Join Our WhatsApp Group

BOYAYYEN YARIMA Complete Hausa Novel Document by BOYAYYEN YARIMA


BOYAYYEN YARIMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 3382



BOYAYYEN YARIMA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 30, Nov 2023

Author: Salmaji Yar Lelen Royal Star ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07033371851

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 18.14 kb

File Type: txt

Views: 2015+

Download: 454+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: BOYAYYEN YARIMA(MUTANEN DAJI).


BY

ƳAR LELEN ROYAL STAR.


Alhamdulillah! Alhamdulillahi Allah Kulli Halin, Alhmdllh, ina mai ƙara Jaddada Godiyata ga Allahu Subhanahu Wata'ala da ya bani Rai da lafiyar Fara Rubuta Wannan Littafin nawa mai Suna Ɓoyayyan Yarima, Wanda na yi Tsawon Lokaci ina Nazartarsa da Son Fara rubutasa, Allah bai yi ba sai Yau, Ina fatan Jinkirin Rubutasa da Na yi ya zama Alkhairi ga ni ga Dukkan Wanda zasu Karanta, Ina fatan Ubangiji ya bamu Aron Rai da Lafiyar da Zan gamasa cikin Kwanciyar hankali da Salama.


P.1


Fur.

Wata Ƙabila ce Wace Galibinta ke Zaune a Yammacin Ƙasar Sudan, sun fi karkata ne a Yakin Darfur, inda Mafiya Yawan Ƙabilar suna Magana ne da Yaren Fur.

basa magana da ko wani Yare in ba Yarensu na Fur ba, Sun fi yawan zama A jeji, basu cika sanya Sutura ba, suna Rayuwarsu ne kamar Arnan daji, Mazansu basa sanya suturar kirki sai dai Bante, Matayensu kuwa basa rufe samansu Suma fin ganewa su Rufe Ƙasa.

Basa bin wani Addini Face Sunni-Islam da shi suke Amfani basu yarda da wani Addini bayan shi ba.


Cikin natsuwa Suke Tafiya akan Dawakansu, da suka kasance Farare sosai, sun sha Adajensu Mai kyau, Dubana na kai akan Mutanan da suke kan Dawakan da Aƙalla ba Akasaru ba zasu kai kusan Mutum Ashirin, Gaba daya Shigarsu kala daya ce, gasu wasu irin Baƙaƙe na ƙin Ƙari, Baƙinsu irin Baƙin nan ne Marae kyan Fasali irin Baƙin da zaka ga Mutum har Wani mai-mai yake musamman in ya shiga rana, Dukkansu Jikunkunansu Suba daure da Wasu kalar Yadi ne mai kama da Jikin Kura-kura, Wanda suka Rufe Tsiraicinsu daga Ƙasa daga Sama kuma An mishi kamar Hirami, an gyalashi a gefe daya, Sai Yadin da Aka musu kamar Hular , Suka zagaye Goshinsu da shi, Gefe da Gefen Ƙugunansu sun Sanya Manyan Wuƙaƙe Irin na Zuwa Yaƙi , gaba daya dai sun yi Shigar Yaƙi, Haka gaba daya shigarsu take, sai guda Daya da ya banbanta da su, Kayan Jikinsu kala daya ne sai dai shi Ya Rufe dukkan Fuskarsa Idanuwanshi da suka kasance Blue, Saɓanin nasu Idanuwan da suka kasance Farare, Wanda su ne kawai zaka iya kallo wanda ya kasance fari a duk jikinsu, tafiya suke Cikin ƙasaita Sosai.

Basu yi tafiya mai Nisa sosai ba suka fara Shigowa Cikin Wani gari, Mai dauke da Bukkoki a matsayin gidaje, Tun daga nesa suka hango yarda Uwayen Mutane suka taru A ƙofar shiga cikin Garin, Suna Riƙe da Ganguna, da kayan kiɗe-kiɗe, suna ƙara dososu Sosai aka saki Kiɗe-kiɗe irin na mutanen Da. Mutanen Da din ma Irin na Mutanen Daji, wanda yake tayar da Tsumi,kiɗa suke sosai suna Rawa na Murnan Mutanansu sun Je Yaƙi sun Dawo, tare da Ɗumbin Nasarori, gaba daya Washe bakunan su masu dauke da Jajayen Haƙora Wanda aka musu Adon Wani Ɓakin Abu a Haƙoran Wanda su a Ganinsu Kyau suka yi da Abun.


Har suka iso kusa da juna suna Washe bakunansu, saukowa suka shiga yi daga kan Dawakansu, suna Gaishe da Sarki da Mutanan garin, duk Wannan Bidirin da Ake yana kan Dokinsa bai ko motsa ba, Sannan bai kalli gaba daya mutanan da suke gurin ba, haka zalika bai buɗe Fuskarsa da take Yane da wani Farin Kyalle ba.
Aƙalar Dokinshi ya fara Ƙoƙarin Juyawa domin Wucewa Cikin gari, babu wanda ya dakatar da shi, don sun san Kafiyarsa akan Abun da yake Buƙata, In yace zai yi Abu bb wanda ya isa ya hanasa, in kuwa kayi Ƙoƙarin hakan, bazai ji komai gurin Cire kan ka, kuma ya yi Abun da ya yi Niyyar yi ba.


Suna kallonsa ya wuce Cikin Garin nasu, mai kyan gani, Haka ya Ringa tafiya har ya ƙaraso Gurin Wata Babbar Bukka da tafi gaba daya Bukkokin Garin Girma, ko ta Sarki bata fi tasa ba sai dai su kara, sai da ya ƙaraso kafin ya sauko daga kan Dokinsa, Gurin da ya tanadar Domin Ahiye Dokinsa yaje ya Kulle dokinsa a gurin, ya dawo ya shige Bukarsa, Kan yaloluwar Abun Shimfiɗar da yake Gefe ya kwanta, tare da sauke Sanyayyan Numfashi, lumshe idanunshi ya yi, dan-danan Barci mai nauyin Gaske ya daukesa, bai Farka ba sai da dare ya Ritsa sosai, Sai da ya ji Kiɗe-kiɗen da Ake sun cika masa kunnuwansa, ya yi ƙoƙarin toshewa Amma sautin yarda kadan cikin kunnuwansa ake yinsa haka yake ji.


A dole ya tashi ya zauna, yana wawware Blue Eyes nasa, da suke Sheki ta Hasken Farin watan da yake Haskowa har cikin Bukar, Miƙa ya yi, cikin jin wata kalar Kasala, Cikin Izzarsa da ta zamar masa jiki a ko da yaushe, ya miƙe ya fice daga cikin Bukkar.

Yana fita Ya ɗaga kansa, sama yana kallon Garin yarda yayi baƙi Wuluƙ sai hasken Farin wata da ya yi masa ƙawanya, ga Taurari Masu Haske sosai da suka Haɗu sukawa Samar Ƙawanya, Lumshe idanunshi ya yi, ya ƙara buɗewa akan Sararin Samaniyar wadda ta burgesa sosai, wanda har yaji kamar ya Dawwama yana tsura mata idanu kar ya dauke.


Hasken Wutar da ya fara hangowa ta gefe da gefen idanunshi, da sautin Ƙiɗe-kiɗen da suke Kaɗa kansu da kansu a duk Daren da Aka dawo daga Yaƙi kuma ya zamana Sune da Nasara.


Ranar Gaggarumin Biki ake yi a cikin garin, Randunan Giya, Da sauran Abubuwan Shaye-shaye na Mutanen Daji ake haɗawa, a tara Yan mata, da Samari, ga Wuta a Tsakiyarsu su ringa rawa, daga karshe bayan An gama, Za'a ajiyewa Zaratan Sojojinsu Mata kala-kala duk wadda kakeso ka dauketa a Matsayin Mai kula da kai, Wasu Daga nan suke Auren Hadiman da aka basu, Wasu kuma basa Samun Aurensu, to yau ma Abun da yake faruwa kenan, Sun fara gudanar da Bikin da suka saba yi, gaba daya mutanen Cikin Dajin suna gurin sun Zagaye Wutar da take gurin.
Kowa na Jiran Isowar Kwamandar Yaƙi, Wanda ya jagoranci Yaƙin , wanda kuma Shine Yarimansu, Wanda ya kasance Ɓoyayye a cikinsu, Ɓai taɓa Buɗe fuskarsa Wani ya gansa ba, kullum Fuskarsa tana a kulle, hakan ne ma yasa aka sanya Masa Ɓoyayyen Yarima, Wanda Asalinsa Ɗan Mutan Darfur ne, Kaura suka yi suka shiga cikin Ƙabilar Fur, wanda ya taso a cikinsu tun Yana Yaro, da haka Har ya tashi, ya tashi cikin Zaƙwaƙuranci, ta yarda yake bige Gaba daya Sa'aninsa, baya da wasa baya son A masa, wasa baya son Abun da baya so, yana matuƙar girmama Abun da yake so kuma yana son a girmama masa, baya son raini baya son Zalumci, yana da tausayi sai dai ba Akan kowa ba.


Dirarre ne Mai kyan jiki , yana da Tsawo da Ƙibi da Faffaɗan Jiki Irin Jarumai, yana da cika Ido da Kwarjini na Musamman, ta yarda Duk wanda ya kalli Tsakiyar Idanunshi ko ya kallesa ba zai iya furta komai ba Saboda Mutuƙar Ƙwarjin da ya kasance yana da shi, Yana dai Baiwa sosai, Ya iya Sihiri kala-kala, Yana bayar da ko wani Kalar magani, Yana da Ilimi sosai, Wanda duk a cikin Kauyen bb mai iliminshi, gashi da Kimiyar haɗa Abubuwa, yana Ƙoƙarin gurin ganin ya haɗa Abubuwan da zai taimaki Rayuwar Danginsa na cikin Ƙasar.


Yana Ƙarasawa Gurib Aka basa guri, chan kusa da Sarki akan wata Kimtsatsiyar Kujera mai kyawun gaske, Zama ya yi, tare da Nannaɗe Ƙafafunsa, kamar yarda Al`ada ta tanadar, bayan gama dukkan kalolin Bukunkunan da suka dace , Aka fara Bukin Zaɓen Mata, a Ƙa'idance Kwamanda ake fara bawa Damar Bude ido ya Zaɓi Macen da yake so, sai dai shi hakan baya cikin lissafin Tsarin Rayuwarsa, bashi da wani haɗi da Mata, baya shiga dukkan wata Sabga tasu, hakan yasa ko kallo basu ishesa ba.


Haka Aka shiga Zaɓe, kowa na zaɓar wadda ta Masa a cikin Matan da suke gurin, Yancinsu an daukesu, Sai wata guda da take Gefe daya ta tsure jikinta guri daya ta haɗa kanta da Guiwa kamar mai jin sanyi, Gaba daya jikinta a Suturce yake, har gashin kanta baya buɗe, sai hannayenta da Ƙafafunta, sai kuma Bayanta da Suturar bata samu ta gama rufewa ba.


Haka aka gama aka watse Amma ita babu wanda ya je gareta balle a Dauketa a matsayin mai Hidima, haka taro ya shiga Watsewa, Wata Yar Yarinya ce ta zo ta riƙe hannunta, tare da mata magana a hankali, maganar da taji ne yasa ta laluɓj Sandarta , A hankali ta miƙe , hannunta daya na riƙe da Sanda dayan hannun kuma na Dafe da Kafaɗar Yarinyar da tazo gareta, Tafiya suka fara yi a hankali , har suka ɓacewa gurin hasken Wutar.


A hankali shima ya miƙe daga gurin ya nufi hanyar da ya fito, Cikin Izza yake takawa, yana kallon sama da idanunshi, har ya ƙarasa bakin Bukkarsa, shiga ya yi tare da turo Ƙofar bukkar ya rufe.
Inda ya tashi ya koma ya kwanta, tare da dan Sanya hannunsa a gefen Zuciyarsa, ya lumshe idanu yana jin yarda take Bugawa da sauri-sauri.


WASHE GARI.

Da sassafe ya fito Saboda Aiken Sarki da yace zasu Fita, hakan yasa Hasken Alfijir na ketowa, ya miƙe shirinshi ya yi cikin Sulkesa , ya fita, yana takawa cikin Taƙama, duk hanyar da ya nufa ana faɗuwa tare da gaisheshi, har ya isa Bukkar Sarki.
A waje ya tsaya Jakadiyarsa ta shiga , bayan mintuna ta fito tare da mishi iso cikin Bukkar.


Zaune ya samu Sarkin yana jin Gasasshen Nama, da akawa Gashin Ruwa-ruwa, mai dadin gaske sai kamshi yake.
Zama ya yi tare da gaisheshi, bayan ya Amsa ne ya mishi Umarnin yazo su ci, A ƙa'idar Mutanen Dajin bb mai yiwa Sarki musu, hakan yasa ya matsa suka dan ta, bai ci da yawa ba ya tsame hannunsa tare da matsawa baya.
Yana zaune a gefe har ya gama, A tare suka fito gari suka fara zazzagayawa, daga nan kuma suka shiga cikin Jeji, sune basu dawo ba sai da gari ya dan fara Alamar yin duhu.


Tafe suke,akan Dawakansu, wanda da Alama tafiyarsu tayi, nisa kasancewar yarda su kansu Dawakan, tafiya suke cike da gajiyawa.


Zaune take a ta chan bayan gari, Fuskarta a Buɗe, Kyakyawace sosai , Launin Fatarta ba za'a kirasa baƙi ba sanan kuma ita ba fara ba, Sai dai ace mata Chocolate calour, tana da dogon hanci da Dan ƙaramin baki, mai dauke da Siraran Ƙananan Fararan Haƙora, Idanunta kalar Gold ,wanda suka ƙara mata kyau, suka kara fitar da kyawun Fuskarta,
Tsurawa Zara-zaran yatsun Hannayenta idanu tayi, wanda idan baka santa ba, ko kuma ka mata kallo daya zaka dauka Tana gani da Idanuwan nata, sai dai ko kaɗan bata gani da su, Amma kuma suna da kyau sosai
.


Zaune take gefe daya, ta nannaɗe ƙafafuwanta, shiru ita kaɗai da ita, kallo daya zaka mata, kasan cewar ba wai taji dadin zaman gurin bane, ko kuma ta zaman gurin ne cikin jin dadi a'a, Zamanta gurin yafi kama da zaman wanda yake cikin matsananciyar Damuwa da Begen wani Abu da kayi Rashi Zama ne irin na wanda yake Mararin samun Wani Abu, zama ne na irin wanda ya miƙa gaba daya Ragamarta da Aqalar Rayuwarta, Zama ne irin na Tsammani.


Jin Ƙarar Takun Dawakai yasa ta kara Rabewa, a bayan bukkar da take, ta lafe sosai, jikinta na dan karkarwa, Har sai da ta ji Takun Dawakan ya sihirta Alamar sun bar gurin kafin ta sauke Nannauyar Ajiyar Zuciya, Sandarta wadda take mata Jagora ta Laluɓa wa, har Allah yasa ta ji inda take, cikin sauri ta dauka, tare da miƙewa, gyara Tufar jikinta tayi, tare da fara Ɗaddogara Sandar tana laɗuɓe har tayi nisa sosai, Gurin Wani Bukka ta tsaya, tare da zama tana goge zufar da ta tsatsafo mata a goshi.


"Ɓul-ɓul!", ta ji an kirata, a dan zabure ta Amsa tana mai kama jikinta guri daya, Cikib Yarensu ta fara zaginta, da watsa mata wasu Suturu irin nasu , ta bata Umarnin ta je ta wanke mata su yanzu ta kawo mata, Dauka tayi, ta nufi Rafinsu inda suke yi wanki, Babu kowa a gurin, Haka ta fara Wankin , Magana taji a bayanta da Sauri ta waiga, tamanta da tana gaban Ruwa, juyawar kuma da tayi ni yasa ta ƙara kusanci da Ruwan Sosai, Wata gigitacciyar Magana da ta tsoratar da ita ta ji, baya tayi cikin wani irin tsoro.


Bata Ankara ba ta ji ta faɗa cikin Babban Rafin da yake garin, mai zurfi da Faɗi, facal-facal ta shiga yi cikin ruwan tana neman Hanyar da zata bi ta fito daga cikin ruwan, Ita ba Idanu ba, balle ta taƙala wani gurin ko ta kama wani abun ta fita, gashi gurin babu mai ceto, gashi ko ruwan bata iya ba.


Hakan yasa ta fara nutsewa cikin ruwan, ta shiga yin Ƙasa, dai-dai lokacin da ya ƙaraso Gurin Rafin domin shayar da Dokinshi, kaya ya gani a Gefe, bai kawo komai a ransa ba ya fara bawa Dokinshi ruwa, kamar An ce ya daga kanshi ya kalli Cikin ruwan ya fara hango Kwayayen Numfashi, dan ware ido ya yi, dubawa ya ƙara yi da kyau, Tabbas mutum ne a cikin ruwan, Cikin wani irin sauri ya nutsa cikin Ruwan.


Nemanta ya shiga yi, Ya dade sosai yana nemanta kafin ya sameta, Fiddo kanshi ya yi daga ciki, haka ya ɗagota fa ha gigitacciyar Magana da ta tsoratar da ita ta ji, baya tayi cikin wani irin tsoro.


Bata Ankara ba ta ji ta faɗa cikin Babban Rafin da yake garin, mai zurfi da Faɗi, facal-facal ta shiga yi cikin ruwan tana neman Hanyar da zata bi ta fito daga cikin ruwan, Ita ba Idanu ba, balle ta taƙala wani gurin ko ta kama wani abun ta fita, gashi gurin babu mai ceto, gashi ko ruwan bata iya ba.


Hakan yasa ta fara nutsewa cikin ruwan, ta shiga yin Ƙasa, dai-dai lokacin da ya ƙaraso Gurin Rafin domin shayar da Dokinshi, kaya ya gani a Gefe, bai kawo komai a ransa ba ya fara bawa Dokinshi ruwa, kamar An ce ya daga kanshi ya kalli Cikin ruwan ya fara hango Kwayayen Numfashi, dan ware ido ya yi, dubawa ya ƙara yi da kyau, Tabbas mutum ne a cikin ruwan, Cikin wani irin sauri ya nutsa cikin Ruwan.


Nemanta ya shiga yi, Ya dade sosai yana nemanta kafin ya sameta, Fiddo kanshi ya yi daga ciki, haka ya ɗagota da hannu daya zuwa Gabar Rafin..........



#400.

1499884120
UMMA SALMA SANI
ACCESS BANK.


07033371851


P.R.O SALMAH🤙🏽

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta...


Read / Download BOYAYYEN YARIMA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
4 Comments On BOYAYYEN YARIMA
avatar
aisha-9-8-5

5 months ago

Reply

Please cigaban boyeyyen yarima ataimaka

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to aisha-9-8-5

Littafin na kudi ne sai dai ki siya daga wajen marubuciyan

avatar
aisha-1-7

5 months ago

Reply

Pls cigaba

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to aisha-1-7

Littafin na kudi ne sai dai ki siya daga wajen marubuciyan

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album