Join Our WhatsApp Group

SILAR MUTUWA Complete Hausa Novel Document by SILAR MUTUWA


SILAR MUTUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14789SILAR MUTUWA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 12, Jan 2024

Author: Fatima Rabiu (Zarah Royal Star) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08130479973

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 80.37 kb

File Type: txt

Views: 541+

Download: 146+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔
(Horror Story)

ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️


*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*PAGE 1️⃣➡️2️⃣


*Federal University dutsinma*Wata y'ar madai-daiciyar mota ce ta tsaya cikin filin school d'in bud'e marfin motar akai cike da takon k'asaita take ta fito daga cikin motar bak'in gilas d'in dage manne da fuskarta ta cire tana bin school d'in da kallo kasancewar zuwanta ne na farko.


Can ta tsinkaye wata murya na faman kiranta cike da murna taji an rungumeta da sauri ta waigo tana yamutse fuska da sauri ganin yadda duk suka rirrik'eta ta k'ara b'ata fuska ta ce "wai Bilki dake da Nawwara wai yaushe zaku canza ne shi yasa fa ban so zuwa school d'aya daku ba shi yasa again na ce ku fara yo gaba nabi bayanku shine daga isowata duk kunbi zaku wani kada ni", ta idasa maganar tana k'ara bin school d'in da kallo yadda taga duk Arna sunyi yawa a cikinta da sauri Nawwara ta d'an saketa ta ce "kai Surayya kefa akwai yarfa mutum wallahi mufa murnar zuwanki ne yasa kingah bamu san kowa ba a cikin school d'in nan", Bilki ce ta amshe da cewa "kai gaskiya Surayya daba dan mu k'awaye bane tun na yarinta da tuni mun barki da halinki akwai ki da murd'and'an hali".Ganin kamar sunyi fushi yasa Surayya cewa "kufa dad'i na daku akwai saurin fassara mutum nidai kun sani sai kuna hakuri dani school d'in ce kamar b'ata kwanta min a rai ba", ta idasa maganar tana tafiya kamar ba ita tayi maganar ba ganin tabi wata hanya yasa da sauri Nawwara ta ce "Surayya ki tsaya ba'a cika bi ta wannan hanyar bafa tana da matsala", d'an dakatawa tayi da tafiya tana waigowa ta ce "to sabon salo ai na ce dai ana bi dai ko kuma zata iya kaini a inda nake so ina ce hakane?", d'aga mata kai sukai cike da d'an tsoro Bilki ta ce "dan Allah Surayya kiyiwa Allah karki bi ta wannan hanyar akwai tantiran makaranta dake zama ta wajan nan duk school d'in an sansu kuma ana tsoron su ba wadda bai san tarihin su ba".


Surayya kuwa tsaki taja tana ci gaba da tafiya tana cewa "zan so jin tarihin mi suka aikata har ake jin tsoron su, to daga yau za'a sake kafa wani tarihin cewa ga wadda bata shakkar kuwa dan banga wadda ya isa ya hanani zaga ko ina ko shiga wani waje dake cikin school d'in nan ba indai zuciyata taso hakan", ta idasa maganar tana shan wata kwana da sauri su Bilki suka rufa mata baya suna mamakin rashin tsoro da kafiya irin na Surayya.Koda tasha kwanar idonta ya gane mata dan-dazon maza sun kai su bakwai sai zuk'ar sugari suke zuciyarta ce ta buga dumm dammm dakewa tayi tana tafiya irin ko a jikinta tana niyar wuce su, da sauri wani cikin y'an iskan dake zaune wajan ya ce "Oga Goga ga wata mai rabon shan duka ta biyo da hanyarka miya kamata muyi mata danna tabbata an sanar da ita waye kai", ya idasa maganar yana kallon Goge dage kallon Surayya da wani salon iskance ya ce "barni da ita wannan daga gani kalar mu ce", ya idasa maganar yana yin wata shegiyar mik'a ya nufi wajanta.Surayya kuwa batai aune ba taga mutum a gabanta ganin sa gaf da ita kamar zai shige jikinta yasa da sauri tad'an matsa tana tushe hancinta saboda warin giyar da yake.


Wani murmushin gefan baki yayi yana fiddo harshan sa yana lashe bakinsa kamar tsohon maye yana kallon gefe yana cewa "da alama baki san ana tsoron biyowa ta nan hanyar ba ko? kuma baki san waye Goga ba baki binciki tarihin sa ba dami-dami ya aikata harya kawo wannan matsayin ba kohhh?", ya idasa maganar ya ware mata jajayen idonsa.


Da sauri Surayya ta d'an k'ara matsawa cike da k'arfin hali ta dake tana aika mai da wata shegiyar hararara kamar idonta zasu fad'u, ta ce "waye kai kuwa inbanda bawan Allah kuma an gaya min ina sane na biyo hanyar tunda naga ai ba wani ya gina hanyar ba kowa nada ikon wucewa in...... Kamin ta idasa maganar ya daka mata wata uwar tsawa da cewa "keeee y'ar gidan abun wacece ke koh y'ar gidan wacece bata isa ina fad'a tana fad'a ba ba'a yota ba, kuma baza a tab'a yinta ba", dai-dai lokacin su Bilki suka k'araso suna tsaye gefe, ba abinda jikinsu yake sai kyarma na tsananin tsoro.


Goga ya bud'e baki da bud'ad'd'iyar muryarsa ya ce "kai guy's ku d'akko min ita sana ku had'a da y'an matan can", wata irin zufa ce ta yanko ma su Nawwara, suna fashewa da kuka suna cewa "Surayya kinga abinda kika zamana ko?".Suna gaf da isa inda su Bilki suke Surayya ta saki wata irin dariya mai amsa kuwwa wadda tasa gaba d'aya wajan amsawa, d'an gyalan dage jikinta ne ya cire daga kanta gashinta ya sauka har gadon bayanta ya rufe mata fuska, ta duk'ar da kanta k'asa, cike da mamaki su Nawwara ke dubanta.


Goga kuwa dariya shak'iyanci yayi ya ce "mu zaki firgita da aljanun k'arya kai ku dakata bari na d'akkota da kaina", da sauri wadda suka nufi inda Surayya take suka tsaya dan ba k'aramar girgiza su dariyar tayi ba, ko dai Goga baiji dariyar da kyau bane kamar fa bata mutane ba ce kai wannan dariyar tafi k'arfin mutum yayi ta.


Kamin ya kai gare ta Surayya da wata irin murya wadda kwata-kwata ba tata bace ta ce "da alama har yanzu Goga baka daddara ba baka daina abinda kake can baya ba dama irin wannan yarinyar nake so tazo wacce bata da tsoro da ita zanyi anfani na shiga jikinta naci ubanku hankali kwance bazan tab'a kashe ka ba dan yanzu ba Goga saina gana ma azabar da sai ka gwamce mutuwa da rayuwa tunda kayi SILAR MUTUWA ta nida wadda nake k'auna", wata irin zabura yayi jin muryar wadda har duniya ta nad'e bazai mance mai ita ba, hantar cikinsa ce ta kad'a wata irin zufa ce ke yanko mai kota ina sai zazzare ido yake, su kansu wadda suke bimai baya ganin kamar suna Shirin tsire wa yasa ta k'ara sakin wata irin dariya mai firgita ruhin d'an Adam ta nuna inda suke niyar guduwa da hannu dan da nan wasu irin halittu suka bayyana masu mummunar kama fuskar su ba kyan gani suna zaro zungureran harshan su ga wasu zafga-zafgan bulali a hannunsu kamar na k'arfe umarni ta basu kan su fara aiki ai ko ba shiri suka fara zafga masu bulali wata irin azaba suke ji ihu suke babu mai jin su baka Jin k'arar komai sai na ihun su da k'arar bulala.


Juyawa tayi tana shak'ama su Nawwara wani farin abu nan take wani nandauyan bacci ya sure su tana sa hannunta ta shafe su b'at suka b'ace daga wajan.Goga kuwa da yayi suman zaune ganinta gabansa tana wata y'ar iskar dariya gashinta ne yayi baya mummunar fuskar ta bayya na da tasa Goga sakin fitsari ganin rabin fuskarta naman dake wajan duk ya zaizaye tsutsotsi na bin wajan idonta ya koma fari fari fat ko d'igon baki babu bakinta wasu irin hak'ora ne y'an guntaye masu masifar tsini wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki...........✍️


*ZAHRA ROYAL STAR CE*Share fisabilillahi🙏🥰


*💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔
(Horror Story)

ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*PAGE 3️⃣➡️4️⃣Wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki, nuna sa tayi da hannunta wani farin haske ya fito ya shigi Goga wata irin zabura yayi yana makyarkyata kamar wanda wutar neper ta kama sai da taga ya wahalu sana ta saki wata irin dariya mai k'arar gaske sana ta b'ace b'at sai dariyar da tayi ce ta karad'e lungu da sako na wajan wata irin amsawa kuwwa dariyar ke yi kamar yanzu ne take dariyar.Su Goga kuwa ganin sun tsira ba wadda ya tsaya d'aukar wanni abu suka arce da mugun gudu yadda kasan ita ce ta biyo su a baya.Basu sauka a ko ina ba sai a wani rub'ab'b'an gida wadda suke kwana kai daka kalle su kasan sun jiga tu wani daga cikin su ya ce "kai Oga na kasa tuna miye ma ya faru a wajan shin muryar wacece muka ji ne?", Kowa shuru yayi dan kwata-kwata kamar anyi masu yasa a cikin kwanyarsu sun kasa tuna shin muryar wacece ma suka da ainahin miye ya faru abinda baza su manta dashi ba dai shine sunsan sun tare wata budurwa ita kanta sun kasa tuna fuskarta, share abun sukai duk dukan da suka sha suka fara jinya ba k'aramar jinya sukai ba suna suka wartsake suka koma fagen shashancin su.A wajan su Surayya kuwa tsintar kansu su kai a gidan da suka kama na wajan makarantar a cikin d'aki sai sharar bacci suke koda suka farka basu kowa komai a ransu ba dan kwata-kwata suma ba'a basu damar su tuna wani abun ba.Zaune Surayya take suna waya da Ammee tana mata fad'an danmi bata Kira su ba, data isa ta sanar dasu isarta gashi kinsa mijinki cikin damuwa, dan kuwa Surayya nada aure karatu ne ya kawota an d'aura auran ne a bisa sharad'in saita gama karatu zata tare.


Zunb'uro baki Surayya tayi ta ce "Ammee amma ba sai ya kira ni ba sai yaje ya tada miki hankali yana ganin ke kad'ai kika rage min Allah sarki Daddy na Allah ya jik'an sa da rahma ina kewar Daddy", ta idasa maganar wasu hawaye na neman kufce mata ita kanta Ammee cikin raunin murya ta ce "kin ganki ko zaki sa zuciyoyinmu karyewa abinda nake so dake yanzu shi SADEEQ mijinki yasa an samar mai aiki a nan school d'in taku, zai rink'a koyarwa har ki gama, dan saboda ke yasa a samar masa aikin nan", cike da kid'ima Surayya da d'an kishi-kishi ta ce "amma Ammee miye da sai yazo nan wallahi Ammee karki ga school d'in duk Arna sunfi yawa ga y'an mata wadda kwata-kwata basu da kintsi bare kamun kai d'ai-d'aiku ne zaki ga yarinya ta zauna tayi abinda ya kawo ta in...... Kamin ta idasa maganar Ammee ra tare ta da cewa "kinfa san waye mijinki kinsan yafi k'arfin ya zauna yana koyarwa kinsan waye shi a k'asar nan kema Allah ne ya inganta rayuwarki kuma ya dasa masa soyayyar ki, kin manta irin wahalar da kika sha na soyayyar ku aka rasa wazai furta yana san wani cikin ku shi girman kai kema haka duk da ya kasance d'an uwa a gare ki duk sadda yazo gidan nan danke yake zuwa amma saiya wani share yayi kamar badan ke yazo ba, to taya za'ai mai irin wannan hali kike zaton ya kalli wata mace yadda ma yake sonki ke kinsan hakan ma bazai yuwu ba", kunya ce ta kama Surayya yadda Ammee ta fahimci kishi ke damunta Ammee ta k'ara mata fad'a kan cewa "Surayya ki kama kanki karki ga cewa ai gaku waje d'aya ki basa kanki tun kan a kaiki d'akinsa ki kankaro ma kanki daraja again kuma ki kama kanki Kinga ke matar aure ce koda yake tunda Sadeeg na kusa nasan shi shima da d'an banzan kishin tsiya dole nasan zuwansa sai kafa miki doka ni wallahi yayi min dai-dai ma daya biyo kin", ta idasa maganar tana sauraron yadda Surayya ke zuba shagwab'a ita fa za'a takura mata, bayan sunyi sallama da Ammee .Su Nawwara dake yankan kayan miya sun d'ora abinci Bilki ta ce "ai wallahi Ammee gaskiya take fad'a miki ni Sadeeg yamin dai-dai daya biyo bayanki ni dama nasan za'a rina, tsawon shekaru bazai iya hakurin rashinki ba bare baya ganinki", Surayya ta d'an gyara zama akan katifar da take ta ce "ni ba wannan ba kawai dai school d'in nan akwai k'ura dan na rantse duk wacce ta shiga harkar miji na kunsan Allah zan iya mata koma miye indai akan Sadeeg ne dan haka za'a sha kallo wallahi", ta idasa maganar tana tab'e baki Nawwara ce ta ce "hmm shi kansa saiya miki shamaki da kowanne d'a namiji ko gaisawa kuwa wadda shi yama fiki kishi GARKUWA kai zafa asha kallo wani ma bai tab'a zaton zaiga Garkuwa da idonsa ba amma ta dalilinki zai gansa duk Najeria fa ansan mijinki Garkuwa ai wallahi Surayya ki k'ara godema Allah, ai kawai dai Allah ya kyauta ni ban tab'a ganin soyayya irin taku ba".
Washe gari tun wajan k'arfe 8:00am dai-dai suka fita lecture da yake duk abu d'aya suke karanta suna cikin class kowa na harkar gabansa ana jiran Malamin da zai shigo na gaba wasu na wajen class, ba zato ba tsammani wani arnan k'amshi yayima gaba d'aya class d'in sallama duka mutanan dake ajin har rige-rigen waigawa suke suga wannan wane sabon Malami ne aka kawo musu, ita kuwa Surayya da tun isowar k'amshin a hancinta tasan waye zuciyarta sai bugawa take jinin jikinta na gudu lumshe idonta tayi tana da tabbacin kenan shi ne wadda zai d'auke su English tab ta tab'e baki tana bin y'an matan ajin da kallo yadda ko wacce har suna rige-rigen furta "WOW", kai bama mata ba hatta maza sai da suka sarama Sadeeg.


Tafiya yake cikin k'asaita harya isa gaban allo tsayawa yayi yana juyowa gaba d'ayan sa gaba d'aya y'an matan dake ajin sai da sukai MUTUWAR zaune d'an kuwa kyan sa da kwarjininsa ba k'ara min tafiya yayi da imaninsu ba sanye yake da wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya da hular zanna bukar dake zaune a kansa dogo ne ba irin sosai d'in nan ba, yana da k'irar k'arfi, daka kalli damtsin hannunsa kasan cewar yana motsa jiki gaba d'aya jikinsa a murd'e yake, yana da yawan gashin gira girarsa har had'ewa take, idonunsa kuwa hmmm wai wai wai Allah yayi halitta tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halitta mai tsananin kyau da kwarji, idonsa daga cikinsa kalar ruwan k'asa ne sosai har wani shek'i suke fari kal dasu in aka zo fagen hanci kuwa ba'a magana dan hancinsa dogo ne daga k'asansa ya d'an bud'e kad'an saiya k'arama fuskar sa cikar zati, idan aka zo wajan bakinsa kuwa kai ya Allah ba'a cewa komai bakinsa mai zanan love ne d'an k'ara mi dashi daga saman lab'b'ansa sai ka rantse yasa janbaki ne, amma ainahin kalar su ce jawur dasu.Babu abinda y'an matan ke furtawa sai Masha Allah ko wacce...


Read / Download SILAR MUTUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album