Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin naji ya kece da wata mahaukaciyar dariya, se alokacin na sami damar kallon fuskokin waɗannan mata, jikina har yana rawa wajan kallon fulani umma, matar sarki kishiyar ummi gefenta kuma safiya ce matar baban Abdul - Naseer, dariyar wannan baƙin matsafin ita ta saka na koma dai dai, cikin zarewar jan idanu ya dubi fulani umma.
"kin ɓata mana aiki naja'atu! kin ɓata mana aiki naja'atu shekaru 22 da suka wuce kinsan aikina baya son haɗi dana kowa meya dawo dake wajena bayan kin gujeni?" rawar baki fulani umma ta somayi tare da basa hakuri kamar xata ari baki, dariya ya kece da ita tare da cewa"Asirin jikin kishiyarki ya karye domin ayoyin karya sihirin datake yawan sakawa sun ƙona min aljanuna har guda hamsin dana tura mata lokacin data haifi tagwayen nan, sune suka dinga sakata tana farfaɗiya" dariya ya kuma kecewa da ita sannan ya dubeta a karo na biyu,"Meyasa zaki gangancin baiwa ɗan waziri ƴarki?" ko kun manta ƙudirinmu akan dukkan matar daya aura a farko ta zama tamu zamu kasheta mu baiwa dodon tsafi jininta" kecewa ya kumayi da dariya sannan ya ɗora da kallon safiya"Shekarun baya da suka wuce kinzo kin kawon kokenki akan bakya haihuwa kuma bakya son ganin ɗan mijinki" nan da nan ya ɗauko wani kasko mai cike da gaushi hoton Abdul nasir ne ya fito muraran acikin kaskon, nuna mata shi yay, "Kince na kashe shi, nace miki baze mutu ba sabida yana da taurin kai tare da ƙarfin addini amman zan masa wani aikin da duk matar daze aura a farko tabbas zata mutu sabida bama son ya haihu bare har wani ɗaukakar hawa kujerar mulki ta sameshi idan muka kashe wannan matar tasa kuma zamu cire masa tunanin aure kwata kwata a ransa har abada, daga nan kinga burinki ya cika" cikin tsananin mamaki fulani umma ta dubi safiya koda wasa safiya bata taɓa gaya mata wannan maganar ba wato inda tai ganganci sakina ta auri Abdul kenan zata mutu, amman taso meema ce tai wannan aure sabida tafi son meema ta rasa ranta dan ƴar ta cika mata hancinta da ƙudundune, se kuma ta kawar da wannan tunanin ta kuma duban safiya waddai ƙuri da idanu na rashin gaskiya sam bata so bokan ya bayyana wannan sirrin nata a gaban umma ba, dan ita babu ruwanta da wata ƴar umman daze aura ita fatanta taga bayansa,ita kuwa umma mamaki da tsoron ɗan adam ne ya shiga ranta ashe daman safiya ta bada wannan aikin amman da ita ake cusa masa sakina ya aura,lallai kaji tsoron mutum maganar bokace ta dawo dasu tunaninsu"Zamu ɗauki fansar ƙunar da akama aljanunmu tabbas a wancan karon sunci nasara amman a wannan basu da ita, zamu kashe matarsa mu baiwa dodon tsafi jininta sannan shikuma musaka baƙar aljana ta auresa ya kasa kallon kowace mace aduniya" ya kuma kecewa da dariya cikin jin dadi safiya ta dubi boka"Aikin ka yana kyau uban ɗakina dole nai kukan murna yadda ban haifa ba babu maici, daman ni abinda ya kawoni shine tsawon wata uku da aurensu amman naji shuru, sannan kuma mai yasa boka yayar mai taurin kai bata aureshi ba se ƙanwar naso ita ta aureshin sabida kowa yafi sonta acikin gidan", dariyar bokace ta kuma kaurewa"Wannan" ya nuna umma"ita ta ɓata aikin domin ita taje wajan wani mai irin aikina amman bai kaini ba ta karbo asirin da ƴar zata turje taƙi yarda da auren ita kuma ƴarta ta shiga bata san ƙudirinmu akansu ba, wannan aikin nata shiya ɓata mana komai" ya kece da dariya"Amman da tuni babbar ita zata baƙunci lahira domin alƙawarinmu ne na baƙaƙen aljanu dole musha jinin mutum guda domin diyar kunar aljanu hamsin", yakai maganar yana dariya,
Cikin sauri umma ta dubesa "Haba uban ɗakina aimin afuwa domin ni yanzu naga munafurci ido da ido lallai mutum ba,a iya masa, ana zaune dakai ana zagayewa ta bayan gida, kaimin rai uban ɗakina, ka sauya akalar nisanta shi da kowace mace, koda dai ka kashe matar tasa na fansarku, to kada ka bari yaƙi aure domin nafison a wannan karon nima ƴata ta shiga gidansa" dariya boka ya kece da ita, "Ƙorafin ki ya karɓu mun fasa aura masa aljanar amman bazan miki aiki dan ya auri ɗiyarki ba domin kin ɓata min rai, dan haka kuje akwai mata da yawa mai rabo ta samu, amman tabbas ayau ƙudirinmu ze cika na tsawon shekaru 22" yakai maganar yana dariya'Boka........ya dakawa umma tsawa tare da saka hannunsa ya kaɗe inda suke nan da nan suka ɓace ɓatt.......cikin wani irin yare na arna bokan ya soma wani irin maganganu nan da nan naga wata kwalba ta bayyana a gabansa, wadda da kanta ta fashe a ƙasa, se wani baƙin hayaki ya bayyana tare da tsutsa ƙatuwa guda ɗaya, nan da nan naga tsutsar ta soma motsi kafin wani hayaki ya fice daga jikinta....dariya ya saki tare ɓacewa daga wajan.


Basu kuma tsintar kansu a ko ina ba se a bakin motarsu cikin yanayi marar dadi fulani umma take jan motar ko kaɗan taƙi yarda tai magana da safiya, basu suka isa gida ba se magariba, harta je part ɗinta tana mamakin halin mutum, wato wannan halin safiya tai mata, ita ta yarda da ita ashe ba kaunarta take ba inama laifin ta bari ya auri ƴarta amman dan baƙin ciki shine ta zaga taje ita kaɗai wajan boka tai wannan makircin kuma tana sane da hakan take tura sakina ta aureshi, bayan wannan kuma dan tsabar mugunta irin ta mutum shine tace a nesan tashi da auren kowace mace daga karshe ma tace a aura masa aljana sabida kar gaba ya auri ƴarta kenan, amman a fili nuna mata take bama ta zuwa wajan bokan wanda ko yau data ce zata wajansa jiki na rawa safiyan tace zata bita ashe akwai makircin data kulla tabbas ta koyi darasi kuma yau bada ban itama dana ta ƙullin ba daseta nunawa safiya ƙarshen makirci amman babu damar hakan sabida safiya ta cuceta data gama jin sirrinta....
Haka ta xauna a ɗaki tana faman tunani ko sallar datake kanta ta kasa yi, ita kuwa safiya cikin murna ta koma part ɗinta tare da ƙudurin se komai ya lafa zata kuma satar jiki ta koma wajan boka akan kadafa yabar Abdul ya kuma aure yau ɗinma dan da waccan tsinannar ne da seta faɗa amman komawarta ya zama dole ta faɗa tare da hayewa saman gado kamar wata yarinya tana tsallen murna..



*UK*
Rahina tana dawowa daga wajan salima tai cikin ɗakinta tana shirya kanta sabida tun ɗaxu ta gama komai domin isowar yaya Abdul - Naseer daga ƙasar spain.
Tana kokarin saka rigar hannunta taji wani irin murɗawar ciki wanda ya saka tai saurin tsugunnawa ta dafe, tana salati can kuma taji kanta yana wani irin sarawa, kafin kuma jikinta ya hau wata iriyar rawa kaf! kaf kamar mazari nan da nan ta soma fitar da dafara,
Duk abinda ke faruwa bayinta basu sani ba sabida suna nasu ɗakin, karfe biyar da wani abu ya sauka a kasar bayan yan abubuwan gabansa yayo gida tun daga falo yaga komai need, cikin farin ciki ya nufi ɗakin yana cewa "Beby i miss your body"cikin sauri bakinsa ya katse ganinta a tsakar ɗaki tana fama rawar jiki idanunta sun kafe se farin daya mayesu,hankali a tashe ya ɗagota ya karasa saka mata rigar sannan ya ɗauketa kamar beby yay falo da ita yana tofa mata addua ganin abun yaƙi yasa ya kira habu da salima duk iya yinsu sun kasa komai haka suka dauketa zuwa asibitin dake kusa amman ina ciwo kamar karosa ake *DR MUHAMMAD ANWAR SAMEER* ( MAS! ) Cikakken ɗan arewa mazaunin wannan ƙasar kafin ya komo ƙasarsa ta gado yaga halin da jama,arta ke ciki har ya fito a takarar *ƊAN MAJALISSA* shiya dubi ABDUL -NASEER ALIYU ADAM DAULA! PRINCE A,A, tare da kamo hannunsa kana yace masa"Sorry my frnd idan da hali ka miƙa wannan baiwar ALLAH ga mahaifanta domin wannan ciwon nata baya da nasaba da asibiti" zuciyar Abdul ta karye, adaren shida habu suka sami viza ta mutum biyu, karfe sha biyu acan ƙasar suka sami shiga cikin jirgin dayayo ƙasar nigeria direct wanda ba dan ma ficen da Abdul yay a ƙasar ba da ba,a bashi vizar a wannan gajeren lokacin ba, seda jirginsu ya ɗaga sannan su habu suka baro airport ɗin duk jikinsu yay sanyi, akan habun ze kokarin ganin ya sanar da coach ɗin club ɗinsu, cikin tashin hankali yake rungume da ita a gefensa, duk daya ɓoye fuskarsa cikin baƙin glass tare da abin rufe fuska sabida gudun idanun mutane, ALLAH-ALLAH yake ya gansa agida jiyake kamar acan za,a cire mata ciwon ko waya bai yiba yana tunanin sesun sauka ze kira wayar ko a airport ne...........



*DA IZZATA*
*PLS*
*COMMENTS*
*DON'T SHARE*
*ALHAMDULILLAHI YA ALLAH FOR EVERY THING*🙏🙏
6/30/21, 11:19 PM - Buhainat: *DA IZZATA*

47 - 48

*NIGERIA*

_Kano Murtala Muhammad International Airport_

Agogon Nigeria, 2:00am dai dai, wanda yayi dai-dai da, lokacin da jirgin daya ɗebo fasinjoji daga  ƙasar Egland babban birnin london ya sauka a cikin katafaren Airport ɗin jahar kano murtala muhammad international airport, bayan jirgin ya gama landing ɗin komai fasinjojin cikinsa suka soma fitowa, cikin harshen turanci Abdul - Naseer kewa ɗaya daga cikin ma'aikatan cikin jirgin magana akan yana son a kawo masa ɗan gadon da ake tura marasa lafiya tare da nurses guda biyu mata na cikin airport ɗin waɗanda aka ajesu in case for emergency issues, cikin mintuna goma aka kawo gadon tare da taimakon nurses ɗin aka ɗago rahina wadda take shinfiɗe  tamkar gawa bakinta yana fidda dafara, aka sakata acikinsa sannan suka turata xuwa clinic ɗin ciki kamar yadda ya buƙata kafin a samu azo ɗaukarsu, cikin zafin nama ya fito tare da nufar bakin gate ya tsaya, wayarsa ya fito da ita ya soma neman layin baba waziri, swich off, ta Ummi swich off, ta hajja fulani haka zalika ta baba sarki abin tamkar a alma'ra tsaki yaɗan ja kaɗan tare da kallon number faisal, sedai shidaya kirasa yaci sa,a a kunne amman kiran duniya yaƙi ɗauka, tsakin ya kuma ja, at two times sannan ya kira number adam shima swich off,
A,a kai jama'a yafaɗa acikin ransa meema ce ta faɗo masa, rabon daya kirata tun kafin yay aure, tsaki yaɗan ja akan dole ya kirata dan ko giyar wake yasha baya tunanin ze kira fulani umma ko, safiya, cikin sauri ya lalubo number meema yana ayyana suma su ummi ba,a samesu ba bare ita amman dai bara ya gwada ya gani, cikin ikon ALLAH yana kira yaji user busy! mutstsi ke idanunsa yay tare da kallon time, 2:15am metake a waya zuwa wannan lokacin, baya da lokacin wannan tunanin dan haka ya kuma kira still wannan karon call waiting, yakai kusan sau biyar yana kira call waiting, tsaki yaja da karfi tare da dafe kansa yana yamutse sumar datake kwance bisa kan nasa.

MASARAUTAR DAULA!
Kwance nake dagani se net gown, iya gwiwata tunda na tashi yau gabana ke faɗuwa wanda na rasa na minene? ko school ban jeba duk da muna cikin semister ɗin ƙarshe karatun mu ya ɗauki zafi amman haka hajja fulani tace bazani ba saboda bana jin daɗi, har zuwa dare ina kwance bana aikin komai se sallah ko abinci ban iya ciba se ruwan lipton kaɗai, ganin dare yayi sosai yasa na mike tare da, sauka nayo alwala nayi sallar nafila raka'a biyu, janyo wayata nayi wadda take yashe akan bed site drower, na kunnata sabida tun jiya ban kunnata ba, saƙonni ne suka fara shigomin kuma duk na su hapcy, suna tambayata lafiya yau ban shiga school ba kuma ban masu wayaba, ina cikin duba saƙonne kiran Ayshert ya shigomin, wara idanuna nayi karfe biyun dare da mintuna, cikin fargaba na ɗauka"Ke ko yau lafiya baki shigo ba munta kiranki ɗazu akan zancen assingment ɗinnan wallahi wayarki akashe, nima yanzu haka ina google ne ina duba wani aiki, saukata kenan kamar da wasa na gwada kiranki ta shiga, dafatan dai lafiya?" tafaɗa cikin kulawa,"Eh! lafiya kalau ayshert kawai ban samu shigowan bane".nan muka cigaba da hira akan abinda aka mana yau da nai missing, ina tambayar ta tana bani amsa, cikin haka naji kira na shigowa, sharesa nai sabida ina tunanin ko kamfanine, kuma har na gama wayata da ayshert mukai sallama ana kiran amman ban duba ba, haka na kashe ƙwan ɗakin na koma gado na kwanta.

******************

Ya jima yana kaiwa da komowa na rashin makama, ganin har 2:30am tayi yasa ya kuma shahadar kiran layin nata kota gama wayar, cikin ikon ALLAH ta shiga amman still ba,a ɗauka ba, iska ya kaima naushi cikin jin haushi ya kuma danna wani kiran a karo na barkatai,........ringing! ɗin wayata ya daman ga bacci yanata fusgata tsaki naja tare da janyota a fusace ina masifar wallahi daga wannan ɗaukan kashewa zanyi dan ayshert naga alamun yau ita ranarta ce ba dareba, ko kallon screen ɗin wayar banyi ba na ɗauka, "Hellow......, ban kaiba naji muryar data sakani dira daga saman gadon ina murza inanuna, cikin sauri kuma na ɗago wayan daga kunnena ina duba sunan ABDUL! Nagani sunan danai masa save kenan, "Dalla malama bana son shirmenki ki gayawa ummi muna airport yanxu a turo mana da mota" Ƙitt! naji ya datse kiran kuma dagajin muryarsa kamar cikin tashin hankali yake.
Da sauri na ɗauko dogon blue hijab har ƙasa na ɗora akan kayan baccin jikina cikin sauri na fita daga ɗakin, kaina tsaye ɗakin ummi na nufa dayake yau ina part ɗinta sabida part ɗin hajja ƴaƴan yakumbo maryam ne suka zo daga abuja toni kuma banson yawan jama,a yasa na keɓe kaina anan sabida rashin jin daɗin jikina.
Murɗa handle ɗin kofar ɗakinta nayi sannan naja na tsaya ban karasa cikin ɗakin ba seda nai sallama sau uku sannan ta amsa min tana zaune akan darduma da carbi a hannunta hasken ɗakin ta kunna, sannan ta dubeni"Lafiya naganki cikin daran nan?" ƙifta idanuna nai kaɗan"Daman yaya abdul-naseer ne yace nagaya maki suna airport wai a tura mota ta daukosu" tun kafin nakai aya.ummi ta mike tana salati tare da furta"ALLAH gani gareka ko lafiya"? bata bi kota kaina ba haka ta ɗauki hijabi ta fice nima fita nayi falo na zaun na rafka tagumi takai muntuna goma sannan ta shigo mikewa nai "ummi lafiya?"........zama tayi hannunta riƙe da carbi "Nima ban saniba amman babanku ya tura a taso su faisal zasuje ɗauko su yanzu.ALLAH jishshe mu Alkairi dai" da "Amin" na amsa mata haka mukai jigum a falon, ganin shurun tai yawa yasa ummi cemin mu tashi muje ɓangaren hajja fulani domin an sanar mata tuni ta tashi, hakance ta faru tashi mukai muka nufi can anan muka tarar da yawanci mutan gidan azaune kowa yay shuru kamar ba dare ba, ashe mune kaɗai bamu hallaraba amman abin mamakin harda su fulani umma a zaune dasu adda zainab.
Neman guri ummi tai ta zauna nima wajan adda zainab naje na zauna,abin mamaki ganin fuskar adda zainab nai tana hawaye, cikin sauri na dubeta"Addana lafiya naga kina hawaye?" cikin kiɗima na faɗi hakan, da kallo ta bini"meema ina kukan ban san miya dawo dasu ba a wannan dare fatana ALLAH ya tsare mana ƴar ƙanwarmu mai haƙuri amin" da kallo na bita tabbas! albasa batai halin ruwaba nikam na shida ALLAH ma kuma ya shida adda zainab tagari ce wadda samun irinta a ƴan uba da wuya nikam na cireta ma acikin ƴan uba yanzu tazamen babbar ya!"Insha ALLAH adda zainab lafiya kalau, suke" nafaɗa tare da xama a gefenta ina bata baki harta daina hawayen , kallon gefenmu nayi duk su amira suna zaune amman babu abinda ya damesu haka zalika su umma duk hirarsu suke seda fulani hajja tai maganar akan idan cika mata gu zasuyi da hira tofa su tashi su bar mata falo sannan kowa ya kama kansa.

Zaman mintuna kusan 40 mukai,kallon agogo nayi karfe 3:30am dai dai wanda kuma yayi dai dai da lokacin da mukaji ƙarar buɗe babbar ƙofa alamun sun shigo kenan tsit falon yayi har na wajan mintun goma, sannan baba shamaki ya shigo fuskarsa da alamun damuwa, ya tsugunna gaban hajja bamuji miyace ba haka naga hajja ta mike tare da riko hannun ummi suka fice, cikin rawar jiki fulani umma ta mike zata bisu, yakumbo rabi,a wadda suke ciki ɗaya da baba, kuma mata ga baba chiroma ƙanin baba waziri,ta dakatar da ita, komowa tai ta xauna, haka kowa yay jugum, atakaice seda akai kiran sallar asubahi sannan kowa ya kama gabansa domin yay sallah sabida har lokacin babu duriyar su fulani hajja babu kuma wani labari.

Zuwa wannan lokacin babu kalar tunanin da banyi ba, kuka kam ko ƙwayar idanuna ta koma ja sabida kukan danake a ɓoye domin tunda aka kira ummi na saddaƙar da abinda ya sami rahinata, sharrin sheɗan nan da nan na soma tunanin ƙila ya baiwa matsafan turawa jininta ne anyi tsafi danya sami ɗaukaka domin abin nasa da kamar tsoro daga fara buga ball wata uku haryafi waɗanda sukai shekaru a harkar samun ɗaukaka da jama,a.
Cikin sanyi jiki na fita daga part ɗin hajja fulani, ina share hawayena part ɗin ummi na nufa koda naje ban ganta can ba, alwala kawai nai tare da sallah sannan na tayar dasu sadiq, suma sukayi zama nai afalo ina kuka, cikin haka, naji sallamar anty habiba kanwar ummi, tare da yakumbo sa,a yayar ummi, abin mamaki ya bani cikin sauri anty habiba tayo kaina,"Meema se hakuri cuta ba mutuwa bace xata warke da izinin ALLAH"wara idanuna nai na mike tsaye"Anty habiba rahina ce ba lafiya?miya sameta?hatsari sukai?" nafaɗa in jijjigata kamar xan hau iskoki, ganin kamar hankalinta baya kanta yasa yakumbo sa,a zaunar da ita tana mata addu,a, sun jima akaina kafin na dawo dai dai se uban kukan danake a fili nake furta"Shiyasa wallahi jiya babu wanda ya rintsa acikinmu wayyo rahinata" na faɗa ina kuka!"Kull meema addu,a zaki mata ALLAH ya bata lafiya, dan yanxu ma haka kinga suna can cikin wani kauye wajan mai magani, da babanku yace yazo nan amman duba lokacin yasa aka tafi da hajja fulani da umminku da mijinta da kuma chiroma da shamaki muna nan muna zuba idonsu" cewar yakumbo sa,a wanda se a sannan na gane shurun da mukaji ashe basa nan wannan wace irin cuta ceto? bani da mai bani amsa haka muka xauna jugum ko tunanin kari bamai, har xuwa rana babu su babu labarinsu , da ƙyar anty habiba ta takura nakai kunu bakina, sannan mukai sallah muka kuma zubawa sarautar ALLAH idanu.
Basu suka kamo hanyar gida ba se wajan la,asar tare da maganin da mutumin ya basu akan cewar insha ALLAH zata sami lafiya domin yace musu kamar sihirine,dan haka ga magani nan ya basu indai ba cutar ajali bace ba ALLAH ze bata lafiya, tsantsar ayoyin karya sihirine tare da ruwan rubutu aka haɗo masu suka tawo gida, dayake ummi kaɗai da hajja fulani ne suka shiga wajansa shiyasa koda suka fito Abdul yana tambayarsu mi akace yana damunta, ce masa kawai sukai shigar iskace sukaja bakinsu sukai shuru gudun maganganun jama,a babu yadda take kuma bata gane komai na rayuwa haka aka tarairayota aka kaita mota, ko maganin da aka ɗura mata ya biyo miyau ya fito se kaɗan daya shiga.
Tagumi ummi tayi tana kallon rahina wadda take kwance akan cinyarta hawaye ta share tare da furtawa a zuciyarta daman tasan akwai rina a kaba tabbas bata xargi amman tasan da wuya mutan gidansu subar wannan aure, cutar da aka so mata daga haihuwar su meema shine yanzu aka koma kan ƴarta mutane kamar bazasu koma lahira ba.
Itafa ta gaji da wannan abin, kwata kwata auren ya fita aranta batajin ko rahina ta warke xata koma ɗakinta domin bazata iyaba idan ita ta jure wannan yarinyace bata san komai na rayuwa ba, maganar da meema ta gaya mata kwanakin baya ce ta faɗo mata akan kalamin fulani umma gareta"Yadda ƴaƴana basu aureshi ba kema baxaki aura ba, haka zalika itama rahinar datai gangancin auren sa bazata zauna lafiya ba"! cak ummi ta tsayar da wannan tunanin tare da saurin la,antar shaiɗan tana ayyana babu kyau zargi, hakan yasa taja carbinta tana istigifari har suka iso gida..........
7/5/21, 7:26 AM - Buhainat: *DA IZZATA*


49 - 50


Cikin nutsuwa motar faisal ta shigo harabar masarautar daula, bayan yayi parking su ummi suka fito haka zalika itama hajja fulani ta fito da ƴar sandarta ta ƙarfe datake dogarawa, Abdul-Naseer shine na ƙarshen fitowa bayan ya xaga baya inda ummi ta jingine Rahina, ɗaukota yayi tamkar ƴar beby tare da kallon hajja fulani kana yace"Ina muka nufa" cikin sauri sabida yamma tayi ga fadawa kota ina suna shawagi, cikin bada umarni hajja tace akaita part ɗinta cikin jarumta ya nufi sashin hajja fulani ɗauke da rahina ahannunsa tamkar gawa, kwantar da ita yay akan kujerar falon tare da xama a ƙasa yana kallonta shi kansa ya rasa mike faruwa haka, shidai yasan lafiya yabarta amman dubi yadda ta koma, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ahaka su hajja da ummi suka shigo falon wanda kafin wani lokaci, sarki abubakar da kansa yazo yaga halin da ake ciki da taimakon Abdul ya ɗagota ya zuba mata ruwan tofin addu'oin a bakinta cikin amincin ALLAH tare da tsantar tsarin dake cikin ayoyin alkurani rahina ta buɗe idanunta tana kallon kowa sedai kuma sam bata um, bata um,um, kafin wani lokaci labarin dawowarsu ya gama baza cikin masarautar wanda tuni duk dangi sun hallara a wajan ganin mutane yasa Abdul zamewa ya nufi sashinsa wanda yake nan ɓangaren hajja fulani, wanka yayi tare da yin sallah kana ya ɗan kwanta sabida ya gaji.
Cikin sauri baiwa salma ta shigo falo hartana tuntube kallonta nai tare da mayar da hankalina gareta kacokam ina jiran bayaninta sabida ita na aika akan taje wajan, motoci tamin shawagin ganin dawowar su ummina"Ranki ya daɗe ALLAH ya dawo dasu lafiya yanxu haka suna ɓangaren hajiya" cikin sauri na mike daman ba sauya kaya nai ba tun dai wannan hijabi da net gown har yau banyi wankaba, ko gayawa su anty habiba banyi ba haka naja hannun sadiq muka nufi part ɗin hajja jikina har yana rawa.
Koda muka shiga falon nata cike yake da ƴan uwanmu abin mamaki harda baba wanda yake zaune riƙe da hannunta yana tofa mata addu,a cikin sauri na bangaje su amira kana na ƙarasa gabanta,"Sannu rahinata yaya jikin naki?" na tambayeta ganin tai ƙuri da idanunta tana kallon sama"Bafa ta magana yanxuma ai da sauki amman ɗazu baki ɗaya fa bakin ya datse amman yanxu cikin amincin ALLAH gaya nan ta buɗe idanu" cewar hajja fulani kenan wadda take zaune, walida cousin ɗinmu tana danna mata kafafunta domin sun tasa sabida tafiyar datayi.
Zama nayi agefenta ina share hawayena wallahi duk abinda ya sami rahina bazan taɓa yafewa Abdul ba haka naketa nanatawa araina jinai wata sabuwar ƙiyayyarsa ta dasarmin araina, da kallo nabi falon kowa yana zaune harda su yaya faisal amman shi kam banga koda ƙeyarsa ba tsaki na kumaja ina kallon rahina wadda naga kamar tana motsa bakinta.
"Zan sha ruwa" abinda ta faɗa kenan, Cikin sauri ummi tayo kanta tare da ɗagota tana kabbara! baki ɗaya murna ta gama kama kowa, sabida yadda mukaga rahina tai magana abu kamar shigar iska, cewar hajja fulani kenan,Ummi ce ta taimaka aka bata ruwan tasha, ganin haka yasa baba tashi sabida yaga komai ya koma dai dai.
Abun kamar al'ajabi mukaga ta mike tare da kallon ummi,"Ummi yanzufa ba kamar ɗazu ba naji sauƙi, kaini nai wanka" tafaɗa tana son ta mike daga kan kujerar.
Godiya mukaiwa ALLAH, daya bata lafiya cikin sauri anty safiya matar baba waziri ta taso tare da riko hannunta, muje na taimaka maki kiyi wankan, zuruf na mike tare da rufa masu baya zuwa ɗakin dake kusa dana hajja, "Maza meema ki ɗebo mata kaya a ɗakin ummi" cewar anty safiya kenan ganin yau tana rawar jiki akan ƴar uwata yasa nai wuf na fice tare da nufar kofar fita adai dai ....bakin kofar dazan bar part ɗin nagansa jingine.


Tun kafin ma na ƙarasa

Please Login or Register in order to submit comment