Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DUK KYAN TAKALMI Complete Hausa Novel Document by DUK KYAN TAKALMI


DUK KYAN TAKALMI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 101848



DUK KYAN TAKALMI

Reading Time: 8 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Jamila Umar Tanko ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 532.8 kb

File Type: txt

Views: 1107+

Download: 1443+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: Sunana Aisha farida umar, 'yar asalin jihar
katsina amma zama ya kai kakannina garin
shagamu. Anan aka haifi mahaifi har yayi
aure aurensa ya hayayyafa don haka babu
garin da muka fi sani wanda ya wuce
shagamu. Mahaifiyata ma 'yar garin
shagamu ce. Yanzu shekaruna ashirin da
uku a duniya, na fito daga dangi wadanda
suke talakawa liki. Ilahirin dangina kakaf na
wajen uwa dana wajen uba basu da hali.
Koda yake akwai daidaiku masu rufin asiri
amma ba za a kira su masu arziki ba amma
dai sunfi wasu. Wannan dalili yasa bamu
cika karatu mai zurfi ba wasu daga primary
suke tsayawa, wasu sun shiga scondary
amma talauci sai yasa a cire su basa
karasawa. Masu dan gara gara ne ma suke
kammala secondary amma fa jami'a ta
gagaresu sai dai kallo. Danginmu suna da
dimbin yawa mata da maza, yara da manya
gamu da tsofaffi tukuf tukuf Allah Ya ara
musu tsawon rai. Mahaifina yana daya daga
cikin dattijan domin ya tsufa jagof, tun tashi
na daman a tsohonsa na ganshi har ya
makance saboda tsufa. Shine babba a cikin
'yan gidansu don haka yafi kannensa tsufa
kuma yafi sauran 'yan uwansa talauci
kasancewar yafi su tara mata har guda hudu
da tulin 'ya'ya har guda arba'in da uku.
Nice 'ya ta arba'in da biyu a wajensa,
kanwata guda daya kacal mai suna
munauwara. Mu biyu ne kadai muke uwa
daya uba daya a gidan domin mahifiyarmu
ce amaryarsa, ya aure ta tana kankanuwa
yayin da yake tsohonsa. Sauran matansa
ma duka sun tsufa wasu daga cikin manyan
'ya'yansa sun girme ta suma har sun aurar
da 'ya'yansu suna da jikoki wadanda suka
fini ma. Don haka ban mori dadin uba ba,
sanda na fara wayo baya ganina kasancewar
ya makance.
Aikina shine kullum inzo dakinsa in riko
hannunsa in fito dashi kofar gida sai in
zaunar dashi akan kujerar katakonsa sannan
ni kuma in zauna a gefensa ina sauraron
hirar da sukeyi shida abokansa,
makwabtansa da 'yanuwansa tsofaffi. Ina
jin dadin sauraron tsofaffi labarai masu
al'ajabi na mutanen da. Ina fahimta sosai
kuma ina rikewa a kwakwalwata tas, babu
abinda nake mantawa harma idan suka fadi
wata kalma da ban sani ba sai in tambayesu
su bani amsa. Idan babana ya aike ni dauko
ruwa, fura ,koko ko kuma kurtun tofin
yawunsa a dakinsa sai inji duk raina ya baci
saboda za'a tsallake wani shashi daga cikin
hirar. Sai in zura da gudu don inyi sauri in
dawo kada a wuceni, idan na dawo kuwa na
sa su dole su dawo da labarin baya. Anan
na koyi iya magana mai ma'ana da jan
hankalin mai saurarona da kuma fitar da
lafazai masu girma da hikima tamkar wata
babba. Daga nan na samo suna "Farida
tsiri" inji kawayena haka suke kira na domin
duk wanda na zauna dashi zaiyi tunanin
wayona yayi yawa zan cuce sho ko zanyi
masa dubara ko in yaudare shi. Duk sanda
zanji labarin anyi gulmata bai wuce ace na
cika iyayi ba da dadin zance rai-rai-rai
kamar aku. Ko kuma ace na cika kissa da
kisisina bana fushi ko ma za'ayi min, ga tsiri
ina magana kamar wata tsohuwa wacce
taga jiya taga yau. Ina jin dadin halayena
kuma dashi nake cin ribar zaman duniya.
Zan iya zama da kowanne irin mutum ne
komai bakin halinsa da muguwar zuciyarsa,
duk sharrinsa ko alkhairinsa haka kuma duk
in da ya kai ga masifa da zafin rai zamu
zauna lafiya. Da kowacce irin kabira zan iya
zama lafiya. Da bakar fata da inyamuri,
hausa, babarbare, bafillatani, bayarabe,
ibira ne, tangale ne, mumuye ne, margi ne,
basayi ne, ba'are ne, dan niger ne ko kuwa
adon dawo ne dan bur sudan duk na san
yadda zan tafiyar dasu.
Mahaifina yana da yawan magana ba zai iya
zama shi kadai ba, ba tare da bakinsa yana
motsi ba, sai na gado sho don haka tamu
tazo daya sai mu hadu muyi tayi. Har baya
so in matsa daga gabansa don haka ban
cika zuwa makaranta ba, ko yayyena zasu
korani sai in ruga da gudu dakinsa in labe a
bayansa. Sai yace musu "inga mara kunyar
da zai shigo ya banbare aisha daga bayan,
baza taje makarantar ba nan dakin ma
makaranta ce". Aji ne mai zaman kansa don
darasi take duka na iya rayuwar zaman
duniya. Ku fada min ko a jami'a wanne
darasi ne za'a zaunar da dalibi a karanto
masa rayuwa karara balle dan primary aji
daya? To ku kyale ta ba in da zata je sai ta
ga dama sannan zata je makarantar. Dalilin
zuwanta makaranta don ta koyi rubutu ne
kawai. Idan sukaji yana fada basa karasowa
cikin dakin, su gama labe-labensu ina hango
inuwarsu ta jikin asabari sai inki fita, sai sun
gaji da jirana sannan su tafi. Idan hantsi
yayi sai inje zaure in kinkimo kujerar katako
in kai masa kofar gida, sannan in share
wajen in shimfida tabarmi a kasa wasu
tabarmin in shimfida akan wasu dakali biyu
da suke kofar gida. Sannan in dawo dakinsa
in mika masa sandarsa na riko hannunsa in
fito dashi kofar gida wajen kujerarsa, sai ya
laluba ya zauna sannan in koma gefensa in
zauna sai ya fara bani labari ko tatsuniyoyi.
Sannu a hankali sai 'yan majalisarsa su fara
bulbulowa daga gabas wasu daga yamma
wasu daga barin kudu, wasu daga arewa.
Yawancinsu kannensa ne uwa daya uba
daya, ko uba daya. Wasu kuma kakanni
suka hada, wasu makwabtaka ce ta hada ko
auratayya, wasu kuwa manyan abokansa ne
da akayi kuruciya tare. Babu wanda yake da
kasa da shekaru sittin a wajen. Anan na
samu tarbiyar girmama babba duk
kankantarsa, domin idan na gaishe su daga
tsaye ko daga zaune ba zaus amsa ba ko
kuma inji duka dal a bayana wai nayi rashin
da'a. Sai kaji sun daka mintsawa suce inzo
in durkusa har kasa sannan in gaishe su.
Tun ina jin haushin inyi kuka har na daina,
tun ina mantawa har na saba. Sannan na
koyi durkusawa har kasa idan zan mikawa
babba abu koda kuwa da kadan ya girme ni
kuma da hannu biyu. Sun hana ni mikawa
sa'ana ko yaron dana girma abu a
wulakance ko da hannun hagu. Sun
gargadeni ni da na guji wulakanta dan adam
ko da kuwa almajiri ne domin babu kyau
wulakanci da girman kai.
Anan nakoyi daubarun cin jarabawa a
makarantar boko ko kuma saurin haddace
kur'ani a makarantar allao. Sunce in zamana
mai yawan kallon bakin malamina ina
sauraro, ina ganin yadda yake fitar da
lafazinsa daga hanka, ganda, tantanin
makwallato da kuma dumbarun bakinsa. Yin
haka zai sa in dinga fitar da kalma yadda
ake bukata a fada. Kada in dinga zama a
bayan aji, ko da yaushe kujerata ta zamana
a gaban malam saboda gudun yin wasa da
yara. In zama mai yawan tambayar duk
abin da ban gane ba anan take ba sai an
wuce wajen ba. Sannan in dinga kwafar
rubutu daidai in da ban gane ba ko ban
gani ba in tambayi malam ko wani na kusa
dani wanda nasan yasan abin da yake yi.
Kada in sake in koma gida in yarda jakata
ko allona ba tare da nayi bita ba. Sunce da
zarar naci abinci na huta in samu lungu in
shiga inyi ta tilawa zanji na fahimci abin da
ban gane ba a a aji watakila saboda yunwa
ko gajiya ta hana in gane a lokacin. Suka
shawarce in yawaita yin aikin gidan
(homework) tare da yayyena wadanda suke
ajin gaba dani, kada in sake in dinga yi ni
kadai ba tare da wani ya duba min ba. Duk
abinn nan dana fada min na haddace sai dai
anan nake zubarwa saboda bana kaunar
zuwa makaranta, har gara ma makarantar
allo dan itama a kofar gidanmu take dole
inje.
Idan rana ta bude sai majalisa ta yoye, ni
kuma sai kama hannun tsohona in shiga
dashi daki sannan inje in karbo masa
abincin rana daga wajen matar da take da
girki. Tuwo ne dai na masara ko na dawa,
miyar kuka ce ko danyen karkashi. Shinkafa
sai jifa jifa ake siyowa a dafa ko kuma idan
an samu wani dan albarka cikin yayyena ko
sirkiai su kawo mana a dafe ko danye. Da
yamma sai in sake zuwa inyi shimfida in fito
dashi, 'yan majalisarmu basa tashi basa
manta lokacin sai kagansu daya bayan daya
suna bulbulowa. Duk wannan zance da
nake yi muku ina da shekara hudu ne zuwa
tara, ban cika shekara goma ba a duniya
Allah Ya karbi ran mahaifina. Mahaifina ya
rasu a ranar wata juma'a da safe. Bazan
taba manta wannan ranar ba saboda itace
ranar dana taba makara ban tashi da karfe
bakwai na safe banje wajensa ba, domin
kullum karfe bakwai a dakinsa take min.
Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyar wata
kasala da wani yanayi da jikina yake min ba
dadi. Ni ba mai barci ba, haka ni ba ido
biyu ba. Tamkar wani abu mai nauyi aka
saka aka dirirritseni na kasa juyi. Sai dai
kuma idona a rufe ba kamar mai tunani
kamar mai mafarki domin abinda nake
nanatwa hirar da mukayi da mahaifina ce a
daren jiya kafin inzo in kwanta. Daga ni sai
shi bayan 'yan majalissa sun watse muna
labari kamar yadda muka saba. Ya laluba ya
dafa kaina yace aisha ki zama mai rikon
amana a rayuwarki yin haka zai ja miki farin
jini a wajen al'umma. Ki kiyayi munafunci,
ma'ana gulma shine yi da mutum yin haka
zai zubar miki da kima. Ki guji sata duk
rintsi kada ki taba abin wani yin haka zai
zubar miki da mutunci ke da zuri'arki gaba
daya za'a dinga yi muku gori. Ki guji yin
zina, laifi ne a wajen Allah kuma rashin
mutunci zai dasu a idon jama'a zaki zama
abar zagi, kowa ya fada miki magana, sai ki
zama ballagaza ko yaro karami ba zai
girmamaki ba. Ki kiyayi kwadayin abin wani,
ki nema naki na kanki duk kankantarsa
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DUK KYAN TAKALMI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album