Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


*DA IZZA TA !*
( Painful Love )





*Mallakar*
AUTAR MANYA🌹



*SADAUKARWA GA*
Khausar Salis Usman




*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*


🅿�? *1*


Cikin shigar doguwar riga mai roba-roba na fito wadda tai matuƙar kamamin ƙirar jikina wadda narasa wace irin ƙirace dani wadda dik wasu kaya dazan saka bazata taɓa ɓuyaba,farar alkyabba tass na ɗora bisa kan wannan doguwar riga, tare da hularta, cikin sauri nake takowa daga sashen fulani umma abokiyar zaman ummina, inayi ina amsa wayar dake maƙale a kunnena kuyanguna suna gefena suna tattaremin alkyabbar tawa wadda take sharar ƙasa, ina kammala wayar na juyo tare da maka masu wani wawan kallo wanda yasa babu shiri suka jada baya, da kaina na ƙarasa bakin kofar sashen ummi wadda yawan bayin dake wajan yafi na kowace ƙofa sabida kula da lafiyar ummi, wani wawan kallo na maka masu wanda yasa babu shiri suka baje daga wajan suka koma gefe guda.
Cike DA IZZA TA! wadda tabi jikina da dukkan wani motsina naja kofar tare da zira haɗaɗɗan takalmin dake ƙafata na taka har cikin babban falon ummi.
Ganin babu kowa se kuyangunta yasa na juya sabida yadda su hapcy ƙawayena ke jirana zamu fita dasu, kuma nasan tabbas! idan na shiga ummi zata zaunar danine tamin nasihar tata data saba.
Cikin yauƙi da gwalli nake takun nawa kuma duk taku guda se jikina ya kaɗa tamkar da gayya domin na lura hatta hadiman dake wannan sashe hankalinsu yana kaina.
"Takawarki lafiya jinin sarauta ƴar sarauta ɗiyar sarki jikar sarki mai takalmin zinare hajiya asma'u ikon ALLAH mata agidan manyan mutane ba ƙananu ba duk wanda rabbi yasa ya sameki ya dace da MACE MAI IZZA DA MULKI gadon gidanku ba haye ba".
Cewar wani bafade kenan wanda tun isowata harabar gidan namu naga yana bina abaya, nasan ba komai yake bukata ba face kuɗi, cikin izzata na bude ƴar jakar dake hannuna na zaro kudin da bansan adadinsu ba na watsa masa, inaji yana cigaba da kirarinsa nidai haka na wuce kaina cike da girma.
Ta ƙofar baya na zaga sabida anan nacewa su hapcy su jirani domin nasan idan har na fita ta kofar wajan fada se ansami wani munafikin daze kaiwa mai martaba gulmata.
Cikin isa da izza nake taka ƙafafuna har sanda na isa gaban kofar wajan da ake adana motoci na nufa tare da isa gaban farar motar dasu hapcy suka shigo mana da ita.
"Se Meemah".
Shewar su hapcy kenan ƙawayena na amana waɗanda suka biyomin fita domin mu zaga gari muga mai gari ke ciki.
Ƙyafe bakina nai tare da kallonsu a ɗage inajin kaina a sama tare da matsawa gaban motar.
Ina saka hannuna zan bude marufin motar naji andafe da ƙarfi, wani irin zare idanu nai waɗanda suka fito sukayo waje.
Mayar da ajiyar zuciya nayi tare da tamke fuskata tamau.
Tsaye yake agabana da kayan gadon nasa wato farar rigar J.C ta ƴan ƙwallo se baƙin wando dogo, yawani harde hannunsa akan kirjinsa ɗayan kuma ya dafe marufin motar dazan shiga, cak su hapcy sukai tare da sakin baki dik jikinsu ya ɗau rawa.
"Dalla malam kasa karmin marufi kazo zaka ɓatamin lokaci" nafada cikin tsiwa.
Tsareni yayi da masifaffun kaifafan idanunsa masu kama dana mai jin barci batare daya tankani ba.
Wannan hali nasa yana mugun ɓatamin rai..
Tura bakina nai gaba tare da juya masa baya.
"Hajiya bafa zaki fita ba wallahil azim babu inda zaki".
Naji sautin muryarsa acikin dodon kunnena.
"Sannu ubana"
"Nafi ubanki mah".
Yabani amsa kai tsaye yana fesamin numfashinsa sabida kusancin dake tsakaninmu.
"ALLAH ya sawwaƙe kazama ubana wallahi Yaya Abdul-Naseer kazame min masifa! nagaya maka bana son dik wani kusancina dakai domin kaima kasan xaren ba kalar yadin bane DA IZZA TA! billahi nafi ƙarfinka".
Murmushi yayi tare da ɗauko cingam daga aljihunsa ya ɓare ya saka tare da fara taunawa yana yi yana jefamin wani irin birkitaccen kallo.
"Inna IZZAR TAKE?"
Yafaɗa yana jan numfashi sannan ya cigaba.
"Nikam banga izza anan ba wawuya kawai wallahi koki koma kona saka takalmi nai ƙwallo dake!!"
Yakai maganar a fusace.
Ganin ransa ya ɓaci dik jijiyoyin kansa sun motsa yasa na kwashe da wata shegiyar dariya tare da cewa.
"Tabb lallai iska tana wahal damai kayan kara idan banda abinka ina ƊAN WAZIRI yake da IKO akan SHALELEN SARKI,wallahi ko a ƙafa aka ɗauran kai sena kwance kada kaga kai ɗan uwana ne wallahi bana kaunarka Abdul".
Nakai maganar cikin girman kai.
Kallo guda zakaiwa kyakykyawar farar fuskarsa kasan ran ƴan mazan ya ɓaci duba da yadda fuskarsa tai wani irin mugun ja! idanunsa yay wani irin kaɗawa sumar kansa har wani yamutsewa tai dan tsabar bacin rai.

Dasauri ya ɗago..........!



*Kamar yadda kuka sani wannan littafi mai suna DA IZZA TA! na kuɗine Normal grp posting sau 1 a rana 200, Vip grp post Sau Biyu a rana 500, Masu son adinga basu ta p.c base sun shiga grp ba posting sau biyu a rana 600, gamai buƙata ze turo da kuɗinsa tanan 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinka ta nan 08142105218, pls ƴan vip da ƴan s.p bana son kati zakiyi transper through accnt idan baki da shi kije pos su ɗauki naira 100 na yafe, vip ki turo 400, sp,500 idan sun ɗauki kuɗinsu, idan kuma kinada account shikenan, sena jiku masoya, da kijira a saya a baki gwara kin biya kuɗinki domin kada ayi babu ke! ƴan nijar masoya kuma zaku iya min magana ta number ta dake sama, sena gaya muku yadda zaku biya naku, sena jiku masoyana ƙashin bayan nasarata abin alfaharina*


*ZUWA GA MASOYA*

*Gamasu buƙatar comple littattafaina dana gama, ƊAN MAJALISA, KOBA SO, H A S KE, Zaki turo naira 700 ta wannan accnt ɗin 0078174806, Shedar biya 08142105218, Sena jiku masoyana*✍�?
6/30/21, 11:02 PM - Buhainat: 🌹 *DA IZZA TA !*  🌹
           ( Painful  Love  )  

                    


*Mallakar*      
   AUTAR MANYA🌹  


*SADAUKARWA GA*
   Khausar Salis Usman



*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*

                         🅿�? *2*

Dasauri ya ɗago tare da zuba min manyan lumsassun idanunsa waɗan da tsantsar ɓacin ran daya riske shi  a yanzu yasa suka juye suka koma launin jajur wanda har wani ruwa-ruwa ne ke kwanciya acikinsu dan tsabar jan dasukai, farar fatar fuskarsa kuwa tai wani irin ja! itama haka zalika sumar kansa wadda take baƙa siɗik irin ta fulanin usul tai wani irin curewa a wuri guda, kallo ɗaya zakai masa kokai waye ka kauda kanka domin yadda zaka hango tsabar rashin mutunci acikin ƙwayar idanun tasa, ga jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu har wani harbawa suke dan tsabar ɓacin rai.

Hannunsa ɗaya ya ɗora a saman kansa wanda ya cika da gargasa har wajan ya tsunsa waɗanda guda biyu suke ɗauke da zobunan arzurfa, jan cikakkiyar sumar dake kwance a saman kan nasa yayi tare da hargitsa ta baki ɗaya.

Taku ɗaya yayi abinka da ɗan ball ansha training ya kaiwa tsintsiyar hannuna damƙa da ƙarfin tsiya wadda ta saka su hapcy rugawa da gudu batare, dasun shirya ba.

Nima a wannan karon duk tsabar taurin kaina da rashin kunyata wani mugun ɗaurewa marata tayi acikin raina nake ayyana,hoho yaya Abdul-Naseer bai da kyau shiyasa kowa yake shakkarsa amman ban dani Asma'u.

Jin riƙon tsaurin daya ma hannuna har wani amsawa yake shiya bani damar ɓare ɗan ƙaramin bakin tsiwata zan saka ihu! ɗayan hannun nasa wanda ya ɗora akansa ya ɗago tare da ɗane min bakin nawa.

"Asmi"
Yakira sunan daya ke gayamin bai jira cewa taba ya ɗora da cewa.
"Miyasa kike son bani ciwon kai, ke wai ALLAH bai dasa miki kunya ba".

Yakai maganar cikin alamun gajiyawa.
Nikuwa tura bakina nayi gaba har da cinnawa ina bukatar ya sakarmin hannuna kawai na wuce tare da zabga masa ALLAH ya isa abina.
"Nidai Ya Abdul kaiwa ALLAH ka sakemin hannuna wannan takurar taka tai yawa nagaya maka zaren ba kalar yadin bane wallahi ko maza sun ƙare bazan aure kaba DA IZZA TA! wallahi nafi karfinka".

Dariyar kina hauka ya jefa mata yana mamakin wannan girman kai na Asma'u yarinya karama amman ta dauki girman kai da izza da wulakanci tamkar ba daga tsatso guda suka fitoba.
Shikam komai zatai baya jin ze iya rabuwa da ita sabida wasu dalilai nasa yagama sakin ransa akanta yana hango abubuwa da dama game da itan.
Jan hannuna nake tare da gaya mashi dukkan maganar datazo bakina daga karshe na ƙarasa da "wallahi sena kaika ƙara wajan baba waziri ( mahaifinsa kenan) tunda naga hajja fulani bata ƙaunar laifinka kai ɗan gaban goshinta ne".
Munafukin gemun daya tara yaɗan ja yana fesar da zazzafan numfashi tare damin kallon daya saba wanda mutane kecewa kallon wulaƙancine, batare daya ce min komai ba ya sakarmin hannuna.
"Ki wuce kije part ɗin ummi ki taimakawa Rahina wallahi na ganki acan part ɗin sena balla miki hannu ɗaya".
Ya faɗi maganar cikin bada umarni.
Wawan kallo na zuba masa tare dajan tsaki! nan da nan idanuna suka kawo ƙwalla ni wallahi Abdul-Naseer ya uzzuramin wannan wani irin masifane.
Fuww! naja alkyabbata tare da nufar komawa ciki, nabarshi a tsaye wanda ina ganin fita shima zeyi.
Amai makon na koma part ummi senai part ɗinmu wato part ɗin fulani umma abokiyar zaman ummina wanda anan nike da zama baki ɗaya tundaga yaye.
Cikin takun izzata na isa cikin babban falon fulani umma ina faman turo bakina gaba, ilahirin bayin dake cikin falon suna gyare-gyare duk sukai baya sanin halina, na wuce falon farko na shiga na biyu, adda zainabu da adda sakina duk sunazaune ana matsa musu ƙafa, ban dubesu ba nai ciki ina faman kiran "Umma kina ina! hakimce fulani umma take akan wani lallausan carpet gefenta manyan pillow's ne se kuyangun dake gabanta ɗaya tana bata apple gudar kuma tana matsa mata ƙafafunta.
Da hannu tai masu alamun su bamu waje sannan ta saka hannunta ta rungumoni.
"Ɗiyata yaya akai Hala wancan tsinan nan yaron ne ya hana ki fitar?' takai maganar tana bawa abin mahimmanci.
Share hawayena nayi tare da ɗaga kaina sama alamun "eh!.
Wani irin ƙwafa tayi tare da zaunar dani a gefenta sannan taci kunu tana kallona.
"Asma'u kina jina?"
Gyaɗa kaina nai alamun "Eh!.
"Daga yanzu kada ki kuma bin hanyar dazaki ga ABDUL! sabida bana son mai martaba yaji zancen yana sonki sabida kinsan iyayenku da son zumunci tabbas idan maganar taje fada wallahi se anyi auren nan"...............





*Kamar yadda kuka sani wannan littafi mai suna DA IZZA TA! na kuɗine Normal grp posting sau 1 a rana 200, Vip grp post Sau Biyu a rana 500, Masu son adinga basu ta p.c base sun shiga grp ba posting sau biyu a rana 600, gamai buƙata ze turo da kuɗinsa tanan 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinka ta nan 08142105218, pls ƴan vip da ƴan s.p bana son kati zakiyi transper through accnt idan baki da shi kije pos su ɗauki naira 100 na yafe, vip ki turo 400, sp,500 idan sun ɗauki kuɗinsu, idan kuma kinada account shikenan, sena jiku masoya, da kijira a saya a baki gwara kin biya kuɗinki domin kada ayi babu ke! ƴan nijar masoya kuma zaku iya min magana ta number ta dake sama, sena gaya muku yadda zaku biya naku, sena jiku masoyana ƙashin bayan nasarata abin alfaharina*


*ZUWA GA MASOYA*

*Gamasu buƙatar comple littattafaina dana gama, ƊAN MAJALISA, KOBA SO, H A S KE, Zaki turo naira 700 ta wannan accnt ɗin 0078174806, Shedar biya 08142105218, Sena jiku masoyana*✍�?
6/30/21, 11:02 PM - Buhainat: 🌹 *DA IZZA TA !* 🌹
( Painful Love )





*Mallakar*
AUTAR MANYA🌹



*SADAUKARWA GA*
Khausar Salis Usman




*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*


🅿�? *3*


Wara manyan idanuna nayi ina kallon fulani umma dasu cike da gamsuwa da abin da take gayamin domin nasan a tsakaninmu babu wata cutarwa.
Cigaba tayi da maganar tata kamar haka...............
"Koda wasa bana ƙaunar na ganki da yaron nan wallahi har zuciyata domin nasan ba domin ALLAH yake sonki ba tabbas! akwai wata a ƙasa, kuma wannan maganar ba kowane ze kinsa masa itaba face Hajja fulani sabida naga kamar tama fi sonsu akanku kuda kuke jikokinta".
Numfashi ta kuma ja sannan ta cigaba da maganarta.....
"Ke idan banda abinki nawa ma kike dudu yanzu kika shiga shekaru 20 baki ganin su, sakina duk gasu nan a zaune duk babu mai zuwa wajansu seke za,a ɗagawa hankali to wallahi ba dani ba sam wannan tsinan nan haɗin baze yuwuba kuma ki kula da jakadiya kada ki yarda koda wasa taga giftawar sa akusa dake domin ina hango makirci a idanunta, nikuma zan saka amintacciyar baiwata ta jiyo mana dukkan abinda, ke faruwa a sashen fulani hajja dama sashen su wazirin baki ɗaya".
Takai maganar tana shafo kaina cike daso da kaunata.
Murmushi na sauke tare da kallonta ina jin muguwar ƙaunar matar wallahi fulani umma tafi sona akan ummina, wannan matar bamma san dami zan saka mata ba sedai nai mata fatan alkairi domin yadda takemin ko amira sa,ata ƴar autar ta wallahi bata mata hakan, kodan taga yadda mahaifinmu ke mugun sona ne oho?
Nakarasa maganar araina tare da kallonta.
"Umma ki kwantar da hankalinki wallahi tun kafin ma ki nuna min izzata tafin karfin Abdul! wallahi nima baimin ba umma".
Nakai maganar ina dariya.
Itama dariyar ta saki cike dajin daɗi marar kwatance tacemin.
"To daman ma'una aike ba kalar kananun mutane bace wannan kalar fatar taki mai tsadace karkiga duk ƴan uwanki farare ke baƙa keme tsadace, kalleki da kyau matar manyan mutane ba matar ɗan wazirin uban taba, wanda fafur tundaga jami'a yaƙi cigaba yaƙi aiki ya tsaya buga ƙwallo a tsakanin unguwanni nera biyar wannan idan ba wazirine ko waccan tsohuwar data dauki son duniya ta ɗora masa ba, indai basu suka basa ba seya wuni bai ganta ba, amman se uban fafa da yauki da kallon raini da uban haɗe rai kullum kamar wani dodo".
Takai maganar cikin tsana, wadda nikaina ina mamakin yadda umma bata kaunar duk dangin mahaifinmu musamman ƴan ɗakinsu baba waziri.
Miƙewa nayi tsaye ina karkaɗe rigata tare da kallonta.
"Umma share wannan banzar maganar wallahi nifa baya gabana duk abinda kika dorani akansa haka za,ai".
Nakai maganar ina miƙa, tare da fita ina jin umma tana faman sakamin albarka.
Wucewa nayi daga wajanta nafita zuwa sashen ummi sabida nayi mantuwa ɗazu ashe fa, Baba ( mahaifinmu mai martaba) ya bayar da saƙo ta ajiyemin na kuɗin danace yabani wanda ya bawa jakadiya takaiwa ummi, kuma ɗazun danaje harna fito ban tuna ba kodan ban haɗu da itan bane ba.
Tun daga farkon sashen fulani umma har xuwa sashen ummi bayine shaƙe suna zubamin uban fadanci tare da kirari, kasancewa ta ƴar lelen mai martaba kuma ƴar gaban goshinsa shine yasa kowa yake jidani yake riritani idan kacire hajja fulani wadda wancan ɗan rainin wayon yaje ya tsare komai nata.
Cikin isa da izzata na shiga babban falon ummi wanda yake cike da bayi kusan su nawa suna faman aiki da gyare gyaren kayan itatuwa.
Zubewa sukai suna kwasar gaisuwa agurina nikuma ban kulasu ba na wuce abina.
Saratu na duba babbar amintacciyar baiwar ummina wadda take tsaye a bakin falon tana gyara kwanon inibin dake hannunta.
Cikin sauri tai kasa tana gaisar dani.
"Barka da rana Gimbiya asma'u meemah".
Tafaɗa cikin ladabi da biyayya.
Duk da ta girman amman hakan bai sa ta tashi daga durkushen nataba harseda na tasheta sannan na wuce cikin babban falon ummina na biyu wanda babu wani daya isa ya shiga cikinsa idan bamu ba.
Rahina ƙanwata na tarar zaune, akan one seater tana tsefewa huda ƴar autar ummi kanta, batare dana wani tsaya wajansu ba nai ciki abinda duk da ina jinta tana faman cemin.
"Adda meemah barka da rana". amman haka nai banza da ita na wuce abina.
"Ummi! Ummi!! wai ummi kina ina ne nafaɗi maganar ina turo bakina gaba irin a shagwaɓan nan.
Abin da nagani a saman sopar bedroom ɗin ummina shine ya ɗagamin hankalina............!!



*Kamar yadda kuka sani wannan littafi mai suna DA IZZA TA! na kuɗine Normal grp posting sau 1 a rana 200, Vip grp post Sau Biyu a rana 500, Masu son adinga basu ta p.c base sun shiga grp ba posting sau biyu a rana 600, gamai buƙata ze turo da kuɗinsa tanan 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinka ta nan 08142105218, pls ƴan vip da ƴan s.p bana son kati zakiyi transper through accnt idan baki da shi kije pos su ɗauki naira 100 na yafe, vip ki turo 400, sp,500 idan sun ɗauki kuɗinsu, idan kuma kinada account shikenan, sena jiku masoya, da kijira a saya a baki gwara kin biya kuɗinki domin kada ayi babu ke! ƴan nijar masoya kuma zaku iya min magana ta number ta dake sama, sena gaya muku yadda zaku biya naku, sena jiku masoyana ƙashin bayan nasarata abin alfaharina*


*ZUWA GA MASOYA*

*Gamasu buƙatar comple littattafaina dana gama, ƊAN MAJALISA, KOBA SO, H A S KE, Zaki turo naira 700 ta wannan accnt ɗin 0078174806, Shedar biya 08142105218, Sena jiku masoyana*✍�?
6/30/21, 11:02 PM - Buhainat: 🌹 *DA IZZA TA !*  🌹
           ( Painful  Love  )  

                    

*Mallakar*      
   AUTAR MANYA🌹  

*SADAUKARWA GA*
   Khausar Salis Usman


*Dasunan ALLAH Mai Rahama Maijin Ƙai*

                         🅿�? *4*



Hangoshi nayi kwance akan sopar ɗakin ummi, yayi irin kwanciyar nan ta rigingine, fuskarsa tana kallon ƙasa, a wannan karon ba j.c bane ajikinsa dakakkiyar shaddar geznar ce yar gasken, mai kalar sky blue babu hula akansa se tulin kwantacciyar sumar kansa wadda ta sami waje ta lafe.
Araina na ayyana shin bai fitan ba kenan amman ɗazu da muka haɗu senaga kamar fita zeyi, komai ya hanasa fitar oho! sanin babu mai bani amsa yasaka naja jikina ahankali zanbar ɗakin.
Sabida banji ɗuriyar ummi ba ko tana turakar mai martaba ne oho?.
Harna kai bakin kofa zanja handle naji gyaran muryarshi! kafin kuma naji ya furta.
"Asmi! Zonan".
Sarai najishi amman ban juyaba sema tsakin! danaja a fili tare da nufar kofar kaina tsaye.
Nidai banji takun saba sejina nai akan cinyar mutum a zaune, ƙoƙarin miƙewa nake amman yaƙi bani damar hakan, sema ƙara gyaramin zamana dayayi akan cinyar tasa, nikuwa duk ƙamshin mayen turarensa ya isheni gawani haushi daya bani.
Turo masa mitsitsin bakina nayi gaba tare da furta.
"Nidai dan ALLAH ka rabu dani yanzu wannan dacewa ne?".
Nakai maganar cike dajin haushinsa.
Yatsan shi guda ya saka tare da ɗale bakina kaɗan sannan ya furta.
"Miye aciki dan mace tahau cinyar mijinta" yafada yana jan numfashi tare da kai yatsansa guda gefen lip's ɗina yana zagaye dashi.
Doke hannunsa nayi tare da furta.
"ALLAH yay min tsari wallahi Yaya Abdul! ni nafi karfinka kuma billahi bazan aureka ba, idan ma kwaɗayin arzikin mu kake ka daina".
Nakai maganar kaina tsaye domin haka umma tagayamin tun kwanakin baya kan cewa shidin kwaɗayin dukiyar masarautar yake shine dalilin dayasa ya nacemin.
Jim yayi kafin yasaki wani killer smile wanda har dimple point ɗinshi seda suka lotsa kaɗan, kana ya dubeni dakyau.
"Asmi Ninafi karfin in soki domin wani dukiya, hasalima ni sarautar bata gabana".
Yakai maganar cikin nuna alamun rashin jin daɗinsa ƙarara.
"Kaji dashi dai ni dallah sakarmin kafaɗa na wuce".
"Bazan saki ba kina da karfi ki ƙwace mana"..
Yakai yana ɗagamin girarsa kaɗan.
Ɗago fusakata yayi tare da ƙuramin manyan idanunsa yana bina dasu kamar wani maye.
"Ina sonki Asmita! wallahi ni kaina bansan adadin son danake miki ba ko ummi sedai ta nunan haihuwarki amman a sokam wallahi bazata nuna minba".Yanumfasa kaɗan sannan ya cigaba.
"Kidaure ki sauke wannan IZZAR da GIRMAN KAI! muso junanmu wallahi namiki alƙwarin bazaki dana sani ba ina sonki ASMITA".
Yakai maganar ƙwalla tana taruwa acikin idanunsa yana kuma lumshe su kamar yanajin bacci.
Awannan karon ne,na kare masa kallo tass.
Babu laifi ya Abdul-Naseer namiji ne iya namiji tsayayye ingarma mai jida ƙarfi da lafiya a mintuna guda ze iya tafiya da zuciyar duk wata ɗiya mace kasancewar sa dogon bafulatani fari tass mai cikar sura da zatin kyau uwa uba addini tare da biyayyar mahaifa yana da mugun ƙoƙari ga tsayawa akan ra'ayinsa wanda hajja fulani ke cewa yana da taurin kai tare da miskilanci domin idan ya kafe akan abu babu wanda ya isa yace no.
Sosai yake da cikar kamala tare da haiba, ataƙaice dai xan iya cewa wallahi ya abdul mugun mai kyaune na abuga ajarida, wanda yake tashe acikin wannan gari namu kasancewar sa ƙwararren ɗan buga ƙwallon ƙafa duk da dai a iya garin namu kaɗai yay suna, amman haka kurum xakaga ƴammata suna ɗora hotonsa akan suna sonshi.
Dogone sosai mai cikar surar jiki farine shi tass kalar mahaifiyarsa yana da idanuwa manya masu lumshewa kamar na mai jin barci bakinsa baƙi-baƙine kaɗan, yana da ɗan gemu na samarin yanxu, mayen taunar cimgam ne sannan kuma bai fiye buɗe idanunsa tar

Please Login or Register in order to submit comment