Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

NAWAFF Complete Hausa Novel Document by NAWAFF


NAWAFF

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 70068



NAWAFF

Reading Time: 5 Hours

Added On: 25, Feb 2025

Author: Bilkisu Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09093044460

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 426.6 kb

File Type: txt

Views: 199+

Download: 377+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: ☆☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆☆


NA BILKISA IBRAHIM💞




DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINK'AI, ya ALLAH kabani ikon fad'ar abinda zai amfani al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar da al'ummarka.


Assalamu alaikum,
gaisuwa da fatan alkairi, inamai farin cikin sake had'uwa daku asabon littafina mai suna NAWAFF, ALLAH yasa ya amfanar damu baki d'aya. Amin
🙏🏻.



Page👉🏻1&2

Yau antashi da tsananin zafi, saka makon ranar data kwalle🌞, mutane kowa yana neman mafaka, a karkashin rumfa ko bishiya.
Ga k'arar ababen hawa data cika birnin na kano, dukda katafaren gosulo d'in daya cinkushe titin, dayawa mutanen dake cikin moto cin sun gala baita, da tsananin zafin ranar.
Amma wannan bai hana 'yan tallah daf dalaba suna yayata tallar ababen sana'ar su, musamman masu tallar ruwa, saboda yanayin zafin mutane suna buk'atar ruwa mai sanyi.
Nakai dubana bisa wata farar mota mai k'yawun gsk, wadda daka mata kallo d'aya kasan mai ita yagama wada tuwa.
Wata k'yak'yk'yawar yarinya nagani kwance a bayan motar, farace saidai farinta bamai haskeba sosai, tanada kala irinna 'yan itopia, tanada dogon hanci da manyan idanuwa, kwance take abayan motar tana nazarin littafi.
Agaba kuma direbane, tad'ago kai tareda fad'in balarabe kaga abinda nake jiye mana ko?, shiyyasa nace kar mu biyo ta nan, gashi har ina neman makara, kuma inada lectures yanzu wlhy.
Balarabe ya ce, "kiyi hak'uri hajiya, wlhy banyi zaton zamu sami wannan cinkoson ba.
Ta d'anyi k'aramin tsaki tana fad'i ni wlhy saima karasa abinda yake haddasa irin wannan cinkoson a garin kano?, batareda ta saurari sharhin da balarabe yake mataba ta bud'e motar ta fice.
Tafito dai2 sanda wata jar mota 'yar k'arama ta tsaya saitin ta, ahankali aka zage gilashin motar zuwa k'asa, wani had'ad'd'en saurayi ya bayyana, saikuma wani danake tunanin abokinsane.
K'yak'yk'yawan saurayinnan ne matuk'in motar, kallo d'aya zaka masa ka gano yana cikin farin ciki, dan sai kad'a kai yake da alama wak'a yakeji, kuma wak'ar tana masa dad'i.
Ya d'akko kwalin hollanddia yana sha ahankali yana cigaba da kad'a kai, harda had'e yatsun hannunsa biyu yana bugawa.
Karku d'auka wannan k'yak'yk'yawar yarinyar shitake kallo, A'a ko kad'an hankalinta baya kansa.
Jitai wani abu yadaki k'irjinta, da sauri ta kalli jikinta.
Hummm kunsan miye kuwa??.
Ba wani abu bane illa kwalin hollanddia da gay d'innan yake sha, takuma bin jikinta da kallo, dan ganin yanda yogot d'in yay mata kaca2 da bak'ar jallabiyar dake jikinta, ta maida kallonta ga motar dan ganin wane wawane yay mata wannan aikin??.
Saitaga mutum yana kallonta yana tuntsirar dariya harda dukan sitiyari, d'ayan saurayin dake gefensa ya d'ago yana kallonsa, ya ce, "kai malam lafiyarka kuwa?, kanata dariya kai kad'ai kamar wani shafar aljanu.
Cikin dariya ya nuna masa yasmeen dake tsaye tamkar gunki tana kallon ikon ALLAH, tana mamakin wannan wane irin shashashan mutum ne, yayi mata abu amma yana nunata yana dariya.
Mas'ud ya ce, "amma kaidai d'an iskane NAWAFF, yazaka b'atama yarinya jiki, kakuma rink'a yimata dariya??.
Kasan kuwa wacece wannan kalli nomber motar data fito fa.
NAWAFF ya gallama Mas'ud harara yana fad'in aii bani nace tazo ta tsaya anan ba tana yima muta ne iyayi ko?, dazakace nawani kalli nomber mota, to saimi idan na kalla.

Duk abunda suke fad'i Yasmeen tana jinsu, dan haka sai zuciyarta tak'ara tunzura, cikin fasifa ta k'arasa gurin motarsu.
Ta ce, "kai wawa wanda baisan darajar mutaneba, shin kobaka ga b'arnar dakayi bane??.
Cikin fushi NAWAFF ya kalleta ya ce, "waye wawan??.
Itama cikin tsiwa ta ce, "masa kai mana!!!, ko wawan yayi maka kad'an saina had'a da mahaukaci, dan naga kanada k'aramar kwakwalwa.
Afusace yabud'e mota yafito, ya wanka mata mari, jikake wani tasss.
Dayawan hankalin mutane yadawo gurin musamman 'yan tallah.
Ta dafe kunci tana kallonsa, sai kuma ta d'aga hannu itama zata wanka masa mari.
Da sauri ya rik'e hannun ya murd'e, ta ce, "kai karamin d'an iska ka sakar mini hannu, hannu yad'aga zai k'ara marinta mas'ud yay saurin shiga tsakkiyarsu, ya ce, "haba NAWAFF yazaka mata laifi sannan ka daketa??.
Cikin masifa ya ce, "dalla malam nibakaga raahin kunyar datake minbane?, ko kai kurmane?.
Mutane sai kallonsu sukeyi.
Mas'ud ya ce, "haba NAWAFF kasan dai fuskarka sananniyace dammi zaka aikata haka?, yanzu sakaji 'yan jarida suna yayataka aduniya kadai sani sarai.
NAWAFF yaja tsaki, karsu fasa gayawa duniya abinda nayi kajiko, kodan kar afad'ama duniya saina zauna yarinya k'arama tayimin rashin kunya.
Ya juyo gareta 👉🏻ke kuma ki rubuta ki ajiye saina nuna miki ni👈🏻 nafi mahaukaci hauka.
Yasmeen taja tsaki ta ce, "wlhy nikuma saina nuna maka nike maganin dukkan wani mahaukaci komai haukansa.
Aifa yasake harzuk'owa zai mareta, mas'ud dake tsakkiyarsu ya kare, wai ku miye hakane? dan ALLAH, waishin bakwa ganin kallon da'ake mukune??, gashi kun tarema mutane hanya.
Sai asannan NAWAFF ya lura gabansu babu kowa, duk tarin gosulo d'innan ya b'ace, saidai mutanen dake bayansu, sunata danna musu hon.
Balarabe da tund'azu yake bama Yasmeen hak'uri, amma tak'i saurarensa, ya ce, "kiyi hak'uri Hajiya kizo mutafi kinga kin makara.
Harara ta watsa masa sannan taja tsaki, mas'ud ya ce, "plz kiyi hak'uri dan ALLAH kinga a titi muke.
Juyawa tayi ga motarsu dan ganin kawai kallon da'ake musu, amma tad'auki alk'awarin duk ranar data sake had'uwa da gay d'innan saita nuna masa shi k'aramin d'an iskane wlhy.......................✍🏻

Tusk'ashi masu karatu, komi zai faru?, shin waye NAWAFF??? Miyasa 'yan jarida zasu iya yayatashi???? Wacece Yasmeen?? Kuma 'yar wacece??, kubiyoni danjin amsoshi tambayoyinku....

Taku har kullum BILKISA IBRAHIM (Bily)
( Mrs Abdus'salam)
Ku kasance dani!!!!!!👈🏻

Zaizo gareku nanbada dad'ewaba......😘😘luv u oll

©2016
💞Bilyn Abdul💞

[1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆




NA BILKISA IBRAHIM💞




page👉🏻3


Ta ce, "da direba maidani gida.
Cikin tsoro ya ce, "to hajiya makarantar fa??.
Cikin masifa ta ce, "gida nace ka maidani ba dogon bayani na tambayeka ba, kajiko.
Ya ce, "yi hak'uri hajiya ALLAH ya huci zuciyarki.
Bata tanka masaba domin zuciyarta sai tafarfasa take, babu abinda take tunowa sai abinda gay d'innan yay mata.
Tun kafin yayi fakin tayi waje, da gudu tashiga gida.

Humm kunsan abinda yaba ni mamaki??, gidan da yarinyar tashiga daka gani gidan talakawane, bazaka tab'a tunanin yarinyar da motar 'yan gidan bane,, tokomadai miye agaba zamu sani.

Tashige falon tana kuka.
Wata dattiyuwar mace tana zaune a matsakaicin falon, farace tas maik'yau, suna kama da yarinyar, daka ganta kasan ma haifiyarta ce.
Tafad'a jikinta tana kuka, cikin hanzari dattijuwar ta rungume d'iyar tata tana fad'in yasmeen injidai lafiya?, bakije makarantar bane??.
Cikin kuka ta ce, "umma bamun tafiba shine gosulo ya rik'emu.
Umma ta ce, "to mikikema kuka? Ko gosulo d'in?, ta girgiza kai alamar A'a.
To minene?, umma ta tambaya.
Ta share hawaye bawani ne ya mareniba, mari kuma? Miki kai masa?, tana kuka tana bama umma labarin abinda yafaru.
Umma tashiga lallashinta tana bata hakuri, babanta yashigo da sallama, dan tunda suka shingo yagansu, yatsaya tambayar balarabene abinda yafaru.
Yashafa kan yesmeen ya ce, "karki damu mamana ALLAH yana tareda masu hak'uri, dan haka kiyi hakuri watarana sai labari.
Ahankali tad'ago manyan idanunta wad'anda sukayi jajur saboda kuka, ta ce, "karka damu abba kabarni dashi dakaina zan rama, wlhy abba saiya raina kansa, dan na daina zama ana rainamu, dan kawai muna talakawa saikowa ya ce, zai rainamu, abba aii babu maraya sai rago.
A'a mamana kibarsa kawai kinji, abbanta yafad'a yana shafa kanta.
Shuru tayi batace komai ba, dan tasan bazata iya hak'ura ba.
Umma ta ce, "mudai idan tamune ki hak'ura, yasmeen bana son tsiwar nan taki, idan kikayi hak'uri sai ALLAH ya saka miki, ki barmu muji
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download NAWAFF

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album