Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman lafiya...............Nai alƙawarin Abdul baka da mata se sakina ƴata ko banza za,a kirata ƴar sarki kuma matar sarki mai jiran gado"! tai wannan furucin tare da saka dariya.
Nikuwa cikin sanyin jikin jin kalamanta na ɗazu nai ɗakina agurguje na ɗauki wayata da system ɗina nabar part ɗin gudun matsala........Koda na koma part ɗinmu ma,ana part ɗin ummina tuni na tarar har bayin sun jeren kayana tass, zama nai bakin gado ina gyara saitin takalmana ina kuma nanata maganar umma araina lallai zan bada mamaki acikin gidanmu.
Ban tashiba seda aka kira azahar asannan ummi tasan da zuwana bakaramin mamaki taiba amman dana mata bayanin cewar baba yace na dawo seta saki ranta..........tare muka haɗa lunch, saboda daman ummi bata yarda bayi su mata girki, sannan mukai wanka, ni ina fashin sallah dan haka na zauna naci na koshi na barwa ALLAH lamurana bani da wani damuwa komai ALLAH yay shine dai-dai,mun jima da rahina muna hirar ƴan uwantaka abinda bamu taba ba, sannan na koma ɗakina zan duba wani assingment da aka bamu, araina ina lallai ɗan uwa akwai daɗi a part ɗin umma kuwa da bani da abokin hira se waya......haka zalika koda aka kira sallar la,asar ummi ta shigo ɗakina lokacin na gama assingment ɗina ina zaune ina yankar ƙunbata, ta ƙafa da kanta ta haɗamin ruwa mai ɗumi tace nai wanka na ɗauro alwala, hakan ce ta faru bayan na fito tace nai azkar na fito kicin zamu fara haɗa dinner,atare mukai aikin farar shinkafa mai miyar ganda da alaiyahu nida ummi rahina kuma ta haɗa mana lemu, sukam daman bayin sashin suna nasu girkin daban, jina nai sakat, kamar zanyi ihu dan murna sedai haryau akwai damursa acikin raina ina dai gwada dauriyane sabida maƙiya naga za,a nemi shiga tsakaninmu.
Bayan sallar magariba muka zauna afalo muna kallon wani sereis film, afra tai baccinta daman se sadik da rahina da ummi wadda take lazumi

Tun kafin ya shigo naji gabana yana faduwa kafin nai yunkurin komai naji sallamarsa, daga cikin falo tare da muryar bayin dake can babban falon suna gaisar dashi, lumshe idona nai ina warasu akansa sanye yake cikin gezner ƴar gasken dark green, se hula daya saka wadda tai marching da kayan jikinsa, babu abinda yake se daukar kamshi tare da annuri kana kallonsa kaga zero tension, da gudu sadiq ya nufesa tare da ɗanesa "Oyoyo yayanmu barka da zuwa" cewar sadik ina kallon sanda yake Raɗama sadik magana a kunnensa da gudu naga sadik yaje wajan ummi yana gaya mata sannan yay ɗaki, rahina ce ta gaisar dashi tare da mikewa tai cikin ɗakin ummi cikin jarumta nima nace masa"Barka da dare" fuskata babu alamun damuwa ko takaici, yana neman wajan zama akan ɗaya daga cikin one seater dake falon ya ɗago ya kalleta sanye take cikin doguwar rigar atamafa ja se jan hijabi data saka kallo ɗaya yay mata yasan tana fashin sallah, ɗan kanne ido guda yay tare da furzar da iskar cikin baki kana ya dubeta"Barka dai Anty asma'u"! maganar ta shigarmin dukkan ilahirin jikina cak nai da raina ina kallonsa tabbas! akwai aiki agabana ganin ummi bata kallon wajanmu yasa nai murmushi nima amman bance masa komiba.

Numfashina ne ya kusan daukewa lokacin danaga Rahina ta fito sanye cikin dark green less se jan mayafi data yafo akanta"Ummi zamu wuce" sannan ta dubeni "Adda meema zamu je gidan yakumbo nefa kozaki?" Yakumbo na nanata araina ƙanwar baba wazirice ma,ana ƙanwar mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya ita kebin baba waziri ita tana nan cikin tarauni tana aure mezasu je suyi acan? ganin babu mai bani amsata yasa nai gumm tare da ƙaƙalo dauriya"A,a no rahina bazani ba amman but bara na baki saƙo ki bawa safiya sannan kuma kice mata ranar asabar ne karfe 5:00pm na fada tare da mikewa, nai ɗaki domin na daukowa rahina card ɗin bikin wata course mate ɗinmu, wadda ta kasance ƙawar safiyace itama ta sec to shine ta bani na bawa safiyan ɗiyar yakumbo ta uku kenan sa,ata, banfi minti biyu ba na zakulosa na baiwa rahina tare da ce masu sesun dawo, duk yadda kaso ganin bacin raina ya buya, mayar da wayarsa yay aljihu gami da kallon ummi cikin ƙasan maƙoshi yace"Semun dawo ummi" batare daya kalli inda nakeba sema wani hade ransa danaga yayi tamau tamkar bai tabayin dariya ba"ALLAH ya tsare" Ummi ta fada tare da tashi tabar wajan nima ɗakina nai ina jin raina babu dadi......alwala nai tare da kwanciya sabida gobe inada morning lecture, washe gari ban tsaya break ba nabar gida amman seda ummi tai ta faɗa ko a school su hapcy sun kasa gane kaina haka na wuni sukuku har wajan...la,asar sannan naiwa su hapcy drop nina wuto gida.........Ahanya wata ƙawata da mukai primary mai suna nasma wadda ada bani da ƙawa sama da ita, amman tashin da sukai daga kano suka koma katsina yasa muka rabu kwatsam kum yanxu taimin waya wai sun dawo nan garin sati mai xuwa ma za,ai bikinta, naji dadin sake jin nasma, dan haka babu bata lokaci na bata lokacin da zatazo gida ta saman sabida muyi shirin abinda zamuyi sabida nasmat kawatace tun ta kuruciyar primary school ana gaf da magariba na dawo gida, wanka nai tare da shiryawa cikin kayan shan isa nai dakin ummina, anan naji labarin wai yau ya wuce gombe da safe sannan kuma gobe za,a kawo lefen Rahina wanda baba Chiroma ne duk ya dauki nauyin yi masu lefen bikin yakama nan da two weeks masu zuwa kenan acewar ummi! lokacin datake gayamin har wani jirine yake kwasata wato dai da gaske ya Abdul ba mijina bane ba lallai haka ikon ALLAH yake amman nima ina da laifi domin naa watsi da damar da ALLAH ya bani a tun farko, yaya zanyi dole na ɗauki hakuri ALLAH nima ya bani nawa nagari amin, Ummi ta ɗora min da nasiha sannan ta nunan jajurcewa wajan yarda da ƙaddara tabbas akan abinda kafiso ma ALLAH yafi jarrabaka, sosai na gamsu da hakan amman dana koma ɗaki seda nai kuka! mai cin rai wanda bacci ya kwasheni ahakan.....


TSOKACI!

_Imanin mumuni baya cika seya yarda da ƙaddara mai kyau da marar kyau! Rayuwar bawa bata tafiya seda jarabta dan ALLAH kada ku ƙosa kubi labarin nan aduk yadda yazo maku alƙalamina ke rubuta shi, insha ALLAH bazan baku kunya ba! labarin yana da abubuwan bam mamaki, dan ALLAH bana son complain na auren Rahinatu d A,A kuyi hakuri komai girman gona akwai kunyar ƙarshe haka zalika rayuwa tana xuwar wa bawa kashi da kashi duk kudinka duk mulkin ka duk sarautarka baka isa ka tsallake ƙaddarar ALLAH akan kaba yana jarabtarka kashi da kashi fatana kuyi koyi kuma kuyi darasin ayyukan alkairin dake cikin wannan book kuma na sharrin ciki ku watsar labarin yanzun muka shigesa ada can shinfida muke, MUJE ZUWA READERS, karku manta sakani acikin addu,arku ALLAH ya biyamin bukatuna na alkairi kuma ya biya muku naku tare da dukkan musulmi baki ɗaya Amin_





*DA IZZATA*
6/30/21, 11:17 PM - Buhainat: DZ


33 - 34


Baccine marar daɗi ya kwasheni wanda ban farkaba se wajan sallar isha'i zama nai jugum akan gado tare da saka tafukan hannuna na rafka tagumi na dauki mintuna kusan goma a haka kafin na mike tare da nufar cikin bathroom tarar ruwa nayi mai sauƙin zafi na samu na watsa ajikina na fito daure da tawul, na sauya pad tare da kintsa jikina cikin doguwar rigar yadi marar nauyi, ban saka hijabi ba haka na fice zuwa falo, zama nayi akan ɗaya daga cikin seater's ɗin falon tare da zabga tagumi na jima a zaune kafin naji shigowar rahina wadda muka rabu tun jiya dazasu tafi gidan yakumbo, "Adda meema sannu da hutawa" naji saukar muryar rahina acikin dodon kunnena, murmushi nayi mata tare da kamo hannunta ta zauna agefena"Rahinar ummi amarya" nafada tare da sakin murmushin yaƙe, saka hannunta tai tare da rufe fuskarta kana ta sada kanta a tsakanin cinyoyinta wai ita kunya"Ɗago mana muyi magana rahina ayke yanzu ba yarinya bace ba kinyi fa candy last year kinga kuwa baza,a ce maki yarinya ba, ko haka zakije kinawa yaya agidan nasa?" nafada ina dariya girgiza kanta tai alamun A,a sannan ta ɗago ta kalleni"adda meema nifa tsoron yaya Abdul - Naseer nake dan baya dariya ko jiya a hanya ya kusan buguna wai dan nace masa zan bawa adda safiya katin da kika bani, wai wallahi na bata seya zaneni" Jim nai ina nazarin maganar tata sannan nai murmushi "Karki damu sister babu wata matsala insha ALLAHU kinji kedai kidinga masa biyayya kuma nasan ma ay kina son abinki" nai maganar ina dariya itama dariyar tai tare da ɗaga kanta"ALLAH adda meema ina son yaya Naseer sabida yadda yake son ummin mu" dum dum! naji gabana ya faɗi amman sena basar tare da kallonta ina dariya kaɗan ahaka muka dauki lokaci muna hira har ummi taxo itama muka ɗora kafin kuma nai masu sallama na wuce ɗakina kayan barci na zira tare da dauko littafina ina naxari na dauki lokuta masu tsaho ina abu guda sannan na mike naje na kama ruwa na dauro alwala kana na kwanta bayan na shafe jikina da addu,a tare da kashe hasken ɗakin.



Ƙarfe huɗu da wani abu na yamma tai masa acikin garin na gombe mahaifar mameey mahaifiyarsa kenan, kansa tsaye anguwar da kakanninsa suke ya nufa wanda ya kasance wani ɗan ƙaramin ƙauye ne dake cikin jahar ta gombe, cikin murna familyn mameey suka karbesa abinka da fulanin kauye masu kara tuni suka cika masa gabansa da kayan abinci harma dana sha, bayan ya huta ya zaga danginsa ƴan uwan mameey kenan dayake gidan suma kamar family hause ne a ɗakin kakarsa ammi ya, yada zango yana hutawa ammi mahaifiyar mameey kenan tsohuwa mai ran ƙarfe, bai bar gidan kakan nin nasa ba se wajan magariba sannan ya wuce inda mameey take wanda ya kasance cikin gari ne nan ɗin ba kamar gidan kakannin nasaba sosai mameey ta tarbi ɗan nata ɗaya tilo agareta jitake tamkar zatai tsalle dan murna ya jima yana amsar gaisuwa daga wajan ƙannansa waɗanda suke uwa ɗaya kenan su biyar mata waɗanda mijin mameey ya rasu yabarta dasu shekar biyu data wuce, yanxun haka mameey business ɗinta take na kayayyakin mata kamarsu less atamfa material da sauransu kuma babu inda bata tura kayan nata, da wannan sana,ar tata take samun rufin asirin ALLAH, sedai kuma time to time Abdul yana mata aike ta account wanda hatta kudin karatun su husaina shike biya masu......Seda yaje yay sallah ya shiga cikin ɗakinsa wanda ta ware masa idan ya shigo gomben, zama yayi acikin ɗakin tare da fito da wayarsa yana neman ummi, tajima tana ringing sannan ummi ta ɗaga, lokacin tana ɗakinta tana sabgar gabanta shaida mata yay ya sauka lafiya sannan ya tsinke wayar, Cikin ɗakin mami ta shigo, hannunta rike da kofi wanda ta cikosa da kunun ayar data masa mika masa tai tare da zama agefe"Yanzu kai yaushe xaka koma kano ɗin?" shafa kansa yay "Mameey gobe mana aini wannan kiran naki ya sakanifa na tsure" yafada yana dariya itama dariyar tai"Daman ai kasan dole kazo kodan shirin hidamar bikin nan yaya kake ganin za,ai?" hade ransa yay tamau tare da kallonta"Mameey dan ALLAH base kowa yazoba kuyi addu,a daga nan ma ya isa" kallo ta bisa dashi"Baka isaba uban mutane dole zanzo da dangina nima nai maka biki kamar yadda uwa kewa ɗanta kodai baka son talakawa suzo gidanku ne?" tafadi maganar cikin zafi sanin halin mami na zafi yasa ya sassauta"Nifa ba haka nake nufiba mami kimin addu,a ALLAH ya bani ikon rike wannan yarinyar amman harga ALLAH bana sonta mami dan dai kar inki amsarta ne ay mana dariya kuma naiwa ummi butulci kenan amman ummi ba da ban hakaba wallahi da bazan yarda ba" yakai maganar cikin damuwa kallon tausayi ta masa sannan ta soma masa magana cikin kwantar da hankali"Ka amsa ALLAH ya maka albarka yasa hakan ya zama alkairi a rayuwarku, amman nikam haryau raina bai daina son asma'u ba sabida wallahi rannan bakaji kukan datake akan itafa tana sonka" mameey takai maganar tana jin babu dadi aranta anan kam bai ce komai ba se sada kansa kasa dayay yana danna wayarsa....sun jima suna maganganu da mameey kafin tai masa sallama ta fita,tube kayansa yay tare da barin singlet da boxer ajikinsa ya kwanta a saman katifar ɗakin yana hasko dukkan wani motsin dasukai tare da ita, ya jima yana saka wasikar jaki kafin ya mike da ƙyar yay sallar isha'i ya kwanta baccin gajiya, washe gari da wuri ya dauko hanyar kano bayan ancikasa da tsarabar gombe

Bai shigoba se wajan yamma lis a ɗakin fulani hajja ya baje yana huce gajiya wadda hajiya ta sakasa agaba kamar xata mayar dashi ciki, baima san an kai lefe ba sedaga bakinsu faisal da suka shigo.

Washe gari da wuri muka ta shi sabida yawan bakin da mukaitayi sabida kawo lefe, karfe hudun yamma aka kai lefen rahinatu part ɗin hajiya fulani akwatuna goma sha biyu ciff fadin dukiyar da aka kashema bata bakine kowa ya kalla seya maya haka zalika nasu yaya faisal ma ankai, nikam idan na kadu ban bazaka taba gane a yaya nake ba, ansaka biki nan da kwana goma masu zuwa........Antynmu kanwar ummi ita ta wuce da Rahina gidanta dake rijiyar zaki wai za,a fara mata gyara sbd babu lokaci dansu ranar daurin aure zasu wuce london....har dare part ɗinmu yana daukar ɗan adam bamu sarara ba se da dare yaja sannan bakin suka tsagaita, haka muka kwanta baccin gajiya washe gari na wuce school ban shigo gida ba se 6 tunda na dawo na wuce ɗakina ina faman nazarin wani aiki da aka bamu ban fitoba se washe gari shima dan nasma tace zata zone...

Na tashi da tsarki dan haka banyi wani dogon shiriba nai falo na bada umarni a haɗa mana daining sannan na wuce waje dan na bada umarnin shigo da ita, a dai dai farfajiyar part ɗinmu na gansa yana waya, tunda ya dawo daga gombe bamu hadu ba se yau dauke kaina nai tamkar ban san da shiba na wuce abina.......da kallo ya bita yana taɓe baki tare da shiga cikin part ɗin ummi, sosai nai murna da ganin nasmat har muka karaso falonmu ban gansa acikiba dayake ummi tana bedroom zama mukai a falo muna hirar yaushe gamo har ummi ta fito suka gaisa anan nasma ke gayawa ummi za,ai bikinta.......kuma bata daukemin ba.....sedai kuma date ɗin bikin nata ya kama ranar daurin auren rahina ne amman zan daure naje mata koda a tsayene, mun jima da ita sannan tabani card ta wuce........haka kwanaki sukaita ja lokaci babu wuya yau aka soma gudanar da kamun amare waɗanda suka kasance duk ƴan cikin gidane sedai guda biyar dazamu kwaso a waje, a farfajiyar gidanmu aka gudanar da kamun wanda ya kasance na gargajiya faɗin yadda rahina tai kyauma bata bakine tai wani fresh kirjinta ya ciko kana kallonta kasan taci gyara ta goge sosai...anyi kamu lafiya angama lafiya tuni dangi sun cika gida haka zalika ko ina ka duba agari ana fadin shelar bikin nasune, mameey ma yau ta diro kano tare da kanwarta guda se matan yayyenta wanda ta dira a part ɗin ummi aka ware masu ɗakuna daban......anyi kamu lafiya angama lafiya amman nikam banga ango ba, gobe za,ai mothers day jibi kuma ayi dinner washe gari daurin aure, dan haka na zame da magariba nabi su hapcy lokacin da zasu tafi, zan tsaya nai gyaran gashina sannan nai kunshi a shagon saloon..........


_Sautari abinda muka ɗaukanta daso bai fiye zame mana alkairiba, idan zaɓin ALLAH yazama zaɓinka sam baka da matsala_



*DA IZZATA*
6/30/21, 11:17 PM - Buhainat: DZ

35 - 36

*DAN ALLAH KADA A FITAR MIN WAJE MAI SO TA BIYA TA KARANTA NA KUƊINE*


Kasancewar gidan namu akwai yawan jama,a marasa adadi, shine dalilin dayasa kawai nai ficewata batare dana sanarwa da ummi ba domin naga ummi tana cikin busy na jama,a ta ƙofar baya muka fita ban tsaya daukar mota ba domin bana son ɓata lokacina ga marigaba ta kawo kai, da ƙafa muka ƙarasa bakin titi muka tari napep, kai tsaye ayshert ya fara ajewa, sannan muka  ɗauki hanyar gidan da hapcy take wanda ya kasance a unguwar ɗan bare, nikuma za,a ajeni a rijiyar zaki, na wanke kaina. ana idar da sallar magrib na sauka bayan munyi sallama da hapcy dogon hijabi har ƙasa ajikina, senai amfani da face marks sabida banson jama,a su shedani, koda yake wama yasanni amman dai a wannan lokacin dole mutum yazama yana ɓoye kansa, sabida tserar da lafiyarsa, agurguje na ƙarasa wajan saloon ɗin, ban tsaya bata lokaciba na faɗa ɗakin dana ga toilet aciki nai alwala na tayar da sallah bayan na idar, na fita ina zaman jiran matar daza,a gamawa seni, Mintuna kusan goma, sannan aka kammala mata, nata nima na matsa batare dana tube hijabina ba haka naja wuyan ƙasa kawai aka somamin gyaran gashin nawa, wanda yake da mugun tsaho da yawa.

Acikin masarautar daula!  kuwa babu laifi angudanar da kamun ƴammata guda biyar ciff, a tsakiyar farfajiyar masarautar wanda ya halacci manyan mata waɗanda suka amsa sunansu anyi harka ta girma angama cikin mutunci, kowa ya koma part ɗinsa yana huce gajiyar rawar kiɗan kwaryar da aka gudanar na al,adar hausawa, part ɗin ummi cike da ɗan adam danginta da dangin mameey dasuka dira ɗazu, Anty zainab, ƙanwar ummi ta biyu, itace ta dubi ummi acikin ɗakinta,"Ummi nikam banga meemah ba ko lafiya?" Cikin murmushi ummi tace, "Ƙila tana ɗakinta, amman kije ki duba ko lafiya naga ɗazu har ƙawayenta ma sun shigo ai domin mun gaisa dasu" ummi bata rufe bakinta ba sega  Rahinatu sun shigo tare dasu aisha su safiya da dai ƴaƴan gidan yammata, "Ummi ina adda meema yaya Abdul - Naseer, yace wai  taje yana kiranta yana ɗakin da mameey ta sauka" cewar Hassana kenan ƙanwarsa, waɗanda tunda sukazo suke faman nemanta amman basu gantaba, hatta mameey neman ta take bata gantaba to shine ya shigo ɗakin mameeyn yaji suna cigiyar meeman sanin halinta yasa yace suce injishi domin yasan idan akace mameey tana kira bazata zoba sabida tun fill azal meema kunyar mameey take bata yarda su zauna waje ɗaya, shiyasa ko wani abun tai ana cewa za,a gayawa mameey take saurin bada hakuri,"Kuje ɗakinta mana ni bata nan" cewar ummi, "Ummi ai munje bata can", inji rahina, cikin sauri ummi ta lalubo wayarta tare da kiran lambar meema sedai harta gama ringing! bata ɗagaba babu shiri ummi ta ɗauki mayafi tai cikin falonta wanda yake shake da ɗan adam,kanta tsaye ɗakin meeman ta nufa, sedai itama ta gansa babu kowa, gumine ya tsirgo mata, cikin sauri tabar ɗakin hartana karo dasu rahina suna ƙoƙarin shigowa suma"Ummi kinji wayar ta,ta?" cewar rahina, "A,a bara na leƙa garden" tafadi maganar jikinta yana rawa sabida atake anan tunani kala kala ya shigeta, har garden ummi taje babu meema, wanda zuwa lokacin tafara sharar hawaye mema zata cewa mai martaba idan yaji meema bata gida? "Ummi lafiya dai" taji saukar muryarsa a kanta"A,a Abdul wannan yarinyar ce ban ganiba tun ɗazu fa" cewarta, "kuma bata ɗakinta nima mameey tace bata ganta ba shine na turo yaran can su kirata" yafada yana lalubar wayarsa, bai tsaya jin karashen ba ya shira kiran layinta, Lokacin an gama wanke mata kanta, cikin azama matar ta miko mata wayar tana ce mata madam ana kiranki cikin kosawa meema tace mata pls ɗauka min ce ina cikin saloon, Yana jin an ɗaga wayar ya karo volume, nan yaji muryar mace tana ce masa wai ana mata gyaran gashine amman ankusa, bai wani tsaya bata lokaciba ya tambayi matar kwatancen wajan, cikin mintuna biyu, ya katse wayar tare da kallon ummi"Bara naje mu taho tare karki damu tana wajan gyaran gashine fa" mayar da ajiyar zuciya ummi tayi"Amman tai wauta yanzu haka ta fita bata sanarmin ba, salon taja mana tashin hankali" bai tsaya jin karashen ba yabar wajan, yana ayyana kar wani abun ya sameta ita ɗaya awaje.Ummi fita tayi zuwa ɗakin mameey ta sanar da ita cewar meema tana wajan gyaran gashi, sannan ta komawarta ɗakinta tanajin ranta yay sanyi, shikuma wajan parking space ya nufa ya shiga mota tare da nufar rijiyar zaki a 360, koda yaje
a bakin shagon ya tsaya tare da kurawa kofar wajan ido kamar ya faɗa ciki.

Bayan an kammala min gyaran gashina aka wankemin ƙafata, ban tsaya kunshiba ganin har 8 ta wuce, agurguje na bata kuɗinta mukai sallama, ban tsaya, ma duba waya kiraniba, sabida hankalina yay gida bani son ummina ta shiga cikin damuwa, garin ko ina da haske ga motoci suna wucewa sabida a bakin titi wajan saloon ɗin yake, da ƙafa na ƙarasa bakin titi, na tsaya jiran masu napep ko ALLAH ze kawosu, tunda ta fito ya kafeta da ido yana jin abubuwa marasa daɗi acikin ransa, Ko tana ciki n dubban jama,a dole ya shaidata bare wannan abun kare hancin data saka baze hanasa shaidata ba, buɗe marufin motar yay tare da fitowa ya jingina da jikin motar yana kallon yadda take faman ɗaga hannunta sama alamun tsaida abun hawa, dariyama taso ta basa sabida kana ganinta kasan bata saba tsaiwar titi parking ɗin da wani mai baƙar CRV yay yayi dai dai da karasowarsa bayanta, cikin sauri na cikin crv ɗin ya fito daga motar tasa ya ƙaraso gabana, "Barka da dare malama" naji muryar babban mutum akaina, ɗagowa nai na dubesa, sau ɗaya sannan na kauda kaina gefe cikin izzata ina faman basarwa,"Idan bazaki damu ba kozan iya sanin sunanki?" ɗagowa nai akaro na biyu domin na bashi amsa, wanda yay dai dai da bayyanar Abdul agabana, cikin wani irin kallo naga ya jefi mutumin, "Malam dalla kauce daga nan kona sauya maka kalar fuskarka" naji ya faɗa cikin sauri tare da cafkar tsintsiyar hannuna"Dan ubanki shige mu wuce daman abinda ya fito dake kenan", Tsaye muka bar mutumin tare da binmu da kallo, har yana tuntube dan sauri haka yajani kamar wata ƴarsa ya wurgani cikin mota tare da saka lock, shima ya zaga ya shiga muka dauki hanyar gida...........


Manage se dare insha ALLAH.


*DA IZZATA*
6/30/21, 11:18 PM - Buhainat: DZ


37 - 38



Tunda muka ɗauki hanyar gida yake faman masifa kamar ze dukeni, munzo dai dai wajan go slow ɗin daze sadaka da hanyar gida, ya doki wata mota kuma dayake yana cikin masifa ko kallon na motar bai ba yaja motar ƙiiiiiiiiiiii! kamar ze zubar damu, "Nidai gaskiya ka tsaya ka saukeni dan ban shirya mutuwa yanzu ba" nakai maganar cikin fushi, wani irin ja yama sitiyarin motar tare da dukan gaban motar kamar ze kifa sannan yaja burki ya tsaya" gwara na kashemu ai dan ubanki tunda baki da mutunci baki san ciwon kanki ba ballagaza mai tallan kanta atiti" yafaɗi maganar cikin hucin masifa tare da zubomin jajayen idanunsa kamar gaushin wuta, Kuka na saka tare da kallonsa ko kaɗan tsoronsa ya kau araina, to mai ma nayi daze gayamin wannan kalmar sekace wadda maza suka danne,"Niba ballagaza bace ba wallahi to ina ma ruwanka da duk abinda zanyi idan ba shish............,ban kaiba naji saukar tagwayen maruka akan fuskata, first in history Abdul - Naseer ya mareni, dafe kuncina nayi na ɗago cike da ƙunar rai,"Nika mara ko?" nafada ina ɗigar da hawayena, bai min magana ba illah kunna motar dayay ya bata wuta ,cikin fushi, hannu na saka ina kokarin fita daga motar amman ya mata key, babu damar fita,"Mina maka ka mareni bayan ka kirani ballagaza maye haɗina dakai dazaka mareni idan ma har dan ina sonka ne yasa zaka min haka to wallahi bana sonka bana ƙaunarka, na tsaneka har abada bazan taɓa son.........,"Ya isa haka Asma'uuuuuuuuu!!! Yaja sunan da ƙarfi tare da sakin kan motar baki ɗaya ta dinga taga taga a titi zata kifar damu, Dafe kansa yay tare dayin ƙasa da kan nasa, ganin babu sarki se ALLAH ga motar tana kokarin yin gefen titi yasa na ƙwala ƙara! "Wayyo baba ze kashe maka uwa na shiga ukuna"! na faɗa

Please Login or Register in order to submit comment