Join Our WhatsApp Group

GORAN DUMA Complete Hausa Novel Document by GORAN DUMA


GORAN DUMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 95960



GORAN DUMA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Maimuna Idris Beli ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 517.56 kb

File Type: txt

Views: 1534+

Download: 919+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: GORAN DUMA
Na Maimuna Idris Beli.
Ebook Publish by http://hausaebooks.cf

Izan kuna bukatan wasu litttafan sai ku ziyarci shafinmuu na yanar gizo akan adireshi
http://hausaebooks.cf
Farkon littafi.

.
.
Rumaisa'u wankan tarwadar mace matsakaiciyar tsawo
da kiba, fuskar ta nada alamun hakuri da sanyin hali a
wajen wanda ya karanci mata, amma mai rashin matsaya
ga mutumin da ya cikawa kansa zargi a cikin mutane
saboda rashin son maganar ta da karancin fara'ar ta.
Ta na xaune a matsakaicin palon gidan su ita kadai, a
tsakiyar palon bisa kapet tayi kaca-kaca da takardu. Ga
wayoyin ta da na'urar kwanfuta(laptop) dake kapet, ga
kuma robar ruwa da kwalin lemo a gepe.
Wannan yasa ba sai an padi ayyuka ke caja gabban ta
wanda fuskar ta da gabban suka kasa nuna gajia, watakila
dan juria da son aikin har zuci.
Can daya daga cikin wayan ta dake zube ta saki wata
siririyar kara amma abun mamaki duk da haka sai ta
firgita, ta dubi wayar da sauri kuma a tsorace xuciar ta na
bugawa, duk da haka ta latsa sakon ya pito.
A pili cikin ta Ya bayar da wani kuuu... Har sai da ta dan
rankwapa na alamar ba a karar ya tsaya ba har da haipar
mata ciwo.
Ga abun da ke rubuce a cikin wayar '' yaushe ne kika
shirya barin nunpashi na ya huta?
Duk yadda kike jin aiki da dawainiya a rayuwa bana jin
kin kama kapa ta, amma kin san wani abu?
Mamakin yadda kike share al'amra na ma wani tapkeken
babi ne a kundin da na ware miki, wanda ko wannan
babin aka barni dashi ya isa abin wahalar da xucia.
Rumaisa'u bayyana min siririn ki wanda ya rike ni na kasa
ampani da Karpi wajen maganin ku ke da zucia ta!
Ware min ko sakan goma ne daga lokutan ayyukan ki kiyi
min wannan aikin Rumaisa.
Daga MAHAUKACIN MASOYI.
Tayi wurgi da wayar kamar wadda ta galla mata cixo a
bayan ta, bayan ta kammala karanta sakon, tana satar
kallon wayar, san nan ta koma satar bin palon da kallo,
musamman jikin labulaye, harshen ta pal ambaton
Hasbun Allahu wa ni'imal wakil, ta dora da padin '' A uzu
bi kalimatuLlahi tammat min sharri makhalak ''
Duk illahirin gabobin ta sunyi sakayau, babu nauyi
tamkar idan an yanketa jini baxai bullo ba saboda tsoro
da wasi wasi
Tsawon piye sati hudu kenan tana pama da sakonnin
wanda ke Kiran kansa da MAHAUKACIN MASOYI mutun
da a yanxu ta para shakkar mutun ne ko aljan, mutun da
aljan din na xahiri ko kuma ifiritai ne (hackers) suka
hauro layukan wayoyi kamar yadda akan same su a yanar
gizo?
Cikin zarginta uku kowanne ta canka babu dama a cikim
sa, in mutum ne ta wanne bututun yake hango halin da
take ciki a lokacin da yake turo mata sako?

Kamar yanzu da yayi maganar cakudewar ayyuka.
Idan aljani ne ma wani bakin tashin hankalin ne dan babu
ta inda aka gwamutsa mu'amalar mutane da ta aljamu
bare har a gayyato musu batun soyayewa a irin haka.
Zargin 'hackers' din ne ma mai dam sauki wai idan ta
kawar da kai ga rashin yawan bayyanarsu a layukan waya
ta wannan sigar, ko kuma lissapin nemo manuparsu a
kanta da suka dame ta ita kadai...
Wata dattijuwar mace para mai tsawo da kiba , tayi
sallama ta shigo palon, da sauri rumaisau ta gyara sahu ta
hadiye maitarta ta amsa sallamar matar, purkarta da
gabobinta suka nuna ladabi, tana murmushi ta amsa
sallamar matar mai alamin zapin nama ta dubeta tace,
'' Rumaisau ki saki aikin nan ki huta haka,ga pura mai
kyau can Alhaji ya shigo da ita, kije ki dama kisha...
Rumaisamu tayi kokarin tattare tashin hankalim da take
ciki tabawa cikin ta ajiyarsa, ta tare matar da rawar
murya dake kokarin komai ya zama ba komai ba,
''Oh Abba ya shigo Hajia?
Hajia tayi murmushi ta amsa mata tun da hamida ta bar
mu gidan ya zame mana kamar hurumi, kirikiri alhaji ke
nuna pipiko tsakanin mu, ni kaina sai na zage nake sanin
shiga da pitar sa.
Rumaisau tabi wayar ta da kallo tana murmishin hadawa
zuciyar ta ayyuk biyu, tunanin gudan jinin ta Hamida, da
kuma tausayin ta a matsayinta na mace mai rauni, wanda
kuma zata tsaso kila cikin ratuwar da tapi tata wadda take
tapia a cikin ta yanzu muni. Sai kawai taji hawaye na son
cika mata ido, amma ta dage ta dadiye, ta cewa hajia '' to
hajia wannan dai tsakanin ku ne''
hajia ta bar amsawa Rumaisau maganarta tabi ruwa,
saboda damum kanta da nazarin rumaisau'un da take
sonyi wanda puskar ta ke son karyata abun da zuciyarta
ke kokarin bayewa, amma data hada nazarin nata da
wasu daban sai ta yi saurin sharewa gudun batawa kai
lokaci, ta jima da sanin rumaisa duk inda ake neman
mutun mai kawaici ta cika mizami, mawuyacin abu ne
kaji korapi a bakin ta duk yadda ka kai ga kwarewa hilarsa
wani ya amayar da abun da zuciyarsa ta boye.
'' baki da bukata ko ta neman addu'a ce daga gare ni!''
hajia ta sami kanta da furta wa rumaisau cikin tsura mata
ido, sai rumaisaun ta dan diririce saboda pargabar ko tayi
wani abu da ya dago halin matsin da take ciki. Ta hau
hada takardu tana cewa '' hajia kiyi min izinin gobe na kai
rubutun nan abuja nayi submiting.
Hajia taci gaba da kallon ta, kallo mai cike da tuhuma. ''
rumaisau kwanan ki nawa da zuwa Abuja kuma tunda
kike rubutun nan kin taba kai shi takanas?
Ji nake ta Email kike tura musu?''
a ladabce Rumaisau ta shiga kokarin kare kanta.
''akwai matsala ne hajia, kinga ban gama bugawa ba
kuma ka'ida gobe laraba mujallar ke pitowa. Ba wai lallai

ya zama sai nakai din ba,amma dai ina neman alparmar
zuwan hajia saboda muhimmanacin rubutun''
hajia tayi siririyar daria tana ci gaba da yi mata wani irin
kallo, wanda rumaisau ta kasa daurewa har sai da hajia ta
ci gaba.
Ko dai alkunyarki ke son gazawa ba zaki iya rashin
Hamida ba ko?
Ni dai abun da zuciata ta karantar dani ke nan,
da sauri rumaisau ta tareta cikin zaro idaon bijirewa
batun hajiyar tace ''ah! Hajia to na pasa zuwa tunda kin
zargi hakan..
Wallahi ko kadan ba dan hamida zanje ba hajia.
Nan da nan hajia ta tareta da na yarda daje rumaisau zan
kuma sanarwa Alhj amma da sharadin zaki tashi yanzu ki
nemi wani abu kisa a cikin ki.
Cike dq jin dadin kulawar da hajia take mata ta yalwata
para'arta da murmushi tace "ai na bari tuni
tun bayan pitar hajia ta janyo wayarta a gajiye tankar
wadda tayi gudun shekara ta kasheta, ta jepa akan kujera
samnan ta pice debo purar da hajia ke mata tayi.
Ta kori hataniya da rudin wannan duniyar da tilastawa
kanta shan purar sosai har ta gamsar da ita,
tayi wamda ta sallaci Isha'i, sannan ta zauna azkar din
yammaci da bata samu damar yun sa a kan lokaci ba, sai
tayi shi a yanzu tana mai nutsuwa da kaskantar da kai ga
Mahalicci.
Abin da ya karpapa mata gwuiwar isa gadon baccinta da
wuri tare da tsammanin zatayi barci a nutse shine a zacin
da tayi na kashe waya tare da yunkurin barin kano a gobe
dan ganin gudun ruwan MAHAUKACIN MASOYI , wayar
da yake kiran ta ta kashe, garin kano idan ma kyamarar
sirri (CCTB) ya makala a garin to ta bar shi, cikin kwana
biyu kuma sai ta gani ta ina zai leko ya rikitata?
ABUJA
karpe biyu da rabi na rana ta pito ofishin da jaridar
Aminiya dake jabi da komawa masaukinta wajen Innarta
a anguwar wuse.
Duk a rikice take tun saukarta Abuja taji wata bala'in
rashin nutsuwa ya mamaye ranta har yake bayyana a
gabban ta, wayi ayyuka.
Misali. Tana sauka bus din da ta kawota garin a
matsayinta na wadda ta taho Abuja a gaggauce, dan zuwa
opis maimakon ta dauki shatar motar da zata kaita Jabi
kawai sai ta buge da daukar wadda zata kaita gidansu
Wuse cikin wasiwasi,
a cikin tadi din ne ta budo naurarta mai kwakwalwa ta
lalubo rubutunta tana nazari da shawarar ta tura shi
kawai ta Email din ta wuce gidan ta kwanta,
anan kuma ta lalubo Moderm dinta cikin jakar sai ta tarar
ta baro shi a kano, nan take ta yanke shawarar tsayawa
wani kataparen kantin harkokin sadarwa da ke nan titin
da zai sada ta da wuse daga Utaho kawai, ta tsaya anan ta

tura rubutun,
ana isowa Annur ta yiwa direba umarnin ya tsaya anan ta
shiga ta pito.
Ta kwashi i laptop tayi ciki , kataparen waje mai kamar
komai da ruwan ka a bangaren sadarwa, wayoyin hannu ,
layukan waya, katin wayam kwanputa da sauran tarkacen
da suka dangance ta,
modem din da ta baro a gida ma wancan zuwan nata ta
saye shi anan,
haka dai gurin yake bangare bangare ko ina da abubuwan
da ya kunsa.
Yau tana shiga bangaren cafe ta tunkara, amma kamar
wadda tazo daga kauye duk kaparta rawa take sai
sassarpa take har ta isa inda ta nupa.
Ba wani abu ne ya janyo hakan ba sai gain yadda kamar
kowa a wajen ya zuba mata ido ne,
da yake yawancin katangar dake tsakanin bangarorin ta
gilas ce, kamar duk ma'aikatan wajen sun doro
hankalinsu akanta.
A gajiye ta karasa wajen ta zube a kujera tana
numparpashi tamkar wadda tayi gudun pampalaki, ta yar
da jakar naurar gepe ta zube wayoyinta akan tebur,
mai kula da bangaren ya dago kansa daga printer da yake
zaro wasu takardu yayi mata wani kallo shi ya tsinke
tunanin ta,
ta shiga zargin ko wani mummunan abu ne a jikin ta da
mutane ke binta da kallo haka?
A dabarance ta para nazarin shigarta , tana sanye ne da
bakar after dress mai sheki da abon shudayen kananan
dumatsu kalar riga da siket din material dinta na ciki,
kanta nade shi da mayapin rigar kuma da yake ba zata iya
putowa a haka ba sai ta kara da nade kapadar ta da
lallausan mayapi mai matsakaicin girma shi ma shudi,
jakarta da takalmin ta duk shudaye , idon ta sanye da
siririn parin gilas,
a zatonta ko ba ganin idon ta ba, ganin idon kowa ma
babu kauyanci ko digo a cikin shigarta,
duk da haka bata gamsu ba sai ta saci ido ta bude jaka da
sunan lalube ta kalle puskarta tsab ta cikin jalar komai
pes hatta hodar puskarta da man lebe (wetlips) babu abin
da ya gigita su.
Ta zuge jaka tana sauke ajiyar zucia cikin tsananin tashin
hankali wanda ya karu lokaicn da ta lura mai wajen ya
kapa mata ido ya pada da karpi laa kamar barauniyar da
tazo tayi sata jiya... Lol.
.
GORAN DUMA 2
.
.
Ta zuge jaka tana sauke ajiyar xucia cikin tsananin tashin
hankali wanda ya karu lokacin da ta lura mai wajen ya
kapa mata ido kamar barauniyar da tazo tayi masa sata

jiya yau ma ta dawo.
Sai bakin su ya hau rawa shi da ita.
'' madam... Madam.. Me kike bukata?
Ita kuma tana rawar bakin cewa don Allah... Zan tura
wani aiki... Ta na'urar kwanputa, ta me zan tura...
Bai iya amsa mata ba sai gyada kai kawai yake kamar
kadangare yana kallon ta kai tsaye , hannunta sai
karkarwa yake ta parke jakar system dinta shi kuma da
sauri ya karaso ya tura mata foot stool waiko zata dora
kapa.
Da wasa ba zata dorar da abun da tayi a naurar kwanputa
ba, musamman da shi mai wajen ya dauki waya yana
magana da wani harshe da bata samshi ba alamunsa
kuma na nuna hankalinsa na kanta.
Ba a dauki ko cikakken minti daya ba sai ga wani matsashi
ya shigo mai matsakaicin tsayi da kaurin jiki puskarsa na
da alamun para'a amma a halin yanzu kai tsaye ba za a yi
masa passara ba , ya nemi guri ya zauna bayan sun gaisa
da mai kula da wajen sai ya nemi kujerar da ke
puskantarta ya zauna yana satar kallon ta, tana latselatsen
keyboard,
can tayi namijin kokarin dagowa suka dubi juna ido cikin
ido shi ya kawar kamar a razane ita kuma ta hade puska.
Ta nuna masa TV plasma dake makale a sama tace.
'' bawan Allah kaga abun kallon can.'
yayi pirgit ya dubi talabijin din sannan ya dube ta
muryarsa na rawa yace ina... Patan dai ba tsarguwa kikayi
ba?
Ya mayar da kanta rai a bace tana matsawa siririn
hancinta hura iska. Alamar dai haushin ta ji, amma bata
tanka ba.
Shi ma ya kawar da kai yana cewa batawa kai lokaci ne
kayi abun kallo kace baza a kalle ka ba.
Ta dago da sauri ta dube shi amma ba ita yake lallo ba
balle ko a puskarsa ta karanci abun da yake nupi. Ta
kokarta tace ko?
Ya juyo cikin kada kai haka nace. Saboda haka kallon naki
yapi kallon wannan akwatin da kike nuna min kaye...
Yanayin yadda yake magana duk kwakwalwarta ta kasa
gane inda ya dosa , puskarsa babu walwala bare ayi
zargin irin mazan nan ne masu latselatsen yanmata.
Tsam! Sai ta tattara kwanputarta ta mayar a haka ta zuge
jaka tana cewa bari na bar muku wurin ko? Kila kuyi abin
da zai ampane ku, dan kallona babu ma'anar da zai baku..
Malam nawane kudina?
Ta mike rataye da jaka tana duban mai wajen ya girgiza
kai kamar a darare me kika yi na kudi? Kije kawai .
Ba ta ko tanka ba ta juya ta pice kaparta na hardewa
kowa na damuwa da kallon ta har ta pice cikin sassarpa.
Bata sami direban da ta bari cikin mota ba, sai kawai ta
rungume hannu ta jingina da motar cikin rudani tana
zuba idon ta inda zai billo.

Cam sai gashi da mujalla a hanu cikin zapin nama ya
bude motar yana neman apuwar ta , ta hango wannan
gajeran mutumin da yake kallonta yapi talabijin yana
doso inda suke.
A hanzarce ta cewa direna sauri mubar wajen nan, cikin
direba ya dauki wani kugi da yasa shi kasa bin umarninta
yanayin yadda tayi maganar ya sa yayi zargin babu gaskia
a tare da ita, tsoro ya ke ko wani abun ta sato tasa shi
taka sawun barawa.
Yakai ta ya sauke lambar motarsa kuma ta shiga kundin
masu laipuka. Saboda haka kawai sai yaki tapia har
gajeren mutumin ya karaso ya mika mata wayoyinta ta
windon motar.
Madan sanyin AC wajenmu ya sabbaba miki mantuwa.?
Ta karba tana mayar masa da raddi haka ne musamman
da yake daga kauyen mahudar rana na pito ba.
Ya juya ya koma da karamin murmushi a puskar sa.
''Allah ya baki hakuri idan gaskiar tawa zapi tayi miki.
Direba yayi ajiyar zucia ya tashi motar yana cewa kinga
gara ma da muka tsaya. Ko kala bata ce masaba har suka
hau titi, sanan tayi masa umarnin ya kaita opishin jaridar
Aminiya kai tsaye ta gyara shirmen da tayi. Acam kuma ta
watsar da dimuwarta tayi abin da ya kamata, karpe biyu
da rabin nan ta pito da dokin zuwa gida don samun
nustuwar zucia amma dai ta san wahalar da kai ne dan
gaba daya tsarge take, sai kissipawa kanta take wani na
biye da ita, bata jima bakin titi ba ta samu mota kuma da
yake tsakiyar rana ne titin babu cunkoson ababen hawa,
sai nan da nan tapiyar tayi musu sauri suna kan Berger
flyover kiran innarta ya shigo wayarta da ke kunne ta dag
cikin muryar ladabi tace Momi ina hanya kusa da isowa
tana sauke wayar sai tabi ta da sabon sako hankalin ta
kwance ta bude shi, dan a amintacciyar wayarta sakon
yake, wayar da bata taba hadata da gigitaccen sakon
Mahaukacin masoyi ba, saboda haka karsashinta ta para
karantawa.'' Rumaisau garin Abuja ni'imtaccen gari ne
ma'abocin dauke kewa da gadar da nutsuwa tankar
yadda salihar puskarki take, amma yau na shiga rudani
da nake ganin puskarki da ayyukanki a gigice.
Kila kin halarci Abuja ne bisa radin kanki ban kuma cire
tsammanin dan ki samarwa kanki nustuwa bane, amma
yaya kika hana zuciyarki da gangar jikinki hakan
Rumaisa?
Laipin me wayarki tayi kika kashe ta?
Inajiran amsa.
naki MAHAUKACIN MASOYI.
A Uzu bi kalimatuLlahi Tammat min sharri ma khalak.
Wannan adduar ta karabto tana juya wayar duk da kuwa
tayi mata nauyi a hannun, a yau kam taji a ranta ba
bil'adama bane mahaukacin masoyi ba, kuma ba hackers
bane duk...


Read / Download GORAN DUMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

4 months ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

4 months ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album