Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ASHPA KO ASHNA Complete Hausa Novel Document by ASHPA KO ASHNA


ASHPA KO ASHNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15265



ASHPA KO ASHNA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 04, Apr 2025

Author: Khadija Umar Abdullahi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 78.7 kb

File Type: txt

Views: 22+

Download: 24+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story:
ASHPA KO ASHNA

Episode 1

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

STORY AND WRITING BY
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)

بسم الله الرحمن الرحيم

Kyakykyawar budurwa ce fara sol doguwa, bata cikin sirara kamar yanda bata cikin basu ƙiba, tana da goguwar fuska da dogon hanci, mnyan idanuwa ma"abota gazar gazar ɗin gashin ido baƙiƙirin, gashin girar ta yana da yawa sosai saura kaɗan ya hade, ɗan ƙaramin baki gare ta tare da pink lips, tana da siririn wuya da cikakken dukiyar fulani, cikin ta a shafe kamar babu komai a ciki tana da hips madaidaici .

Baƙar doguwar riga ce a jikin ta ta yafa farin mayafi ɗn ƙarami a saman kanta, inda ta jawo mayafin ya rufe rabin fuskar ta, yanda take tafiya kaɗai kamar bata son taka ƙasa ya isa ya sanar da mutum ajin da take da shi.

A bakin titi take tafiya kan ta na kallon ƙasa, wata ƙatuwar baƙar mota ta taho da gudu a kan titin daga bayan ta, tn kafin su ƙasaro suka buɗe ƙofar motar, daidai inda take suka iso ɗaya daga cikin su ya zuro hannu ya ja hannun ta da ƙarfi ya jefa ta cikin motar suka ƙara gudu.

Daga cikin motar ta kalli gefen ta hagu da dama wasu ƙattai ne guda hudu suna ta muzurai kallo ɗaya zaka yi musu kaga tsantsar rashin imani a tare da su.


gefe wasu ƴammata ne guda biyu da tsohuwa ɗaya jikin su banda rawa babu abnda yake yi suna ta kuka, sosai suka bata tausayi ta maida kallon ta gaban motar, mutum ɗaya ne driver yana sanye da kayan sojoji sai wata mace a gefen sa cikin riga da wando da ƙatuwar gun a hannun ta.

Saida ta gama ƴare musu kallo tsaf sannan ta sauke ajiyar zuciya ta gyara zaman ta acikin motar.

Sosai suke sharara gudu a titin har suka iso wani daji ma'abocin dogayen bishiyoyi da duwatsu, akwai ƙarancin haske a wajan, wasu fararen ƙyallaye suka ɗakko suka ɗaure musu fuskokin su dashi sannan aka fito dasu, mutum biyu a gaban su biyu a bayan su suka nufi cikin jejin .


Tafiya sukeyi sosai cikin dajin sunyi nisa sosai wani ɗn ƙaramin dutse ya gangaro ya faɗo gaban su, cikin waɗanda ke gaban su wani yaji an jashi baya da mugun ƙarfi, saura kaɗan ya rusa ihu sai Kuma yaji an sake shi, da mamaki yake kallon hannun da yayi masa wannan ruƙon, yana shirin yin magana ta ɗaga masa hannu tare buɗe ɗn ƙaramin bakin ta fara motsa shi a hankali tace ""zakayi tuntuɓe da dutse ne shiyasa na jaka".


Zagaye ta sukayi gaba ɗayan su da bindugu wani daga cikin su ya cire ƙyallen dake fuskar ta ya ɗakko baƙi ya ɗaure mata fuskar sosai dashi sannan suka cigaba da tafiya, shidai wanda aka ja har yanzu jikin sa bai dawo daidai ba, tnda yake a rayuwar sa bai taɓa jin hannu mai ƙarfi irin wannan ba, har yanzu hankalin sa bai kwanta da yarintar ba haka ya dinga saƙe saƙe a zuciyar sa har suka iso saman ƙaton dutsen da ogan su yake suka dangwarar da waɗanda suka kamo a gaban wani dn siririn bafulatani.


Shima kayan sojoji ne ajikin yana tsaye ya jingina wata ƙatuwar bindiga a jikin ƙafar sa kansa da baƙar p cap baa ganin fuskar sa.


Wani uban ihu ogan ya kurma yana juyawa a wajan ya daga bindigar sama ya harba ta saboda tsabar murna, gaba ɗaya wajan sai da ya amsa sautin harbin, su dai ƴammatan da tsohuwar daga nan basu ƙara sanin inda kansu yake ba.


Su kansu waɗanda suka ɗakko su saida suka koma gefe saboda sun san babban burin oga Jibo shine ya kashe mutum lokacin da ya samu kansa cikin farin ciki sannan ne farin cikin sa yake cika.


Dawo da kallon sa yayi gare su dn ya tabbatar da yayi abnda yake so wato tsorata mutane, ja da baya yayi cike da mamakin kallon yarinya guda ɗaya a zaune ta tanƴwashe ƙafa idanun ta a rufe da baƙin ƙyalle, ""kodai kurma ce ya faɗa a zuciyar sa yana ƙara mamakin wannan halittar, matsowa kusa da ita yayi ya cire mata ƴyallen sannan ya ƙara ɗaga gun ɗn sama ya sake har bawa, yasan dole ta tsorata koda kurma ce ai idon ta yaga abnda ya faru, ƙara maido idon sa ƙasa yayi da mamakin sa still har yanzu tana zaune saima ƙara gyara zama da tayi tana kallon sa, dk da idon ta a lumshe suke amma yana hango ƙyallin ƙwayar idon ta wacce bazai iya tantance kowace colour bace.


Ransa ya ɓaci sosai ganin rashin tsoron yarinyar, cike da ɓacin rai ya dakawa yaran sa dake tsaye tsawa ya basu izinin kaisu masauki, Babu musu kuwa suka nufi inda suke a takure sakamakon ƙarar harbin gun na biyu daya farkar dasu daga suman da sukayi.

Yanda suka zo a tsakiya haka suka ƙara saka su tsakiya, ita dai banda kalle kalle ba abnda take yi.

ɗaya daga cikin wanda suke bayan su ya sa ƴasan gun ya zunguri kanta tare da daka mata wata razananniyar tsawa wacce tasa su juyo wa gaba ɗaya, wani irin kallo tayi masa tare da watsa basa kwala kwalan idanuwan ta, Damm ƙirjin sa ya buga ganin blue ƙwayar dake cikin idon ta, sai dai ya dake ya gyara tsayuwar sa yana muzurai shi kar a raina shi, ya sake tamke fuska ya dube ta yana wani ciccije leɓe yace "" ke!! baki san ina ne nan ba ko? To kibi a hankali idan kika yi wasa a take a nan zan tarwatsa kanki , ki mutu kowa ya huta "" dn ƙaramin murmushi tayi sannan ta dube shi a raine tace """ ka taɓa ganin an kashe gawa? wani irin juyi cikin sa yayi yayi baya zai faɗa ramin dake bayan sa, da sauri ta sa hannu ta shaƙo yuwan rigar sa ta dawo dashi ya tsaya ƙyam akan ƙafafun sa, ta sakar masa murmushi tare da ɗaga masa gida ɗaya ta juya ta fara tafiya, kamar wasu dolaye haka suka fara binta tana gaba har suka iso ɗakin da suke ajiye mutanen da suka kamo.




Ashna! Ashna!! Wata dattijuwa take take ta kira a tsakar gida, jin shiru yasa ta canja kiran zuwa Ashfa, daga cikin ɗakin wata bdrwa ta fito, (nidai bazance komai domin wacce na baro a daji kmr ita na gani anan) "" duba min yar uwarki tana ina? cewar dattijuwar tana kallon wacce ta kira da Ashpa, zoben dake hannun ta budurwar ta murza shi tare da kallon tafin hannun ta, a razane ta ɗago kanta sai kuma ta fashe da dariya ta fara rawa a tsakar gidan tana ""mai rabon ganin baɗi ya gani"" , rawa take sosai tana juyi, dattijuwar na kallon ta rai a ɓace ta daka mata tsawa tare da cewa ""kee Ashpa menene haka? Cewa nayi ina Ashna take""? sake sheƙewa da dariya Ashna tayi sannan tace "" wani mai rabon tsautsayin yayi kidnapping ɗn Ashna, kaiii Inna Ina ma nice akayi kidnapping ba ba Ashna ba ta ƙarasa faɗa tana sake cigaba da rawar ta tana mai rabon ganin baɗi ya gani.



Wani ƙayataccen palour ne wanda ya haɗu yaji kayan alatu da komai na more rayuwa, wasu manya manyan kujeru ne cikin palourn yayin da wasu ƙammata ke zaune a kai suna operating wayoyin su, daga upstairs wata dattijuwa fara mai ƙiba ta sakko tana shafa cikin ta, direct dianing ta nufa saidai ganin wayam ba komai yasa ta sautin juyowa tana kallon yammatan dake zaune kan kujera tace "" meenah ba dai wannan matsiyaciyar yarinyar har yanzu around 09: bata zo tayi mana breakfast ba"? ""Bata zo ba momy"" wacce aka kira da meenah ta faɗa ba tare da ta ɗago kan ta ba.

daɓas momy ta zauna kan kujera ranta a ɓace ta fara masifa"" Talaka !! Talaka!! hmm wato saboda taga idan nace zan kore ta dadyn ku yana hanawa shi gashi uban masu tausayi shine ta samu damar barin mu har yanzu ba breakfast to bari tazo zanga uban da ya tsaya mata...



OUM SHARIFAT CE IDAN NAGA COMMENTS ZAAGA TYPING...

IDAN KIN KARANTA KIYI SHARE PLEASE


ASHPA KO ASHNA
EPISODE 3-4

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽

Ina matukar godiya ga masoya masu bibiya ta love you oll amma yau sai kunyi hkr da typing dn🙈🙈

بسم الله الرحمن الرحيم

Shiru mama tayi tana kallon yanda Ashpa ke rawa a tsakar gida kmar ba wani abu
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ASHPA KO ASHNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album