Join Our WhatsApp Group

MARAICIN RAHMA Complete Hausa Novel Document by MARAICIN RAHMA


MARAICIN RAHMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41959MARAICIN RAHMA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08061929616

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 217.57 kb

File Type: txt

Views: 1315+

Download: 658+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ENJOY READING.

MARAICIN RAHMAH

1-5

By
Asma baffa

Jinjina da dubun godiya ga masoya makaranta novel dinnan馃檵鈥嶁檧馃憤

Bismillah

Kebbi state,na wuce gari,kauyuka da dama,Wani daji na cinna tafiya nake katsam sai ga asma a wata rigar fulani Wanda babu komai face yan gidaje Wanda akayi su da ainihin karan dawa da yayi irin dai gidaje na asalin fulanin daji,babu komai a dajin sai korayen bishiyu,ruwa da gonaki da mutanen yankin suke noma,gidajene daya can daya can,tsalli tsalli,sai wata yar kasuwa,garin ALLAH ya albarkacesu da niima kala kala,wannan ne yasa na tsaya kallo, can wata yarinya na hango kyakyawar gaske,yar doguwa fara fara ja ja,gashinta har gadon baya amma shi ba baki ba kuma ba ja ba kalar na fulani dai,hancinta me tsayi amma ba can ba me kyau,idonta dara dara,ga eyelashes baki,bakinta hakora kana na lips pink dan cut dashi,kai karshe dai tayi,sanye take da wasu yagagun kaya, wata kodadiyar atamfa ta jeme,takalminta duk ta daure da Leda,amma daga ka ganta kaga me tsafta dan komi Fes take,sai dai kana gani Kasan tana wahala.

Yarinyar baza ta wuce yar 15yrs ba sanda ce a hannunta tana kada yan shanunta Wanda gaba daya shanun guda uku ne kacal,saniya,sa,da dan maraki wato dan saniyar,binta nayi ina dauko muku rahoto,tiryan tiryan naga dai dai wajen magariba ta nufi wata yar bukka wacce take zagaye da katangar kara,sai toilet guda shima na kara da yayi ne,harda rumfar girki da yan watsatsun tukwane da sauransu a wanke fes a gyare.

Jira nake naga wani ko wata ta fito amma shuru,yarinyar naga ta daure shanunta a wani bangare na gidan ta cire kayanta ta daura wani jememen zani ta ebi ruwa ta shige bayi da dan kwandon soson buhu da wani koren sabulun wanki,ta dan jima ta fito Ashe wanka ta sillo,dan Vaseline ta shafa da kwalli,ta dauko wata t.shirt ja ta saka ta daura wani zani Wanda shi na fulani ne,kayan data cire da zanen wanka ta hada ta wanke da koren sabulunta,ta shanyasu,wata sandarariyar shinkafa da manja ko yaji babu tacinye ta bude randarta tasha ruwa,wata futilar kwai ta kunna a cikin yar bukkarta ta dakko wata tsohuwar jaka,wasu littaatafai ta dakko,

Abin mamaki teach your self na hango da brighter grammar,sai littatafan koyon rubutu da karatu na Hausa,da bironta sai littafin rubutu guda 2 ciki Wanda a su take rubutunta,sai da ta gama karatunta kuma ba laifi ta iya sai ta kuma dauko Qurani tayi ta karatu cikin dadan murya,tabbas da gani ba jahila bace ko daga yanda tayi sallah ma komai dai dai,da azkhar du ta dan iya ba laifi,bayan ta gama karatunta ne naga tayi sallar isha tayi adduoi,amma tana zub da ruwan hawaye tare da kuka me tsuma zuciyar me sauraro,bayan ta gama ne ta kwanta,sai bacci,washe gari da asuba tayi sallah da azkhar,bayan rana ta fito ne ta kwanta bacci sai wurin Tara ta tashi,tana tashi naga ta dauko wata Leda ta Ciro toothpaste da brush duk da brush din tsohone tukub,da gani yaci duniya,amma tayi kokari,ta goge bakinta tas,sannan ta shige rumfar girkinta wuta ta hada ta dauko tukunya ta zuba madarar shanu 1 cup,ta dafa ta bayan ta huce ta sha abarta ta koshi,sannan ta wanke kwanikan da omo,wani botikin karfe ta dauka Wanda yama gama bulewa ta ko ina ,ta fita,Garin mutane sun fito jefi jefi,wani dattijo me kamala ya tareta cikin hausarsu da batafita yace a,a RAMATA da sauri ta durkusa baffajo ina yini,yace lfy ramata maza ki tafi kiwo,zan aiko,miki da geron hura yau kanji yata,murmushin dadi tayi tare da zuba godiya,gidanta ta cika da ruwa,sannan, ta share ko ina fes,tayi wanka ta tatsi madara a saniyarta ta rufe a daki,ta kada su sai kiwo,da alama haka takeyi kullum.yau ma kamar kullum haka tayi,bayan kwana uku ranar ta kama ranar juma,a ramata bataje kiwo ba, ciyawa da ruwa taba shanunta,fura naga tayi me yawa da lafiyayyan nonon kirdirmo,ta shirya komi a sabuwar kwaryarta da faifai,du komi sabo me kyau,har kokunan dama furar ta,ta sa kayanta me kyau da wani takalmin roba shima ba laifi,sai kasuwa.tana karasawa kasuwa tun a hanya ake ga ramata fillo nan,wasu na ga ramata,wasu fillo,ba wanda ta kula ta nemi waje ta zauna,kafin kace me har ta kusa saida furarta,mata masu talla sai gulma da jin haushin ramata suke. ko ya asalin wannan yarinya take oho Ku biyoni.

Asmah baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

5-10

By
Asma baffa

Cikin murna da jindadi ramata ta siyar da furar ta, tattara komai tayi ta shiga kasuwar ta siyo kayan abinci dan dai dai ta boye ragowar canjin sai gida,a hanya ta tsaya cikin gona tayi ciyawa ta tafi da ita dan bawa shanunta,da kyar ta kai kanta gida sabo da nauyin kaya ga ciyawa,tana komawa ta bawa shanunta ciyawar ta Adana kayan abincinta,wanka tayi,ta fito sai gidan baffajo,sallama ta rangada,inno matar baffajo Ce ta amsa cike da murna tana ah ramata yan mata malam yace ga itacen ki nan a baro ki tura ki kai gidanki,godiya tayi sosai irin taimakon da baffajo ke bata,ta tabbata ko baffanta abinda zai mata kenan,ba ita ta bar gidan ba sai da taci tuwon dare tayi sallah sannan taja kurar itacenta ta kai gida,sosai inno da baffajo ke birgeta dan ba karamin taimaka mata suke ba bata da kamarsu duk fadin rugar su..

Wace ramata

Ramata asalin sunanta rahmah abubakar amma da yake fulani ne usul suke ce mata ramata, Abubakar Wanda aka fi sani da bukar shi kadai ne wajen iyayensa Wanda sun jima da rasuwa sai danginsa,malam bukar mutum ne me tsatsan addini dan kaf garin ba mai illimin addini kamar sa,mutumin kwarai dattijon arziki,da matarsa mero dattijuwar arziki me hakuri ita kadai bukar ya aura,har suka haifi rahmata,Kaf mutan rugar ba Wanda ya kaai bukar arziki,gonaki da dabbobi,a sanadiyar haka yan uwansa suka tsaneshi babu me sonsa,daga shi sai matarsa da yarsu rahmah tunda iyayensa sun rasu,haka rahma ta taso cikin gata da kulawa,ya sata a makarantar islamiyya da boko,dan har wani malam hassan wanda a lokacin yake zuwa daga birni,ya dauka yana biyansa kudi yana koyawa rahma karatu extra lesson kenan duk wani dan turanci a wajen malam hassan ta koya kafin a masa transfer,

Haka mero ta koyawa shatu tarbiya da girki da sauran Ayyuka tun tana karama ta saba,suna cikin jin dadi da koshin lfy,rahma na 13yrs kwatsam wata ranar asabar da dare wasu arna yan fashi suka shigo gari satar dabbobi basu hari ko INA ba sai gidan bukar,motsi malam bukar yaji ya fito yana fitowa suka harbeshi har wuri uku,wannan Harbin ne ya farkar da rahma da mero Inda suka rugo da gudu,yan fashi na ganin zasu Tara musu mutane suka dorawa mero bullet a goshi ko shurawa batayi ba tace ga garinku nan,haka cikin Sauri suka kwashe dabbobin duka yanda suke sauri ne yasa suka bar shanu guda biyu, sa da saniya,sai wata akuya daya sai kaji biyu su kadai rahma taa gada sai gidan da take ciki,ranar mutan gari sunsha kuka,da bakin cikin babban rashi da akayi,sai kuma tausayin rahma kowa da yakeji, wacce sai kuka kawai take ko magana ta kasa,suma kuwa ta suma yafi a irga,da kyar aka shawo kanta,

Amma rashin imanin fulani watarana in ya motsa,ba Wanda ya yace a bashi ita ya rike,sai baffajo da yake mutumin kirkine shi da matarsa,kuma abokin malam bukar na amana,shi kadai take kula da rahma,dan shi ya dauketa tana 14yrs tace ita sai ta koma gidanta da zama,ba yanda ba ayi ba taki ji,yan uwan bukar da mero kuwa ko kulata basa yi,in ta gaishesu ma da kyar suke amsawa,tun tana zuwa har ta dainaa ma,rahma ita kadai take fadi tashi a wannan gida,don Allah yasa me gari ya kafa doka duk Wanda aka kama da mace zaiyi fasikanci hukuncin kisa ne,kuma haka ake zartarwa ko dan uban waye shikenan zaawarawa da yan mata da masu zaman Kansu irin su rahma suke zaaune lfy,

Itakam rahma zuciyarta ta gama bushewa bata tsoro gwara taa dinga tuna iyayenta,baza ta zauna wani wajee ba sai gidan baffanta tana tunawa dasu tana musu addua,dan ta kudirce ko aure baza ta taba yi ba,haka zata kare rayuwarta tana wa iyayenta addua,dan burin rahma kenan,shi yasa bata kula kowa a maza,dan su baffajo sunyi har sun gaji,dan yanzu tana 15 kuma suna aurar da maata suna 12 13 11ma itakam rahma ai kowa kallon tsohuwa yake mata,wai ta tsufa ga kyau ba aure,har tsokanarta suke a gari tsohuwa me Kyan banza,ita kam ko a jikinta,wannan kenan,rahma dai wahala ita ta kara dorawa kanta,dan tana da su baffajo ta zabi zama ita daya tana wahala,ko innce kuruci dangin hauka,ace mace ta kudirce ba ita ba aure maji ma gani, Ku biyoni

Asmah baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

10-15

By
Asma baffa

Haka rahma take kullum yau da dadi ba dadi,gobe taci me kyau jibi ta kwana da yinwa,gata Allah yayota me kara da kunya da kawaici,akan ta roki wani abu awajen wani koda baffajo ne gwara ta kwana da yinwa,gata da hakuri da juriya amma ba aure a tsarinta,baffajo da inno abun na damunsu har me gari sun rasa ya za suyi da ita,gashi duk danginta basa kula lamarinta bare a samu a daura mata aure da wani ko da dan uwanta ne,abinda basu sani ba rahma ta sawa ranta in akace za a aura mata wani to tabbas guduwa zatayi ta bar garin.


Birnin tarayya abuja wani gangamemen gida na hango na alfarma dake cikin unguwar maitama gidane wanda ya amsa sunansa ko a abuja sai an yi da gaske a samu kamar gidan,wasu zaratan sojojine a kofar gidan su 5 suna zagawa da bindigogi,gidane na gaske wajen tsaruwa da kyau Wanda yafi gaban kwatance masu karatu,cikin gidan aljannar duniyane,flowers masu kyau,garden tare da grass carpet,swimming pool har 2 kowanne design daban,ban garden motoci kuwa ba karama,dalla Dalla ne na gaske birjik,part uku ne a gidan part din mom and dad komai golden color ne,sai part din sauran yaran gidan dark brown and golden,sai na babban yaya komai white color ne,gidan ya tsaru komai na akfarma ne,duk yanda zan fada bazai fadu ba,abin ya wuce a iya fada sai Wanda ya gani,

Wani handsome guy na hango yana sakkowa daga saman steps da alama wurin dad take dan a part din yake,wata dattijuwace ta biyosa tana my boy wait tsayawa yayi yana murmushi,turare ta fesa masa me dadin kamshi,yace tnx mum I luv u,kai ta dungure masa tace ammar kenan,wai Ina sauran yara na ne kuma yau banga Ahmad ba,gashi rana har rana tayi,ammar yace mum kin San yaa A.A fa mum shi halinsa daban ne,bari na nemo miki su Mimi suna part dinmu.

Numfashi mum taja tace kafin ka fita ka kira min Ahmad da duka yaran kace ina nemansu kuma karma ka manta yau dady na Neman kowa a dare tunda yau Sunday babu me fita bare ace an gaji,yace yes mum daria sukayi duka ya wuce ta koma wurin dad.

Dare wurin 9 duk yaran dad sun hallara su bakwai maza uku many a mata 4,dady ke bayani kan gidan gonar da zai Gina a wani kauye dake kebbi state,tare da yin gagarumin noma a yankin,yace Ahmad Kaine babba dole da kai a tafiyar this time around,sabo da sadiq ke zuwa irin wannan wurare dan haka yau ba sadiq a tafiyar kuma ka sani dani da kai da ammar da kuma Mimi za a tafi kuma sai munyi 2wks munga komai na tafiya sannan mu dawo,muna da masauki a kauyen da yarana masu kula da harkar,amma dole a fara a idonmu,tunda dad ya fara magana Ahmad ya bats fuska dan baya son doguwar tafiya,kuma baya son nesa da gida,gashi kuma wait kauye zasu zauna har 2wks shikam ya tsani Noman nan da dad ke so,shi began wani alfanu a harkar gona ba,shi an takura masa,amma dole ya bisu ya ya iya,dan a 1 day ma ai zasu iya zuwa a dawo amma ace har 2wks haba,
Shi kuwa ammar da Mimi murna kawai suke,dady yana kula da ahmad ya share shi kawai,suna fitowa daga dakin dad kowa ya baje a palo mum ce ta fito,autarsu amal ce ta fada jikin mum tana momi nima zanje pls mum,mum ce ta shafa gashinta tace amal sai watarana zamuje,da sauri amal ta mike tana kuka ta fice,ita kam salma tabe baki tayi taci gaba da game a wayarta,sadiq kam mum yawa sai da safe ya wuce,ahmad kuwa da magana ma wuya take masa chanel kawai ya canja yana kallon news har suka fara magaba da mum sama sama,mimi kuwa ta cika mum da lbr,haka kuwa akayi kwana biyu tsakani suka hau daya daga dalleliyar motarsu babba,me tsadar gaske,driver na jansu sai kebbi.

Su waye ahmad

By asma baffa
[13:59, 1/24/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挗馃挗馃挗

MARAICIN RAHMAH

15-20
By
Asma baffa


Alh. Abdullah shehu shine dady Baban su Ahmad,dan asalin nijar ne iyayensu wanda sun dade da rasuwa su uku suka haifa,abdullahi,sani sai autarsu hauwa,sani shima yana da arzikinsa ba laifi sabo da shi doctor ne yayi boko,kuma a nijar yake da zama,tare da matarsa fati da yaransa 4,dattijo me dattako kenan,sai hauwa wacce take auren wani ambasador ita tana nijar,dady ne babba kuma shine baiyi boko ba iyakacinsa secondary,kuma shine yafi kowa arziki a family su,kasancewar yana da zafin nema,kuma da san,ar noma ya fara har yayi karfi,noma ne ya kawoshi nigeria kuma ta karbeshi shi yasa yayi zamansa,inda ya samu matar kirki me addini wato aisha mum kenan,abdullah ya mallaki dukiya me tarin yawa da kadarori,ga kamfanonuwa da dama,ga gidajen mai da sauransu,matarsa aisha mum fara tas yar fulanin kebbi ce,a nan suka hadu ya aurota itama...


Read / Download MARAICIN RAHMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album