Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) Complete Hausa Novel Document by WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)


WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE  KO SHARRI)

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 266201



WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Reading Time: 22 Hours

Added On: 28, Feb 2025

Author: Maryamah Farouk ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 7014979567

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.35 mb

File Type: txt

Views: 91+

Download: 330+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ο»Ώhttps://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


Na Maryamah_Mrs AM

Page 1

Lagos Nigeria

Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar idan bazan makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani conference meeting da aka turani daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu nisan tazara tsakanin unguwar tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani cewa " not now please" azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani waiwayawa, megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali Yara kuma suna ce masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya saka masa da ya rasu sati biyu kafin na haifi Aliyun.

Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara'a amma dai ai yanayimun nidai. Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da gajeran murmushi nace "Baban Ali ka ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan a jaka ashe batayi ba (Amna Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da Mahaifiyarmu ta sake aure).

"Uhm" kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata tareda ratayata na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita

"Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe" muryarsa ta doki kunnena,

"To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse" na sa kai na fice daga dakin. Already Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da yara suka biyo ni suna yimun.

Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai wani abune ya faru a bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan nayi waya da yan uwana kuma ba abinda akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai kawai zakuje Gombe ba. Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi.

A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin bari na kwana a Kanon dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan kwana ba nasan bazasuji dadi ba musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci abincin da Aliyu ya kawo min, ina zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana cikamun zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da sauran wani damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su.

Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu shekaru 13 ya shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha Allah yana da qoqari tamkar Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad su Shidan nan sune rayuwata ban kuma hadasu da komai ba.

Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi, sauqin dana samu tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din nan bacci zan shaqa. Sallamar Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa dan shi dama be fiya zama ayi irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya Amsa yana nufar dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima ganin kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze shige dakin ga kuma fita da yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi dakinsu matan ma haka.

A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa "Ashe baka nan, na tambayi yara sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki"
"Uhm" ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin Hasala amma fa ina da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya tambayeni ya hanya koda yake dama duk satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban kula shi ba nasan qiris yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki tareda cewa "Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo ka juyemun to bazan tanka ba". Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum fada kamar ko yaushe kuma akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad, Ahmad da Abdallah Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za'a kwanta shine a sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace sedai dan uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu muka karanta Azkar din bacci naja musu qofa tareda kashe fitila.

Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na shiga dakina, jikina na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake nema yasakani kashe fitilar da ya bari a kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata gajiya na sake saukar mun.

"Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe" ya sake fada, sena gyara kwanciyata ina cewa "Allah ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa surutu zamuyi tayi dan dai yasan abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba kowanne ba se yayi corresponding hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka ana tsakiyar Term yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk sanda nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban farka ba se Qarfe 7 harda Rabi na safe.

Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta danne ni banajin ko juyi nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai baccin ya sake ni bane na fito palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter. A tare suka gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi
"Kunyi karatun Asuba ne" na tambayesu suka amsamin da eh
Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma bacci. Kafin na fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka na zauna kan Dining ina shan Tea ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa 12 harta gota na rana.

A dakin nai wanka na shirya kafin na fito ina jin gajiyar ta sake ni. Palour kamar Gidan biki saboda hayaniya Farida da Jafar na musu akan wani film da suka kalla. Da gudu Ahmad da Moh suka nufoni har suna neman kadani na riqe hannayensu muka qarasa cikin palour.

"Ina Abbi" na tambayesu dan koda na farka ban ganshi a dakin ba kuma dai nasan Saturday Sunday yana gida seda babban Dalili yake fita kafin su bani amsa ya shigo da sallama ciki ciki, kallo daya yamun ya dauke kai tareda nufar kan Dining ya aje abunda ya shigo dashi, jin an fara kiran sallah yace su tashi suyi Alwala suka wuce masallaci da Mazan mu kuma muka tayar da tamu a Gida.

Abun mamaki bayan sun dawo kuma se gashi ya zauna a palour tareda yaransa suna hira dan nidai kitchen na shiga na fara qoqarin dora mana abincin rana dan na dare a waje zamu je muci
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album