata musu tsari. ita kuwa sai ta ce idan zaa so ta dole a so ta da 'yarta.
Ko tafiye-tafiye su ka yi qasashen waje da yake makarantar kudi ta yi kuma dukka qawayenta 'ya'yan masu hali ne ta kan fada musu ita bata son su siyo mata komai su siyowa 'yarta Hamidah. Ko ba ta fada ba ma sun san abinda zasu yi ya faranta mata rai shine su yiwa Hamdah sayayya.
Daman gashi kamarmu daya ni da Shariqah dan haka Hamidah ta yi kama da ni sai ta yi kama da Shariqah.
Aure ne kadai ya raba Shariqah da Hamidah. Na tabbatar da ta auri miji mai fahimta da daman da ita za ta tafi amma bata yi wannan sa'ar ba. Aka bar Hamidah a wajen mahaifiyarmu.
Mahaifin Hamidah ba mutumin da ya san darajar gidansa ba ne, haka ba mai kula da haqqin iyalansa ba ne, shiyasa ma ya bar 'yarsa ake riqonta dan bai sauke nauyin da Allah Ya dora masa ba.
Hakan ya fiye min alkhairi saboda idan na dauko ta na kawo ta gidana ma akan Hamidah kullum sai mun yi fada.
Mutum ne da baya son zaman lafiya ko kadan, Idan ya na so ya bani haushi ko ya takale ni da fada toh sai ya hau azabtar da ita dan haka ne ma ta taso da tsoronsa kuma bata son ganinsa ma ko kadan.
Bai sauke haqqina da Allah Ya dora masa na ciyarwa, sutura, asibiti, muhalli ba, dan haka bai hana ni fita neman kudina kowacce kasa ba. Dan mutuwar zuciya ma nawa yake so ya ci saboda zuciyarsa ta mutu.
Mahaifiyata na tsaye tsayin daka akan matsalolina da na 'yata dan haka da jarina da na ta nake juyawa.
Hakkinmu da ya tauye shine ya jawo masa koma baya, baya ganin daidai a dukka aiyukan da yake yi. Kullum ana korarsa daga aiki ya na wahalar neman wani aikin. Wannan kuma na bar shi da Allah, na ci gaba da kula da kaina da 'yata da taimakon Allah da taimakon mahaifiyata.
Mu ka bar Hamidah a Karkashin kulawar mahaifiyata amma kuma a koda yaushe tana zuwa gidan Shariqah kasacewar gari daya ne kuma tazarar unguwannin babu nisa.
Allah Ya bawa Shariqah haihuwa a jejjjere ba tsayawa. Allah Ya jarrabe ta da auren miji mai tsanani da kishiya da 'ya'yan kishiya mararsa kirki. Babban abinda ya kara kawo tangarda su na zaune su dukka a cakude a gida daya, bata jin dadin zama da su ko kadan.
Shariqah mace ce mai hakuri, komai sai ta rufe bata fadar damuwawarta. Hamidah ce kadai ta san komai ita ce abokiyar shawararta amma sai ta ce ma ta kada ta fada min. Saboda sun san ina da zafi wasu lokutan bana son rainin hankali.
Mahaifiyarmu mace ce mai son yara kuma a tsaye take akan matsalolin yaranta.Ko bayan rasuwar mahaifinmu ba mu ce wayyo Allah ba, saboda ba mu rasa komai ba. Mace ce mai kamar maza ta yi nata ta yi na wasu ma.
Wahalar da Shariqah take sha a gidan miji bai nuna ba saboda ga ta a kusa da mahaifiyarta mai sonta mai taimakonta da dukiyarta da nuna ma ta so da kauna da bata shawarwari akan ta yi hakuri rayuwar aure ibada ce.
Sai bayan da mu ka rasa Mamarmu sannan maraici dukka ya bayyana a jikin Shariqah.
Bayan masifaffen kulle wanda ko islamiyya baa zuwa a gidansa, daman biki ko suna da gaisuwar mutuwa, dangi dukka sun sallama ta baya bari ta je a cikin Kano ma balle a wani gari.
Dukka kayan dakinta masu kyau masu tsada na kasar waje, sai da suka kwankwatse, baya gyara balle ya canja musu kuma ke matar gidan da kudinki ba ki isa ki kawo masu gyara su shigo masa gida su gyara miki ba. Har da mugunta 'yayan waccan matar suke zuwa su lalata mata komai dan ita bata magana.
Ta rame, ta yi baqi-qirin ta fita daga hayyacinta. Wataran kudin Pampers guda daya jal sai ta gagare ta balle na cerelec da zata bawa yaranta bata da shi, kuma shi babu wadannan a cikin lissafinsa.
Yaranta sun tashi babu kuzari da yawa ma tana goyonsu sai da suka...


Read / Download HIRA DA MATATTU NA BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album