Join Our WhatsApp Group

MAKWABTAKA Complete Hausa Novel Document by MAKWABTAKA

MAKWABTAKA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 145358

MAKWABTAKA

Reading Time: 12 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Jamila Umar Tanko ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 725.26 kb

File Type: txt

Views: 2373+

Download: 1575+

Last download: 2 days ago

Description/Story: MAKWABTAKA
Na Jamila Umar Tank
Ebook publish by - http://hausaebooks.cf

PART 1
A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin
Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia.
Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya,
ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana
kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin
saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin
suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar.
Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin,
yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da
kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari
bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin
kalar halittunta.
Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material)
mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji,
wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause),
sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan
gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da
*yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko
riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin
bakake ko wasu kalolin.
*Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran
hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da
tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne
kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa
shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so.
Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka
kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin
Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan
aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja.
Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce
shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace
*yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba
kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka
ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu
kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da
laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami
irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo
ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba.
Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma
sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin
garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda
annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon
zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a
hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan
mai sanyi.
Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe
a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke
Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi,
wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa
da suka sha mana kai.
Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido,

musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu
kiwon shanu.
Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji,
mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia.
Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar
gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta
shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana
kallonta kamar yadda ya saba.
Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike
da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita
sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta
babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta
sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta
daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta
tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma
shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin
mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta
sakewa a farfajiyar gidanta.
Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne.
Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun
sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai
hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a
gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa
madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne
na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa
zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki,
kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara
jiyowa.
Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana
da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta
fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito
tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda
(pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe
pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar
Malaysia.
*Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a
kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da
yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu,
amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi
saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana
isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo
get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na
mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta
shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu
daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne.
Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana
sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa.
Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan.
Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta
bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba,
sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana
hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun

kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin
mota sai dai su bi ta gada.
Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis,
kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar
murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu
da aiki.
Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta
yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai
dai idan ta lunguna ya biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya
ba ta ga kowa na biye da ita ba.
Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero mata
tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa ko guda daya
ba, harya fara tunanin ko ba ta jin turanci ne?
Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara kacaccala
Turancin yadda ko dan koyo zai gane.
Ya ce, ''Are you from Sudan? Libya? Egypt? Ethopia? Or
Mali?''
Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da tafiya. Hat
yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke sauri haka shi ma
yake yi.
''What is your name?
Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake ganin
wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle shi sama da
kasa , cikin takaici ta ce, ''MAYE kawai, sai nacin tsiya !''
Ta yi murmushi ya ce, ''Your name is Maye? Wow nice
name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya bita yana ta
bayani cukin harshen Turanci, duk magana daya sai ya
ambbaci sunan nan ''MAYE.
Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta rasa
yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya fada mata ita ce.
''My name is Abdul-Sabur''
Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta wuce ta nufi
hanyar makarantarsu ko tantama babu a FTMS GLOBAL
COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta nufi hanyar makarantar.
Idan kuwa *yar jami,ace ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci?
Sai dai idan idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan
hujjar mai karbuwace.
Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba ta kara
dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba ta tsaya a ko'ina
ba sai a cikin ajinsu, a inda ta sami kujera ta zauna.
Zamanta ke da wuya sai Malami ya shigo ajin ya fara yi
musu darasi akan abin da ta ke karantawa, wato soft
ware engineering.
****************************************
Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah ta sake
fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da bakar abaya,
sauri ta ke saboda tana da test karfe goma sha daya. Yau
ma a bakin get ta ci karo da mutumin nata Abdul-Sabur,
shi ma zai fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta
yi da gaske ta gane shi, don ya sauya taga ya kara kyau.
Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama gami da
dorawa da ambaton sunan nan da yake zaton sunanta ne,

wato, ''MAYE''.
Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi ta wuce ba
tare da ta amsa masa ba. Sai ya shiga mamakin yadda
*yar musulma ta ke da bakar zuciya haka ko sallama ba
ta amsawa. Ba shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan
alamu harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta ke
tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke.
Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba ya san
tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa, watakila ta gwada sau
daya ta ga babu riba, dole ta kyale ta don ba don haka ba
ya san yadda ta ke da matukar son mutane, gata da fara,a
ko ka ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana.
Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka dunguma
su uku suka yi bakin titi. Umaima na gabansu su biyu
suna baya suna ta hirarsu cikin harshen Nasara (English).
Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi halittarsa
anan saboda ko a larabawan ma kafin ka sami mai
kyauwu irin na Faduwa sai ka bincika. Bata da tsayi kuma
tana da *yar kiba amma a dire take, hanci dogo, ga
manyan idanuwa, da lallausan gashi har yana taba
cinyarta dan ma koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata
*yar gayun gaske ce tana shiga suturunta na larabawa a
mutunce, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan
sana,ar ta dace da surarta.
>>>>>>>>> MAKWABTAKA <<<<<<<<<
PART 1
A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin
Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia.
Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya,
ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana
kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin
saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin
suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar.
Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin,
yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da
kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari
bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin
kalar halittunta.
Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material)
mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji,
wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause),
sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan
gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da
*yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko
riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin
bakake ko wasu kalolin.
*Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran
hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da
tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne
kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa
shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so.
Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka

kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin
Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan
aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja.
Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce
shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace
*yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba
kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka
ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu
kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da
laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami
irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo
ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba.
Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma
sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin
garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda
annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon
zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a
hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan
mai sanyi.
Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe
a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke
Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi,
wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa
da suka sha mana kai.
Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido,
musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu
kiwon shanu.
Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji,
mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia.
Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar
gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta
shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana
kallonta kamar yadda ya saba.
Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike
da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita
sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta
babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta
sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta
daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta
tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma
shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin
mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta
sakewa a farfajiyar gidanta.
Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne.
Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun
sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai
hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a
gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa
madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne
na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa
zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki,
kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara

jiyowa.
Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana
da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta
fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito
tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda
(pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe
pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar
Malaysia.
*Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a
kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da
yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu,
amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi
saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana
isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo
get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na
mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta
shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu
daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne.
Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana
sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa.
Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan.
Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta
bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba,
sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana
hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun
kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin
mota sai dai su bi ta gada.
Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis,
kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar
murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu
da aiki.
Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta
yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai
dai...

Read / Download MAKWABTAKA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

7 months ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album