Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta soma ringin sunan rahina abu umar ne ya bayyana ƙarara a saman screen ɗin wayan tasa da harya juya baze ɗaukaba amman ganin danshi tazo ƙasar yaga dacewar ya ɗaga domin ya bata kulawa a amatsayinta na baƙuwarsa kara wayar yay a kunnensa, "Hellow ya kike?" daga nata ɓangaren lumshe idanun ta tai tare da janyo pillow ta matse a tsakanin ƙafafunta ɗaya kuma ta ɗora a saman kanta tare da daɗa limshewa a tsakiyar katafaren gadon hotel ɗin kana tace"Ba lafiya ba tunda bana tare da sanyin raina" tafaɗi maganar dawani irin salo mai narkar da zuciya, ko kaɗan kalaman nata bai burgeshiba haka zalika narkar da muryar datai bai saka yaji komai ba domin seda so akejij feeling, bare shida baya cikin kwanciyar hankali tayaya zeji wani feeling, "ALLAH sarki sannu fa" yafaɗa cikin sigar rainin hankali, sannu fa! ta mai maita acikin ranta cije bakinta tai tare da furta masa"Haba my prince danfa kai nazo yaya xaka cemin sannu ciwo nayi"tafaɗa cikin rashin jin daɗi,"To me kikeso nace maki?" yafaɗa yana rufe idanunsa dan bacci yakeji sosai, tare da kuma buɗesu tar wanda lokacin yay dai dai da buɗewar idanun meema tana kallon saman ɗakin.
Kukan shagwaɓa ta soma rera masa tana haɗawa da kirsa tare da jan hankalinsa, sam arayuwarsa yatsani kukan mace yana saka yaji rauni gami da tashin hankali, cikin sauri ya soma mata magana"Kinga kiyi shuru kaina yanzu baya ɗaukar wannan baki ganin ina cikin halin rashin matata, kiyi shuru kizo gobe da wuri ki ganni yayi miki hakan" yafaɗa a rarrabe cikin rashin sabo,
"Kizo da wuri ki ganni yayi maki hakan"!nafaɗa a fili tare da saurin kallo wajan dayake kishingiɗe, jikinsa sanye da singlet ilahirin surarsa ta karfafan maza ta bayyana gawani irin baƙin kwantaccen gashi a saman kirjinsa, yayi wani irin haske tare da sheƙi ladanin dake tsakiyar goshinsa na sallah ya ƙara wani irin duhu, babu alamun wani matsala a tare dashi, wayarsa yake hankali kwance wanda na rantse da ALLAH da budurwa yakeyinta, wani irin tuƙuƙin duhun haushin sa naji ya turniƙeni idanuna har wani irin huci yake irin na masifa, tayaya yau matarka ta sunna ta rasu amman kazo kana waya da wata mahaukaciya jakar mata kucaka, na rantse tazo gidanmu gobe sena ƙonata.
Nafaɗa cikin raina jikina har wani irin rawa yake, yunƙurin tashi nake ammman daga na miƙe sena koma sabida wani azaba da ƙuguna kemin, wani irin kuka na saki mai sauti tare da komawa na kwanta, cikin sauri ya yarda wayan hannunsa daman kuma sunyi sallama tare da nufo gadon datake duk yay tunanin wani abunne ya sameta, a tsorace yakai hannunsa jikinta da zummar ɗagota, cikin zafin rai na make masa hannun tare da fisgewa "Ni ka matsa wallahi ka matsamin akaina bana son ganinka mugu azzalumi" nafaɗa ina gunjin kuka, cikin amincin ALLAH kuma cak na mike hannuna bisa ƙuguna na bangajesa ina kokarin wucewa na fita taku ɗaya biyu na zube aƙasa sabida yadda wajan kemin zafi, kuka nake ina turjiya a ƙasan carpet tamkar mai hawan iskoki.
Ganin zata tara masa jama'a tunda darene sound ya soma ɗaukewa yasa ya miƙe daga gefen gadon, duk tunaninsa bugun ɗazu daya mata dakuma zafin rasuwar rahina ya sakata yin wannan haukan, dan haka seya ja ƙafafunsa zuwa gabanta still yana try ƙara kai hannunsa jikinta.
Bige hannunsa na kumayi a zafafe na miƙe zaune ilahirin jikina yana mazari na kalleshi da manyan idanuna waɗanda sukai wata shegiyar kaɗawa tamkar gaushin wuta"Kada ka kuma yunƙurin kai wannan ƙazamin hannun naka jikina wallahi zakai nadama, mayaudari mu......" ban kaiba ya bigemin bakina da hannunsa,Jikinsa yana wani irin rawa ya dubeni"Asma'u! miye haɗina dake zakina gayamin waɗannan munanan kalaman, ni sa'anki ne miya ruwana dake?" yafaɗa cikin tsawa tare da yowa kaina kamar ze dukeni, kuka nake saki ina jada baya harna ida jikin gadon daya kareni"wallahi kai mayaudarine kuma mugu kuma.....kuma....kuma....ALLAH ze sakawa Rahina, tayaya yau matarka ta sunna ta rasu amman ka zauna kana waya kaida wata!" nafaɗa cikin zafin rai"wallahi kama gaya mata bama nemanta acikin wannan masarauta tabbas idan harta kuskura tazo wallahi sena nakasa ta dan kutumar ubanta kowace dabbace jaka ballagaza marar........". ban ƙarasaba ya kuma kaimin maka da gefen hannunsa, wanda ya sakani yin shuru ina sosa bakina saboda zafin dayake min,. se asannan tunaninsa ya kaisa ashe duk wannan abin datake wayar dataji yanayi ne da rahina, murmushin gefen baki ya saki tare da miƙewa tsaye yana jifana da wani irin kallo na ƙasan idanu,"To ita kuma budurwar tawa ina ruwanki da ita kodai har yau kina sonane anty na?" yafaɗa yana jifana da wani irin kallo,"ALLAH ya suturta na aureka ko mazan kano sun ƙare, kawai dai naga rashin dacewar hakanne" nafaɗa ina goge hawayena"kishina kike ko tuhumata kike yanzu kinbar layin ƴan zargina kin koma na kishi?" yafaɗa yana murmushin dole"ALLAH yay min tsari" abin da na basa amsa kenan"To shish shigi yakaiki inda ba,a gayyaceki ba ko akan mace zaki ganni miya ruwanki wannan ai saka idone" kuka na saka wanda yazomin babu shiri"Ai wallahi nafi ƙarfin nai shishshigi akan ɗan uwana kuma mijin ƙanwata kawai ina jin takaicin cin amanar dakama rahina ne" dariyace taso kufce masa amman seya kanne tare da ɗan matsoni kaɗan"To Alhamdulillahi nagode! ƙanwata kuma indai dan rahina ne kwantar da hankalinki wannan ma sunan ta kenan kuma zata ɗaukeki kamar yaya insha ALLAH", Yafaɗamin tare da barin wajan yana kokarin fita daga ɗakin baki ɗaya, wani irin miƙewa nayi tare da bin bayansa aguje hannayena duka biyun na ɗora a saman gadon bayansa tare da ɗaneshi kana na zagaye ƙugunsa da ɗayan hannun nawa, bayan na sauke daga bayan nasa, ɗayan kuma na riƙe sa tamau ina sakin wani marayan kukan rashin makama, baki ɗaya nagama sakar masa da nauyin jikina asaman bayansa, jijjigasa nake da iyakacin ƙarfina amman shiko ko gezau, kuka nake ina faɗin"Dan ALLAH kada kaiwa Rahina haka, wallahi kowacce shegiyace tai gigin shiga gonar rahinata wallahi zan iya yi mata muguwar illah" nafaɗa tamkar zararra ina sakin wani irin kuka wanda hatta singlet ɗinsa seda ta jiƙe da hawayena sabida yadda suke gudu tamkar famfo.
Yanajin ɗigar hawayenta tamkar saukar dalma acikin ruhinsa shi so baya ƙarya duk wanda yace maka so! daga baya yace maka ƙi! tofa sedai ɓacin rai, tabbas har yau har gobe matsayinta bai bar zuciyarsa ba yana mata mugun so marar adadi yana jinta fiye da zato acikin zuciyarsa da ruhinsa da kuma dukkan ilahirin jikinsa, koda ya auri rahina kawai ya karbeta ne a matsayin ƙaddararsa bai taɓa jin mace aransa kamar asmah ba, ko yanzu yay mata hakanne sabida takaicin wasu abubuwan data masa wanda ya barwa ransa ya kumayi alkawarin bata wahala da soyayyarsa a wannan lokacin, sekuma tunanin mai zeje ya dawo daga wajan magabatansa baya son ya zaƙe da yawa azo kuma aƙi masa madadi da ita a karo na biyu.
Da wani irin yanayi wanda yafi ƙarfin kan auta, yafi gaban kwatance ya jiyota gabansa, wanda tsayinta ko rabinsa bata kaiba, ya ɗora hannunsa adai dai ƙugunta wanda yaga ta rintse idanunta like wajan yana mata ciwo, baya da wata nutsuwar ruhin daya wuce yajita ajikinsa, riƙota yay baki ɗaya tare da bata kyakykyawan masauki acikin kirjinsa, wanda ita kanta seda ta sauke wata iriyar ajiyar zuciya.
Hannayensa ya sauke agadon bayanta yana shafa mata su tundaga tsakiyar bayanta har zuwa, dai dai kwankwasonta, yanajin wani irin nutsuwa agame da ita, yanajin yadda take sauke ajiyar zuciya tare da zazzafan numfashi amman kuma tai luff ajikin nasa wanda daga gani itama ta amintu da wannan rungumar daya mata.
Lumshe idanunsa yay tare dajin dukkan girman ɗakin yay masu kaɗan baiƙi su dawwa ma a hakaba, tabbas ya yarda adukkan mata babu mace mai masa son da ma'u ke masa illah ita kawai wannan izzar data nuna masa tun farko ita tai masu cikas amman harga ransa ya yarda tana masa mahaukacin so mai tafe da zazzafan kishin dashi kansa yana tsoron randa xatai ido huɗu da rahina domin tabbas baya kaunar wannan rana sabida sanin halinta tsaf zata iya jamasa magana, lumshe idanunsa yake tare da kokarin rabata da jikinsa sabida yadda yaji mood ɗinsa na niman sauya akala.
Ɗagota yay cak gami da nufar falonsa da ita a tsaye ya jinginar da ita yana binta da idanu tare da haɗe ransa tamau kamar bai taɓa dariya ba,
Ganin ya fitar dani falo tare da tsareni da idanu yana hukuntani dasu yasa nasha jinin jikina ina sada kaina a ƙasa"Kije part ɗin hajiya ki kwanta tunda dare yayi no need kitafi na ummi and kuma kada ki kuma gigin rungumata danni yanxu bakya gabana babu abinda zanyi dake daga yau babuni babuke kuma ko budurwata tazo wallahi ko ciwon kai tai senai shari'a dake wawayi kawai marar aji" yafaɗa tare da tureni kaɗan yay bedroom ɗinsa.
Najima ina nanata maganganunsa acikin raina, tsam kuma na mike ina ɗingishi jikina duka yay sanyi na mike na fita falon hajja na nufa tare da raɓawa cikin ɗakinta can karshen gado kusada mutane naje na kwanta ina aro jarumta tare da rintse idanuna ina auna dukkan maganganunsa.
Cikin sauri kuma na miƙe naje toilet ɗinta nayo alwala tare da tayar da sallah najima ina ramuwar sallar dasuke kaina kafin na mike banajin sha,awar ko ruwa haka na kwanta zuciyata dauke da tunanin maganganunsa dasuka dirarmin a ƙirjina suka ƙi tafiya, wani irin sanyin jiki dana zuciya ne suka tarar min lokaci guda............






*DA IZZATA*
7/5/21, 7:26 AM - Buhainat: *DZ*


56-57


Najima ina malelekuwa asaman gado wanda harna kusadani ƴaƴan ƙanwar babanmu yakumbo rabi'a waɗanda sukazo tunkafin rasuwa daga abuja sukaso farkawa, ataƙaice dai se bacci ɓarawo, ban sami tashiba seda asubahi ina kuma yin sallah, nai azkar na koma bacci tare da ƙudundune jikina da ƙaton bargo saboda zazzafan zazzaɓin daya kawon cafka, inajin muryar hajja fulani sama-sama akaina tana cewa nabila ɗiyar yakumbo rabi,a ta uku"nabila kutashi ku komo ɗakin danake kar hayaniyarku ta tayar da asma'u wallahi yarinyar tausai take bani tin jiya an kasa gane kanta, yanzunnan mahaifiyarta ta aiko kanwarta dubata ashe bacci take" jin ɗakin shuru ya bani tabbacin sun fice aikuwa daɗa jan bargon nai banyi wani dogon yunƙuriba bacci mai daɗi ya kwasheni duk da jikina yana da zafi gau! na zazzaɓi.


Tunda ya shiga ɗakinsa yakejin ransa wasai baya da wata damuwa wadda ta wuce ta rashin rahina, abun kuma daya saka shi jin farin ciki shine hango tsabar rikicin soyayyarsa dayay a idanun ta,wadda yake azabtuwa da sonta, tabbas ya yarda asmi tana masa mugun so mai tattare da tsantsar kishinsa, kwanciya yay adai dai saitin data kwanta yana shaƙar ƙamshin humurar datake amfani da ita wadda ta kama masa blanket( macen data san kanta bata rabo da ƙamshi domin shima sirrine kuma daɗin martabane)lumshe idanunsa yay tare da ƙamƙame blanket ɗin tsam yana fesar da numfashi ,shi kaɗai yasan yadda yake jin feeling ɗinta dakuma yadda yay missing rigimarta.
Wayarsa dake yashe asaman sopa itake faman ƙara da ƙyar ya sauka yaje duba mai kiran, number oga james ce daga club ɗinsu.
Zama yay tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya( hohoho gado girman ALLAH sarautar ce ta motsa ) gaisawa sukai da oga james (cikin harshen turanci ) sannan oga james ya ƙara masa ta'aziya sannan ya ce masa nan da kwana uku, ƴan team ɗinsu zasuxo nan su masa gaisuwa, cikin jin daɗi ya amsawa oga james amman ya dakatar da zuwan nasu akan wasu dalilai nasa wanda daga ciki harda rashin son hayaniyar jama'a wanda idan harsuka farga da zuwan manyan super star na ƙwallon ƙafa wajansa tofa zasuyita cunkoson zuwa ganinsu ne abinda shikuma yanzu baya so kenan hayaniya dan shikansa ɓoye kansa yake yanzun.
Sun jima suna tattaunawa da oga james kafin daga ƙarshe sukai sallama, cikin sauri kuma oga james ya kuma kiransa a karo na biyu, seda ya ɗauka sannan oga james yake shaida masa akwai wani Gasa daza,a buga a tsakanin team's guda biyar nan da sati biyu masu zuwa kuma wasan big champion ne domin duk wanda yay nasarar lashe number ta ɗaya kota biyu kota uku baƙaramin lunƙume manyan daloli zeyiba, kuma ze shiga jerin cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafar ƙasarnan, anan oga james yake cemasa ribar abin shine harda club ɗinsu domin shine ya fito a jerin number ta biyu cikin wasan, kuma harda shi acikin waɗanda akai salecting domin shinema number na 3 kuma bawai dan bai iyaba aka bashi wannan number ba a,a sabida gudun jin haushin ragowar, kasancewarsa sabo a cikinsu.
Seda ya gama jin dukkan bayanin da oga james yay masa sannan yace"Naji dukkan maganganun ka amman sedai na baku haƙuri a wannan karon yina zeyi wuya sabida rasuwar matata gaskiya bazan sami damar fita wani wasaba"..........nan da nan hankalin oga james ya tashi ta cikin wayar gumi yana keto masa duk ya zata kowani club ɗinne suke farautar Abdul ɗin, sosai oga james ke lallaɓar Abdul yana kuma bashi baki tare da nuna masa mahimmancin wasan da irin nasarar daze samu harma da ɗaukaka, amman firr Abdul yaƙi yarda daga karshema cikin zafin rai ya datse wayar, yana mita, wanka yay tare da faɗawa gadonsa ya kwanta.
Shikuwa oga james yay alkawarin bazasuyi rashin Abdul ba idan ta kama ma har nan ɗin ze iya zuwa wajan baban Abdul ɗin da kansa ya rokeshi domin wannan harkar ta ƙaruwace dan ba daban Abdul ɗin bama baza,a saka club ɗinsu a jerin gasar ba.

Da asubahi yay wanka sannan ya shirya cikin milk ɗin boyel, harda hula wadda tai dai dai da kayan jikinsa tare dayima kansa ɓarin turare kana ya nufi masallaci koda ya idar da sallah wajan mai martaba ya nufa suka gaisa sannan yaje wajan mahaifinsa,ƴan uwan safiya matar mahaifinsa fall cikin ɓangaren haka ya wucesu zuwa wajan babansa sun jima suna maganganu kafin ya fito zuwa sashin hajja fulani, lokacin karfe bakwai na safiya gaigaisawa sukai da ƙannen mahaifansu mata waɗanda sukazo sannan ya ƙarasa wajan hajja, itama ya gaisa da ita, sannan ya miƙe zuwa sashen ummi lokacin har rana taɗan fara fitowa tunda ya fito bayi ke zubewa suna masa ta'aziya harya ƙarasa cikin falon ummi duk yana jin wata kunyar idanun jama,ar dasukai masa caa suna kallo.
Gaisawa sukai da yayyen ummi harma da ƙannenta sannan ya wuce bedroom ɗinta zaune ya risketa tana jan carbi jikinta sanye da hijabi, tsugunnawa yay ya gaisar da ita, cikin kulawa ummi ta amsa tare da yi masa ta'aziya, cikin sauri shima ya amshe yana mata tare da bata haƙurin rashin datayi, zama yay a ƙasan wajan ummi tana sama, suna ɗan hira sama sama ta halayen rahina har zuwa wani lokaci sannan yay mata sallama, ya nufi ɗakin da mameeyn sa ke ciki, sosai mamakin yawan ƴan uwan mameey dasuka zo ya bashi mamaki, tsugunnawa yay yana gaisar dasu sukuma suna masa ta,aziya kana ya nufi wajan mameey itama suka gaisa zama yay suna ɗan taɓa maganganu sannan mameey ta miƙe mintuna biyu tazo masa hannunta riƙe da kofin data cikosa da kunun gyaɗa miƙa masa tai "Maza sha kabani kofi" ganin fuskar mameey babu walwala yasa ya amsa ya shanye haka ta kuma cewa kanwarta taje ta zubo masa ƙosan da akai atakaice dai seda mameey taiwa ɗan nata ɗurar dole sannan ta sake suna hira yana tura mata baki, kamar ze saka ihu jin cikinsa na niman fashewa.
Dayake duk na cikin ɗakin sun koma falo saboda ganinsa da sukai dan haka ya sami damar sakewa da mameeyn tasa sosai.



Wajan ƙarfe goman safiya su hapcy da ƴan class ɗinsu meema suka zo cikin masarautar domin saƙon rasuwar da aka faɗa agidan redio tun jiya ya isar musu, a ɗakin ummi suka yada zango bayan ancika su da kayan karin kumallo, ummi ce ta tashi kanwarta taje ta kira meema har lokacin bata farkaba fafur hajja ta hana a tayar da ita seda su yakumbo suka saka baki sannan tabari aka tayar da ita.
Cikin baccina mai daɗi naga anty habiba akaina "Meema ki tashi kizo ƙawayenki sunzo" tafaɗa tare da ficewa daga ɗakin.
Murza idanuna nayi tare da tashi naja hijabina tare da zuwa toilet na zubda miyau sannan na fita waje duk idanuna ya kumbura na barci.
A falo na gaisar dasu yakumbo sannan na wuce koda naje sashen ummi jama,ane fall haka akaita min gaisuwa inajin wasuma nacewa ALLAH sarki itace ƴar uwar aida da ita za,ai ALLAH baiba, daga gefe naji wata tana aikuwa ƙila a mayar da ita ɗakin ƴar uwar tata nidai ban tanka ba haka naje ɗakin ummina gaisar da yayyen ummi nai tare da ita kanta sannan na koma wajansu hapcy muka gaisa sukaimin ta,aziya ina kallon yadda ummi ke faman kallona tai kalar tausayi, haka muka zauna dasu duk na koma wata shuru shuru abar tausayi.
Mikewa ayshert tai "Bara mu tafi school se ranar bakwai amman fa akwai text nan da kwana bakwai ɗin" duka sauran suka mike "Ki kaisu can ɗakin suwa mameeynku gaisuwa sesu tafi" cewar ummi, sallama sukaiwa ummi suka fita.
Ɗakin dake kusada dana ummi muka shiga gabana ke faɗuwa amman haka na daure muka gaisa da waɗanda nagani a falo sannan muka shiga bedroom ɗin, kaina sunkuye na karasa gabanta ganin Abdul zaune a gefenta kansa babu hula suna maganganu, jin sallamarmu bai sa ya ɗago ba sema wayarsa daya dauka yana dibawa, mameey muka gaisar sannan na gabatar mata dasu hapcy a matsayin abokan karatuna sannan sukai mata gaisuwa,ayshert ce ta soma gaisar dashi sannan hapcy da sauran kalma guda ce dai amsar tasa"Lafiya" Nikuwa ban yi gigin gaisar dashiba sabida mugun tsoron sa danaji ya dirarmin tun jiya akan abin dayamin.
Mintuna biyar mukai aɗakin muka mata sallama tare da ficewa,wajan hajja na kaisu suka gaisar da ita,a hanya naji hapcy tana faman zuzuta kyawunsa tare da shariyarsa nidai ban kula ba, har muka fito, wajan parking zan rakasu sesu fita ta baya saboda yawan mazan dake bakin fada, adai dai kwanar dazamu sha na gansa jingine da bango sam su hapcy basu kulaba, dan haka suka wuce nikuwa ina kokarin wucewa naga ya tare hanyar"Malama ki koma dan baki da hankali zaki ratse waɗancan mazan ki fita" ban iya tanka masa kuma banyi musuba najuya nabar wajan, mamakintane ya kamasa yau wace rana, Shikuwa yay hakanne sabida karasowar rahina domin tsoron haɗuwarsu yakeji da ita.
Koda na koma ɗakina na wuce na kwanta wani baccin tunda daman bai ishanba.
Ita kuwa rahina karasowa tai wajan Abdul jikinta sanye da ƙaton hijabin da shi kansa yay mamakin ganinta cikinsa wajan mameey ya kaita domin baze kaita wajan ummi ba ai abin zezama kamar cin fuskane, daman yaywa mameey bayaninta tun ɗazu bata sami wani sakin fuskaba wajan ƴan biyun mameey ma harara take samu bata wani jima ba ya kaita inda zata bi ta fita sukai sallama, akan idan yay free zexo su gaisa bai gigin kaita ko inaba mameey ma dan mahaifiyarsa ce zata masa uzuri shiyasa haka ya koma wajan zaman karbar gaisuwa daga wurare da dama.
Tsahon kwanaki shida ana karɓar gaisuwa daga wurare da dama kuma har yau rahina bata tafi ba, tana nan inda ta sauka tana mitar baizo sun gaisaba tayi kokarin zuwa wajansa a karo na biyu amman yaƙi gudun rigimar meema wadda ya kasa gane kanta sam tamaƙi yarda a yanzu yaganta ko waje yazo yanzu zata kwanta tai baccin karya, haka zalika bata yarda ko giftawa tai a inda yake wannan abin yana damunsa amman miskilancinsa ya hana kowa gane hakan.
Yau takama kwanaki bakwai da rasuwar rahina, babban masallacin dake cikin masarautar daula ya cika da manyan mutanen da sukazo daga wurare da dama wajan halartar ta,aziyar bakwan rahina bayan anyi addu,a ga rahina haka zalika kuma anyi sadaka.
Sarki abubakar ne yaɗan taɓo limamin masarauta na yanzu liman ne ya miƙe sannan ya ɗauki loud speaker ya soma magana kamar haka.
Bayan godiya ga ALLAH tare dayiwa rahina addu,ar samun rahamar ubangiji sannan ya ɗora da cewa........"A addinan ce ya halarta yaya ta maye gurbin ƙanwarta idan ALLAH ya ɗauki ranta kokuma kanwa ta maye gurbin yayarta idan ALLAH ya ɗauki ranta haka zalika ƙani ze iya auran matar yayansa, kamar yadda yayan ze iya auran matar ƙaninsa idan wani daga cikinsu baya raye. addini duk ya bada damar haka sabida addini mai sauƙine kuma nasiha ne ataƙaice kenan! dan haka wannan masarautaɗ mai adalci wadda Sarki Abubakar daula ke jagorantar ta cikin adalci, ya ƙara bawa ɗansa kuma ɗan ɗan uwansa ƴarsa a karo na biyu domin ta maye gurbin ƙanwarta. Maganganu ne suka fara tashi daga cikin masallacin tare da kabbara kafin kuma sarkin shela ya miƙe ya umarci kowa yay shuru.
Mintuna goma aka ɗauka acikin shurun kafin naji sautin maganar liman "AN ƊAURA AUREN ASMA'U ABUBKAR DAULA! DA ABDUL-NASEER ADAM ALIYU DAULA! akan sadaki mai daraja wanda mai martaba shiya zama waliyin ango shikuma wazirinsa ya zama waliyin amarya ALLAH ya bada zaman lafiya amin.
Kabbara mutanen ke faman saki tare da jinjina adalci irin na wannan sarki.

Tunda aka fara kansa ke sunkuye har aka ida, "Abdul Naseer ka tashi daga wannan zama yau Alƙawarin ALLAH ya cika akanku" cewar jabir kenan..........



*DA IZZATA*
7/5/21, 7:27 AM - Buhainat: *DZ*


58-59

_Assalamu Alaikum my fans wannan shine updated na gobe idan ALLAH ya kaimu domin bazan sami damaryi ba sabida uzurin bikin damuke yi sabida karkuji shuru yasa na hana idona barci na maku domin nasan kowa ya matsu yaji cakwakiyar dake gaba_


Muryar amininsa kuma ɗan uwansa kenan jabir wanda yanzu haka shi yana ƙasar indiya yana aikinsa tare da matarsa mabaruka wadda suke cewa ma!wannan rasuwar ce ma tasaka jabir aje tarin ayyukan dake gabansa ya tako ƙasarsa ta gado domin jimantawa aminin nasa rashin matarsa dayay dakuma tayashi yaƙin neman tsohuwar zumar sa, sekuma gashi ALLAH yasa komi yazo masu acikin sauƙi.
Shikuwa Abdul-Naseer murza idanunsa yake tare da ɗan dukan saman kansa kaɗan, anya da gaske kunnensa yaji dai-dai kuwa, kodai shigar sauri kunnen nasa yay masa wajan jin wannan kalaman da idan wanine ya gaya masa dafa tabbas ze iya mallaka masa komi nasa, daya mallaka batare dayaji koda ɗar aransa ba.
Ɗago kyakykyawar farar fuskarsa yay tare da zubawa jabir narkakkun idanuwansa yana kallonsa batare daya tanka ba secan kuma yace"Jabir dan ALLAH da gaske Asmi! yanzu Mallakina ce?" yafaɗa idanunsa suna ciko ruwa, kamar ze kuka abinda bai ba a rasuwar rahina amman jibi daga daura masa aure ze kukan murna lallai Abdul abin naka babba ne, ɗage masa gira ɗaya jabir yay tare da furta masa"Wallahi an ɗaura amman kabi gayyarsu baba kaji daga bakinsu" tunma kafin jabir ya ƙarasa maganarsa Abdul ya sunkuya tare dayin sujjada yana hawaye yana godewa ALLAH buwayi gagara misali mai kyautar da babu kamarta ALLAH kennan mai annabi muhammadu s.a.w., yajima yana godiya ga sarki ALLAH kafin ya ɗago yaja hannun jabir ya nufi waje dashi yana sakin murmushi.
Seda suka fita sannan ya saita kansa kana sukaje wajan su baba waziri sukai godiya kamar yadda al'adarsu take wajan hajja fulani suka nufa wadda itama kanta ta cika da murnar wannan lamari"Um nasiru kaga ikon ALLAH ko?" cewar hajja tana kallonsa yana kurɓar furar data rage wadda ada ko zatai me baze shataba amman yau dan tsabar murna ya dauketa ya shanye.
Lumshe idanunsa kawai yake tare dajin baccin daya jima baiba koyanzu ze bacci mai daɗi tunda ma'u tazama tasa, yakumbo ɗinsa suma haka suka sakasa a tsakiya suna masa tsiya shikam baya cewa komai harya zame yabarsu da jabir.
Tuno yadda take masa yanzu yasa yaji gabansa ya faɗi danshi yanxu kwanto ze ya nemi shiri domin bayajin yanzu ze lamunce tawani ƙarasa karatun ta gwara ya tarkata sunbar ƙasar baki ɗaya.
Part ɗinsa ya nufa yay kwanciyarsa a ɗakinsa tare da kashe wayoyinsa yanajin yau ze ramuwar baccin shekaru.


Acikin gida kuwa sosai sarkin shela kebin kowani lungu da saƙo yana shaida cewar "Jama'a yaufa alƙawarin ALLAH ya cika an ɗaura auren gimbiyar mata asama'u da jaruminta Abdul-Naseeru" har wannan saƙon yaje ga part ɗin ummi wadda ta daskare awajan, sam amman mai martaba ya shammaceta fatan alkairi tai a

Please Login or Register in order to submit comment