Join Our WhatsApp Group

MABARACIYA Complete Hausa Novel Document by MABARACIYA


MABARACIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 69280



MABARACIYA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 24, Aug 2023

Author: Feedohm ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 366.27 kb

File Type: txt

Views: 1381+

Download: 1232+

Last download: 2 days ago

Description/Story: *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)

🅿️:1️⃣

Dan dazon mabarata ne cike da 'kofar wani makeken gida ,dukkanin su a zaune suke ,kamar dahadin baki kuma duk suke tashi taye ga alama mai gidan ne xe fito ,se turereniya sukeyi ,kamar daga sama saiga wata matashiyar yarinya ,kutse kawai takeyi a cikin jama'a ita birinta baiwuce taganta a gaban layiba saboda tasan ta hakane kawai zata kusanci ganin mai gidan ko matar gidan domin bata damu se mai gidan ne zata gani ba ko matar tagani tasan ta wadata.

tana isowa a gaban sahun se taja ta tsaya ,sedai abun mamaki duka tsofaffine a wurin babu yaro ko daya ,kuma ga Alama ba yaune tasaba zuwa ba domin matan nan babu wacce tayi complain akan abunda yarinyar tayi

sai wani zare ido take kamar wacce tayi karya ,sunfi 30 minutes a wurin sedai babu alamun cewa masu gidan zasu fito ,hakan ne yasaka jikinta yayi sanyi ,sega hawaye masu zafi suna bin kuncinta ,wata tsohuwa da take taye kusa da ita ta dafata "kiyi hakuri Ameerah,ga alama yau ma masu gidan basanan ,amma kekam ina iyayenki da sukabar yarinya kamarke kina yawon bara, ai da sun sani zaunar dake sukayi a gida sukuma sufito ,saboda yanzu duniyar nan babu gaskiya wani ze iya anfani da dukiyarsa ya lalata miki rayuwa ,duk maganar nan da take hankali Ameerah baya gunta domin ta tafi duniyar tunanin hanyar da zata sadata da mai gidan

Saida tsohuwar ta girgizata ,tukuna tadawo hayyacinta ,murmushin yake tayi tace " karki damu Innah gobe ma zan dawo ai mainema baya gajiya ,daga daga haka tajuya da nifin komawa gida ,itadai matar nan da ido kawai ta bita saboda tarasa gane me yarinyar ke nufi itadai idan kaganta bazaka kirata *MABARACIYA* ba domin bata tattre da wahala irin na mabarata ,gashi ita mai tsabtace "ya Allah ka wadatamu abunda ta fada kenan.

Saida Ameerah tayi nisa sosai tukuna ta juyo sedai bata hango kowa ba a bakin gidan ,murmushi kawai tayi batasan me yasa ba ko yaushe tazo wurin zata sami mutane da yawa a bakin gidan ,amma kuma da ta tayi nufin barin wurin se kowa ya watse ko meyasa haka,tambayar da takeyiwa kanta kenan sedai bata da mai bata amsa,wuri tasamu ta sauna tana tunanin wace hanya zatabi shin domin samun cikar burinta ,tabbas bazata dakata ba harse ta cimma manufarta , tacikawa yayarta alkawarin da tayi mata ,kuma dole se ta dauki fans a akan Saudahhhh....

#shin wacece Ameerah kuma wacece saudah wane burine takeson cikawa

Comment dinku shi ze bani tabbacin labarin yakarbu

#followme on wattpad@damselfeedo

Real@bazamfaria💙

It's ur Feedorh
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:2️⃣


,,,,,,napep ta tsayar ta shiga fada masa unguwar da xekaita tayi ,sunyi tafiya me dan nisa ,ta sauka

Wani madai-daicin gida ta shiga da sallamarta ,kai tsaye daki tanufa tare da furta " aunty na dawo ,da sauri wacce takira da aunty ta fito tace "Meerah andace? Ajiyar zuciya ta sauke tace " ankusa dai aunty "kinga Meerah nifa da zakiji nawa da kin hakura kinbarwa Allah komai domin kuwa shi ba azzalumin sarki bane na tabbata yaji kuma yagani da sannu sakayyar Maryam ze biyo baya

Seda ta sauke ajiyar zuciya ,cike da rauni tafara magana " tabbas aunty nasani Allah yanaji baya bacci kuma a addinance ma anbamu damar idan aka zalunceka bazaka iya yafewa ba ,to karama kwatan kwancin abunda akayi maka ,katseta Aunty tayi da fadin " natabbata idan Maryam na raye zata yafe takuma shafe abun a ranta dan Allah Meerah gada kijamana abunda yafi karfinmu ,matar nan tanada iko fiye da tunani zata iya komai saboda mutuncinta ,shin meyasa ke bazaki hakura ba,takarashe maganar tana kafeta da ido ,cike da kwarin gwiwa tace "aunty ,duk wani gata idan ba na Allah bane to ba dawwamamme bane ,bamuda kowa amma muna da Allah saboda haka shine zai taimakeni ,wlh matukar bandauki fansar 'yar uwata ba ,to bazan sake kiran kaina a cikin a halinku ba ,kedai kixuba ido ,ni yunwa nakeji ina abinci na ,girgiza kai kawai aunty tayi tare da fadin " yana da kin ki nakai miki ,Ameerah bata sake magana ba ta nufi dakinta.

Seda tafara watsa ruwa tukuna ta dauro alola bayan tagabatar da sallah ,se ta dauko wani littafi ,ta dade tana kallon murfin littafin ,kamar zata bude sekoma ta maida ta ajiye ,shiru tayi tana tunani can kuma se ta fashe da kuka, cikin kukan ne take suratai " tabbas baikamata ace har kinkai yanzu ban cika alkawarina ba yaya Maryam ,ke Kadai ce gatana kece wacce ta sadaukar da mutun cinta saboda nawa ,kin kula dani kinhani nayi kukan maraici ,tabbas bazan samu sukuni ba se Sauda ta tozarta ,tabbas zan wulakanta ta a idon duniya ,zansa ta fahimci ba komai ne kudi da mulki ke bayar wa Allah yagafarta miki tafada tana kara sautin kukanta ,seda tayi kuka sosai tukuna ta rarrashi kanta saboda bata son Aunty ta fahimci halin da take ciki hakan ze zama kamar tayi butulci ne da irin kokarin da take mata

Ahaka bacci mai nauyi ya dauketa

Ba ita ta falka ba seda akafara kiran sallahr asr da ciwon kai tafalka saboda kukan da tayi lallabawa tayi tayi sallah ,tukuna tafito don dora girki ,a kitchen ta samu aunty marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "aunty shine baki tashe ne ba ,murmushi kawai tayi mata " to kawo nakarasa aikin ,se a lokacin aunty tayi magana "aa Meerah nasan kingaji kitafi ki huta kawai " aa haba aunty dan Allah kema ya kamata kihuta hakan tafada tana amsar jajjagen da takeyi dole ta sakar mata ,tana tausayin rayuwar Ameerah gata yarinya mai gata da natsuwa amma saboda rashin adalci da son zuciya irin na wasu yana Neman sauyata ya Allah ka kawo d'oki a ratuwar Ameerah

"Amen taji muryar Ameerah ta amsa ashe a fili tayi addu'ar ba'a zuciya ba ,murmushi sukayi dukansu Ameerah tace " Aunty kinason Ameerah fiye da tunani nikaina a duk lokacin da na tuna dangina nakan samu kaina cikin zubar hawaye naji na tsane duniya baki daya sedai da na tuna Inada ke se naji damuwata ta gushe ya Allah yakara zaman lafiya a tsakaninki da yaya yakawo zuri'ah tagari yabani ikon kyauta ta miki nagode sosai aunty tafada kwallar da ta cika idonta yana subowa ,lakace mata hanci aunty tayi tace "to Mr tears nasan yanzu zaki fara zubar hawayen ai kedai bansan tsakanin ki da kuka ba babu damar ayi maganar arxiki dake sekinyiwa mutane kuka ,maza ki share hawayen indai baso kike aunty tayi fada da MABARACIYAR kanwata ba ,dariya sukayi dukansu






Follo me on wattapad@damselfeedo



#Real@Bazamfaria💙
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:3️⃣


,,,,,,,,,,Washe gari tunda safe Ameerah ta shirya ,koda ta leka dakin aunty bataji motsinsu ba da alama basu tashi bacci ba saboda haka kawai tafita domin yau tasawa ranta ganin sauda ko ta halin yaya ,tana fitowa tasamu Napep ta shiga shiru tayi tana tunanin wane karya zatayiwa get man yabarta ta shiga ,hakadai har suka isa dan nesa da gidan ta sauka ,dakafa tafara takowa har gaban gidan sedai yau babu kowa a kofar gidan ,jikinta ne yayi sanyi domin ga alamu masu gidan basunan

tana tsaye bakin gidan Sega get man din yabude get ,kamar a mafalki taga wata motor kirar Elentra 2019 ta fito da sauri ta nufi motor din ,winning nacikin motorn yayi domin ganin wata bakuwar fuska tana tunkaro shi karaf idon su ya sarke cikin najuna ,faduwar gaba Meerah taji take taji tarasa duk wani kwarin gwiwa nata ,ganin da yayi ta dakata ne yabashi tabbacin ba wurinshi tazo ba saboda haka yacigaba da tafiyarsa ,koda ta ankara sedai taga kurar motor alamar har ya wuce ,wasu yawu masu daci ta hadiye nan take xuciyar ta tafara kai da komo

Shin wanene wannan mutumin ,a iya binciken da tayi akan Saudahh batada 'da babba hasalima yarinyar ta tafarko macece ,to ko shine mijinta wannan din ,haka kawai tasamu kanta fa faduwar gaba tare da baiwa kanta tabbacin ba mijinta bane

'Karasawa tayi bakin get din tayi knocking, lekowa get man din yayi ,seda yagama kare mata kallo tukuna yace "Ke yau baza'ayi sadaka ba ,wai meyasa Ku Mabaratan nan bakuda godiyar Allah ne komai aka baku baya isarku ,ji kukeyi kamar kuyi sata, ina jiya ba da dadewa ba ma matar gidan nan seda tayi sada'ka to yanzu menene na dawowa?

" Baba kana nufin jiya matar tafito kenan "Ehhhh mana kuma taraba kudi saboda haka yanzu bata gari ma tayi tafiya ,idan kuma zama zakiyi to ga wurinan yafada yana rufe get din

" ohhhh god ,Ameerah tafada tana dafe kai "meyasa nayi gajen hakuri na tabbata jiya da ban tafi ba ,da nahadu da Saudah ,ok dama lokacin da na jiyo naga babu kowa Ashe sun shiga cikine ,Murmushi tayi kuma da ta tuna mutumin nan na dazu da yafito daga gidan ,to waya sani ma ko kwarton tane ,sekuma ta girgiza kai " aa shi baiyi kama da mutumin banza ba daga ganin shi yana da kamala

,to waye shidin ,haka tacigaba da tafiya tana sanbatu ,hartayi nisa bata sani ba ,horn taji anayi mata abayanta ,dan waigawa tayi ,sedai tayi nasarar bin motorn da ido domin bazata iya ganin Wanda yake cikiba kasancewar bakin glass ne a motor ,cike da jin haushin rainin wayon mutumin juyawa tayi taci gaba da tafiyarta ,ganin mutum tayi a gabanta "Assalamu alaiki , ya furta cikin silent voice dinsa ,kamar bazata amsa ba sekuma taga ai sallama ne kuma shi da yayi sunnah ya 'dabbaka ,amma ita wajibine ta amsa masa domin yin sallama ga musulmi sunnah ne amma maidata wajibije

Amsawa tayi batare da ta dakata da tafiyar ba " baiwar Allah idan bazaki damu ba ki shigo narage miki hanya domin baikamata mace kamarki ace ta bari rana yana dukanta ba ,karkisa hukumar kare hakkin mata ta hukun tamu yafada cikin sigar tsokana

Kara tamke fuska tayi ,cikin rashin son zancen yayi tswo tace "na gode bana bukata " haba ke kuwa ai cancantar ki ne yasa nace ki shigo bawai se kina bukata ba ,bata sake cewa komai ba tarabashi ta tafi

Yana tsaye a wurin har seda yaga tayi nisa alamar dai da gaske ba shigar zatayi ba tukuna yakoma motorn shi




Follow me on wattpad@damselfeedo





#Real@Bazamfaria💙
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:4️⃣


,,,,,,,tunda daga ranar Ameerah batasake zuwa gidan ba ,amma ko yaushe plan dinta taya zata shiga gidan sauda takeyin shi tanasone idan tayi nasarar haduwa da ita ,duk wani shiri nata yayi aiki ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunani ,murmushi tayi tare da fadin " aunty ce da kanta ,itama murmushin ta mayar mata tace " to yau najiki shiru nama zata ko kinfita ne shine nace bara nazo na dubaki tafada tana zama gefen katifa

" wlh aunty ina nan bana fada miki shegiyar tayi tafiya ba ,tana can wurin fasadin nata Ameerah tafada tana cixon baki da alama abun yana yi mata ciwo ,dafata aunty tayi tace " Ameerah nifa inaganin wannan abun da kikeyi ba mafita bane taya xa'ayi ki ajiye karatunki ,kawai saboda kinaso ki dauki fansa kinsani burin Maryam be wuce taga kinyi karatu ba to mezesa saboda ita ki ajiye karatun ki nidai anawa shawarar ki koma makaranta na tabbata ko baki tona asirin Saudah ba yau da gobe Batabar komai ba asirinta se ya tonu ,amma yarinya kamarki a ce kina yawon gidaje tare da amsa sunan Mabaraciya wanann ai ba solution bane

Ameerah dai batace komai ba hasalima se wani zancen ta dauko ,tunda aunty taga haka tasan cewar ba daukar shawarar ta zatayi ba ,bata taba ganin yarinyar da ke rike abu a ranta ba kamar Ameerah, abunnan anyishi tun bata wani mallaki hankalin kanta ba amma yakasa barin xuciyar ta
"Akwai dalilina na dakatawa da karatu ,kinsani lamarin karatu yana bukatar kudi kingani yaya bawani karfi ne dashi ba kema ba wani Sana'a kikeyi ba ,shin me kike tunani idan nasaka araina cewa dole se nayi karatu ,bafa dole se mutum yayi karatu bane ze iya dogoro da kai ,nasani karatun ma yanada matukar anfani amma idan inada rabon yi sekiga nayi konan gabane ,nifa araina banajin komai saboda dakatar da karatu na kawai dai idan natuna burin yaya Maryam kenan senaji wani iri cikin raina

" hakane Ameerah amma kinsani indai kinason karatun nan na tabbata Isma'l ze iya daukar dawainiyar komai "hakane aunty nagode sosai da kokarinku amma dawainiyar da kukeyi dani haka ma ya isa fatana rabbi yabani ikon kyautata muku

Niger state

Wata matace zaune ta hakimce daga ganinta kasan tana da isa da kuma izza waya takeyi cikeda takama ,Sam bakajin me take fada kasancewar sedai bakinta ya motsa yarane 'yan mata tsugune a gabanta waya takeyi amma tana kare musu kallo ,se bayan tagama wayar ne tukuna tace " zaku iya zama ,tashi sukayi suka zauna cikeda tsoro

Kallon su tayi tasake wani killer smile cikeda isa tace " to ya kun shirya abunda nake bukata ko kuwa cikin kyar kyarwa dayar tace " munshirya Hajia daga mata hannu tayi tace "naji naki amsar kefa ,tafada tana nuna dayar budar bakin ta tace " tabbas duk Wanda babu Allah a cikin ranshi to ze iya aikata komai ,dama idan bakada kunya to ka aikata abunda kaso kidubemu hajiya anan ciki babu wacce baki isa haifarta ba amma kuma kice mune zamu zameki ababen jin dadi ,daga karshe kuma kitura mu karuwanci anabaki kudi wa'iyaxubillah ,amma ba lefinki bane lefin iyayen mune da Allah ya dora nauyim mu akansu amma suka kasa saukewa har wasu suka yaudaresu suka daukomu da sunan aikatau ,domin subata mana rayuwa

duk maganar da yarinyar nan keyi babu wacce ta taba zuciyar hajiya itadai abunda tasani dole zata biya bukatar ta dasu takuma samu kudi ta dalilinsu ,daya daga cikin masuyimata hidma takira tace "tafi dasu kitabbata sun tsabtace jikinsu domin bana bukatar na shaki wari ko akasinsa ,kuma ki koya musu yanda zasu sarrafani domin naji dadi daga nan zuwa gobe




Wacece wannan matar?
Kucigaba da bina asannu zan bayyana muku komai

#comment and share


Follow me on wattpad@damselfeedo




#Real@Bazamfaria
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )


*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

*By*

*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)


🅿️:5️⃣



,,,,,,,, haka matashiyar matar nan ta tafi da...


Read / Download MABARACIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album