Join Our WhatsApp Group

NOORUL HUDA Complete Hausa Novel Document by NOORUL HUDA


NOORUL HUDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 181297NOORUL HUDA

Reading Time: 15 Hours

Added On: 14, May 2024

Author: Khaleesat Haidar ,

Ebook Compiler : Umar Dalha Funtua.

Author Group : Haske Writere

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 912.5 kb

File Type: txt

Views: 399+

Download: 1072+

Last download: 22 minutes ago

Description/Story: Compiled By Umar Dalha Funtua.All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance, priviledge and ability to write this Novel, i dedicate this first page to my sweet siblings and our Mum like no other, Allah ya bar min ku Ameeen.
My Special greeting goes to my frnd my abokin fada *Captain Ajay* ⚓ Allah ya kare ka ya biya maka bukatun ka na alkhairi a duk inda kake.

💫 *Noorul Huda* 💫1......

A hankali ta karashe rufe windows din dakin ta juya tana kallon makeken agogon dake manne bango dakin, karasawa gefen gado tayi ta xauna murya can kasa tace "Rain? Not today pls..." Bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri Mahaifiyarta dake tsaye bakin kofar tace "Ki tabbatar kin sa sweatern ki, kiyi addu'a ki kwanta haka kuma sai da safe!" Bata ce komai ba uwar ta juya ta fita, sake kallon agogo tayi taga bakwae da kusan rabi, Wayarta dake ajiye kan gado ya shiga ring ta mike ta dauka ganin me kiran ta daga ta kai kunne tace "Hello!" Daga daya bangaren aka ce "Kar ki ce min baxa ki xo ba sbda ruwa?" Ajiyar xuciya ta sauke tace "Kema kin san mumy...." Katse ta tayi tace "A'a gaskiya baki min adalci ba, it's already dark just sneak out ki fito yanxu bbu wanda xai sani ae kince Abba baya gari fahhh" D'an langwabar da kai tayi tace "Alryt bari inyi kokarin yin hakan, gani tahowa" daga haka ta ajiye wayar, cikin kankanin lokaci ta gama shirinta ta dau jakarta ta saka waya da kudi snn ta dau rain coat ta saka, ta kashe fitilar dakin, cikin sanda ta fito daga dakinta, ta dinga bin corridor da kallo dim haske ta hango daga bedroom din Mum dinta ta sauke ajiyar xuciya a hankali don tasan me take yi, tana gamawa kuma xata kwanta sai kuma gobe, da sauri ta sauka downstairs taga duk an kashe fitilun parlon ta nufi kitchen tana lalube lalube ta bi ta kofar kitchen din ta fita ta tura a hankali ba tare da ta rufe ba, ko da ta isa gate mai gadi bai ce mata komai ba ta bude gate ta fita, da sauri take tafiya don anguwar tsit bbu kowa sai haske, a haka ta isa babban titi ta samu d'an sahu ta fadi masa inda xata ta shiga, haka kawai gabanta ke faduwa don tunda take bata taba abinda ta yi ba yanxu, gashi dai yau kawa ta sa ta, kawar ma warce basu jima da sanin juna ba, basu kuma wani saba ba, takwas saura ta isa wani babban gidan duk da ruwan da ake tsulawa hakan baxai hanaka jin sautin kidan dake tashi a gidan ba, ta shiga gate jiki a sanyaye ta karasa kofar da xai kai ta babban parlon da ake birthday din, mata ne da maxa a cakude ana ta rawa abun ba tsari, k'awartata wato celebrant din ta hango ta ta karaso da sauri cikin flowing gown dinta ta rungumeta tace "Ohh babe am happy you came to ki cire rain coat din mana, you are already missing" sauke hulan tayi tace "But i never knew the birthday will be like dis, it's just disorganized...." Katse ta tayi tace "Nothing is disorganized a nn idan xaki karaso ayi bidiri da ke ki karaso" tabe baki tayi ta cire rigar ruwan jikinta, doguwar gown na kanti ne jikinta me kyau ta saki dogon gashin kanta kawarta ta kashe mata ido tace "Waow besty kinyi kyau ina ma Boo dinki ya gan ki yanxu" murmushi tayi tace "Uhm" hannunta ta ja suka karasa inda ake ta shagalin birthday din, waje ta samu ta xauna ta dau maltina ta bude tana sha tana kallon yanda mata da maza ke ta watsewar su ga hayaki ko ta ina, duk bata saki jiki ba a gun abun ka da wanda bai saba ba, a xuciyarta kuwa tunani ta dinga yi anya xata iya ci gaba da tarayya da Clara kuwa, she's rough, bata yi minti goma da xama ba wani guy ya dawo inda take ya xauna yace "Hi babe how you doing?" Ta d'an kallesa tace "Good" yace "Pls may I know you futher?" Girgixa kai tayi tace "Noo" yafito ta da Clara ke yi yasa ta mike ta nufeta, ya bi ta da kallo, can ya kalli drink din da take sha, cikin seconds din da basu wuce 7 ba ya fiddo wasu kwayoyi ya jefa a gwangwanin malt din snn ya fiddo wayarsa da sauri yana dannawa, ba a dau lkci ba ta dawo ta xauna ta ajiye sticks din meat dake hannunta da cake ta dau gwangwanin malt din ta ci gaba da sha, ya cije lebe yana d'an murmushi bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba, bayan kusan minti goma taji ta fara jin bacci sosai, mikewa tayi da kyar tace "Excuse me" ya mike shi ma yace "Ohh no probs, gida xa ki ne?" Ta d'an kallesa sai kuma tace "Ehh" yace "Toh mu je kiyi ma kawar ki sallama sai inyi dropping din ki that's my duty here" bata ce masa komai ba suka karasa gun Clara, da mamaki tace "Haba babe da wuri haka" a takaice tace "Ehh am feeling sleepy" kallon guy din tayi sai kuma tayi murmushi tace "Toh shknn take her home directly plss Sam" Yace "Alryt" da sauri ta nufi kofa jin kamar kanta na juya mata, suna fita ya kama hannunta suka nufi gun motarsa, xuwa lkcn ruwan ya d'an tsagaita sai yayyafi, ya bude gaba ya sa ta snn ya shiga ya ja motar suka fita, basu yi nisa ba yyi parking yace "Baby ina ne gidan naku" ta kallesa da sexy eyez dinta tace "Tarauni...." Ya kamo hannunta yace "Ohh that's very farrr" bata ce komai ba ya fara shafa hannun a hankali yana jan long fingers dinta, ta lumshe ido tace "Take me home...." Jawota yyi jikinsa yana shafa fuskarta lkci daya ya shiga tura hannunsa rigar ta ya kwantar da kujeran motar cikin tsawa tace "Stop itt...." Sosai idonsa ya kada cikin lallami yace "baby...." Wani mari ta sauke masa ta bude motar ta fice ya xaro ido hannunsa dafe a kuncinsa, fitowa yyi da sauri shi ma tana ganin haka tafara gudu duk da juya mata da kanta yake, iya karfinta take gudun yana biye da ita, suka yi nisa sosai, taji ta kasa ci gaba da gudun, a gaban wani gida ta hango wani mutum tsaye yyi backing flowers waya na kare a kunnensa, tana haki ta karasa kusa da shi jikinta na rawa tace "Help plsss...." Tsit tayi ganin taban dake dayan hannunsa ta juya da sauri xata bar wajen ya yarda taban ya fincikota, ihu ta fasa dai dai lkcn da Sam ya karaso gun, kallo daya biyu yyi ma mutumin sai kuma ya juya ya koma inda ya baro motarsa, sai ta gwammace da ma a hannun sam din take akan wnn mutum kkrin kwace hannunta take ko ina na jikinta na rawa amma ta kasa, wani kallo yake mata daga sama har kasa da manyan idonsa, ta fashe da kuka a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri ka kyaleni" fixgota yyi dai dai fuskarsa yace "Me ya fito da ke da?" Turarensa mai dadin kamshi da ya hade da warin taba duk ya isheta, ganin jiran amsa yake bakinta na rawa tace "Birthday din k'awata na fito" daga sama har kasa yake kallonta yace "Shine aka biyo ki xa ayi maki fyade knn?" Hawaye ne ya shiga bin kuncinta ta kasa cewa komai yace "Da na san daga inda kika fito knn da na bari yayi fata fata da rayuwar ki...." Daga haka ya tura ta ta bar gun da sauri tana gudu, bin ta yyi da kallo har ta kusan shan kwana sai ya ga ta tsaya, wasu samari biyu ya hango tsaye gabanta duk da ba wani haske gun, ta juya xata canxa direction wani ya sha gabanta, jan ta yaga suna yi xuwa gun wani mota da alama tasu ce ya xaro ido kafin ya ankare har sun isa gun motar yana kuma iya jiyo ihunta daga inda yake duk da uban nisan wajen, wani mahaukacin gudu ya saka kamar xai tashi sama kafin yaje har sun tada motar sun ja, yace "Shit!" juyawa yayi ya koma gun motarsa da sauri ya shige ya kwasa a dari da sittin ya bi bayansu, da kyar ya kamosu a dai dai wani round about ya kusa cin karo da su ya bude motar ya fito daya daga samarin ma ya fito da shirin masa bala'in ya buge masa mota bai ko sauraresa ba ya bude backseat din motar yaga bakinta suka rufe da wani kyalle, fixgota yyi daga motar duk suka tsaya kmr sokaye suna kallonsa ya bude tasa motarsa ya jefata a baya ya koma driver seat ya shiga ya ja motar, tafiya yayi me nisa kafin yayi parking gefen titi ya juya yana kallonta kife kanta ya ga tayi a bayan motar, yace "Keeeh" ya ji shiru, wani tsawan ya sake mata nn ma bata dago ba, ya bude motar ya fito da sauri ya bude backseat din ya dago kanta yaga ta dawo, xaro ido yayi ya shiga motar da sauri ya rufe ya dago kanta, komawa baya yyi jin warin abinda ya bugesa, yayi saurin cire kyallen ya wurgar waje, gashin kanta ya mayar baya yana kallon fuskarta, idonta a lumshe ga lashes kamar an dasa su ne, hancinta dogo kamar an xana mata, a hankali ya sauke idonsa kan karamin bakinta me kala biyu pink nd black, dauke kansa yayi sai kuma ya kwantar da ita ya bude motar ya fita ya rufe ya jingina jikin motar yana tunanin yanda xai yi da ita, d'an bude ido yayi sai kuma ya bude motar da sauri ya shiga ya dagota ya kai hannunsa dai dai hancinta, tsaki yayi ya saketa ya dafe kansa, can ya kwanto a hankali ya kai bakinsa dai dai nata, ya sa hannu ya bude bakin nata ya daura nasa kai ya shiga hura mata iska, ya kusa minti bakwae yana haka tayi wani uban atishawa ya dagata ya koma baya da sauri ya ciro handki aljihunsa yana goge bakinsa da fuska, a hankali ta bude ido sai kuma ta mike xaune ta rike kanta, shi dai kallonta kawae yake, sauka yaga take son yi daga kan kujera ya rike ta yace "ke malama stay still...." Ta fashe da kuka tana jujjuya kanta tace "Where is this please take me home my head is aching" wani uban harara yayi mata kamar tana kallonsa yace "Wani ya fito da ke yawon birthday?" Da kyar ta bude idonta da yayi jajur tana kallonsa muryarta na rawa tace "Take me home pls kaina na ciwo...." Tsaki yaja ya jefar da handki din hannunsa ya fito ya koma front seat ya tada motar ya hau titi, a fusace yace "Ina ne gidan naku?" Cikin muryar kuka ta gaya masa, waka ya kure yana bi don ma ya daina jin sautin kukan nata, parking yyi kamar wanda aka umarta yyi hakan, sai kuma ya fara reverse har ya iso wani babban pharmacy da ya wuce, ya bude motar ya fito ya shiga ciki bude motar tayi xata fita ta kasa don ji tayi kmr duniyar aka aza mata a kai ga wani jiri da take gani, ta fashe da kuka ta koma ta xauna, ba a dau lkci ba ya dawo rike da ledan Magani ya bude inda take ya jefar mata snn ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, tana masa kwatance har suka iso gidansu, ya juya yana kallonta da d'an mamaki bayan ya gama kare ma makeken gidan kallo, ta bude motar da kyar xata fita ya daure fuska yace "Ga Magani nn for the sake of Allah and Islam!" Kallonsa tayi da rinannun idonta sai kuma ta dau ledan ta fita daga motar saura kiris ta fadi amma hakan bai sa yace komai ba, tana layi ta nufi gate, yayi tsaki yayi reverse ya kwasa da gudu ya bar wajen, a daddafe ta isa bedroom dinta ba tare da ta yrda tayi ko wani kara da xai ja attention din mum dinta ba, ta jefar da ledan drugs din hannunta ta fada kan gado ta shiga juye juye hawaye na sakko mata.

📚✍🏻
[7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk: 💫 *Noorul Huda*💫

2......

Yana gama parking a space din da aka tanadar don yin hakan a gidan ya bude mota ya fito, kalle kalle ya dinga yi kafin ya xaga xuwa gun shan iskan dake gidan ya ciro kwalin cigarette a aljihunsa da lighter ya ciro stick daya ya kunna mata wuta ya hau zuka, stick biyu ya gama da cikin d'an kankanin lkci ya mayar da sauran aljihu snn ya mike ya koma gun motarsa ya bude ya fito da wani abu kamar turare ya feshe bakinsa da shi ya mayar ya kulle motar snn ya shiga gida cike da tafiyarsa ta kasaita, a hankali ya murda kofar parlor ya shiga ya rufe a nutse yanda baxa a ji ba yana kallon agogon dake manne parlon yaga har karfe daya, xaro ido yyi da mamaki, how time flies, yaushe ya ajiye yarinya snn yaje gidan frnds dinsa suka tafi club amma har lkci ya wuce haka bai sani ba, stairs ya nufa yana tafiya a hankali kada ma aji footstep dinsa, yana isa corridor din rooms aka bude wani kofa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 da wani abu ba ta fito tana kallonsa, wara ido yayi yace "Mamiiii!" Ta karaso inda yake bbu yabo bbu fallasa tace "Daga ina kake Abuturrab?" Ya shiga sosa kai yace "Am Mami daga clinic nake ban gama aiki da wuri...." Ta girgixa kai tace "Karya kake!" Shiru yayi bai ce komai ba, Cike da damuwa Mami tace "Yanxu Aliyu baxa ka ma kanka fada ba, it's high time fa kasan inda ke maka ciwo, banda bin mutanen banxa bbu abinda ka iya a rayuwa, what's the use of this, me yasa baxa ka bar ni in huta bane a rayuwar nan, idan kanninka suka yi kuma kace me?" Shiru yayi ya sinnar da kai bai ce komai ba, ta karasa gabansa kamar me son gano abu, ya rike breathe dinsa da sauri, ta kamo hannunsa ta kai hancinta ta girgixa kai tace "Ae shknn, continue destroying ur life, ur being an only son does not mean u are an only child...." Ya marairaice yace "Plss Mami am sorry...." Tsawa tayi masa tace "Shut ur mouth!" Yayi shiru yana kallonta ta juya ta shige bedroom dinta ta...


Read / Download NOORUL HUDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album