Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasan ranta haka xalika mameey itafa seda ta cikawa sarkin shela aljihu da kuɗi duk da rasuwa akai amman seda mameey ta taka rawar murna aɗakin datake tabbas yazama dole ta tafi da meema gombe tabata gyara na daban yadda ɗan nata ze ɗauketa ata daban.
Haka zalika yayyen ummi ƙannenta duk murna suke hatta ga bayin part ɗin ummi sunji daɗin wannan lamari domin sam ba,a wani yi ja injaba manya ne,suka nuna isarsu akan ƴaƴan nasu.
Baccina nake a ɗakina duk na takure waje ɗaya naji sautin dun du a bayana da sauri na miƙe ina sosa wajan.
"Tashi hajiyata yau ranarki ce mrs abdul yaudai baba ya nuna keɗin ƴar lelensa ce" cewar sumayya ɗiyar adda yakumbo kenan wadda muka taso kamar ƙawaye, "Ban ganeba dalla ni kinxo kin tayar dani ina baccina mai sugar" dariya sumayya tai tare da cewa "To buɗe kunnenki da kyau kiji yaudai mai martaba da baba waziri sun ɗaura maku aure da wanda kika ƙi ada muna fatan wannan karon zaki kula lamarin ma,ana an ɗaura fa da yaya Abdul" dum dum gabana ya faɗi riƙota nai "Sumayya kefa marar mutunci ce da gaske ko wasa?" mirmushi tayi "Wallahi da gaske in ina karya ki tambayi ummi" komawa nai daɓas na xauna narasa mikemin daɗi har sumy ta fita ban iya ɗagowa ba, "Yanzu mijin da rahinata tai rayuwa dashi nima zanyi?" se hawaye shaaa kamar famfo atakaice dai ranar rasa gane kaina nai yini kuka nan da nan idona ya haye kuma naƙi buɗe ɗakin nawa sam sabida haushin kowa nakeji.


Cikin sauri anty safiya matar baba waziri ta rarumi wayarta tai ɗakinta neman number na tsakiyar ruwa take amman taƙi shiga jefar da wayar tai tana wani irin kukan baƙin ciki, ita kuwa umma seda zainab ƴarta tai mata ƙaramar roƙiya sabida tsirara ta kusanyi agaban sarkin shela sabida rudewa sumbatu take tana "Ni xakuyiwa haka munafukai to duk sena kasheku" wannan furucin dashi tai bacci haka zalika sakina itama kamar zata shiɗe dan hartafi uwar shiga damuwa.
Wuni waɗannan ɓangare guda biyu sukai cikin tsananin damuwa har dare kamar anyi rashin wani ikon ALLAH hassada babban ciwo lallai safiya da umma kuna cikin halaka.

Abincima anan hassana kanwarsa ta kawomin wanda seda ta gayamin itace na bude mata kofar sabida bayan nagama kukan nawa takarduna na ɗauko ina nazarin gobe sabida yazama dole na fita makaranta sabida tex ɗin daxa,a mana tana ijen abincin ta fita ban tashiba seda aka kira sallar magarib..............


MANAGE BACCI🙏
7/8/21, 1:34 PM - Buhainat: *DZ*



60



_AFUWAN MASOYANA DAN ALLAH KUYI HAƘURI DA JINA SHURU DA KUKAI YAU, WALLAHI BIKI MUKAI SHINE YASA KUKA JINI SHURU KAMAR YADDA NAKE GAYA MUKU KODA YAUSHE KUNA RAINA BURINA NA BAKU NISHAƊI IDAN KUKAJINI SHURU TOFA SEDA BABBAN DALILI, ALHAMDULILLAHI INA GODIYA GA ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI, TABBAS NAGA SOYAYYARKU MY FANS DAGA JIYA ZUWA YAU HAR KUNYAR BUƊE MSG ƊINKU TA PC, NAKEYI SABIDA YAWANKU WASUMA WAYA SUKAIMIN AKAN JINA SHURUN DA SUKAI TABBAS KO YANZU NASAN CEWAR KUNAJIN DAƊIN WANNAN LITTAFIN NAWA FATAN ALKAIRI GAREKU ƳAN *VIP GROUP, NORMAL GROUP ONE & TWO, DAKUMA MASU GAYYA DA AIKI ƳAN SP, DUKKAN NINKU INA GODIYA SOSAI ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKAIRI AMIN SUMMA AMIN_


Ruwa na tara nayi alwala, sannan na fito tare da shinfiɗa sallaya na tayar da sallah, na jima ina addu,a akan wannan aure namu ALLAH ya dai-dai tamu ya shiga lamuranmu yakuma tsaremu daga sharrin dukkan abinƙi sannan na shafa, kana na ɗauki carbi na soma gabatar da azkar ɗina na yamma bayan na idar nai lazumin _Hasbinallahu wani'imal wakil_wanda nake yinsa kullum safe da yamma sabida ba ƙaramin kariya hasbinallahu ke bawa ɗan adam ba, kana na karanta sunayen ALLAH guda99 sannan na karanta _lahaula_ har ƙarshenta itama da adadinta dana ke kamar _Hasbinallahu_ shafawa nayi sannan na koma ƙasan carpet na zauna tare dajan flate ɗin gabana domin na ɗan sakama cikina wani abun domin yunwar da gaske ta soma kawon cafka.
Shinkafa ce da miya wadda taji nama sabida miyar a saman abincin aka zubomin, ɗan tura bakina nayi gaba kaɗan tare da rufewa, sabida nikam ko kaɗan shinkafa bata cikin jerin abincina, miƙewa nayi tare da ɗaukar flate ɗin na fita kaina tsaye kicin ɗinmu karami dake falo na nufa.






Ya jima yana baccinsa cikin jin daɗi da nutsuwa bai farkaba seda yaji phone ɗinshi tana doka ringing! cikin lumshewar idanu irin na wanda bacci yagama cin ƙarfinsa ya ɗauki wayar batare daya duba sunan ba ya kara a saman kunnensa.
Muryar Rahina itace ta karaɗe cikin wayar"Hellow my prince"........"hmmmmm" kawai ya iya faɗi tare da mirginawa yana sakin numfashin bacci, "Yanxu tsakani da ALLAH kayimin adalci kenan? tun ranar danaxo maka ta'aziya baka yarda na kuma ganinka ba gashi gobe nikeson bin jirgi zuwa gida momcy tanata min waya, kuma kai kaƙi zuwa idan kuma ni nace zanxo kaƙi". tafaɗa tana share hawayen zafin soyayyarsa wadda takejin ta kamar bugun zuciyarta.
Seda yagama jin ta bakinta sannan yaɗan juya kaɗan tare da furta"Am sorry rahina wallahi uzuri sun min yawa, amman insha ALLAH gobe zanzo kafin ki wuce am promise". yafaɗa tare da miƙewa baki ɗaya, yana jiyo sautin ihunta wanda yasan na farin cikin ganinsa ne goben, katse wayar yayi tare da wurgi da ita, kayan jikinsa ya rage ya faɗa bathroom wanka yayo tare da fitowa cikin rigar wanka, goge jikinsa yay tare da saka wata......................................................




White.shirt and black jean, mai laushi taje kwantacciyar sumar kansa yayi tare dayima kansa ɓarin turarurruka, masu ɗan banzan ƙamshi, komawa toilet yay ya ɗauro alwala tare da zira black ɗin takalmi mai buɗewar sama a ƙafafunsa ya fita yana zuba uban ƙamshi,masallaci ya nufa sabida jin anata kiran sallar magrib,bayan an idar tare suka jero da faisal wanda yake sauri sabida matarsa bata da lafiya a bakin farfajiya suka rabu dashi, shikam wajan baba waziri ya wuce, sun jima suna magana sannan ya fito domin zuwa ganin mameey wadda zasu wuce gombe a gobe.
Afalo ya tarar dasu harda ummi ga kayan abinci nan gabansu suna faman ci amman falon babu hayaniya sabida har yanxu akwai alhinin rasuwar ajikinsu.
Gaisawa sukai da ummi, wadda take riƙe da carbi a hannunta, sannan ya juya ya gaisar da mameey, ƙannensa ne suka gaisar dashi sannan ya zauna agefen ummi ya riƙo sadik yana tambayarsa yau yaje school? maganganu suke shida sadik ɗin yana biyewa shirmen yaron, sukuwa su mameey hankalinsu yana kan abincin dake gabansu suna ci, suna ƴan maganganunsu sama-sama.
Nikuwa abincin na aje asaman top ɗin kicin, sannan na kunna gas, rasama mizan ci nai mai ɗan sauƙi, dan haka na ɗora ruwan zafi a tukunya, taliya na fasa na zuba bayan ya tafasa, mintuna masu dama na ɗauka a tsaye ina jiran ta dahu seda na tabbatar ta dahun............... sannan na sauketa na kashe gas ɗin.


sannan na taceta kana na zuba a flate na ɗan tsiyaya mata manja,maggi star na zuba asamanta batare dana zuba yaji ba na ɗauki robar yajin baki ɗaya na fito, kaina daman ko ɗan kwali babu dagani se doguwar riga sabida duk banyi zaton zanga kowa a falonba, amman sedai me ina fitowa naga su mameey zaune a falo suna cin abinci da kallo ummi ta bini bayan nayi masu sannu zan wuce ɗaki"Malama ajemin robar yajin nan tunda kin gama ƙuncin baxa kici yaji kizo kina hanamu bacci ba" turo bakina nayi gashi babu damaryin musu ga mameey a wajan danni sam bamma kula dashi ba"Dan ALLAH ummi ki barni ni bana son miyar wallahi" nafaɗa ina kauda kaina gefe"Aikuwa bazaki ciba nagaya miki" cikin jin haushi nai ɗakina bayan na aje mata taliyar agabanta batare dana tafi da itaba"Meema zonan" naji muryar ummi waigowa nayi ashe babu mameey awajan ta miƙe tun ɗaxu tana waya, "Ɗaukemin taliyar nan agabana ki wuce kicinyen ita" tafaɗa babu walwala akan fuskarta ɗauka nai nayi ɗakin da ita dan haushi ko ƙofar ban rufeba na aje taliyar a ƙasa tare da xama a gefen gado na xabga tagumi.
Wasa yakema sadik amman hankalinsa yana wajanta yasan bazata ci wannan abincin ba sanin hali yafi sanin kama"Ummi kiyi haƙuri ki bani yajin nan na kai mata ɗan kaɗan zata saka kinji ummi" yafaɗa kamar ze kuka!.
Mamakine ya kama ummi"Yanxu kai da kanka kake bata goyon bayan cin yaji? to wallahi babu ruwana kai zakai jigilar matarka" ummi tafaɗa tana miƙewa daga wajan.
Suma su hassana kwashe kwanu kan wajan sukai tare da nufar kicin.
Ɗaukar robar yajin yayi tare da nufar ɗakinta zuciyarsa tana dokawa haka zalika jikinsa yana karɓar wani irin sanyi.
Ƙarar tura kofar kawai naji, saurin jiyowa nai bakinsa kawai nagani ya motsa alamun sallama amman nikam bayan nan banji komai ba.
Baƙaramin kyau yaymin ba cikin ƙananun kayan daya saka wanda suka karɓesa sosai.
Tuno gargaɗinsa gareni yasa na kama kaina tare da juya masa baya.

"Asmi"! yafaɗa cikin kwantar da murya ban jiyo ba kuma bam amsa mashi ba, dirar tattausan hannunsa danaji agadon bayana shiyasani saurin rintse idanuna.
"Kinsan banson nai magana ai min shuru ko?" yafaɗa tare da ƙarasowa gabana tsugunne yay agaban nawa tare da tsireni da ido.
Bayan ya ɗago face ɗina da hannunsa haɗe raina nayi sosai batare dana tanka masa ba, robar yajin ya ɗauko tare da ajemin a saman cinyata.
"Gashi nan saura kicishi kamar nama babu ruwan wani" yafaɗa cikin kwantar da murya kamar batasa ba se a sannan na ɗago da kaina nai masa kallo ɗaya"kamayar kawai nagode" nafaɗa ina kokarin jiyowa saurin dafa min cinya yayi tare da miƙewa ya zauna gefena yana fuskantata"Baƙin cikin auren kike naga idanunki kamar kinyi kuka?" yafaɗa a wannan karon face ɗinsa babu far,a ko kaɗan.
"Eh!"...........Amsar dana basa kenan tare da.........
7/8/21, 1:34 PM - Buhainat: *DZ*



61-62


Tare da kawar da kaina can gefe sabida yadda ya tsareni da mayun idanuwansa, saukar hannunsa naji a haɓata ɗagota yayi tare da ƙuramin idanu yajima yana kallona batare daya tankamin ba.
"Ki dubeni da kyau sannan ki kuma faɗin cewar bakya farin ciki da auren da mukai" yafaɗi maganar agalabaice cikin wani irin yanayi nake ƙoƙarin kauda fuskata gefe domin bazan juri wannan ɗan iskan kallon dayake min ba wanda gaf yake daya ɗaukemin numfashina baki ɗaya.
Ɗigar hawayenta ne ya saukar masa a tsakiyar tafin hannunsa sosai ya kuma matsawa jikinta har jikinsu yana gugan na juna.
Ɗago fuskata yay tare da kurani da idanunsa"Asmi kukan mi kikeyi sabida bakya sona yanxu nayi maki wani abunne?" yafaɗa min hakan muryarsa tana rawa tamkar shima zeyi kukan! tura bakina nayi gaba kaɗan cikin muryata datayi ƙasa sosai na fara magana "Ka manta abinda kace min cemin fa kai ballagaza, budurwarka tafini komai sannan kuma kazo ka auri rahina duka ace bazanji haushi ba sekace ba mace ba" nafaɗi maganar cikin ƙunar raina.......mamakin darunta yake sam ya fuskanci meema irin matan nan ne masu rigimar tsiya da zafin kishi amman seya kwantar da kansa tare da furta"Ki ɗauki aurena da rahina a matsayin ƙaddara wannan kuma maganar ƴammatana ki ɗauka kamar shirin film ne domin kuwa basa gabana, wannan ne dalilin ƙuncin naki maza ɗauki abincin ki kici kinji ƴammatana" yafaɗi maganar yana kai hannayensa gadon bayana tare da jawoni jikinsa ya rungumeni tsam yana sakin numfashi da sauri-sauri tamkar ze mayar dani cikinsa, mutsu mutsu na somayi ina niman ƙwace kaina domin ni sam banji daɗin wannan runguma ba sekace ze rabani biyu, shikuwa anasa ɓangaren wata iriyar nutsuwa yakeji atare dashi tunda yake baitaɓa jin farin ciki kamar na yau ba, kuma bai taɓajin nishaɗi kamar nayau ba tabbas ya yarda so makahon zuci ne baitaɓa tunanin akwai macen dazata kai asma'u soyuwa aransa ba, haka xalika bayajin kowace mace tamkarta, kwantar da kaina yayi sosai asaman kirjinsa yana yamutsamin sumar datake kaina duk ƙamshin mayen turarensa yagama cikamin hancina lumshe idanuna nayi tare da waresu asaman kirjinsa inajin yadda gashin gemunsa ki tsikarar min fuskata, ɗagoni yayi tare da janyo pillow ya kwantar dani a saman gadon, lumshe idanuna nayi duk jikina yayi wani irin sanyi gabana yana faɗuwa inajinsa adukkan sassan jikina ina jin sonsa tamkar bugun numfashina idanuna har wani ruwane ya kwanta sabida maitar soyayyarsa araina, ban gama wannan tunani ba kuma banyi aune ba, naji numfashinsa adai dai saitin kunnuwa, buɗe idanuwan nawa nayi tare da zuba masa su, rankwaɓowa yayi saman ruwan cikina sedai bai idda haɗa jikina dana saba sedai yadda mukai gab dashi ya bawa numfashinmu damar haɗewa waje guda yana bada wani irin ƙamshi mai shiga jiki.
Magana yake son mata amman duk yadda yake ƙoƙarin kokawa da numfashinsa ya gaza furta mata komai secan ya fisgi maganar kamar an masa dole"Asmi dan ALLAH badan niba kada kikuma nesanta min kanki da ruhina da gangar jikina a wannan karon idan kika gujeni xaki rasani, ina sonki ina kishinki bantaɓa haɗa soyayyar wata ɗiya mace dataki ba" yafaɗi maganar cikin rawar murya wadda kusan sauran kaɗan ya saki kuka! jawo numfashi nake a hankali ahankali duk nabi na zaro idanuna waje jinake kamar acemin ket na arce saboda nifa yagama bani tsoro domin tabbas wannan murɗaɗɗan jikin nasa idan ya kwantomin sena suma, cikin rawar murya wadda ta haɗemin da kukan shagwaɓa nace"ni dai dan ALLAH ka matsa kada ka faɗomin akaina wallahi nagaji" nafaɗi maganar...........A
rabe kamar zanyi kuka, ɗan kwanto da kansa yay kaɗan adai dai saitin kirjina yana sakin wani irin zazzafan numfashi gogamin kwantaccen sajen dake zagaye da fuskarsa yay kaɗan tare da fesamin wani irin zazzafan numfashi, wata miƙa nayi kaɗan ina lumshe idanuna banƙi mu dawwama ahakaba tabbas! masoyi daɗi gareshi tura masa bakina nayi gaba"Ina sonka Mijina yayana dan ALLAH kada ka kula kowacce mace wallahi hatta su adda sakina na haramta maka kulasu akanka zan iya yin abin da baici ace nayisa ba, mudauki ƙaddarar cewa aurena dakai a farko ALLAH bai ƙaddara ba, se yanzu lokacin namu yayi dan haka mu yada dukkan komai mu rungumi junanmu da amana" nafaɗi maganar cikin dauriya tamkar bani ba.
Cikin wani irin yanayi naji daɗin kalamanta yake kusanto bakinsa dai dai kan nata,.............banyi aune ba naji tudun lip's ɗinsa masu ɗan karen taushi da ƙamshi asaman nawa, yana gogamin su kaɗan, tare da kwantowa baki ɗaya yay min rumfa da faffaɗan kirjinsa hannunsa gaba ɗaya ya saka a saman bayana ya ɗagoni baki ɗaya ya haɗeni da jikinsa sosai yake zagaye saman lip's ɗina dana sa, cikin wani irin salo ya haɗe bakina dana sa waje guda yana faman juyawa tamkar ya sami cwt faɗin yanayin yadda yake sarrafa bakina yana min wani irin kissing ma ɓata bakine, baki ɗaya mungama shagala yamanta cewar a part ɗin ummi muke, burinmu mu farantawa junanmu rai burinmu mu jiyarwa kanmu daɗin damuka azabtar da junan mu na tsawon shekaru, cikin wani irin birgitaccen salo ya xaro da harshensa daga cikin bakina ya dirasa asaman kirjina fatar wajan yaɗan ja da bakinsa kaɗan, wani irin zillo nai tare da lumshe idanuna ina faman sauke numfashi akai akai.
Ɗora kansa yayi asaman wajan batare dayamin komai ba illah zazzafan numfashin dayake sakarmin tamkar mai cutar asma.
Ruwan hawayensa naji asaman kirjina wanda harya sauka zuwa cikin rigata cikin sauri na ɗan ɗago kaina kaɗan tare da ɗora hannuna a saman tulin sumar kansa, batare danace masa komi ba amman tabbas hankalina ya tashi ganin hawaye a saman fuskarsa, bani da bakin magana sabida a halin danake ciki a wannan lokacin sam bazan iya magana ba, ya jima yana hawaye kafin ya ɗagani muryarsa can ƙasan maƙoshi ya furta"Asmi ki rikeni amana ina sonki ina hawayen farin cikin samunki ne" yafaɗi maganar agalabaice tare da ƙara janyoni na kuma faɗawa saman kansa, ya rungumeni tsam yana mayar da numfashi, ɗagani yay tare da manna min kiss a saman kirjina wajan dana shanuna yaɗan fito kaɗan sannan ya aje ƙafafunsa a ƙasan carpet ya miƙe tsam daga saman gadon, hannayen sa ya zube a cikin aljihunsa, "Ki ɗauki abincin kici konaje nai maki take away" yafaɗa yana ɗagemin gira, duk yanajin kansa wani iri wanda yazama dole yabar ɗakin sabida kada yay taɓar gaza.
Girgiza masa kaina kawai nai tare da sunkuyowa na ɗauki flate ɗin dannima nafison ya fita dan kar muyi abin kunya, sannan na ɗago na dubesa"Seda safe" nafaɗa kaina ƙasa murmushi ya saki har sautinsa yana fita a fili"Korata ake wato" yafaɗa yana dariya nima dariyar nai kaɗan tare da kauda kaina ina ɗiban taliyar wadda tama somayin sanyi, "ALLAH yabamu alkairi ƴar sugar!ki kulamin da kanki sosai konazo mu kwanta tare?" yafaɗa cikin zolaya bai kuma tsaya jinta bakina ba ya fice da sauri,"Ƴar sugar"! na kuma nanata abinda yafaɗa ɗin dariya nayi tare da ɗiban taliyar nakai bakina duk inajin yanayin jikina ya sauyawa wanda yasa dole seda nai wanka bayan na gama cin taliyar, kwanciya nayi inajin wata irin kewarsa adukkan sassan jikina.
Koda ya fita daga ɗakinta babu kowa a falon hakan bakaramin daɗi ya masa ba, dan haka kai tsaye part ɗinsa ya nufa, tare dajin wani irin feeling ɗinta yana taso masa wanda seda ya haɗa dashan zazzafan tea yay wanka sannan ya sami sauƙi, alwala yay tare da hawa kan darduma ya soma gabatar da sallar isha'in dayay missing bayan ya idar yay nafilolin sa sannan ya haye saman gado yaja pillow ya kwanta.
Washe gari tundaga sallar asubahi bai koma ɗaki ba bayan gaisar da iyayensa dayay part ɗin ummi ya wuce domin yay sallama da mameey wadda zata koma a yau, bayan sun gaisa da mameey wadda take ɗaki tana haɗa kaya, zamewa yay zuwa ɗakin meema wadda ya tarar da ita tana bacci akan sallaya, ɗagata yay tsam ya ɗora bisa gado tare da rufeta da blanket ya manna mata kiss a goshi kana yabar ɗakin, wajan ummi ya nufa suka gaisa lokacin harsu mameey sun fito da kayansu wanda driver keta jida yana kaisu cikin siyanar daze jasu acikinta, har waje suka rakasu mameey wanda mameey taso meema ta farka dan suyi sallama kafin taje amman hakan bai yuwu ba seda yaga tashin motarsu sannan ya koma part ɗinsa domin ya ɗan kwanta.


Ban farkaba se wajan 8:00am zaro ido nai waje ganin na makara a school a gurguje nai wanka na saka after tare da ɗan mayafinta nayi ɗakin ummi tana wanka ganin zanci lokaci yasa nai mata note: a ƴar pepper na wuce ko break banyi ba ban ɗauki motaba ta ƙofar baya nabi na tari napep seda nai nisa na tuna ban ɗauki phone ɗina ba haka muka ɗauki hanyar school ɗinmu...................
7/8/21, 4:10 PM - Buhainat: *DZ*

_63-64_

Tafiyar mintuna masu ɗan dama yakaimu school, a bakin gate na dakatar da mai napep ɗin gudar dubu ɗaya na xaro daga cikin back ɗita sabuwa dal na miƙa masa, ban tsaya jin tabakinsa ba na wuce cikin sauri, sabida naga time yanata faman ja, "Hajiya kin manta sauran canjinki fa" naji maganar mai napep ɗin adai dai saitin bayana yana faman haki da alamun guduma yay kafin ya cin mani, juyowa nayi kaɗan batare dana tsayaba"A,a kaje dasu na baka" ban tsaya jin irin godiyar dayake min ba nacigaba da tafiyata, cikin sauri na ƙarasa cikin lecture holl, ɗin namu wanda yau yay wata irinyar cika tamkar za,a  fashe wasuma har a wajan bakin kofar sabida sanin kowane malamin daze mana lecture yau bayada sauƙi ko kaɗan.
Nazo gaf da inda na hango su ayshert naji muryar wani guy adai dai saitin bayana yanawa ɗayan na gefensa magana"Kai baba kaga kaya kuwa acan" yafaɗa yana nuno bayana wanda yasakani cikin sauri nai wajansu ayshert na zauna, abin mamaki suma duka kallona naga sunayi kasancewar holl ɗin namu akwai surutu sabida malamin bai isoba hapcy ce ta dubeni tana dariya"Amarya munji abin arziƙi daga bakin safiya cousin ɗinki ALLAH dai yayi ubangiji ya baku zaman lafiya sannan kuma sekin dage sabida kinsan wa kika aura" ɗan haɗe raina nai kaɗan jin kalaminta na karshe "Kamar yaya kuna nufin meye ne  na aura?" nakai maganar cikin zafin rai, dariya suka saki sannan hapcy ta dubeni da kyau"Ina nufin wannan shigar da kikai ko kina budurwa bakiyita ba wallahi har shatin pant ɗinki ana hangowa", tana karasawa ayshert ta cafka itama "ni ai imanine ya cikamin zuciyata kinsan ALLAH komai naki is free ana hango sa" nan da nan naji duk na tsargu da kallo nabi hapcy tare da marairaice mata"Wallahi nima ban san haka na fito ba seda nazo giftawa naji waɗancan mazan nayi dani amman bara mu fita sena ari hijabin ki" duka sunyi na'am da maganata sabida sun san shigar banza is not my habit, haka mukai xaman mintuna biyar kafin malamin namu ya shigo hol ɗin ya sami yin shuru.

Cikin baccinsa yaji wayansa tana faman doka ringing! lalubarta yay ya ɗaga tare da karawa a kunnensa"Hellow my prince na kusan  nufar airport wallahi kai nike jira" cewar rahina kenan wadda tagama cin kwalliya cikin tsadaddun english weares masu tsananin kyau, mirginawa yay kaɗan tare da miƙewa shikansa yasan abinda ya mata bai kyautuba,"Pls kiyi hakuri insha ALLAH kiduba hanyata pls send me your address", cikin mintunan da basu gaza biyu ba ta tura masa da address ɗin hotel ɗin datake harma da room number, idanunsa ya ɗaga ya duba agogon dake manne da bangon ɗakin nasa, wajan 11 na safiya, cikin sauri ya watsa ruwa ajikinsa black armless ya saka tare da army threaquater.


Trouzer Jeans, sayay amfani da p.cap itama army, wanda shigar baƙaramin kyau tai masaba, kasancewar yanayin garin ana ɗan xafi kaɗan shikuma ya saba rayuwar,  turai ko ina sanyi, black snakers  ya saka a ƙafafunsa ya ɗaure tamkar zaije filin training idan ka dubi damtsen hannunsa har wani murɗuwa sukai sabida ƙoshin da sukai a wajan motsa jiki.
Direct wajan parking space ya nufa sabida bai son shiga wajan hajja ta ɓata masa lokaci yafison yaje ya sallami waccan yarinyar tukunna, gashi kuma baison zuwa part ɗin ummi a haka sabida kunyarta yakeji, sedai kuma zuciyarsa tana azal xalarsa dayaga ruhinsa, kota miƙe daga baccin oho, ganin ze azabtune da hakan yasa ya juya da baya zuwa ɗakinsa black jacket ya ɗora asaman armless ɗin jikin nasa tare da nufar part ɗin ummi dukkan bayin part ɗin suna zubewa suna gaisar dashi,har ɗaki ya tarar da ummi bayan yay sallama xaune take akan sopa tana duba wani littafin addini, sosa sumar kansa yay tare da tambayarta ina meema, yana wasa da p.cap ɗin dake hannunsa wadda bai riga ya sakata ba, da kallo ummi ta bishi tare da cewa"Au bata gaya maka tana da morning lecture ba?" cikin matsanan cin mamaki ya dubi ummi wadda take miƙo masa ƴar papper da meema ta aje mata lokacin datana toilet, karɓa yay tare da ƙura mata idanu _Ummina nafita school yau muna da morning lecture ki ajemin break zan dawo around 12_ abunda ya gani kenan yana nazarin yanayin tsarin kyan rubutunta.
Shafa saman kansa yay tare da miƙewa batare daya cewa ummi komai ba but amman dif down na zuciyarsa yana jin zafin yadda ta maidashi sakaran namiji, to idan ba sakarai ta maidashi ba tayaya yana aurenta amman ta fita batare data nemi izininsa ba"Bata gaya maka bane?" Ummi ta faɗa tana nazartar sa"Eh bata gayamin ba" yabata amsa kansa tsaye sabida shi mutum ne sak wanda baya ɓoye-ɓoye acikin lamuransa.
"Gaskiya bai kyautu ba hakan ni ai ban saniba amman kai haƙuri zan mata faɗa insha ALLAH" Cewar ummi wadda taji babu daɗin abinda ƴar tata tai daman tasan yanzu dole setai da gaske wajan nusar da meema akan wasu abubuwan na zamantakewar aure waɗanda bata san dasu ba, "Babu komai fa ummi nima xan ɗan fita ne amman ƙila naje school ɗin nasu madawo tare" yafaɗa yana nufar hanyar fita daga cikin ɗakin wanda ummi ke rakashi da addu,a aranta tana jin kewar rahinar ta amman idan ta dubi meema tana jin kaso biyar daga cikin goma na damuwarta ya ragu gakuma farin cikin aurenta da Abdul wanda ummi taji ta gamsu da auren nasu yadda ba,a zato.
Cikin sauri ya nufi cikin wata baƙar accourd mai baƙin glass, kansa tsaye rivers yay tare da nufar gate wanda babu ɓata lokaci dogaran dake tsaron gate ɗin sunka buɗe masa shi ya fice a miliyan, burinsa

Please Login or Register in order to submit comment