Join Our WhatsApp Group

ZAKIN SARAKAI Complete Hausa Novel Document by ZAKIN SARAKAI


ZAKIN SARAKAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 159061



ZAKIN SARAKAI

Reading Time: 13 Hours

Added On: 18, Sep 2023

Author: Sajida ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍????*

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 856.8 kb

File Type: txt

Views: 1779+

Download: 2005+

Last download: 7 hours ago

Description/Story:
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*


0️⃣1️⃣


Busar kalalo ce ta zagaye baki daya karamin garin mai sunna DOGON DUTSI

Wannan busa itace ta fitar da kwai da kwarkwatar wanda ya kwana ya kuma wuni a wannan gari

Busar ce ta kada hanjin du wani wanda bai tsamaci zuwan wanda ake yiwa busar nan

Babu wanda ya san da zuwan ZAKIN SARAKAI garin na dogon dutsi

Kusan hankali Tashe sarkin garin ke kallon wanda ya kawo masa labarin tawagar ZAKIN SARAKAI ke ratso garin nasu

Mikewa ya yi tsaye a babar fadarshi ya kalli gabas, da yama, kudu, da arewa , cen ya hangi wasu tarin ciyayin ledoji farare wa'inda a da bai gansu ba sai yanzu

Hankali a dan tashe ya ce" Zabga, minana naka gani a ceniya? Ka maza ku dauke duk wani tsinke ko idan Mai garin garinmu ya bar garin nan na gile maku kawunnanku !"

Du a rikice aka shiga sake kimtsa fadar, duda batada wanu dati, ama a haka aka ci gaba da gyara duk wani abinda ya dace ace an gyara

Nan da nan Fadar ta dauki cika, sarki ya je a gurguje ya cenzo sutura da rawani, ya dawo zuciyarsa cike da zulumin abinda ya kawo ZAKIN SARAKAI garinsa


A gigice dawakai suka fara shigowa, lokaci daya kuma aka harba bingida irin ta tokar nan ta yi karra mai karfi gabas da yama, kudu da arewa, sama dau dau dau hakan ya sa wandama bai mike tsaye ba mikewa, dogaran garin suka layu layi layi, masu dawakan nan suka ringa kai hari a dandar kasa sunna danna wani irin algaita sunna hobara har sai da suka tada kura sannan suka koma gefe

Wani tafkeken mutun, sanye da shiga irin ta dogarai ama ya yi dinki irin na fitsara, na kirayi dinkinsa da fitsara ne domin rigarsa ta dogarai bakinta saman hannunsa, damatsunnansa a fili suke jibga jibga da su sunna huci.......*HURRRRRR*.................

Sai da ya wara kafafuwansa ya dauki algaitar dake hannunsa ya kafa a bakinsa ya yi busar da ta karra hargitsa hanjin sarkinsu , ya daga hannunsa ya dajawa kirjinsa duka ya bude katuwar muryarsa ya ce" GYARA KINTSI!, NA CE GYARA KIMTSI! GA ZAKIN SARAKAI TAFE!"

Du wani jinnin sarauta nan take ya gurfana, irin gurfanawar nan ta ajiye gwuiwa a kasa da sada kai, ba gurfanawa irin ta kai hannaye da goshi kasa ba , ko daya, irin ta ba baba girman nan ce

Motoci ne suka biyo bayan dawakan har su hudu, suka layi a tsakanin mutanen, sai kuma wasu dawakan a bayansu ya zamto sun sakasu a tsakiya ne

Shiru wajen ya dauka, fadar du girmanta irin baban fili na masarautar garin sai da ya nemi yin kadan, a hakanma ana ta hanna na waje shigowa domin cincirodon mutane ne ke ta bibilowa ta ko'ina


Dama JIRWAI ya ba Sarkin garin dogon Dutsi kan yana iya karasawa wajen babar motar da aka bude

Da dan hanzari ya karaso, sai da ya rage tsayinsa sosai ya jimke hannunsa ya bude bakinsa ya ce" Hawa lafiya , sauka lafiya jinnin sarakai, barka da gannin yau cikin koshin lafiya barka da shigowa garin DOGON DUTSI *OUMOUGHLOUK ITIBEL*, Allah ya sa alkhairinka da ya yabanya a duniya ya tardo ni a yau Adalin sarakai"

A kalla ya dauki minti biyar da kawo gaisuwarsa sannan wata kafa, mai dauke da dinki irin na sarakai, yadi ne mai haske Sararin samaniya hakan ya sa sai walwal yake, ya dauki dinki na bakin zare da yelow mai dan kyali, kafarsa cikin takalmi kafa ciki irin na sarauta mai lulube da Ado irin na sarakai, ba'a gannin kafarsa ko daya ba'a gannin kalar fatarsa sai hannunsa da ya fitar mai dauke da kira baba, watau yanada girma hannun da kuma jijiyoyi a tsaitsaye a jikinsa, haka kuma hasken farin hannun ba mai ja bane, aa mai haske ne fassss, ya kai shi saman goshinsa ya hangi ranar garin, rana mai zafi mai kwalar kai , rana mai nadar fata sannan ya idasa mikewa ya fito a matsayinsa gaba daya ba tare da ya bar wani saura na jikinsa a cikin motar ba

"Adalin kennan, sarkin Kasata, mai tafe da ikon Allah, mai takama da Ayar Allah, namu gwani bai fito dan ya birge wani ba, namu gwani Allah ne ya nadashi ba mutun ba, NA CE GA OUMOUGHLOUK ITIBEL a gabanku!" Wancen mai darjejiyar muryar ya sake fada yana sake hade hadadiyar fuskarsa ta yadda ya karra rikita zukatan masu saurin sarewa da abin tsoratarwa

Sarkin dake gurfane ya dan zubawa idannuwansa da su kadai ake iya ganni a bayane, Alkyabarsa ta rufe komai, ga rumfar da karti hudu ke rikewa sunna tafe idan yana tafia,
Cike da iza ya waiga Hagu, da damarsa yana kallon Malaman da suka yi tafiyar da su, uwa uba Sarkin dakin duhu dake sanye da bakaken kaya shi din da kansa bakin jikinsa ba abin dadin kallo bane, uwa uba Sharbebiyar wukar dake hannunsa mai walwalwal din alamun kaifi da kaifafa

A nutse, cikin tafiar da Allah ya haliceshi da ita, ba tafia ta wulakanci bace dan shi wane ne, tafia ce da Allah ya nada masa ya bashi a jinninsa, RAWANI ne a kansa ba na siya ko na kwace ba!, RAWANI ne a kansa nadin gado da jama'ar garinsa, RAWANI a kansa wanda ya gagari zamani da gwamnatin zamaninsa, shi din da ake kiransa OUMOUGHLOUK ITIBEL ba shi ya nadawa kansa wannan sunna dake nufin Zakin sarakai ba, SU SARAKAN sunne suka bashi wannan sunna, ba dan su birge shi ba, ba dan fin karfi ba, Magana ce ta cencenta..... Eh lalle shi din *ANNEMOKAL ne mai Adalci da Hatsari!*

A daidai wajen da aka tanadar masa da kujera ya ja ya tsaya ya karewa kujerar kallo
An kawatata da irin ado nasu dan birge shi duda ya zo a lokacin da basu zaci ganninsa ba, ga kuma rantsatsiyar rana a saman kansu

Kansa ya dauke a kan Kujerar, wanda hakan ya saka Dogaransa, Malamansa, Sarkin garin nan, dogaran sarkin garin da du wani wanda ya fahimci Nufinsa ba zai zauna ba kallon kallo da kuma sake gyara yannayi, domin idan bai zauna ba, babu wanda zai zauna, haka kuma babu wanda zai mike daga tsugunon nan

Tsoho, mafi kusanci da sarkin garin DOGON DUTSI aka yiwa iso, ya karaso ya duka a gaban sarakan biyu dake tsaye, daya na dan nesa da daya kadan, ana faman fifita masu fifitun da ba ratsa alkyabar jikinsu yake ba bale rawanin fuskarsu

Takardar dake hannun Dogari ya warware ya bude
Rubutu ne a tausashe , mai isar da sako a hargitse
Tanbayoyi ne masu rikita cikin mai laifi kamar haka" Asalamu alaikum wa rahamatullah., Menene dalilin da ya sa mai laifi bai amshi hukuncin kisa kamar yadda ya dace ace ya samu ba?, Ko sakon takardar a yanke masa hukuncin kisa bai isowa masarautar Dogon Dutsi ba?"

A rikice Sarkin ya kai dubansa kan Zakin SARAKAI, sannan ya sake mayarwa kan Datijo zuciyarsa na dokawa

Datijon kansa zufa ce ta shiga karyo masa a fuskarsa
Yaya zai yi? Me zai ce?

Maganar da ta saka shi sake sada kansa da budar bakinsa a rikice ya ce" RAINA fansa ne ga doguwa idan har ni Datijo Rabe na zama daya daga cikin WA'INDA suka take dokar Zakin SARAKAI!"

Ido Sarkin garin ya sake zuba masa, mamaki da tsoron kar dai Datijo ya fitar da kansa ya saka shi bude baki ya ce" Da doguwa kake Rantsewa Datijo? Doguwa fa? Kar ka sako doguwa a kan laifin da muka aikata baki daya!"

Ido Zakin sarakai ya rintse, takaici, mamakin mutanen na kama shi, Doguwa, ace har daga bakin sarki sunnanta da nuna ita din wata ce na yawo a fili a gaban jama'arsa? DOGUWA din nan Aljana ce da suke rantsuwa da sunnanta!, Doguwa din nan aba ce wace suka yarda da ita, Doguwa din nan itace babar damuwarsu da shiga a duhunsu, sai dai basu sani bane, bai zo garinsu ba sai da ya shirya, yau sai ya kona gawon doguwa da hannunsa, idan ya so ya kama da wuta dan Girman Allah! Doguwar Banza doguwar wofi?

A kausashe, maganarsa ta farko, tunda aka fara kwaramniyar nan, ya bude bakinsa kai tsaye ya yiwa sarkin magana, sarkin kadai, domin mutanen dake nesa babu wanda ya ji furucinsa, na kusan kuwa a lokacin da ya fara sun dode kunnayensu dan ba maganarsu bace

A kausashe ya ce" Kana Musulmi? Dan musulmai, jikan musulmai, ja gaban talakawa kake danne hakin wanda aka cuta, wanda ya tarda matar kanninta ya afka mata, ga laifin Fyade, ga na zina, ga na kisa dan ta kiya ya shaketa har ta mace..........? Lalle idan baka yi wasa ba zan zuba maka petrol a jikin bishiyar doguwarka na kone ku tare AMIRU!"

Shiry Sarki ya yi yana yawo da idannuwansa zuciyarsa na bugawa, subahanalah, bai san yaya zai yi ba, dama wannan maganar ce ta taso da Zakin sarakai? Ya Allah yau ina zai saka kansa? Sai da magana ta tardo shi cewa a zartar da hukunci daidai da yadda adini ya zo da shi, aka ringa cewa a kasar nan ai ba'a kashewa dan an kashe, ga koken matarsa a gefe domin danta ne na wani gidan kafin ya aureta, sai ya yanke masa zama gidan yari, nufinsu idan tafiya ta yi tafiya aka manta sai su fitar da shi ya gudu, sai gashi wannan abin ya faru?


A nutse ya maida hankalinsa wajen Ustaz AL'AMEEN
A yanzu sai ya dan bude muryarsa ta yadda du na kusa kusa zai iya ji ya ce" BISMILLAH Ustaz, menene hukuncin wanda ya kashe bawa ba tare da wani laifi ba? A hukuncin an zo da maganar Zamani ne? Ina nufin zamani irin naku wanda hukunce hukuncen adini suka zamto abin gaba a wajenmu?.....Bismillah"



Ustaz AL'AMEEN, baban alkali ne ne na kotun musulunci na kasar ZAKIN SARAKAI


A nutse Ustaz AL'AMEEN ya matso ya shiga bayani kamar haka" _"A shari'a kisa ba tare da haƙƙi ba babban laifi ne, ba tare da mun ja da tsayi ba, ina ga ubangijinmu da ya haliccemu ya tsara mana yadda zamuyi rayuwarmu, Allah bai yarda wani ya tauye ɗan uwansa ba, hakan yasa da kanshi ya faɗa cewa *ya haramta zalinci a kanshi* bare kuma bayinsa? Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi saboda ya kiyaye rayukan al'ummarshi ya yi hani mai kaushi akan ko da wanda zai tsorata ɗan uwansa ne, haramun ne musulmi ya tsorata musulmi da abunda zai iya cutarwa ko da kuwa ciki d'aya suka fito, sannan duk dan a nuna mana haƙƙin ɗan adam aka faɗa a hadisi ingantacce idan mutum zai yi yanka to ya wasa wuƙarshi da kyau, sannan ya kyautata yankanshi, ma'ana ita kanta dabbar ba'a yarda a wahalar da ita ba. Ina ga wanda zai kashe rai? A suratul Baƙara aya ta 178 Allah yana cewa *Ya ku waɗanda kukayi imani an wajabta a kanku yin ƙisasi a cikin kisa, ɗa mai ƴanci da mai ƴanci, bawa da bawa, mace da mace*... Ma'ana idan ɗane komai gatanshi idan ya kashe ɗa to shima a kasheshi, idan bawa ne shima ko bawan wanene a kasheshi, a yanzu kuma da ya zamana akwai ƙarancin bayi, dole ne muyi ƙisasi ga duka al'ummarmu, dan duk al'ummar da za ta yi shiru bayan an kashe mata rai, to da yiwuwar iftila'i ya saukar mata, dan kuma a suratul Ma'ida aya ta 32 lokacin da Ƴaƴan Annabi Adam Ƙabila ya kashe Habila Allah yace *Saboda wannan muka wajabta akan ƴaƴan bani isra'ila wanda duk ya kashe wata rai ba tare da wata rai ba (ma'ana idan shima ba kisa ya aikata ba) ko kuma ba tare da fasadi ya aikata a ban ƙasa ba, to fa tamkar ya kashe duka mutanen duniya ne gabaɗaya*...kenan da wannan ina ga zamu iya yankewa wannan hukuncin kisa dan kuwa bayan laifin kisa dake kanshi akwai laifin fasadi aban ƙasa, ba wai tausayi bane kuka nuna mishi da kuka ajeshi, dan Allah ma a aya 93 dake cikin suratul nisa'i cewa yayi *duk wanda ya kashe wani dagangan to makomarsa jahanama ce yana mai dawwama a cikinta kuma Allah yana fushi dashi sannan ya tsine masa albarka kuma ya masa alƙawarin azaba mai girma*."_

Gyara tsayuwarsa yayi tare da ƙara jan alkyabbarsa irin ta malamai fara ƙar sannan yace" Hukuncin kisa ne a kanshi ta hanyar jefewa, ba kuma mu ne muka faɗa ba wannan hukunci shari'a ce ta zo dashi, daga cikin mutane ukun da aka hallata jininsu akwai tsoho mazinaci, ba wai tsoho tukuf ba ake nufi, ana nufin wanda ya taɓa aure ko kuma mai auren, dan a nan soyayyar da zamu nunawa wannan mutum ita ce mu jefeshi da duwatsu har sai ya mutu."

Wani irin kuka Matar sarki ta fashe da shi, wanda ta kasa rikewa har sai da hankalin jama'a ya karkata kanta

Da sauri aka riketa ana bata baki kan ta yi shiru za'a saurara masa ta bari a gama magana, an tabata mijinta zai nemawa dan rikonsa sauki a wajen Zakin sarakai!



A dake ya shiga ratsowa duban jama'ar nan, ya zamto an sake budawa masu biye da shi da rumfarsa suna nemi biyo shi, sai dai lokaci daya ya dakata ya masu nuni da kar su biyo shi, hakan ya sa du wani mai makami wanda ke tafe cikin tawagarsa mikar da makaminsa da kuma shiryawa koda ta kwana

Sai da ya zo tsakiya ya tsaya
A nutse ya ringa duban jama'ar dake zagaye , har sai da wajen ya sake daukan wani shirun sosai , a tausashe ya bude bakinsa ya ce" Su wanene mu? Me muka taka? Me muke takama da shi? "
Ya ajiye maganar yana sake duban du wanni wanda ke iya yin ruwa da tsaki a lamarin

Idannuwansa ne basu da sauki a motsinsa, sunne kadai zasu iya nuna maka idan ka tarbi gabansa yana iya cinye namanka danye a masifa, shi yasa ba kowa ke iya ido cikin ido da shi ba, sai wanda ya taki tasa takakiyar shima

A kausashe ya dora da fadin" Laifinsa ne bai isa a zartar da hukuncin da ya dace a kansa ba, ko gatansa ne ya haramta masa daukan hukunci?"

"Mace ce mai daraja, tana dauke da auren kanninsa a kanta, ya shiga dakinta ya haure mata ta hanyar fyade, shedun bayi bakwai muka samu da tsoro ya hanna su magana!, Ya afka mata, ya yi zina da ita, ihun kukan da take yi ya saka shi shake wuyanta da hannayensa idannuwansa sun rufe burinsa ya kai ga ci!, A haka ya kasheta, da Aurenta, da darajarta , shima da nasa auren, ama dan yana dan gata ne...


Read / Download ZAKIN SARAKAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album