Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DA IZZATA Complete Hausa Novel Document by DA IZZATA


DA IZZATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 66237



DA IZZATA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 11, Jul 2024

Author: Autar Manya ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08142105218

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 365.56 kb

File Type: txt

Views: 1176+

Download: 1282+

Last download: 3 days ago

Description/Story:
*DA IZZA TA !*
( Painful Love )





*Mallakar*
AUTAR MANYA🌹



*SADAUKARWA GA*
Khausar Salis Usman




*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*


🅿�? *1*


Cikin shigar doguwar riga mai roba-roba na fito wadda tai matuƙar kamamin ƙirar jikina wadda narasa wace irin ƙirace dani wadda dik wasu kaya dazan saka bazata taɓa ɓuyaba,farar alkyabba tass na ɗora bisa kan wannan doguwar riga, tare da hularta, cikin sauri nake takowa daga sashen fulani umma abokiyar zaman ummina, inayi ina amsa wayar dake maƙale a kunnena kuyanguna suna gefena suna tattaremin alkyabbar tawa wadda take sharar ƙasa, ina kammala wayar na juyo tare da maka masu wani wawan kallo wanda yasa babu shiri suka jada baya, da kaina na ƙarasa bakin kofar sashen ummi wadda yawan bayin dake wajan yafi na kowace ƙofa sabida kula da lafiyar ummi, wani wawan kallo na maka masu wanda yasa babu shiri suka baje daga wajan suka koma gefe guda.
Cike DA IZZA TA! wadda tabi jikina da dukkan wani motsina naja kofar tare da zira haɗaɗɗan takalmin dake ƙafata na taka har cikin babban falon ummi.
Ganin babu kowa se kuyangunta yasa na juya sabida yadda su hapcy ƙawayena ke jirana zamu fita dasu, kuma nasan tabbas! idan na shiga ummi zata zaunar danine tamin nasihar tata data saba.
Cikin yauƙi da gwalli nake takun nawa kuma duk taku guda se jikina ya kaɗa tamkar da gayya domin na lura hatta hadiman dake wannan sashe hankalinsu yana kaina.
"Takawarki lafiya jinin sarauta ƴar sarauta ɗiyar sarki jikar sarki mai takalmin zinare hajiya asma'u ikon ALLAH mata agidan manyan mutane ba ƙananu ba duk wanda rabbi yasa ya sameki ya dace da MACE MAI IZZA DA MULKI gadon gidanku ba haye ba".
Cewar wani bafade kenan wanda tun isowata harabar gidan namu naga yana bina abaya, nasan ba komai yake bukata ba face kuɗi, cikin izzata na bude ƴar jakar dake hannuna na zaro kudin da bansan adadinsu ba na watsa masa, inaji yana cigaba da kirarinsa nidai haka na wuce kaina cike da girma.
Ta ƙofar baya na zaga sabida anan nacewa su hapcy su jirani domin nasan idan har na fita ta kofar wajan fada se ansami wani munafikin daze kaiwa mai martaba gulmata.
Cikin isa da izza nake taka ƙafafuna har sanda na isa gaban kofar wajan da ake adana motoci na nufa tare da isa gaban farar motar dasu hapcy suka shigo mana da ita.
"Se Meemah".
Shewar su hapcy kenan ƙawayena na amana waɗanda suka biyomin fita domin mu zaga gari muga mai gari ke ciki.
Ƙyafe bakina nai tare da kallonsu a ɗage inajin kaina a sama tare da matsawa gaban motar.
Ina saka hannuna zan bude marufin motar naji andafe da ƙarfi, wani irin zare idanu nai waɗanda suka fito sukayo waje.
Mayar da ajiyar zuciya nayi tare da tamke fuskata tamau.
Tsaye yake agabana da kayan gadon nasa wato farar rigar J.C ta ƴan ƙwallo se baƙin wando dogo, yawani harde hannunsa akan kirjinsa ɗayan kuma ya dafe marufin motar dazan shiga, cak su hapcy sukai tare da sakin baki dik jikinsu ya ɗau rawa.
"Dalla malam kasa karmin marufi kazo zaka ɓatamin lokaci" nafada cikin tsiwa.
Tsareni yayi da masifaffun kaifafan idanunsa masu kama dana mai jin barci batare daya tankani ba.
Wannan hali nasa yana mugun ɓatamin rai..
Tura bakina nai gaba tare da juya masa baya.
"Hajiya bafa zaki fita ba wallahil azim babu inda zaki".
Naji sautin muryarsa acikin dodon kunnena.
"Sannu ubana"
"Nafi ubanki mah".
Yabani amsa kai tsaye yana fesamin numfashinsa sabida kusancin dake tsakaninmu.
"ALLAH ya sawwaƙe kazama ubana wallahi Yaya Abdul-Naseer kazame min masifa! nagaya maka bana son dik wani kusancina dakai domin kaima kasan xaren ba kalar yadin bane DA IZZA TA! billahi nafi ƙarfinka".
Murmushi yayi tare da ɗauko cingam daga aljihunsa ya ɓare ya saka tare da fara taunawa yana yi yana jefamin wani irin birkitaccen kallo.
"Inna IZZAR TAKE?"
Yafaɗa yana jan numfashi sannan ya cigaba.
"Nikam banga izza anan ba wawuya kawai wallahi koki koma kona saka takalmi nai ƙwallo dake!!"
Yakai maganar a fusace.
Ganin ransa ya ɓaci dik jijiyoyin kansa sun motsa yasa na kwashe da wata shegiyar dariya tare da cewa.
"Tabb lallai iska tana wahal damai kayan kara idan banda abinka ina ƊAN WAZIRI yake da IKO akan SHALELEN SARKI,wallahi ko a ƙafa aka ɗauran kai sena kwance kada kaga kai ɗan uwana ne wallahi bana kaunarka Abdul".
Nakai maganar cikin girman kai.
Kallo guda zakaiwa kyakykyawar farar fuskarsa kasan ran ƴan mazan ya ɓaci duba da yadda fuskarsa tai wani irin mugun ja! idanunsa yay wani irin kaɗawa sumar kansa har wani yamutsewa tai dan tsabar bacin rai.

Dasauri ya ɗago..........!



*Kamar yadda kuka sani wannan littafi mai suna DA IZZA TA! na kuɗine Normal grp posting sau 1 a rana 200, Vip grp post Sau Biyu a rana 500, Masu son adinga basu ta p.c base sun shiga grp ba posting sau biyu a rana 600, gamai buƙata ze turo da kuɗinsa tanan 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinka ta nan 08142105218, pls ƴan vip da ƴan s.p bana son kati zakiyi transper through accnt idan baki da shi kije pos su ɗauki naira 100 na yafe, vip ki turo 400, sp,500 idan sun ɗauki kuɗinsu, idan kuma kinada account shikenan, sena jiku masoya, da kijira a saya a baki gwara kin biya kuɗinki domin kada ayi babu ke! ƴan nijar masoya kuma zaku iya min magana ta number ta dake sama, sena gaya muku yadda zaku biya naku, sena jiku masoyana ƙashin bayan nasarata abin alfaharina*


*ZUWA GA MASOYA*

*Gamasu buƙatar comple littattafaina dana gama, ƊAN MAJALISA, KOBA SO, H A S KE, Zaki turo naira 700 ta wannan accnt ɗin 0078174806, Shedar biya 08142105218, Sena jiku masoyana*✍�?
6/30/21, 11:02 PM - Buhainat: 🌹 *DA IZZA TA !*  🌹
           ( Painful  Love  )  

                    


*Mallakar*      
   AUTAR MANYA🌹  


*SADAUKARWA GA*
   Khausar Salis Usman



*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*

                         🅿�? *2*

Dasauri ya ɗago tare da zuba min manyan lumsassun idanunsa waɗan da tsantsar ɓacin ran daya riske shi  a yanzu yasa suka juye suka koma launin jajur wanda har wani ruwa-ruwa ne ke kwanciya acikinsu dan tsabar jan dasukai, farar fatar fuskarsa kuwa tai wani irin ja! itama haka zalika sumar kansa wadda take baƙa siɗik irin ta fulanin usul tai wani irin curewa a wuri guda, kallo ɗaya zakai masa kokai waye ka kauda kanka domin yadda zaka hango tsabar rashin mutunci acikin ƙwayar idanun tasa, ga jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu har wani harbawa suke dan tsabar ɓacin rai.

Hannunsa ɗaya ya ɗora a saman kansa wanda ya cika da gargasa har wajan ya tsunsa waɗanda guda biyu suke ɗauke da zobunan arzurfa, jan cikakkiyar sumar dake kwance a saman kan nasa yayi tare da hargitsa ta baki ɗaya.

Taku ɗaya yayi abinka da ɗan ball ansha training ya kaiwa tsintsiyar hannuna damƙa da ƙarfin tsiya wadda ta saka su hapcy rugawa da gudu batare, dasun shirya ba.

Nima a wannan karon duk tsabar taurin kaina da rashin kunyata wani mugun ɗaurewa marata tayi acikin raina nake ayyana,hoho yaya Abdul-Naseer bai da kyau shiyasa kowa yake shakkarsa amman ban dani Asma'u.

Jin riƙon tsaurin daya ma hannuna har wani amsawa yake shiya bani damar ɓare ɗan ƙaramin bakin tsiwata zan saka ihu! ɗayan hannun nasa wanda ya ɗora akansa ya ɗago tare da ɗane min bakin nawa.

"Asmi"
Yakira sunan daya ke gayamin bai jira cewa taba ya ɗora da cewa.
"Miyasa kike son bani ciwon kai, ke wai ALLAH bai dasa miki kunya ba".

Yakai maganar cikin alamun gajiyawa.
Nikuwa tura bakina nayi gaba har da cinnawa ina bukatar ya sakarmin hannuna kawai na wuce tare da zabga masa ALLAH ya isa abina.
"Nidai Ya Abdul kaiwa ALLAH ka sakemin hannuna wannan takurar taka tai yawa nagaya maka zaren ba kalar yadin bane wallahi ko maza sun ƙare bazan aure kaba DA IZZA TA! wallahi nafi karfinka".

Dariyar kina hauka ya jefa mata yana mamakin wannan girman kai na Asma'u yarinya karama amman ta dauki girman kai da izza da wulakanci tamkar ba daga tsatso guda suka fitoba.
Shikam komai zatai baya jin ze iya rabuwa da ita sabida wasu dalilai nasa yagama sakin ransa akanta yana hango abubuwa da dama game da itan.
Jan hannuna nake tare da gaya mashi dukkan maganar datazo bakina
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DA IZZATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album