Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare dayin kukan kura na koma kan cinyarsa tare da riƙe kan motar naiwa ALLAH godiya dayasa na iya mota, cikin sauri na saita kan tare da hawa kan titi seda nai nisa sannan na kasheta na koma mazaunina se a sannan naga abinda nai ashe da akan cinyarsa nake, zama nai tare da mayar da kaina ƙasa ina jiran ikon ALLAH kome yake a haka oho!
Bana sonka na tsaneka! jin kalaman yake kamar saukar narkakkiyar dalma acikin zuciyarsa da ransa da gangar jikinsa, dayaji wannan kalmar daga bakinta gwara yaji a bakin mata dubu ɗari, sosai yake ya mutsa wankakkiyar sumar data kwanta luf a saman kansa, yana jin dik.duniyar tai masa zafi, wannan wani irin ƙaddarar soyayyace ALLAH ya ɗora masa,......duk abin da tai yana jinta amma ya gaza furta mata komai, gajiya yay dan kansa ya ɗago jajayen idanunsa ya ɗora akan sitiyarin motar ya kunnata tare daja aguje yabar wajan,tunda yahau titin bai sake magana ba har muka isa gida, masu tsaron gate suka bude mana gate ya shiga ya faka a parking space jingina kansa yay da jikin seater ɗin motar batare daya fita ba, kuma nima bai buɗemin lock ɗin domin na fita ba, seda wata motar tazo zata faka awajan hasken fitilar motar ya hasko cikin motarmu anan naga abinda yaɗagamin hankalina, hawayene ke fita daga cikin idanunsa yake kuma zubowa zuwa saman fuskarsa, "Ya salam ya Abdul Naseer kuka kake?" nafaɗa a kiɗime tare da ƙara matsawa gabansa,"Kuka kake kaida zaka tare da ƴar cwt 17 nikuma ince yaya?" na kuma faɗin maganar ina ɗora tafukan hannuna a saman fuskarsa ina share masa hawayen dake zubo masa, duk da nasan hakan bai daceba domin halal ɗin ƙanwata ne a yanzu, amman yaya zanyi DAFIN SO, shiya jamin hakan, mun jima a haka kafin ya ɗago idanunsa duka ya zuba min,"Kin cuceni, kuma kema kin cuci kanki, zanyi nesa dake zan xauna tare da ƘADDARATA wadda ALLAH ya jarabcen amman kuma KECE SILA,kije kiyi duk abinda xakiyi ABDUL ze bar maki ƙasarma baki ɗaya, amman ki sani waɗannan kalmomin da kika jefeni dasu ɗazu na BANA SONKA! NA TSANEKA! har abada bazan manta dasuba, kuma waɗannan kalmomin insha ALLAH sekinyi nadamar faɗinsu". yana gama gaya min haka ya ɓalle marufin motar ya fice ya barni zaune ina lissafin bogi, Ganin dare ya fara yasa na fito zuciyata fall tunani, babu kowa a harabar wajan se fadawan dake faman shawagi se hasken sola kota ina haka na wuce part ɗinmu, ɗakin ummi na fara zuwa na gaya mata na dawo faɗa ta kama yi ina muka tsaya? mamakine ya kuma kamani ada ummi bata taɓayin faɗa idan ina tare dashi amman yanzu jibi itama faɗan take, komai yasa oho koda yakema ni koda ɗin canma ba fita muke da shiba, hakuri na bata kawai na wuce ɗakina ina jin babu daɗi, bathroom na wuce na watsa ruwa sannan na dawo na murza key ajikin kofata na koma saman gado na kwanta luff ina saka wasikar jaki,Washe gari aka tashi da dinner inda aka kama babban wajan shagalin biki mai mugun kyau da tsada, tun wuri aka soma shiri sosai amaren suka fito gwanin ban sha,awa nikam bada ban kada a fassarani ba da babu inda zanje, amman haka na daure, nayi wanka na zira ankon nabi tawagarsu anty zainab,Koda mukaje can lungu na samu na zauna, shigowar amare da angwaye yasa dole safi ta takuran akan na fita muyi liki sabida nice uwar rahina, haka na mike muka nufi wajan, wallahi ko waye ya kalli ABDUL se numfashinsa ya kusan daukewa sabida yadda ya haɗu ya kuma haɗuwa, duk da fuskar nan tasa babu alamun sauki amman ba karamin kyau yay cikin fara ƙal ɗin shaddar dasukai ango ta angwaye ba nikam komawa nai da baya nai saurin buya ina share hawaye bazan iya ganin wannan takaiciba daga karshema gida na koma, haka na kwanta a ɗaki wanda ban san ma an dawoba, washe gari aka tashi da daurin auren mutum, goma ras,ABDUL - NASEER ALIYU ADAM DAULA, DA RAHINATU ABUBAKAR ABDUL - NASEER DAULA, FAISAL ISMA'IL DAULA, DA AMINA ISA MUSA, ADAM ADAM DAULA,DA AYSHERT MUHAMMAD DAULA! wanda ya kasance Abdul da rahina na cikin gida ayshert da adam ma haka, faisal, ma ta cikin gidace ɗiyar liman na yanxu,ragowar ne aka fita waje, domin matansu na wajene, lokacin danaji shelar ɗaurin auren daga bakin sarkin shela ɗakina na shiga na dunƙule a bargo ina kuka! Tabbas nikam tawa ƙaddarar kenan,amman babu komai ALLAH yasa hakan yazaman alkairi amin, Ko bikin nasmat data gayyacen wallahi banjeba infact ma, har akai la,asar ina cikin ɗaki zazzaɓi ya kamani, seda anty zainab tazo take cemin nazo zamuyi sallama da rahinatu jirgin karfe biyar zasubi zuwa london, tashi nai na wanko fuskata na zira hijabi na fita falo, dik su mameey suna zaune haka na bisu da gaisuwa sannan na wuce ɗakin ummi, anan naga jakadiya tana jiran agama shirya rahina xata kaita wajan baba, cikin sauri rahina ta, zo gareni ta rungume tana kuka! Addana shikenan na daina ganinku" nima kukan na saka haka zalika ummi ma haka, gaba ɗaya semuka koma abin tausayi, ina ji ina gani aka wuce da ita wajan baba daganan kuma daman mijinta yana can idan aka gama masu nasihar zasu wuce airport, zama nai akan gadon ummi na rafka tagumi shida man tundaga ranar dayay min wannan bakin ban kuma ganinsa se a ranar dinner to nan ɗinma guduwa nai fatan alkairi nai masu na koma ɗakina.......

Sosai baba waziri da baba sarki abubakar sukaiwa ƴaƴan nasu nasiha haka zalika mameey ta bawa Abdul amanar rahina, sannan hajja fulani ma tai masu nasiha, umma ma ba laifi tai nata fatan alkairi kafin ya faisal yajasu xuwa airport wanda zasu wuce birnin london domin hatta gidan dazasu zauna club ɗin data siyeshi ze fara buga mata wasa a matsayin super star na wannan shekarar ta bashi sosai rahina ke kuka, ya faisal bai dawo ba seda yaga ɗagawarsu zuwa birnin london..........



💃💃💃💃💃 *DOLE NAI RAWA MY FANS DOMIN YANXU WASAN YA FARA WAI ALƘALAMINA FA ZE SAUYA SALONSA, TEAM MEEMA KUYI HAKURI KU BINI, TEAM RAHINA KU WANKE HANNU*


*DA IZZATA*
( painful love )
6/30/21, 11:18 PM - Buhainat: DZ


39 - 40



*DAN ALLAH JAMA,ATA KUYI HAƘURI WANNAN LABARIN DUK YADDA KUKE ZATONSA YA WUCE NAN ƘARFIN GWIWARKU GARENI SHIZE BANI DAMAR KAIWA GA MACIMMAR BURINMU, PLS MASU SON ASMA'U KUYI HAKURI SALON ALƘALAMIN NE HAKA AMMAN NAI ALƘAWARIN NAN GABA KAƊAN SEKUNYI RAWA DAN DAƊI*

Tunda na shiga cikin ɗakina ban kuma fitowa ba seda garin ALLAH ya waye, ranar litinin kenan wadda tai,dai dai da ranar da yawancin baƙinmu suka soma haɗa karonsu zasu wuce gidajensu, waɗanda daga cikinsu kuwa harda Mameeyn gombe, ina zaune da misalin ƙarfe tara na safiya, cup ɗin tea ne a hannuna wanda na saka, zulaihat amintacciyar baiwar ummi ta dafomin ta kawon cikin ɗakina, sabida ni bana son fita ko ina jina nake na tsani kowa na gidan namu, na ɗaga cup ɗin zankai bakina naji an murɗa handle ɗin ƙofar ɗakina, dakatawa nayi da kai cup ɗin bakina, na mayar da hankalina kacokam ga ƙofar, mameey ce ta shigo cikin ɗakin jikinta sanye cikin ɗinki bubu na less mai uban kuɗi, daman mameey tun fil azal mace ce ƴar gayun gaske da murmushi ta ƙaraso gabana, cikin sauri na bata waje saman gadon nikuwa na sauka ƙasan carpet na zauna bayan na yayo mayafi na rufe dukkan jikina, "Mameey ina kwana ina gajiya?" nafaɗa bakina yana rawa sabida tsananin kunyar matar danakeji se yanzu nakejin kunyar yadda na nuna bana son ɗan nata, duk yadda take sona takemin aike kala-kala amman, sam na turje ada naƙi gudan jinin nata,"Lafiya ƙalau takwarata, muma yanxu zamu wuce gida".zaro idanuna nayi waje"Kai mameey gida kuma dafa nace su hassana zasu rakani ma anguwa, haba mameey sekace baƙi dan ALLAH kubari se kun jima" nafaɗi maganar da iya haƙiƙanin gaskiyata, murmushin jin daɗi mameey tayi tare da jin rashin daɗin samun suruka tamkar asma,u yarinya mai son jama,a sam bata da matsala,"Ayya baze yuwuba ɗiyata sabida bikin hussaina dayake ƙaratowa nan kusa to dole, in koma da wuri ga kuma costumers ɗina sun dameni".takai maganar tana dariya,"Haka ne mameey ALLAH yasa lokacin semister tazo ƙarshe nazo gombe nasha hutuna".nafaɗa ina murmushi"Au bakuyi hutun ba aini nazata kunyi hutu har nace zan tafi dake can kozaki saki jikinki sabida nan ɗin kaɗaici can kuwa gasu hassana su salima duka" tafaɗa tana dariya"Lah! wallahi bamuyi ba amman insha ALLAH da anyi zanzo amman zaki tambayi baba ko?" cikin kulawa tace"kinci gidanku! nan da can ɗin ay ɗayane duk gidane karki damu da lokacin yayi zan turo a tafi dake".sada kaina nai a ƙasa ina jin tsananin kunyarta maganarta ce ta katseni"Asma'u ke ƴatace ko ba dan komai iya son da wannan yaron yake maki kaɗai ya isa nima nasoki na kula dake! wanda rashin aurenki dashi bakaramin ciwo ya maniba, amman mubarwa ALLAH ikonsa domin shiyafi sanin dai-dai fiye damu, da wannan damar nakeson sake sheda miki ni uwace agareki kuma har abada bazan dena sonkiba, dan ALLAH kicigaba da kare mana mutunci kodan ƴan gidannan da yanxu xasu zuba idanu suka mai ze biyo baya kuma ta ALLAH bata suba, kuma insha ALLAH da xarar kunyi hutu xan turo atafi dake konazo dakaina".takai maganar tana kallona,murmushin jin daɗi nai tabbas! mameey tacika uwa mabada mama, wadda take da son ƴaƴanta tare dason duk abinda sukeso wallahi inda watace bara ta kallan ba, amman jiba ita abinda tace sabida son da A,A kemin yasa har abada bazata daina sona ba"Nagode ALLAH yabar min ke mameey na".nafaɗa ina share hawayen daya zubo min.
Tasowa tai ta kama hannuna muka fice har zuwa ɗakin ummi, sosai mameey ta gargadi ummi akaina kunsan daman nace muku mameey kamar a yaya ummi ta ɗauketa, har bakin motarsu muka rakasu sannan muka dawo, lokacin se ƴan uwan ummi kaɗai a falon, zame jikina nayi na fice zuwa sashen hajja fulani naci sa,a kuwa babu kowa ita acan ɗin domin ƙannan su baba wato su yakumbo abu duk sun wuce gidajansu, tana xaune bayi suna mata tausar kafarta ganina yasa ta haɗe ranta tamau, "Lafiya kika kwaso jiki kika tahomin da wannan bakar fuskar taki tamkar gawayi bayan kin gama tsinkar da mutuncina", cikin sauri na ƙarasa gabanta tare da saka hannu na kama ta"Haba takwarata masoyiyar dame kukeso naji banda ƙwacen ɗan lelenki da akai, yanxu kuma zaki sakamin hawan jini". nafaɗa ina dariyar dole"To dakata dame kikazo yanxu ko dai waccan bakar munafukar ta turoki kiji ta cikina to shidai Nasiru yay maku nisa in ALLAH ya yarda" tafaɗa tare da ɗauko inibi ta jefa a bakinta, cikin sauri na waiga ganin banga bayin wajan ba na mayar da ajiyar heart dan banson ta tsinkani,kwantar da kai nai sosai na dinga lallaɓata ina bata baki har ta sakko, sabida a yanzu sena dinga xuwa part ɗinta zanji dadi sabida kaɗaicin part ɗinmu"Dama fa ni duk cikinku nafisonki takwara keda nasiru to wallahi waccan tsinannar data daukeki yasa naji na tsaneku amman yanzu mun shirya kidawo nan ma baki ɗaya kema kafin kiyi aure, kinga ni yanzu ni ɗayace bani da.ɗan tayin hira tunda nasiru baya nan" murmushi nayi mata "Karki damu hajiyata da anjima zan saka a ɗaukomin kayana amman fa a ɗakinki xan zauna dan wallahi tsoron kwana ni kaɗai nake" abin mamaki senaga hajja fulani tanata murna, aikuwa zuwa dare ta aika jakadiya ta kira mata baba, ba wani bata lokaci ta sheda masa xan koma wajanta, bai wani jaba ya amince aikuwa hak naje na kwaso kayana daga wancan ɗakin na part ɗin ummi, sosai abin ya bawa ummi mamaki amman sanin hajja fulani ba wasa yasa ta aminta hartaji ranta yay ɗaya, haka na dawo part.ɗin hajja fulani na cigaba da xama,
Kwanci tashi ba wuya wajan ALLAH kimanin sati biyu da bikinsu, wanda zuwa wannan lokacin nai mugun shaƙuwa da hajja fulani tsohuwa mai shiga rai se abinda nakeso aike a part ɗinta sangarta ta ƙarar min domin bana aikin komai seci da kwanciya washe gari kuma na buga wankana nai school, kafin na dawo angama mana abinci da komai wannan lamarin yana min daɗi nasan inda a wajan ummi ne da ko.girki ya ishen dan bata barin bayi su mata girki nikuma gashi naƙi jinin aiki rahinace daman gwanar aiki itama dan rainon ummi ce shiyasa. wannan kenan.



KIMANIN WATA GUDA CIF!



*LONDON BABBAN BIRNIN CIKIN ƘASAR ENGLAND ( UK )*




AREA: _Covent garden and strand_

Babbar anguwace acikin wannan gari na birnin london wadda ba kowa ke zama acikinta ba se ka kai wani ƙwaro sannan zaka zauna acikinta, mafi akasarin gidajen arean ma masu irin tsayin nan ne sannan ko wani gini xaka ga yana ɗaukene da bene hawa uku ko fi, kuma unguwace mai kyau sam babu hayaniya, gata ta cakuɗe da turawa tare da mutanan wasu ƙasashen maxauna cikin birnin london.*BLOCK 003* ƙaton ginine mai ɗauke da flate a ƙalla kimanin 20 Kuma mazauna cikin wannan block ɗin yawancin su turawa,ne ƴan cikin club ɗin datai farautar abdul - naseer tun kafin yabaro gari wadda wannan club ita ta dauki nauyin zaman dukkan wani member nacikinta zata bashi, flate guda mai dauke da one falo and two bedroom se toilet and bathroom, se kitching da store.
Hakance ta kasance ga Abdul, bayan barinsa ƙasarsa ta gado wadda ya tafi cikin kewa da alhini tare da kuma fatan cikar burinsa, bayan saukarsu awani hotel aka soma ajesu, kafin, washe gari tayi, coach,ɗin club ɗin da kansa yazo bature ne mai suna james yana mugun son Abdul haka xalika shi yay ta nacin Abdul ɗin har wajan baba waziri sabida ya yaba da ƙwazon yaron tun a wancan lokacin.......oga james shiyay masu shatar taxi har xuwa cikin block 003 wanda babu abinda rahina keyi se faman raba idanu shikuwa Abdul ya ware sunata zabga hira da oga james cikin harshen nasara kamar shima baturen ne, mamakinsa ne ya kamata yadda taga yanata zuba hira kamar bature har suka sauka oga james shiyama wani ɗan nan arewa waya wanda shima ɗan ƙwallon ƙafane acikin wannan ƙungiya, wanda yake dauke da lamba 6 bayan rigarsa, sunansa Habu sarki! wanda baki ɗaya sunansa da sunan dake bayan rigarsa hakane ajiki yana xaune ne shima a nan block ɗin tare da matarsa guda ɗaya dayazo da ita wannan dalilin yasa oga james ya soma haɗa Abdul da sarki, domin shine ɗan garinsu nageria cike da murna sarki ya fito shida matarsa sukaiwa su Abdul jagora har flate ɗinsu mai number 19, shikuma sarki yana number 18 kenan sun zama makota wannan abu yay wa sarki daɗi sabida daman shi ɗayane bahaushe acikin wannan block, seda komai yay setting sannan oga james yay ma su Abdul sallama ya wuce akan gobe zasu haɗu a club don a soma nunawa Abdul training da komai,Salima matar habu sarki ba ƙaramin murna tayi da ganin rahina ba duk da taga yarinyar karamace sedai kallo guda xaka mata kasan daga babban gida ta fito tun kafin ma tasan cewar rahina ɗiyar sarkice, salima ita ta taya rahinatu aikin gyaran kayanta da komai domin shi ogan tunda ya faɗa ɗakinsa bai kuma fitowa..........har zuwa dare salimat ita ta kawo masu abinci kafin washe gari rahina ta masa lissafin abinda zasuyi amfani dasu.
Kiminin sati guda sukai suna faman gyare gyaren gida konace ita tanayi domin shi kam idan ya saka kafa ya fita baya dawowa se dare yana can harkarkokin sa na training sabida next month january, on 2 Abdul - Naseer Aliyu Adam Daula ( A, A DAULA) ze soma buga wasansa wanda xasu kara da wani fitaccen club wanda tuni oga james ya basa lamba ta 3, acikin jerin ƴan wasan cikin ƙungiyarsu, wanda Abdul ze fito a matsayin super star na wannan shekara. kuma ba ƙaramin mahaukatan kuɗi club ɗin zata bashiba kunsan dai yadda ƴan ball ke samun kuɗi.
Tsahon sati guda yay yana faman zirga zirga sam baya samun time na zama, se a week end ne ya samu ya huta sama sama yake ɗan jan rahina a matsayin kanwarsa, bawai dan yana sontaba, yawanci ita kuwa rahina idan bayanan suna tare da salima suna hirarsu idan ya dawo seta komo gida.
Haka rayuwar ta kasance har tsahon wata guda, cif wanda yau litinin ya kama ɗaya ga wata gobe ake saka ran Abdul - Naseer ze soma buga ƙwallonsa cikin hukuncin ALLAH wanda tuni zancen ya cika cikin garin kano da kewayenta harma da sauran jahohinmu na nigeria, duk inda kaga tarin samari tofa maganar PRINCE A,A ake, sabida yadda ake baza labarin a kowani kafa ta sadarwa hatta cikin masarautar daula ba,a barta abaya ba wajan saka ɗan nasu acikin addu,arsu ALLAH ya bashi sa,a akan wannan wasa daze soma bugawa gobe talata biyu ga watan jan!........



*DA IZZATA*
6/30/21, 11:18 PM - Buhainat: DZ


41 - 42


Yau talata tun gabanin karfe takwas saura kwata nabar gida sabida ina da text sannan kuma wani malaminmu ya bamu group assignment wanda ya zaman dole na fita da wuri sabida mu samu muyi da wuri before azo yin summiting koda naje school zaune na tarar dasu hapcy abakin bishiyar da muka saba zama muyi karatunmu idan bama da lecture, cikin barkwanci muka gaisa ayshert ce ke cemin "A,a wai yaya naganki a school tun yanzu?" da kallon mamaki na bita tare da ce mata "A,a to ban gane wannan banxar tambayar taki ba dallah mai yasa xaki gayamin hakan?" dariya duka suka kwashe da ita sannan hapcy ta mikon wayarta "Duba nan muma kammu mun leƙa face book ne muna ganin labaran ball ɗin da yayanki ze buga around 12 wannan dalilin yasa kika gammu anan a zaune" tsaki na ɗanja kaɗan sannan na taɓe bakina, duk da cikin zuciyata naji wani iri amman a fili sena basar tare da ɗaukar hand back ɗita na ɗora a saman cinyata na zage ziff ɗinta na kwaso kayan karatuna na juya masu baya batare dana ce komai ba.
Ina jinsu sunata maganganunsu ƙasa-ƙasa amman ban ce masu komai ba daga karshema ni tashi nayi na nufi cikin hall ɗin damuke lecture nabarsu a zaune cikin ikon ALLAH naga waɗanda aka haɗamu grp guda dasu tuni na shiga cikinsu mukai solving ɗin assingment ɗin maths ɗin da aka bamu, bamufi minti biyar da kammalawa ba malamin daze mana text ɗin ya shigo, cikin sauri naga su hapcy sun rugo suna faman baza idanu dariya na saka masu tare da kanne idanu guda sannan na mayar da hankali akan abinda ake mana, cikin mintuna kaɗan na kammala text ɗin tawa na tashi nai summit, daman ni tun fil azal bana break a capteria wannan dalilin yasa nai xamana a karkashin bishiyoyi ina nazarin littafin dake gabana, ko wajansu ban kuma lekawa ba har xuwa lokacin da muka kuma shiga class 11 dai dai muka kammala lectures ɗinmu dan haka ban wani tsaya wata wata ba na faɗa mota nai gida bakaramin yunwa nakeji ba sabida ban tsaya nai break ba dan haka tundaga bakin part ɗin hajja fulani, na zubewa bayin wajan kayana nai cikin falo ina faman kiran sunanta Abinda ya bani dariya shine zaune na tarar da hajja fulani ta ƙwama uban glass ɗin daya kusan cinye rabin fuskarta ga baiwa guda agabanta hannunta riƙe da remote control tana serching channel, cikin hargagi naji hajja tace "ALLAH nagode ma ke ƴarnan gasu can barmin nan" dariya sosai na tsaya inayi ganin yadda hajja ke actin ɗin a lokacin, ganin abun bana kare bane yasa nayi ɗaki naje na watsa ruwa sannan na nufi kicin na haɗo abinci na shige ɗaki batare dana fito falon ba.
"Asama'u fito fito kiga ɗan uwanki yana tsalle wayyo kada su karya min shi"! tafaɗi maganar kamar ma kuka! take cikin sauri na yada plate ɗin abincin na ruga xuwa falo, abinda idona ya gani nima kaina numfashina ya kusan ya ɗauke, amman yadda naga hajja tana share hawaye daga cikin glass yasani kifawa dan dariya.
Yaya Abdul - Naseer ne sanye cikin kayan ƴan ball jajaye gaba ɗayama ya saje cikin jar fatar se bayan rigarsa mai lamba ta 3 da aka rubuta A,A DAULA 3 da babban baƙi, tsalle naga yayi ya cafki ball ɗin daga raga wanda cikin zafin nama naga golan ɗayan club ɗin ya saka masa kafa ya taɗesa senaga ya kifa da ciki har yana dafe gefen cikin nasa, wannan abun shine fa ya saka hajja kuka! kuma ba hajja kaɗaiba kafatanin matasan gari kabbara suka saka a wannan lokaci suna kiran sunan ubangiji akan ya kai masa ɗauki, cikin ikon ALLAH kuma mukaga ya miƙe cike da zafin nama, wanda tashin sa yay dai dai da jefa ball ɗinsa cikin raga har sau uku, neman waje nai na zauna jikina har yana rawa ban taɓa ganin ƙwallon ƙafa ba kuma bata birgeni amman yau ɗaya na zauna sabida ita, zamana kuma yay dai dai, da lokacin daya kuma ɗaga ball ɗin sama ya kuma jefata acikin raga atake anan lafarin dake tsakiyarsu ya hura usur! wanda yay dai dai da wasu numbers dana ga an jero 3/1 aka rubuta da babban baƙi atake anan naga kafatanin masu jajjayen jc ɗinnan sun ɗagasa sama suna wurgasa suna ihu"wayyo asma,u karsu kashen nasiru ɗaukomin waya ya dawo gida" naji muryar hajja tana faɗa cikin tsoro wanda hakan yayi dai dai da shigowar kuyanga xulaihat cikin rawar jiki"Babban albishir ranki shi daɗe" tafaɗa tana zubewa gaban hajja"Ina mai farin cikin sanar dake cewar jikanki Abdul - Naseer yaci ƙwallo har zagaye uku wanda ya bashi damar xama lamba ta ɗaya acikin kunyarsu ayanxu haka hajja ko ina kika kunna a kafar yaɗa labarai jinjina ake masa tare da yabon ƙwazonsa, wanda tuni matasan gari sun cika gaban masarautarmu sunawa baba waziri murna" kuyangar takai maganar jikinta yana rawa, cikin murna da farin ciki hajja fulani ta dubeta "Masha ALLAH tashi kije zulai kema akwai kyautar dazan miki mahimmiya" Cikin ladabi kuyangar ta mike tana godiya, nikuwa hankalina kacokam yana kan TV ganin yadda ƴan club ɗinsu tiƙar rawa suna tsalle abinda naga yayi shiya bani jin daɗi wato Sujjada yayiwa ALLAH ma ɗaukakin sarki tare da ɗaga hannunsa sama yana nuna godiyarsa ga buwayi gagara misali, yana gamawa ya shafa anan naga yana ɗan matse face ɗinsa yana kuma shafa gefen daya faɗin, cikin sauri turawa guda biyu suka rikesa sukai ciki dashi daga nan aka ɗauke wajan se labaran da aka cigaba da watsowa ta ko ina sedai kaji ana ambatar Abdul - Naseer Aliyu Adam Daula ( A,A DAULA ) ganin hakan yasa na mike tsam nai ɗaki duk hankalina yana kansa har wayata seda na ɗauka, kome ya samu cikin nasa oho? tunawar danai cewar yanxufa yay min nisa sannan kuma ga furucinsa gareni yasa na yada wayar na kwanta lamo ina sake sake acikin raina.


*UK*

Cikin sauri ta yada remote ɗin hannunta tare da nufar bedroom ɗinta aguje wata arniyar doguwar riga baƙa ta saka mai adon stone agabanta setai amfani da bakin space asaman kyakykyawar farar fatar fuskarta, shar ta fito tare da ɗan yalolon gyale a hannunta wanda ko wuya bai zo mata ba, cikin sauri ta ɗauki car key tare da nufar kicin "Momcy! Momcy ware are you?".take faɗi cikin sangarta gami da gayun daya zauna ajikinta, wata babbar mace ce baƙa ta fito daga cikin katon kicin ɗin dake falon "A,a Beby lafiya kiketa kirana haka?" "Momcy zan fita ne bye" tafaɗa tana ficewa daga falon cikin sauri. cikin mugun gudu take bin titin wanda yake tsit babu kowa tafiyar mintuna goma cif ta kaita babban club ɗin, kasancewarta tasan gari acikin ƙasar yasa bata sha wahalar shiga cikiba sedai tasha artabu da masu tsaron room 001 ɗakin da aka warewa Abdul domin ya huta, wanda seda tasha matukar wahala harda ɗan kukanta da ƙyar dai aka barta ta Shiga ciki.

Kwance yake a saman wata doguwar sopa, daga shi se ɗan bom short na maza sanin babu wanda

Please Login or Register in order to submit comment