Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DR AS ZAKI Complete Hausa Novel Document by DR AS ZAKI


DR AS ZAKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 59226



DR AS ZAKI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Safiyya Galadanci ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : EXQUISITE WRITER'S FORUM

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 309.42 kb

File Type: txt

Views: 811+

Download: 1288+

Last download: 27 minutes ago

Description/Story: *Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITER'S FORUM

*SAFIYYA GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY.


SHAFI NA ƊAYA. 1


Tun daga nesa gabanta yake faduwa lokacin data doso hall din tana neman wurin da zata ajiye motar ta, ganin babu kowa a gaban hall din kamar yadda suka saba tsayawa kafin lecturer din ya iso su jira shi, wannan ya tabbatar mata da bazai barta ta shiga ba, hankalinta duk a tashe ta gyara mayafinta bayan ta tsaida motar ta dauki littafinta da karamar Jakarta sai wayarta a ta fito tareda danna lock din motar ta nufi hall din.

Ita kadai ce a wurin ko ina shuru sai muryarsa dake tashi daga cikin hall din da alama dictation yake musu gefen kofar ta samu wuri ta labe tana tunanin shiga dan bata sani ba ko zai barta ta shiga bata taba ganin ya kori kowa ba amma tana matukar tsoronsa, wayarta ta danna tareda kiran kawarta Nana Sule bata dauka ba ta sake lekawa sai suka hada ido dashi tayi saurin ja baya tana dafe kirjinta.

Duk abinnan datake idonsa yanakanta, yana lura da duk wani motsinta, yarasa dalilin dayasa ba dama ta ganshi gaba ɗaya saita firgice masa.
Lokacin daya shigo ajin saida duk ya karewa matan ajin kallo bai ganta ba ya fara tunanin yau bazata zo ba kenan dan bata saba yin latti ba sannan koda yaushe zai ganta a sit ɗin gaɓa sam bata wasa da karatun ta,tunda yaji tsayuwar mota hankalin sa ya lula cen har hakn ya kusa dasa tasirin abinda yake kallo daga ɗaliban dake sauraronsa, wayancewa ya yi ta hanyar ƙara haɗe ransa tare ɗauke dauke idonsa daga kofar dan ya san indai ya maida hankali bazata shigo ba sai dai ya lura da hakan da yayi ma bai sa ta cire tsoron ta shiga ba sai faman lekensa take yi,hakan kuwa ba ƙaramin tasiri yake a kansa ba dan gaba ɗaya ya kasa mayarda hankali akan abinda yake koyarwa,daga nesa da yake ya daga muryarsa tareda cewa "Aisha Nabila is either you come in or disappear from there you are distracting my class(Aisha Nabila kodai ki shigo kokuma ki ɓace daga nan saboda kina ɗaukar hankalin class ɗina)" zaro ido tayi tareda sake lekawa suka hada ido ya dauke nasa tareda ce wa cikin ɗaga murya "get lost if you are not ready(Ki ɓace mun dagani idan har baki shirya ba)" da sauri ta shigo tana jin yadda ido ke matukar yawo akanta tana tafiya kafafuwanta na hardewa, yabita da kallo tareda yin shuru yana mamakin yadda jikinta ke rawa haka, Jakarta da wayarta dake hannunta suka zube a kasa sakamakon tuntuben da tayi yaja dogon tsaki tareda maida hankalin sa ga littafin dake gaban sa.

Saurin kallonsa tayi daga saman stage dinda yake taga ba ita yake kallo ba ta tarkata Jakarta tareda samun kujera daga gaba ta zauna.

Bayan ya gama lectures dinsa ya tarkata yanashi ya fita yana fita ta sauke ajiyar zuciya tareda juyawa bayanta ta kalli Nana sule tana cewa "Banza bazaki kirani ba kinga ya shigo" Nana data taso tazo kusa da ita tana cewa "nima fa yau ina shigowa yana shigowa shiyasa ban kira ba kinsan yadda yake hade rai bazaka ga fuskar yin dogon motsi bama" tsaki tayi ta ce "bar banza gashi ba abinda ya iya se note ni banma san ya akayi yakai matsayin Dr ba" Dariya Nana tayi tana cewa to nidai tashi mu tafi bacci nakeji wallahi" mikewa tai tana cewa "muje amma sena siya abu a refreshment centre din can dan tsabar sauri ba abinda naci yau" fitowa sukayi suna tafe suna surutu irin na kawaye tareda gaisawa da sauran yan ajinsu suka nufi shagon meat pie ta siya guda bakwai tareda sprite babbar roba tayi sanyi sai tsiyayar ruwan raba take, suna tafiya Nana Sule ta ce "ke wai har yanzu baki rage ci ba" ta buntsire bakintana cewa "ai wannan dan tabawa ne zanyi ina gaya miki ga dumamen tuwo can na baro ayimin ina komawa zan bashi mamak..." wani irin dauke numfashi tayi sakamakon karon da suka ci da Dr zaki, shikanshi ta bashi tsoro ganin yadda tayi amma sai ya raba gefensu ya wuce batare daya nuna yama kula da hakan ba, muryarta tana rawa ta furta, "Am so sorry sir" ko waigowa baiyi ba bare ta saka ran zai kula ta. Nana Sule ta dungure mata kai tana cewa "ke dan ubanki ajalinki kika gani"? Bata ce komai ba ta sake rike ledar dake hannunta tayi gaba da sauri tana tuno yadda suka hada ido tana cewa zata bawa tuwo mamaki, sai da ta zauna a mota ta dauki meat pie guda daya ta Gutsira tareda lumshe ido tana cewa "akwai abinda yafi abinci dadi a duniya"? Nana ta harareta ta ce "Akwai wallahi" ta girgiza kai tanancewa "karya kikeyi babu shi, duk me zakimin duniya ki burgeni befi kiyimin abinci kala-kala ba masu dadi" Nana tace akwai shi fa sai dai dan baki sanshi ba ne amma ki bari idan lokaci yayi zan fada miki akwai abinda yafi abinci dadi, ko hadi babu yarinya" shuru tayi mata lokacin da take reverse saida ta hau babban titi ta ce "ina so insamu waje daya mai inuwa inringa ajiye motar nan kinji yadda ta dau zafi" Wayar Nana Sule tayi ringing ta bude Jakarta tareda daukowa murmushi tayi tace "kiyimin shuru na gasken ya kira" dariya tayi kawai, baka ce ba sosai ba amma dai baka ce siririya gaba daya batada jiki irin wanda kallo daya zakaga mace cikakkiya mai daukar hankali sai dai tanada kyau da gashi sannan kuma tana da tsayi daidai misali wannan dalilin ya saka batada kayan da suka wuce doguwar riga, sam bata shaawar dinka riga da skirt duka kayanta doguwar riga ce.

Dr zaki Rike da robar ruwan faro ya fito daga shagon yayi saurin dauke idonsa daga kallonta, baisan wane department take ba amma kullum sai ya ganta a lokuta mabambanta, shigarta tana kona masa rai saboda irin tsarin halittar ta ta kasance mai daukar hankali gata fara tas mai kyau kamar balarabiya, wannan karon riga da skirt ne ajikinta na atamfa sun kamata ta sosai sai wani munafikin mayafi sannan ta bude rabin gashinta duk a waje tana tafiya da earphone a kunnenta, samun kansa yayi da juyawa yabi ta parking space a tsakiyar motoci ya haura sama ta baya ya shiga office dinsa dayayi matukar tsaruwa, zama yayi kan doguwar kujera ya janyo table dinda ke gabansa tareda dora ledar takeaway dinda ya aika aka kawo masa ya bude tareda karewa abincin ciki kallo yayi murmushi mai ciwo saboda Sam baya kaunar abincin siyarwa, gashi shi mutum ne mai son yaci abincin daya yarda dashi amma ya kasa samun wannan damar saboda wani dalili.




Baki ne shima saidai ba sosai ba lip dinshi na kasa pink na sama brown yanada manyan ido da madaidaicin hanci dogo ne sedai yanada jiki baya tara sugar kai amma yana tara saje da gemu wayanda yake kashe lokaci wajen gyaransu suna kuma kawata faffadar fuskarshi da kara masa kwarjini, ya kasance mutum mai son manyan kaya irin na aladarshi ta hausa.

Yana kokarin kai spoon bakinshi aka kwankwasa kofar ajiye spoon din yayi ya kurawa kofar ido....

Fiyyah.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM

*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA BIYU




Mikewa yayi tsaye tare da gyara rigar shi sannan ya nufi kofar ya bude, daga kasa ya dauki kallonta har sama ya sake dawowa da idonsa kasa yai mata irin kallon nan na rainin wayo fuskarsa babu alamar fara'a ya hade girar sama data kasa muryarsa a hankali amma acikin tsawa ya ce "menene"?.

Tunda ya bude kofar taga irin kallon da yake mata tasha jinin jikinta tareda diriricewa bayan ya tambayeta ta soma kame-kame tana cewa "oppis din malam Umar nake nema lakcara ne" kallon kofarsa yayi ya kalleta amma sai yaga taci gaba da tsayiwa shikuma sunan dake jikin kofar yake nuna mata amma bata fahimta ya dan ja baya ya ce "wane department" tana sosa wuya ta ce "political adminisitirashon" ya yamutsa tareda cewa "ke get out" ya rufe kofar shi tareda komawa ya zauna yana cewa "wasu ma samun admission dinsu a jami'a kawai sa'a ce ayita yayibo mana jidali" zama yayi tareda daukar abincin ya soma ci bayan yayi bisimillah.

Nana sule ta fara saukewa gida sannan ita ta wuce, tana shiga gidan ta hadu da babban yayansu mayafinta ta gyara tareda gaida shi tana washe masa hakora yana amsawa ya karbi ledar da take mika masa meatpie ne aciki ya dauki guda daya yana cewa "Acici mala'ikun tauna, har yanzu dai sai abinda yayi gaba ko" tayi murmushi tana cewa "yaya nafa rage tunda kace kar inrasa miji" dariya yayi yana
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DR AS ZAKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album