Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gardi ya hauro mana".
Takai maganar tana zare idanun karyar data zabga.
Dariya! yaya nura yay.
"Tabb amman lallai Ƴar fillo kinci sa,a mutum kamar mai gida ya tsaya magana dake".
"Hmm yaya nura ay ba tanan gizon ke saƙaba itakuma feena tace seta rama abinda yay mata ay".
Walida tai maganar wadda hatta feenah seda ta kalli walida tare da jinjina yadda walida ta iya sarrafa zance.
"To ALLAH ya bata sa,a ita inama zata ganshi mutumin da baya da lokacin kansa matarsa mafa setai wajan kwana biyu bata gansaba sabida yawon garuruwa da kewaye".
Dum!Dum!!Dum!! gaban fina ya faɗi cike da rashin dauriya taso gwafsa masu cikin azama walida ta kaɗa mata idanu tare da kallon ya nura.
"Au yanada mata yaya?"
"Eh mana ay ya jima da aure sedai kuma ALLAH bai basa haihuwaba har yanzu anata dai nema, kuma naji ance matarsa ma ƙanwace awajansa kuma ana faɗar kirkin hajiya hidaya duk da mu bamu santaba amman babu laifi ance gidansu akwai karama da mutunci"
Yakai maganar yana duba agogon hannunta.
Sannan ya mike.
"Ƙanne na ni zan wuce gida kekuma nafisa ina son kiyada makaman yaƙinki akan mai gida! saboda shi sam ƙilama ya manta dawata ke dan shikam baya shiga harkar kowa, idan ba aikin daya saka gabansa ba sam mata basa ruɗarsa.
Naji ancema ranar biyar ga wata ze taro anan filin wasa na ɗawisu square wanda za,a tattauna dashi sosai akan ayyukan daya gudanar sannan ze bada tallafi na mata da marayu da zawarawa saboda haka kinga shiɗin abin sone kuma abin so ga kowa dan haka shawarata agareki ki fita harkar shi tun kafin wanima yaji".
Yana kai maganar ya zaro kudi masu yawa ya basu yay masu sallama ya tafi.
Haka suka kwashi kayan nasu suka wuce hostel wanda nafisa idan banda kuka babu abinda take.
Abakin kwanarsu ta aje kayan ta faɗa saman gado tana sakin kuka kamar wadda aka cewa kaka ta rasu.
"Haba fina maye na kukan nan haka mu fawwalawa ALLAH komai ze mana maganin dukkan damuwar mu".
"Walida dole nai kuka kinjifa yana da mata kuma sister ɗinshi yaya zanyi sonshi nake kishin sa nake........!!


FREE PAGE YA KUSAN ƘAREWA FA WAƊANDA BASU BIYA BA TA KUSAN FASHEWA🔥🔥🔥









*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
6/30/21, 11:12 PM - Buhainat: 🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿? *11*


Ware manyan lumsassun idanunshi yayi waɗanda lokaci guda suka juye tare da sauya kala zuwa jajur.
Cike da tsananin ɓacin rai yake sauraran na cikin wayan nashi tare da ɗan jan numfashi kaɗan ya fesar da zazzafan huci mai sauti.
Fitar amon daddaɗar muryarsa wadda ta cika da zallar ɓacin rai ita ta karaɗe falon.
"P.a mika keson gayamin ne wai?" yafaɗa cikin sautin ɓacin rai.
Bai jira ta cewar p.a ba ya cigaba da magana wadda nan da nan maganar tasa ta koma yadda take ma'ana ɗan saurin baki kaɗan.
"Wallahi nama gaya maka kaje ka samu sardaunah kuyi magana bazan lamunci cin amanaba"
Yaɗan numfasa kaɗan.
"Wannan contract dana basu bawai dan na rasa masuyimun bane ba illah kawai na duba kokenshine, wannan ma ay zancan banza ne da shashanci kace wai aiki ya lalace, suna nufi na ƙara narka wani kuɗin nawa kenan wancan sun tashi a banza?".
Yakai maganar cike da tuhuma.
Daga cikin wayar p.a dake tsaye hannunshi na rawa baki ɗaya hankalinshi ya tashi ganin mai girma mas! ze harbo jirginshi nan da nan yahau bashi haƙuri.
"ALLAH ya huci zuciyar megida!wallahi nima ɗazu ya kirani yake gayamin, amman dai mai gida da antaimaka anɗan daɗo masu kuɗin kamar yadda aka buƙata a daure a duba lamarin".
P.a yakai maganar yana zaro ido shi a dole seyaci kuɗi.
"Dakata p.a.wannan furuncin da kakemin ze iya kawo ƙarshan tafiyata dakai! danni tafiyata ban haɗata da maci amana da marar alƙawariba,sabida haka ka kula".
Yakai maganar a fusace tare da datse wayar ya wurgata can gefe.
Hannunshi wanda yake fari ƙar mai cike da yalwar gargasa ya ɗora a saman sumar kansa tare da lumashi acikinta yana hargitsawa da alamun ran ƴan maza ya ɓaci.
Ya ɗauki kusan mintina biyar a zaune yana faman lissafi acikin zuciyarsa.
Kafin kuma ya miƙe cike da zafin nama yake taka ƙafafunshi ya nufi ciki.
Kai tsaye hanyar bedroom ɗinshi ya nufa tare da buɗe ƙofar ya faɗa ciki.
Agurguje ya tube kayan jikinshi ya nufi bathroom 30 minute ya gama watsawa jikinsa ruwa.
Tare da shiryawa cikin wani farin yadi mai kyau.
Turarurruka masu sanyin ƙamshi ya fesa tare da ɗaukar makullin mota ya nufi hanyar fita.
Hango hiyada yay daga cikin daining area tana setting table.
Ɗan juyowa tayi sannan kuma ta tako cike da nutsuwa ta ƙaraso gabansa.
"Dear kardai fita zakayi?".
Tafaɗi maganar tana ɗan tura bakinta gaba kaɗan..
Shafo kumatunta yay da lallausan hannunshi tare daɗan sakin murmushi kaɗan.
"Haba gimbiya sarautar mata to maye na haɗe ran zani meating ne before ai kiran sallah"
Marairaicewa tayi cike da shagwaɓa sannan ta ɗan matso hawaye kaɗan.
"Nidai ka zauna na samu ladan baka abinci tunda yau kayi wankan baka jirani ba".
Cike da jin daɗin yadda take kyautata masa ya kamo hannunta cikin nashi.
"Ay haƙuri my love bazan jimaba insha ALLAHU".
Janye hannunta tai anasa tare da komawa baya.
"Tun break ɗin safe bamuci komai ba ina faman jiranka nai maka abinci mai daɗi shine zaka tafi bazaka tsaya kaciba nafa san meating ɗinnan watarana senai bacci baka shigoba".
Tausayinta ne ya kamasa tare dajin wata irin soyayyarta mai tsafta acikin ransa.
Kamota yay zuwa jikinsa.
"Tom ay haƙuri bazan kuma ba maza muje muci abincin".
Ya gaya mata haka tare da tallafota suka nufi daining sanin za,a takurasa da waya yasa ya kashe wayar tasama baki ɗaya.


Hostel

Tunda walida ta bawa f.k shawara akan addu,a shikenan nafisa ta mayar da hankalinta ga addu,a babu dare babu rana haka zalika babuji babu gani.
Dukda tana masifar jin soyayyarsa acikin ranta amman haka take daurewa tana harkokinta.
Amman takanas ta nemi radio wadda kullum take manne da ita tanajin program din da akeyi agidan radion ɗawisu wanda akewa take da.
TASKAR MAI GIRMA MAS! kusan kullum tana sauraran shirin wanda ake zaƙulo irin ayyukan dayakeyi afaɗin garin wanda wataran ake magana tare dashi.

"Nafeesah! Nafeesah!! cewar walida wadda take tsaye akanta hannunta ɗauke da sponcase wanda daga gani daga wanka ta fito.
Lumshe idanunta tayi waɗanda kullum kusan a haka suke.
Tare da ɗagosu ta kalli walida kamar zatai kuka tace.
"Walida kin zama ƴar shiga tsakani ko?".
Bata jira mi walida zata ceba......!!!



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
6/30/21, 11:12 PM - Buhainat: 🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*NA*
AUTAR MANYA🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿? *12*


*SECOND TO THE LAST FREE PAGE*👌


Bata jira cewar walida ba ta ɗora da cewa.
"Ina jin shirin TASKAR MAI GIRMA MAS! nefa kika wani zo kina damuna dan tsabar baƙin ciki irin naki".
Sekuma ta kifa kanta akan gadon ta saki wani irin marayan kuka!
"Ni wallahi walida kin cuceni kuma se ALLAH ya sakamin".
Takai maganar cike da ƙunar zuciya.
Sosai abin ya baiwa walida mamaki dariya dakuma tausayi.
Dakewa tai tare da zama a gefenta ganin kamar zata shiɗene a kukan!
Kamo hannunta tayi tare da riƙewa cikin nata.
"Haba ƙawata daga maki magana se kuka! dan dai abin kukan! baya da wahala ki sassautawa zuciyanki kada ki kashe kanki a banza wanda kike bai san kinayi ba".
Da sauri ta ɗago ta makawa walida wata ƙatuwar harara tare da komawa ta kifa tana sakin matsanancin kuka!
"Walida na rasama yaya zanyi akullum soyayyarsa ƙara huruwa take a raina wutar sonsa ƙara bin jikina take na shiga uku ni nafisa yaya zanyi da soyayyar wanda bai san da zamana ba".
Takai maganar cikin mayar da kanta kalar tausayi.
"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki mu mayar da hankalinmu kan karatun mu kinga wani satin zamu soma exam wannan karan sabida kin saka soyayya aranki baki ɗaya text ɗinki baki waniyi abin kirki ba dan ALLAH, ki saki ranki fina komai zezo ya wuce".
Ɗago kanta tayi tare da makawa walida harara.
"Kamar yaya komai yazo ya wuce?"
Ta jefa mata tambayar idanunta cike fal da hawaye.
"Ina nufin wataran haka zan ganku da ƴarku ko ɗanku kunkawomin ziyara kamar bakiyi kukan nan ba insha ALLAHU".
Walida takai maganar tana dariya.
"Hmm walida kenan ALLAH amin Ya ALLAH ka nuna min wannan rana mai tarin farin ciki ga rayuwata.
"Ameen ƙawata"
Ɗan muskutawa tai kaɗan tare da kallon walida sosai.
"Walida ina son halartar taron dazeyi ranar biyar ga wata kinga ranar kwann mu guda kenan da hutu".
Ɗan jimm walida tayi sannan tace.
"Amman senaga kamar hakan bai daceba kasancewarki ba ƴar siyasa ba".
Haɗe ranta tayi sosai sannan tace.
"Walida zanje insha ALLAHU ko a bakin gate na tsaya aidai na gansa ko hankalina ya kwanta".
Murmushi walida tayi.
"Dawasa nake maki ai babu matsala tunda wajene wanda kowa da kowa ze iya zuwa bawai ke ɗayaba nima idan da lokaci maje, sedai kuma ina tunanin yadda zaki taho tun daga can har cikin gari?"
Cike da farin ciki f.k tace.
"A,a zan tawo gidan umma sahura ne tunda daman daga nan bazanje can wajan kaka ba kawai zaku saukeni gidan umma sahura tunda yafi kusa daga nan senazo gidanku mu wuce harda ya nura nasan hajiya bazata hanaki ba".
Tsalle walida ta doka tare da kawo hannu suka tafa!
"Yes ƙawata simple kinga kuwa mabi ya nura kawai batare da munsha wahala ba".
Cike da murna wadda rabon datayi kamarta harta manta ta kuma kaiwa walida hannu suka tafa! tare da sakin dariya tana cewa.
"Kai ALLAH yabarmin ke wallahi keɗin ta dabance ALLAH ka nunan biyar ga wata naga sanyin raina".
Takai maganar tana lumshe idanunta.
Haka ta saki ranta sukaita hira da walida har zuwa sanda aka kaɗa masu karatun yammah haka suka shirya cikin hause ware suka wuce.

Ɗawisu g.r.a

Sun jima a daining suna cin abinci kafin su kammala haka hidaya taƙi yarda ya fita konan da can sabida yau ta wareta a rana ta musamman domin ta angwance itama da mijin nata.
Aikam babu laifi ya nuna mata shiɗin namijine lafiyayye cikakke wanda seda ya bata fiye da tunaninta hardama ramuwar wanda baiba sabida yawan fice ficen dayakeyi.
Dayake wayarsa a kashe take shiyasa babu wanda ya takura masa da kira haka sukasha shagalinsu.

Har zuwa washegari wanda kuma kwanakin da suka biyo baya.
Bashida wani sukunin zama sabida gudanar da ayyukansa baya samun zama ko kaɗan daga nan se nan daga nan senan.
Su kansu su mama sesunyi da gaske zeɗan leƙo a gurguje ya gaisa dasu sannan ya wuce.
Hidaya kam se tai baccima watarana basu haɗu ba sedai da safe amman kuma babu laifi a hakan ma yana kokari wajan sauke mata haƙƙinta na auratayyah.
Aiki babuji babu gani yake gudanawar yau baya can yau baya nan haka yake gudanar da mulkin nasa cike da nagarta.

Hostel

Kwanci tashi babu wuya a wajan ALLAH yau harsu feenah sun kammala exams ɗinsu lafiya kuma babu laifi a hakan tai ƙoƙari sedai bata kai kamar koyaushe ba.
Ranar hutu tun wuri suka shirya cikin uniform ɗinsu wanda ko daining basuje karbar abincin break fast ba.
Haka sukai kwaɗon kwakinsu wanda tun kafinma su xira uniform suka ci suka sha ruwa suka killace kayansu a cikin lokar sannan suka ɗauki school bag ɗinsu da ɗan abinda ba,a rasaba sukai can gate domin isa wajan yaya nura dan sun san yazo tunda shi ALLAH ya zuba masa sammako.
Aikuwa tundaga nesa yake masu inkiya da hannunshi alamun su taho daman kuma su,suke aje nafisa a gida su wuce shiyasa ba,a zuwa ɗaukarta daga gida.
Shigar da kayansu sukai cikin motar bayan sun gaisa da ya nura sannan suka shiga mota suka ɗauki hanya.
Aron wayarsa tayi ta kira number habu ta sanar masa ya gayawa kaka itafa tayi gidan umma sahura.
Cikin ko in kula habu ya amsa mata sannan ta katse kiran ta bawa ya nura wayar tana dariyar dole.
Anan fa walida ta soma yiwa ya nura zancen zasuje wajan taron mai girma mas wanda za,a gudanar a gobe.
Cike da farin ciki ya nura ya kalli nafisa.
"Da gaske wai kuke zaku taron mai gida?"
Yafaɗa yana sakin farin ciki kasancewarsa ɗan amutun mai girma mas ɗin.
"Eh Insha ALLAH yaya zamuje".
Tafaɗa cikin muryarta mai daɗin gaske.
"Aikuwa ki kintsa da wuri zanzo mu ɗaukeki kinsan mune masu masaukin baki kada ki tsaya wannan sanyar taki ki ɓata mana lokaci".
Cikin farin ciki walida tace.
"Anya sis bazamu wuce gidanmu dakeba idan yaso goben kawai semu wuce".
Murguɗa mata baki tayi tare da cewa.
"Nikam yau ɗakin umma zan kwana".
Takai maganar cikin tsokana.
Da haka suka cigaba da hirarsu har suka isa gidan umma sahura dake gefen titi.
Sosai umma sahura tai murna da zuwan ɗiyar ɗan uwan nata hartana kullawa su walida dambun datayi a leda sannan sukai sallama bayan ya nura ya gaya mata gobe zasuzo su dauki feenah zuwa can ɗawisu square wajan taro.
Batai masa musuba haka ta kama hannun nafisa suka wuce cikin gida tana zubawa ya nura godiya sannan tai ɗakinta da kayan feenah a hannunta.
Dakanta ta kai mata ruwan wanka bayi kafin ta fito ta ɗauko mata kaya masu kyau..
Bayan ta fito ta sauya kayan tare da zaman cin abinci wanda harda kifi ta sayo mata sannan tai sallah.
Nan suka hau hira wadda har akai kiran sallar magariba basu ankaraba.
Sumayin sallah suka fita tsakar gida suka dora girki ahaka mijin umma sahura ya dawo yana ganin nafeesah ya hau far,a nan da nan ya fita yaje kasuwa yayo mata sayayyan kayan ciye ciye sabida shima mijin umma sahura yana son fina sannan kuma daman auran zumuncine bayan haka kuma mahaifinta abokinshine.

Zama sukai a tsakar gida bayan sunyi sallah aka hau hira harda mijin umma sahuran seda akai isha sannan fina tai musu sallama ta wuce ɗakin umma tahau gado nan danan bacci mai dadi ya kwasheta.

Cike da ɗaukin ganin gari ya waye domin taga MURADIN ZUCIYARTA.....!!!


*WANNAN SHAFIN DAGA SHI SENA ƘARSHE A CIKIN JERIN FREE PAGE MAZA HANZARTA BIYAN NAKI/ NAKA DOMIN KA TSUNDUMA CIKIN TAFKIN KOGIN WANNAN LABARIN MAI CIKE DA ƊUMBIN DAƊI DA NISHAƊANTARWA*👍




*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO....* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
6/30/21, 11:13 PM - Buhainat: DZ


11 -12


Mamakine ya kama mai martaba amman bai ce mata komi ba illa tsiratan dayay da idanunsa yana kallonta tabbas yasan a yau ankai fatima makura tunda ta furta wannan maganar sabida yasan fatima mace ce mai tsantsar hakuri tare da kawaici.
Gintse fuskarsa yayi tare da ambatar sunanta.
"Fatima nasan tun ɗazu abinda ke maki suka acikin zuciyarki kenan, na abinda asma'u tayi tabbas kuma nasan babu wanda zakiyi kuka! dashi kamarni, dan ALLAH kiyi hakuri fatima ki ƙaddara komai ya faru da bawa muƙaddarine daga rabbissamawati kuma kiwa ƴarki addu,a akan ALLAH ya shirya maki ita, itama kuma rahina seki mata addu,a akan ALLAH ya dai-dai tasu da abdul ɗin baki ɗaya" mai martaba, yakai maganar cikin tsantsar dattako tare da nutsuwa wadda tabi jikinsa, sarki abubakar daula kenan masu dukiyar gado! bayan ya gama gayawa ummi hakan yaja ya kishin giɗa akan matasan wajan tare da ɗora hannun ummi akan ruwan cikinsa yanajin kaunarta har cikin ransa tabbas fatima macece mai tsantsar nagarta ladabi biyayya ga hakuri,wannan dalilin yasa yake mamakin meema sam bata gado halin ummi ba, cikin sanyinta ta katse masa dogon tunanin daya shiga "Naji dukkan maganganunka kuma na yarda da hakan tabbas komi na ALLAH ashirye yake muke ɓata lamuranmu, amman yallaɓai". ( sunan da matansa ke gaya masa kenan sukuma su meema sukance masa baba, ko mai martaba) taja fasali kamin ta ɗora da cewa..............."Amman yallaɓai baka ganin wannan haɗin akwai cutarwa acikinsa kagafa Raheena......." dakata fatima! yay saurin tarar numfashinta......."Bana son ɓacin ranki akan wannan lamari kedai ki mata addu,a jikina yana bani wannan aure akwai nasara ita kuma taje zata gane kuranta wallahi daga yau hatta makarantar na cireta kuma ki shaida mata komai nawa na janye yi mata shi"............Yakai maganar cikin fushi "Kamarni asma'u zata baɗawa ƙasa a idanu harna ce abu takiyi sabida tana jin kanta wata mema tafi yaron nan ne?"........yakai maganar yana huci,"Allah ubangiji ya huci zuciyarka aikamar ina ganin ita wadda ka bawa rikonta ta lalata maka ita itan zakaje kaiwa wannan faɗan amman ni ina ganin babu ni aciki.yanzufa nagama neman alfarma akan a dawo min da ita amman ka nuna vaka amince ba" ummi takai maganar cikin kunar rai abinda bata taɓawa mai martaba ba kenan shine mayar da magana, numfasawa yayi tare da kuma kamo mata hannunta yana kuma jin ninki kaunarta acikin ransa tabbas ya yarda fatima macece mai nagarta wannan dalilin yasa yake girmama komi nata "Haba ummin Rahina" yafada cike da lallashinta........."Mufa manya ne masu mulki muna da kuyangu da sauran masu mana hidima acikin wannan masarauta kinsanni tun asali bana son duk abinda ze jawo mana raini kokuma cece kuce"..........yaja fasali kana ya cigaba "Bakya tunanin da zarar an farga meema bata bangaren naja'atu za,a hau maganganun acikin wannan masarauta tamu, kiyi hakuri kamar yadda kika saba har ALLAH yay ikonsa idan aka aurara da rahina se itan ta dawo gunki, daga nan kinga babu mai cewa komi" yakai maganar yana nazarinta, cikin ladabi tare da ganin mutuncinsa ta amsa masa da "To". kafin ta soma magana cikin sanyinta "Amman yallaɓai baka ganin kamar mun shiga hakkin yaran nan ina abdul zeso rahina yarinya karama" takai maganar tana kallon sarki abubakar, ɗan murshi ya saki irin nasu na manya"karki damu insha ALLAHU zama suso junansu kuma zan kira shi baban nawa, vayan haka kuma zamuyi magana da waziri Aliyu domin musan matsaya amman insha ALLAHU bikinsu na nan cikin karshen wannan watan babu fashi wanda ya kama nan da sati biyu kenan".sarki abubakar yakai maganar yana mai nazarta ummi aransa yaga sam bata na'am da wannan aure amman shikam yasan nan gaba kaɗan zata so auren harma tai alfahari dashi.
Sun tattauna manyan mahimman abubuwa a wannan dare, kafin kuma dare ya nutsa kunsan ance dare mahutar bawa, bare kuma su masu mulki waɗanda suka wuni tare da jama'a.

WASHE GARI.
Bayan na tashi nayi sallar asubahi duk jikina yayi wani irin mugun sanyi, da ƙyar naje wajan umma na gaisarta kafin naja ƴammatan ƙafafuna nayo ɗakina tare da shiga toilet na watsa ruwa doguwar rigar atamfa na saka tare dayin ɗauri mai burgewa sabida 7:30 dai dai nakeson naje school domin akwai wani malaminmu danake son naje wajansa domun yayi attandance banje ba ranar kuma yace c/a ɗinsa ce ta exams lemon green gyale na ɗauka acikin close set ɗina tare da bakar jaka wadda na zuba mata uban tarkacena flate shoe na ɗauko acikin jerin takalman dake ɗakina na zira acikin kafafuna nabar ɗakin bayan na zabga uban turare.
Cikin takuna wanda nakeyinsa da dukkan karfina nake keto cikin falon namu hadiman dake zube awajan suna faman tsaftace falon duk da ba datti yayi ba,haka suka zube agabana suna faman gaisar dani gami da watsomin kirarin gidanmu! ban wani kulasuba sedai akan fuskata zaka san cewar abin yayi min daɗi.
Haka na wuce falon batare danayi ko break fast ba, ban bi ta part ɗin ummina ba haka na nufi bakin katon wajan adana motocin gidan direct wajan wata vakar venz na nufa, cike da sauri dogarin dake jana wataran ya taho yana faman min fadanci kai tsaye na ɗaga masa hannu tare da amsar keyn na nufi gaban motar.
Cak na tsaya ganin ya faisal da wannan safiya haka yana tsaye gaban wata ash colour ɗin corolla, daga ganima hankalinsa baya wajena ganin haka yasa nai inawa nabar wajan na nufi gaban motar dazan hau na bude tare da shiga cikinta.
Rivers nayi ina kokarin bata wuta na hango ya Abdul-Naseer wanda daga gani shi ya faisal ke jira awajan.
Jikinsa sanye cikin sport ware red, se ƙatunan boot ɗin daya saka a kafarsa idanunsa sanye cikin bakin glass bakaramin kyau yay ahakanba, ganin sa nayi ya nufi wajan ya faisal tare kuma suka nufi sashen baba waziri.
Ƙwalla ce ta taromin a idanuna a fili na furta "ALLAH yay ruwan kyau awajanka ɗan balarabe na"........tuno maganar baba ta jiya wai an basa rahina amatsayin na huce dani shiyasa naji wata kwalla ta zubomun ban san lokacin dana kwashi motar aguje ba nayi baki gate..........



*Kamar yadda kuka sani wannan littafi mai suna DA IZZA TA! na kuɗine Normal grp posting sau 1 a rana 200, Vip grp post Sau Biyu a rana 500, Masu son adinga basu ta p.c base sun shiga grp ba posting sau biyu a rana 600, gamai buƙata ze turo da kuɗinsa tanan 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinka ta nan 08142105218, pls ƴan vip da ƴan s.p bana son kati zakiyi transper through accnt idan baki da shi kije pos su ɗauki  naira 100 na yafe, vip ki turo 400, sp,500 idan sun ɗauki kuɗinsu, idan kuma kinada account shikenan, sena jiku masoya, da kijira a saya a baki gwara kin biya kuɗinki domin kada ayi babu ke! ƴan nijar masoya kuma zaku iya min magana ta number ta dake sama, sena gaya muku yadda zaku biya naku, sena jiku masoyana ƙashin bayan nasarata abin alfaharina*

*ZUWA GA MASOYA*

*Gamasu buƙatar comple littattafaina dana gama, ƊAN MAJALISA, KOBA SO, H A S KE, Zaki turo naira 700 ta wannan accnt ɗin 0078174806, Shedar biya 08142105218, Sena jiku masoyana*✍?
6/30/21, 11:13 PM - Buhainat: DZ



13 - 14


Kowa ya dubi motar danake ciki seya kwasa aguje wasu suna gudun ransu ne wasu kuwa tambarin gidanmu dasu ka gani shine ya saka su arta ana kare, inaga tunanin wani abun sukeyi, sosai nake gudu akan titin gwarzo road wanda ze kaini cikin makarantarmu ta b.u.k old side, cikin wani yanayi nayi parking acikin harabar adana motoci na cikin school ɗin tamu, zage zip ɗin jakata nayi tare da ɗauko black ɗin space na saka a fuskata sabida yadda idanuna suka cika da ja! tarkacena na ɗauka da sauran kayana na fito daga

Please Login or Register in order to submit comment