Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADIYU Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADIYU


HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8864



HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADIYU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 45.92 kb

File Type: txt

Views: 579+

Download: 124+

Last download: 1 day ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

HIK’AYAR ALIYUL MASIRIYI D’AN HASANUL
BAGADADIYU
An bada labarin cewa akwai wani attajiri a birnin
Masar, ya kasance ya mallaki dukiya mai yawa
da kadarori na daga jirage da bayi da gidaje
wad’anda sun fi gaba k’idaya.Sunansa Hassan
mai Jauhari, asalin mutumin Bagadaza ne. Haka
kuma Allah ya albarkace shi da wani d’a mafi
kyau daga mutanen wannan zamaninsa. Ya
kasance mai kyawon fuska, madaidacin tsayuwa,
mai santsin kundukuki, ma’abocin kwarjini da
cikar kama da k’oshi. Ana kiran wannan yaro
Aliyul Masiriyi. Yana da ilmin Alk’ur’ani mai
girma da sauran ilmai na fasaha da dabarun
zaman duniya. Bayan ya samu ilmin da ake
buk’ata sai ya zauna wajen mahaifinsa yana
koyon kasuwanci har zuwa wani lokaci mai
tsawo sa’adda cuta ta kama mahaifin nasa, ya
zamana kullum ciwo na dad’a yin gaba gaba, har
dai ya sakankance da mutuwa. Ya kira d’an nasa
ya ce da shi. “ya d’ana hak’ik’a duniya
k’ararriya ce, lahira ce madauwamiya. Duk abin
da ke wannan duniya tilas wata rana ya k’are. Ka
sani kwanakina na wannan gida sun zo k’arshe,
zan tafi zuwa ga Ubangijina. Zan yi maka nasiha,
idan ka rik’e ta ka yi aiki da ita ba za ka talauce
ba har ka koma ga ubangijinka. Amma idan ka yi
watsi da ita ka k’i aiki da ita za ka had’u da
wahala da talauci da wulak’ani a rayuwar ka ta
duniya.” Ali Masriyi ya ce, “ Ya mahaifina, ta
yaya zan ji umarninka daga kalaman bakinka na
aikata sab’anin haka alhali kuwa doka ta wajabta
min yi maka biyayya sau da k’afa?” Ya ce, “ka
sani ya d’ana na bar maka gidaje da kadarori da
dukiya mai yawa ta fi gaban k’idaya. A ciki
kullum ka fitar da dinari d’ari biyar ka yi sadaka,
ba za ka tab’a samun raguwa ba. Ina yi maka
nasihar ka ji tsoron Allah, ka yi biyayya ga
umarnin fiyayyen halittu Annabi Muhammadu mai
tsira da amincin Allah su tabbata gare shi. Ka yi
aiki da umarninsa, ka hanu da haninsa na daga
hadisansa, ka zama mai koyi da sunna tasa bisa
ga aikata alheri da ba da nagarta da abotaka da
mutanen kirki. Ka zama mai sulhu tsakanin
wad’anda suka b’ata. Ka rungumi ma’abota ilmi
sannan ka yi huld’a da talakawa, ka rik’a
yalwatawa miskinai da mabuk’ata. Ka guji huld’a
da miyagun mutane. Kada ka yi ciniki cikin
shubhu, ka rik’a duba ayyuka na k’asa da kai
kana kyautata musu. Sannan ka lura da matarka
da kyau, domin ita d’iyar manyan mutane ce, na
zab’o maka ita domin kwad’ayin Allah ya azurta
ku da haihuwa ku haifi ‘ya’ya nagari.” Ya cigaba
da yi masa nasiha da wa’azi shi kuwa Aliyu na
kuka yana amsawa. Ya ce, “ya d’ana, ni ina
rok’on maka Allah mad’aukakin Sarki, Buwayi
Gagara misali, Ubangijin sama da k’asa da
al’arshi mai girma da ya kub’utar da kai daga
dukkan wani bala’i da zai same ka.” Aliyu ya
sake fashewa da kuka mai tsanani yana cewa,
“ya Abbana, ni kam na narke daga zantukanka,
domin wad’annan kalamai ne irin na wanda ke
bankwana da duniya.” Uban ya amsa ya ce,
“haka ne, ni kam tawa ta k’are.” Ya yi ajiyar
zuciya yana mai fad’in kalmar shahada yana
ambaton wasu surori na Alkur'ani mai girma har
zuwa lokacin da ransa ya kusa fita. Ya ce da
d’ansa, “matso kusa da ni.” Ya matsa kusa, ya
sumbace shi. Ransa ya fita daga gangar jikinsa
ya tafi ga rahamar Allah. Ali Masiriyi ya zauna
yana cikin bak’in ciki. Ya durkusa bisa
gwiyoyinsa yana kuka, abokanen mahaifinsa suka
shigo suka kewaye gawar suna addu’a. Daga nan
aka shirya shi aka yi masa sallah aka kai
mak’abarta aka binne.
Bayan an binned gawar mutane suka kewaye
kabarin suna addu’a tare da karanto wasu
surorin na Alkur'ani mai girma. Daga nan suka
juyo zuwa gida suka yi wa d’an marigayin
ta’aziyya sannan kowa ya kama gabansa. Ali
kuwa ya tafi masallacin Juma’a ya yi wa
mahaifinsa addu’a ta musamman, sannan ya
rik’a yi masa addu’a duk dare har zuwa kwana
arba’in, a wannan tsakanin kuwa ba ya fita
ko’ina sai masallaci. Duk juma’a kuma yana
zuwa kabarin mahaifinsa yana yi masa addu’a.
Ya cigaba da wannan d’abi’a har zuwa lokacin
da ‘ya’yan fatake suka d’unguma zuwa gare shi,
suka gaishe shi sannan suka ce da shi, “har
yaushe za ka zama cikin makoki ka yi watsi da
sha’anin kasuwancinka da abokanka da sauran
jama’a? Hak’ik’a wannan abu ba zai k’are ka da
komai ba face ya raunana maka jiki ya sa ka
wahala matuk’a gaya.” A lokacin da suka shiga
gare shi Iblis na tare da su la’ananne yana gyara
musu magana yana k’awata masa batunsu, har
ya rud’u da maganarsu. Iblis ya ingiza, ya
lamunta da su, ya tashi daga wajen zamansa ya
fita tare da su.

Zanci gaba02 HIKAYAR ALIYI MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADU

A lokacin da suka shiga
gare shi Iblis na tare da su la’ananne yana gyara
musu magana yana k’awata masa batunsu, har
ya rud’u da maganarsu. Iblis ya ingiza, ya
lamunta da su, ya tashi daga wajen zamansa ya
fita tare da su.
, ‘Ya’yan fatake suka yi ta
rarrashin Ali Misiriyi cewa ya bi su zuwa ga
shagalinsu har ya amince cikin hukuncin Allah
da ya yi nufin tabbata. Ya tashi ya daga gidan da
yake makoki ya bi su. Suka ce da shi “ka hau
alfadararka mana mu tafi zuwa lambun waje kaza
inda za mu yi nishad’i, bak’in cikinka ya yaye.”
Ya sa bawansa ya kawo masa alfadara ya bi su.
Yayin da suka shiga wani daga cikin su ya kawo
musu abinci da abinsha suka ci suka sha
sannan suka zauna suna hira har zuwa fad’uwar
rana, sannan suka watse, ya dawo gida. Da gari
ya waye suka dawo suka ce, “ka taho tare da
mu.” Ya ce, “ina za mu je?” suka ce, “lambun
wane da ke waje kaza, ya fi na jiya kyau da
k’ayatarwa.” Ya tashi ya bi su zuwa lambun da
suka fad’a masa. Wani daga cikin su ya kawo
abinci da abinsha sannan ya taho da giya mai
k’arfin sa maye. Bayan sun ci abinci aka kawo
giyar ya ce musu, “menene wannan?” suka ce,
“wannan shi ne sinadarin gusar da bak’in ciki da
b’acin zuciya, kuma yana jawo farin ciki.” Suka yi
ta rud’arsa har ya amince ya sha wannan giyar,
sannan suka zauna suna ta hira har zuwa
fad’uwar rana sannan kowa ya watse.
Amma shi Ali Masiriyi tun da ya sha giyar nan
hankalinsa ya fita daga gare shi, ya rik’a fad’uwa
yana tashi, ya tafi gida da jirkitaccen hali,
matarsa ta gan shi ba yadda ta san shi ba ta ce,
“me ya same ka ne a wannan ranar duk ka
sauya haka?” Ya ce, “yau mun kasance cikin
ni’ima ni da abokaina, mun je wani lambu suka
kawo mana abinci da wani abinsha, kowa ya sha
har da ni sai na rik’a fad’uwa ina tashi kamar
yadda kika ganni.” Ta ce, “haba shugabana,
yanzu har ka manta da nasihar mahaifinka cewar
ka guji huld’a da miyagun mutane?” Ya ce, “ai
wad’annan ba wasu miyagu ba ne, ‘ya’yan
fatake ne, ba su da wani aibu tare da su. Kawai
dai suna son wartsakewa ne da nishad’i.” Ya
cigaba da biyewa abokansa suna zuwa kullum
lambu na yau daban da na gobe suna nishad’i
suna shaye – shaye har zuwa lokacin da suka
ce masa, “to mu mun kammala namu saura kai.”
Ya ce, “wannan babu laifi, gobe kowa ya zo
gidana mu yi walima a can.” Washegari kowa ya
zo, ya sa aka kawo gasasshen rago da dukkan
abin da ake buk’ata na wajen ci da sha ninki
biyun yadda suka saba yi masa. Ya d’auki masu
dahuwa da shimfid’a da sauran kaya suka tafi
zuwa ga lambunsa. Ya zauna a nan wata guda
cikakke suna nishad’i suna cin abinci da
sauraren kuyangi suna musu kid’a da wak’a.
Bayan watan ya k’are Ali ya lura ya ga ya kashe
kud’i masu yawan gaske, amma bai damu ba
saboda gamsuwar da ya samu kuma yana da
dukiyar kamar ba za ta k’are ba. Shaid’an kuwa
ya sake ingiza shi yana riya masa a ransa cewa,
“ko ka kashe fiye da haka babu komai saboda ka
mallaki dubunsu. Ina ruwanka ma da wani lissafi
tunda babu wani abu da ya ragu daga
mallakinka?” Sai kuwa ya hau ya zauna. Ya
cigaba da shagalinsa da abokansa har shekara
uku. Matarsa a kullum na tuna masa nasihar
mahaifinsa amma baya kula da ita ba har ya
wayi gari tsabar kud’i ya k’are gaba d’aya babu
ko dirhami d’aya. Ya zamana yana d’aukar
jauhari yana siyarwa yana musayar tamaninsu
har su ma suka k’are gaba d’aya. Sannan ya
shiga cikin kadarorinsa na daga gidaje da filaye
da gonaki da lambuna har ya kasance d’aya bai
ragu ba sai gidan da yake zaune tare da iyalinsa.
Ya kwshe kayan adon gidan ya sayar. Sannan ya
sa aka b’amb’are dutsen adon ya sayar ya sha
shagali da kud’in. Da kud’in suka k’are ya wayi
gari bai mallaki komai ba sai kangon gida, shi
ma ya sa shi a kasuwa ya sayar ya karb’e
kud’in. Bayan wani lokaci wanda ya sayi gidan ya
zo ya ce masa, “yau nake so ka ba ni gidana.”
Ya fita zuwa ga wani abokinsa ya yi aron d’aki,
ya kasance bai mallaki komai ba daga shi sai
matarsa sai ‘ya’yansa biyu, mace da namiji. Ya
sayar da dukkan bayin da ya mallaka. Ya zama
yana fita wajen dilallai yana musu k’wadago
suna biyan sa abin da bai kai ya kawo ba,
domin ba ya isar sa biyan buk’atunsa na yau da
kullum. Matarsa ta ce, “na sha yi maka gargad’i
kan nasihar da mahaifinka ya yi maka amma ba
ka ji ba, to yanzu kam abin ya zama lahaula
wala k’uwwata. Ka tafi wajen abokanka ko za ka
samu wani abu daga gare su domin mu samu
abin da za mu ci.” Ya tashi ya tafi gidajensu
d’aya bayan d’aya, duk wanda ya je ya yi masa
sallama sai ya b’oye fuskarsa daga gare shi. Bai
samu d’aya da ya amsa masa ba balle ya biya
masa buk’atarsa. Ya dawo wajen matarsa ya ce,
“babu wanda ya ba ni komai.” Da ta ji haka sai
ta tashi ta tafi wajen danginta ta shaida wa wata
mace halin da suke ciki. wadda a baya ta san suna cikin
wadata. Da ta gan ta a wani mawuyacin hali sai
matar ta ce mata,”me ya faru gare ku haka?”
Matar ta kwashe dukkan zance ta shaida mata.
Ta yi kuka mai yawa sannan ta ce, “kada ki
damu, zauna ki yi farin ciki, zan ba ku abin da
zai ishe ku ba tare da neman biya daga gun ku
ba.” Ta ba su kayan masarufi da zai ishe su
wata guda suna amfani da shi. Da ta isa gida
mijin ya ga wad’annan kaya sai ya ce, “daga ina
kika samo wannan?” Ta ce, “daga wajen wance
na samo bayan na shaida mata abin da ya same
mu.” Mijin ya yi kuka mai yawa sannan ya ce,
“tun da ke kin yi wannan k’ok’arin, ni ma zan
fita domin na je wani wurin watak’ila Allah ya
bud’a min a can.” Ya sumbace ta sannan ya yi
mata sallama da ‘ya’yansa ya fita bai san inda
yake tafiya ba har ya gangaro yankin Bulak’u
wajen kogi ya ga jirgin matafiya, yana shirin
tafiya zuwa Dimyad’a ya shiga. A ciki ya tarar da
wani mutum tsohon abokin mahaifinsa, ya gaishe
shi sannan mutumin ya ce masa, “ina za ka je
ne haka?” ya ce, “za ni Dimyad’a ina da wasu
abokai a can za ni mu gaisa na dawo.” Mutumin
ya d’auke shi ya girmama a hanya kuma ya
mutunta shi, ya ba shi wata jaka mai k’unshe da
dinarai. Yayin da suka isa Ali ya sauka bai san
inda zai nufa ba, ya yi ta yawo cikin kwararon
garin. Wani bafatake ya gan shi, ya ji tausayinsa,
ya kai shi gidansa ya zaunar da shi zuwa wani
lokaci. Ali ya ce cikin ransa bayan ya jima a
wannan gidan, ‘har yaushe wannan zaman zai
k’are a gidan mutane?’ ya fita daga gidan yana
yawo har ya zo mashigar jirage ya tambayi inda
jirgi mai tashi ya nufa aka ce masa zai tafi zuwa
Sham. Ya shiga aka tafi da shi. Tafiya ta yi musu
kyau suka isa lafiya sannan ya sauka ya cigaba
da tafiya har ya isa birnin Dimashk’a.
Yana tafiya shi kad’ai sai wani mutum ya gan
shi, wanda zuciyarsa ke cike da alheri ya kama
hannunsa ya kai shi gidansa ya zaunar da shi
yana kula da shi har zuwa wani lokaci. Wata
rana ya fito yana yawo sai ya ga karauka na
shirin tafiya zuwa birnin Bagadaza, sai ya ji
sha’awar shiga cikin su a tafi tare da shi. Ya
koma ya shaida wa maigidansa, ya shaida masa
sannan ya yi masa bankwana. Ya komo cikin
karauka aka tafi da shi. Allah da ikonsa sai
madugun tafiya ya jawo shi kusa da shi yana
kyautata masa yana ciyar da shi gami da ba shi
kyautuka har suka kusato da birnin Bagadaza.
‘Yan fashi suka tare su suka k’wace musu duk
abin da suke da shi na daga kud’i sannan suka
hallaka wasu. Allah ya kub’utar da Ali Misriyi ya
tafi shi kad’ai zuwa birnin Bagadaza. Lokacin da
ya isa rana ta riga ta fad’i daidai lokacin da
masu tsaron k’ofa ke shirin rufe k’ofar ya isa da
gaggawa yana mai cewa, “bari na shiga kafin ku
rufe!” Suka bar shi ya shiga, sannan suka ce da
shi, “daga ina kake kuma ina ka dosa?” Ya ce
musu, “ni mutumin Misira ne daga birnin
Alk’ahira, akwai tare da ni dukiya mai yawa da
bayi da hadimai. Na rigaye su zuwa ne kafin su
iso domin na shirya wurin da zan sauke kayana
na shiga kasuwanci. Ina cikin tahowa a kan
alfadarata na iske gungun ‘yan fashi suka tare ni
suka k’wace min komai, amma na tsira da raina.

ZANCI GABA03 HIKAYAR ALIYUL MASIRIYYU DAN HASANUL BAGADADU

Masu tsaron k’ofa suka yi masa karamci
sannan suka ji tausayin labarin da ya ba su,
suka ce masa, “zauna nan wajenmu har gari
ya waye za mu kai ka wurin da ya kamace
ka.” Ya zauna nan tare da su, ya fito da kud’i
daga wad’anda bafatake ya ba shi ya mik’a
wa d’aya daga masu tsaron ya ce, “karb’i
wannan ka samo mana abin da za mu ci.”
Bayan an jima kad’an mai tsaron k’ofa ya
dawo d’auke da sha’ir da nama. Suka zauna
suka ci gaba d’aya sannan ya kwanta barci a
wurin da suka tanadar masa.
Da gari ya waye suka kai shi wajen wani
attajiri, suka shaida masa cewa bak’on falke
ne wanda ke jiran zuwan kayansa, amma ya
gamu da tsautsayi a hanya. Kayansa na nan
zuwa ba da jimawa ba. Attajiri ya aminta da
wannan labarin, ya marabce shi da kyau, ya
aika gida aka taho da kayan sawa na
alfarma daga cikin nasa sannan ya ce da Ali,
“mu je na raka ka gidan wanka.” Suka tafi
tare, Ali ya yi wanka, ya gyara jikinsa ya
sanya wad’annnan tufafin da attajiri ya kawo
masa. Sannan suka dawo suka yi kalaci na
abinci mai rai da lafiya. Attajiri ya ce da wani
bak’in bawansa, “kai Mas’udu tafi da shi
gidajen nan nawa guda biyu ya zab’i duk
wanda ya yi masa ya zauna a ciki.” Ali ya bi
bayan bawa har zuwa wani kwararo inda
wasu sababbin gidaje uku suke gefe da gefe
duk suna rufe babu kowa a ciki. Aka bud’e
gida na farko, ya shiga ya dudduba sannan
ya fito ya shiga na biyu ma ya dudduba.
Bayan sun fito sai bawan ya ce masa,
“wanne kake son zama a cikin su?” Ali
Misiriyi ya ce, “wancan na ukun mallakin
wanene?” Bawa ya ce, “shi ma na
maigidanmu ne.” “Bud’e min shi ma na gan
shi.”
“Wannan bai shafe ka ba.”
“Saboda me?”
“Saboda duk wanda ya shiga ciki da dare,
idan gari ya waye da safe sai dai a tsinci
gawarsa. Mu kuma ba ma iya bud’e k’ofa
idan za mu kawar da gawar sai dai mu shiga
ta rufin d’aki daga d’aya daga gidajenmu mu
fitar da shi. Saboda haka maigidanmu ya yi
watsi da gidan yana mai cewa shaid’anu ne
a ciki. Ba za a sake saukar da bak’i a ciki
ba.” Ali Misiriyi ya ce...


Read / Download HIKAYAR ALIYYUL MASIRIYYI DAN HASANUL BAGADADIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album