Join Our WhatsApp Group

SAKON SO Complete Hausa Novel Document by SAKON SO


SAKON SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 72101SAKON SO

Reading Time: 6 Hours

Added On: 30, Aug 2023

Author: Aisha Muhammad Maman Shakur ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08108517010

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 424.32 kb

File Type: txt

Views: 4056+

Download: 2025+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 💫 SAKON SO 💫


M SHAKUR ✍🏻


Abu daya zan fadamuku gareku masucin hakki na, da masu daukan book dina suna sawa a site dinsu, damasu sawa a YouTube, da dukma wata ko wani mai amfani da book dina yana kudi without consulting me wlh wlh ban yafeba kuma bazaku taba ganin cigaba ba dan hakkin wani kukeci, kome zakuyi da rubutu na contact me first! 07012181461Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuna kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da Episode biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAIEPISODE 1️⃣
~Masjid Ibn Taymiyah~
Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jama’a kowa yaci manyan kaya manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube, cikeda damuwa yace “he’s 20minutes late Arif kazo mutafi koda na’ibin limamum masallacin nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not cool” girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace “I know he will come let’s just give him some time, Uncle Hamma is just…..” dasauri abokin yace “sociopath” wani mugun kallo Arif yamai zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin nashi yafice daga cikin premises na masallacin dasauri ba dudda jama’a na kwalamai kira ta ko’ina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace “barka da zuwa Uncle Imran” wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft milk yadi daya haska bakar fatanshi dake bala’in sheki tsabagen hutu.


Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne kanshi akasa babu wani murmushi ko fara’a akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace “Arif” wani kalan murmushi Arif din yasaki cike da mugun girmamawa yace “na’am Uncle Imran” tareda dago kanshi yadan kalleshi saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay magana cikeda wannan natsuwan yace “get up kayanka will get dirty” tashi Arif yayi babu gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun sahu, kafanshi na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif dakanshi ke kasa yace “muje ko”? Gyadamaikai Arif yayi yace “to bismillan mu Uncle” yay maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada bala’in dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif yace “waliyin Arif ya iso” karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai addu’a ana gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da kallo yace “dan Allah jibi Arif saikace yaga God” dayan abokin mai suna Muhammad yace “to ai kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu ba” tabe baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace “bakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemu” wani kallo Muhammad kema Aliyu yace “waikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya ba”? Mugun kallo Arif yama Muhammad yace “bazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retire”? Kalan kallon da Muhammad kemai yasa yace “me to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan tsohuwarshi” wani mugun harara Muhammad yamai yace “kainedai kaga tsufan dan ni bangani ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da yara biyu” dasauri kaman jira Aliyu yake yace “kasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba, matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshi” zai cigaba da magana ganin Arif na tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi.💫 SAKON SO 💫


✍🏻 M SHAKURJama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 2️⃣
Tunda yashigo cikin estate dinsu yahango wani magidancin mutum tsaye agaban wani dankareren gida da sojoji guda uku ke tsaye wajen taredashi, kana ganin mutumin kasan zasuyi age mate saidai shi mutumin yafishi tsufa sosai dan ga furfura ko’ina akan fuskanshi, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakarasa gaban gidan batare daya kashe motan ba yasaukar da glass din motan kasa hakan yasa sojojin wajen suka sassaramai Sir! Gyadamusu kai yayi a natse batare daya amsasu ba sannan yasauke idanuwanshi kan mutumin daya taho wajen motan dasauri fuskanshi babu alamun rahama akai baiyi wata wataba babu gaisuwa ko sannu cikeda masifa yace “Alhaji Imrana nagaya maka karabun mini da d’ana kaki I agree cewa lokacin nan nagudu na barsu Kaika sashi a makaranta da sauransu yanzu I am back yarona don’t want anything to do with me, imagine ni mahaifin Arif ina masallacin nan amman ko kallo ban isheshi ba sabida kai sai rawan jiki yake yana binka kaman yaga sarki, karabun mini da dana allow me to be his father” tunda yake maganan kallonshi yake saida batare da yanayi kokuma wani abu na fuskanshi ya chanza ba yagama tsaf sannan yace “nabarka lafiya Baban Arif” tareda maida glass din motan sama aka bude mishi gate yawuce yashiga cikin katafaren gidanshi yabar mutumin awaje yana nuna kanshi yace “ni zaka gwadama miskilanci”? Duk maganganun dayake sojojin kallonshi suke so suke suje su bubbugeshi amman kallon da Oga kadai yamusu is kallon kar wanda ya kula bakona cikinku yagama duk abinda zaiyi yatafi.

Wajen jerin motocin dasunkai kusan 12 acikin gidan yayi karasawa yayi da motan yana tafiya very slow yay parking sannan yakashe motan yakai kusan 5min zaune a motan kaman bayaso yafito sannan yabude kofan ahankali yafito sannan yamaida kofan yarufe yajuya yafara tafiya yana dumfaran cikin gidan ma’aikatan cikin gidan dake aikace aikacen su na gaidashi da kai kawai yake amsa musu yakarasa gaban babban durmemen flat daya rak dake cikin gidan dakeda girman gaske yabude kofan ahankali yashiga wasu yan kananun yarana su biyar da dukansu bazasu wuce shekaru 3, 4, 5 hakaba suna tsalle tsalle suna ganinshi duk kowa ya natsu duk suka zauna akasa atare cikeda gwaranci irin na yara sukace “Abee Assalamu Alaykum” maida kofan yayi sanan yajuyo yabi yaran da kallo dayar karaman murmushi daya bayyana akan fuskanshi a natse yace “wa’alaykumus salam Children” sannan yashigo cikin katafaren falon dawani katon family picture frame ke bangon dake dauke dawata tsohuwa da akalla zatakai 70yrs sai shi yana tsaye agefenta daga yanayin yanda fuskanshi yake ahade zaka gane ko kadan bayason hoton sai wasu manyan mata dasuma sun manyanta masu kama dashi su uku, saikuma wasu maza su biyu dakana gani zakasan kanninsu ne saikuma yara dayawa a frame din, zama yayi kan kujeran sannan yabi yaran da kallo daduk suke kallonshi sai yanzu yama tuna baitaho musu da komi ba this is so not like him saurin dayake yasa yamanta, wannan karan dan murmushi kadan yayi sannan yamike musu hannu yace “kuzo nan” kaman jira suke dawani kalan gudu suka taho murmushi yayi anatse yace “zan dauki kowa one after the other okay” gyadamai kai duka sukayi babban cikinsu dake 5 yafara dauka yace “Muhammad” yaron ya kyalkyace da dariya sannan yadauki na biyun yace “Faisal” yadauki macen yace “Nana” sanan ya ijiyeta yadauki dayan macen yace “Miemie” sannan yadauki karaman dake 2yrs yace “Anees…….” Shiru yayi sabida zafi dayaji ajikin yarinyar hakan yasa yakai hannunshi dasauri yataba goshinta jin dumi yasa yakalli Muhammad yace “call Aneesarh Mom” dasauri yaron yajuya yay kitchen, ko 1sec Muhammad baiyi da shiga kitchen ba wata Yar Babban mace tana kamadashi tafito da apron ajikinta dasaurinta tace “Yaya Imran kadawo” kafin yay magana wata yarinya Yar budurwa fara da akalla zatai 21yrs tafito daga kitchen din da gudunta tana wani kalan mugun murna dudda akwai Aneesarh ajikinshi saida tazo ta gefenshi tawani kalan rungumeshi tace “Abee Assalamu Alaykum” dan murmushi kadan yamata tareda daga kanshi yakalli fuskanta yace “wa’alaikumus salam Kausar, ina dan kwalinki”? Yay maganan yana kallon kanta dababu dan kwali tayi tsifa rabi tabar rabi, dan zaro idanu tayi sannan tajuya da gudu tai sama binta yayi da kallo sannan yadawo da hankalinshi kan kanwarshi yace “why is Aneesarh body hot”? Kaman Maman zatai kuka tace “wlh babu yanda banyi da itaba takishan maganin Ya Imran” kallon fuskan Aneesarh yayi dake kan jikinshi daketa kallon fuskanshi sannan yakalleta yace “kawomin maganin” dasauri tai sama tana murmushi sosai bata taba ganin mutumin da yara ke bala’in so kuma suke tsoro kaman Ya Imran ba dazaran yashigo kowa zai natsu sannan kowa yayta murna suna kallonshi saukowa tayi da ibuprofen na yara a hannunta tazo har gabanshi ta tsaya ta bude maganin ta debamai a marfi 5ml tabashi tace “Allah sa tasha ni karma ta amayo makashi Ya Imran tabata maka jiki” karba yayi sannan yakalli Aneesarh dake kallonshi yadan mata murmushi ahankali yace “haaaaaammmm” yabude bakinshi kadan hakan yasa dasauri yarinyar tabude bakinta tace “haaaaa” samata maganin yayi abaki ahankali with so much care and love kaman yana handling Yar kwai dasauri yarinyar ta shanye murmushi yamata yace “good job Aneesarh” yay maganan tareda sakata ajikinshi tai lamo yana caressing nata sannan yadago kanshi yakalli mahaifiyarta dake kallonsu tana murmushi sosai yace “su Hajiya basu dawo daga gidan bikin ba”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman yanzun nan mukai waya suna hanya, harda Anty Binta itama dazu ta iso da mijinta” gyadamata kai yayi batare dayace komiba hakan yasa tace “nakawo maka tea ko coffee Yaya” girgiza mata kai yayi yace “no anjima” gyadamai kai tayi sannan tajuya tawuce kitchen dan karasa girkin daidai nan itama Kausar ta sauko tana sanye da hula tana kallon mahaifin nata tace “Abee nasaka” kallonta yayi sannan ya Gyadamata kai tawuce kitchen tana murna Maman Aneesarh dake sauke tukunya daga kan wuta tace “mehaka”? Dariya tayi takaraso kusada ita tace “murna nake Abee yadawo kinga zai tayani karasa tsifan” hararanta Maman Aneesarh tayi tace “ke wai bakisan kin girma bako Kausar kullum Babanki zai fita yaje aiki yadawo inhar yashigo gidan nan saikin sakashi yamiki naki aikin bakiji abinda Hajiya tagaya miki bako kina wahalar mata da dand’a” turobaki tayi ashagwabe tace “nikuma ai Babanane” yanda tayi abinma dariya yabama Maman Aneesarh tace “Allah ya shiryeki ina Abdallah baitashi daga lectures din bane”? Dasauri Kausar tace “4-6 yakedashi aini bazan iya Medicine ba ko kadan wlh wahalallen course” ahaka suka cigaba da hiransu suna girkin gwanin ban sha’awa.Yana rikeda Aneesarh a hannunshi yana caressing nata ahaka bacci yay awon gaba da ita, haka yake inhar zai dauki yara su dan jima awajenshi duk rigiman yaro saiyayi bacci, tashi yayi yana rungume da ita a kirjinshi har gaban kitchen din yaje batare daya shiga cikiba yace “Kausar” dasauri Kausar dake kwashe shinkafa a flask tace “Na’am Abee” tasaki spoon din tajuya tafice daga kitchen din dagudu ganin Abee agaban kitchen din rungume da Aneesarh datai bacci yasa tace “Abee gani” ahankali yace “jeki kawo zani ki goyata” gyadamai kai tayi dasauri tace “to” tabi tagefenshi tai bene tafara hawa dagudu anatse yace “what did Abee said about running”? Daina gudun tayi dasauri tai piki piki da ido tace “no running” tana tafiya tai sama bata jimaba tadauko zani tazo har gaban kitchen din ta duka gabanshi tace “Abee samin ita” ahankali yazare ta daga kirjinshi sannan yasamata ita abaya ahankali tareda karban zanin yadaura mata akai itakuma tamike tana...


Read / Download SAKON SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album