Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bata sonta? ummi takai maganar cikin zuciyarta.....amman a fili seta dubi meema tare da cewa"sakeni ni se yanzu kika san da haka lokacin da ake cewa ki gyara alokacin kike ƙi seyanzu da kika riga kika ɓata rawarki da tsalle, ai bakiga komi ba se ranar da sukai aure suka bar miki ƙasar baki ɗaya ma".ummi takai maganar tana kallona.
"Haba ummi kefa mahaifiyata ce dan ALLAH ummi kidaina min wannan mummunan bakin kina nufin bazan auri yaya ba, ummi ki saurareni kiji dan ALLAH ummi ki tausayamin kefa uwace agareni".nakai maganar ina janyota zuwa bakin gadonta biyoni tayi ta zauna"Ina jinki amman dai kinsan ni yanzu bana da wani taimko dazan muku sabida kinje wadda ta fini ta zugaki idan banda abinki kintaɓa ganin inda uwa taki ɗanta, meema gaskiyar danake gaya miki ita tasakafa a wancan lokacin kike guduna, kintafi wajan masu sonki ko baki san sakiyar da babu ruwa suke maki ba".Ummi ta kuma haɗemin waɗan nan karin maganar waɗan da suka kuma jefani cikin tashin hankali..........."Ummi kiyi hakuri wallahi ni ba gudunki nake............


*BARKAN MU DA JUMA'A KADA MU MANTA DA YIWA ANNABI S.A.W SALATI TARE DA ISTIGIFARI TUBA ZUWA GA ALLAH, ALLAH YASA MU DACE AMIN*
6/30/21, 11:15 PM - Buhainat: DZ


21 - 22


.................Bana gudunki ummina hasalima tsoron yadda kikemin faɗane yasa bana zuwa nan ɗin, kekuma sekiga kamar gudunki nake, Ummi ina cikin wani hali ina cikin halin jarabta, wanda umma ta kasa fahimtar hakan harta jefeni dawasu kalamai marasa daɗi a yanzu dana baro wajanta sannan kuma ummi nazo nan dan gaya miki damuwa ta nan ɗinma na kuma ganin wani tashin hankalin".Na numfasa tare da kallon ummi wadda ta mayar da hankalinta baki ɗaya gareni"Ummi kinji sakon baba gareni wai na daina fita school, Ita kuma umma tace sena je shine nace mata baze yuwu naje ɗinba sabida ya riga da ya hana, wannan shine dalilin dayasa umma ta fusata.................tiryen tiryen na bajewa ummi abinda umma ta gayamin" Bayan na gama gaya mata na tsirata da idanu ina son jin ta bakinta amman deaf down na zuciyata yana falo jinake kamar naje na rufesa da bugu domin nafi jin haushinsa over akan Rahina,Maganar ummi itace ta dawomin da tunani na"Duk naji bayaninki kuma wannan sako ta baki ki bani sabida tasan kebaki da hankalin gane wannan jurwayen nata, sabida ta riga ta gama ingizaki shine zata fara zamewa tana fiddo da halinta ƙarara, nidaman nasan naja'atu bata ƙaunarki kawai tai amfani da rikonki ne domin ta cutar dake harma dani, sannan gefe guda kuma tai amfani da hakan ne domin ta rinjayi mahaifinku amman babu komai ALLAH ya fita, ni yanzu babban tashin hankalina yadda zan fuskanci mahaifinki akan wannan auren naku".Takai maganar cike da ɗunbin damuwa"Ummi naji na yarda wallahi koda zan dena karatun baki ɗaya zan auri yaya kuma zanje na baiwa baba hakuri sannan na baiwa hajja fulani hakuri dan ALLAH ummi kada kubawa yaya rahina nice tasa".nakai maganar ina share hawayena,dafani tayi tare da dubana sosai"Naji dukkan kalamanki wanda ada ɗin ba laifinki bane domin kin gamu da mazuga ne waɗanda sukaita azaki har suka cutar min dake, kekuma dayake sakaryace marar kan gado kika kasa ganewa sabida wata banzar izzarki da jijji dakai da girman kai, wanda bai amafane ki da komi ba se tsiya ai daman kamar yadda ta faɗi ɗinne ta yaya zata bari ki ɗaga ga nata a zube ai impossible"! Ummi takai maganar cikin fushi.........."Ummi naji dukkan bayanki kuma na gane abinda yasa umma tai ta zugani ina gasa yaya ashe bata son nai aurene nabar su adda sakina amman ummi naji umma tana cemin tsintattar mage wai lokacin da kina farfaɗiya waya taimakeni idan ba itaba seda na girma nazama mutum sannan zan gujeta ummi ina son wannan fashin baƙin menene yasa baba ya baiwa umma rikona bayan yasan bakwa shiri?" najefa mata maganar ina kallonta, Da kallo ummi ta bini tana nazarta ta kafin ta mike taje gaban wadrop ɗinta ta kaya diba tayi tare da nufar corridow dress ɗin ɗakin, mintuna biyar ta shiryo cikin doguwar rigar atamfata tare da mayafinta jana tayi muka fita ɗan madaidacin falonta wanda xaka fara shigosa kafin ka shigo bedroom ɗin zama mukai asaman carpet kallona ummi tayi"Yau zan ɗan baki labarin dalilin rikon ki da umma tayi" tafada tana kallona sosai gyaran murya tayi xata fara mukaji karar bude ƙofar ɗakin,tun kafin na ɗago naji kamshin mayen turarensa lumshe idanuwa na nai tare da saka hannu na dafe saitin zuciyata "Ummi zamu wuce lasul tana sabida za,a buga wani wasa kuma nine zanyi masu coach Zamuje dasu Beby" sabida daman sunan dayake gayawa Rahina kenan tun kafin hakan ta faru wai yace sunan ta baya da daɗi shine yake ce mata beby, ada wannan suna baya ɗagamin hankali amman yau danaji ya faɗa sena na nemi miyaun bakina na rasa sabida yadda yay amfani da furta beby ɗin senaji tamkar da gayya ya faɗi hakan,"To ALLAH ya kaiku lafiya ka biya gidan ya kumbo Abu katahomin da sakon nan ma kawai".Ummi takai maganar kamar bata san dani awajan ba, ita kuma rahina tuni tai ɗakin ummi ta ɗauko blue ɗin hijabin dake saman gadon ummi ta saka ta fito, tunda suka fara ban ɗago ba bare nai kallon takaici haka suka gama sallamarsu bai kallan ba nima ban kallesa ba suka fita daga ɗakin.
Amai makon ummi ta nuna damuwarta sema farin cikin danaga tana faman yi sannan ta dubeni "Kina jina ko?"...........Wani takaici naji harda guntun hawayena nace mata "Ummm" batare dana ɗago ba sabida idan na ɗago hawayen ze falla samin sirrin boye,"Lokacin dana samu cikinku bana da lafiya domin bana iya komai sabida yadda cikin ƴan biyu keda girma sam hajja fulani bata barin nai komai hatta kwana seda hajja ta soke sabida tace kada cikina ya sami matsala, bare kuma mai gayya mai aiki mahaifinku kenan wanda ya ɗauki son duniya ya ɗorawa cikinku sabida kinsan ita fulani umma mata take haihuwa nikuma alokacin suna min zaton xan haifi namiji,Kasancewar haihuwar farko ce shine yasa ban san komi agame da haihuwar ba, wadda tun wajan kwana uku dazan haifeku nake nakudar tsaye itama kuma umman lokacin tana da tsohon cikin amira, sarai tasan ina nakudar amman bata gayawa kowa ba sabida kinsan bama shiri da ita...........bama dai faɗa amman kina kallon zaman namu kinsan bata kaunata sabida ita macece mai son gado da kishi.............Tana tunanin zan haihu da mahaifinku ga kuma yadda muke da mameey a lokacin kafin tabar nan wannan abun ta rike aranta harta sa suka hadan kai itada safiya matar waziri wadda ya aura bayan mameey tabar gidan........kwana biyu hajja fulani bata ganina gashi kuma ta saba ganin ina zuwar mata aikowa tai bayinta su dubani ko lafiya, anan zulaihat Amintacciyar baiwata ke gaya mata bana da lafiya, cikin kankanin lokaci sega motar asibitin cikin fada, nan da nan aka ɗaukeni aka kaini cikin motar, Zato zunubi nidai lafiya kalau na futa daga ɗakina amman lokacin da fulani umma tazo kaina ta shafamin wani ruwa a fuskata ban kuma sanin ina kaina yay ba haka naita jijjigar data zamo silar kashe kashen kuɗi awajan mahaifinku kafin asami wanda ya bani magani na dainata, wannan jijjigar danake idanuna su ƙafe ita naita yi har sanda na haifeku amman yayanki hassan baizo da raiba sabida yasha wahala wanda seda sarki yay kuka! kekuma lokacin kinci wuya sosai kwana na biyar bansan wake kainaba haka ake shayar dake tare da taimakon anty sa,a yayata da dije ƙanwata ganin haka yasaka hajiya iya mahaifiyata tace adawo dani gida amman fafur fulani hajja taki yarda, ita kuma lokacin fulani umma kullum tana like a wajena tana faman nan nan dani kamar ta ALLAH, cikin haka ta haifi ƴarta amira wadda tsiranku baifi sati uku ba,........wannan dalilin yasa babanku yace ta haɗeku duka ta raina sabida bana jin daɗi a lokacin nono kaɗai ke kawoki wajena, kuma yace wannan shine ze ƙara haɗe kammu sabida ko banza ƴata tana wajanta, da wannan damar ta samu tana juya komai yadda taso acikin gidannan wanda tsakani na da ita se ido agaban kowa tana nuna tana sonki haka zalika agabanki tana nuna tana sonki amman nina san bata kaunarki sabida nima bata kaunata, shikuma babanku mutum ne mai kara tare da ɗauke kai sam baitaba bibiyar halin da ake cikiba, sabida halin dattako irin nasa baitaba kawowa zata cutar masa dakeba sabida yaga iyayenmu na da suna bada ɗansu riko, wannan ne dalilin dayasa kika taso wajanta naso na karboki bayan na samu lafiya wanda aka nemar min magani acan kasar nijar wanda aka ce jifane, amman fafur taki bani ke harda sakawa babanku kuka sabida munafurci wai kada a rabaki da ƴan uwanki, da wannan ta yaudari kowa aka bar ki acan ɗin har ALLAH ya bani cikin rahina wanda anan ɗinma seda cutar nan tawa taso dawomin Amman ba kamar tadaba wadda har yanzu idan raina ya baci ko ina cikin wani hali ina riskar kaina acikin wannan yanayi na datsewar baki wanda ita take cewa farfadiya ce amman mukam munsan jifane akaimin da iska amman cikin hukuncin ALLAH komai yana warwaremin, wanda bada ban karfin ikon ALLAH ba da bazan zauna agidan nan ba bare harna haifeku saboda kowa yasan matar gidan nan bata kaunar kowa ya rabeta hatta dangin babanku bata sonsu musamman ƴan gidansu Abdul sabida tasan duk randa ALLAH ya dauki ran babanku tofa sarautar zata sauya ne ta koma kan waziri baban abdul wannan kwaɗayin ne yasa tace abdul ya auri ƴarta sakina, wannan bakin cikin ne yasa ta hanaki sauraran abdul bare ki aureshi, still bakin cikin datake ciki yanzu shine na auren Abdul da rahina sabida muɗin ne dai bata so..................
Nacewa babanku ki dawo nan yaki yarda wai sena aurar da rahina seki dawo nan babban tashin hankalin ban san yaya zan fuskantar da babanku wannan ZARGEN ba...........Tabbas umma tafaɗi kuma tai nasara a wannan wasan fatan a yanzu zaki gane komai cikin sauki kikuma ɗauka wannan itace ƙaddararki..........koda wasa karki fasa addu,a ni uwace na fuskance ki kuma na yafe miki kije ALLAH yay miki albarka".Ta numfasa bayan ta gama rattabamin wannan labarin da ban san dashiba"Naji ummi kuma na fahimta umma tana min kisan mimmikene wanda ban fargaba se yanzu,ummi yanzu maye mafita?" na jefa mata wannan tambayar"Addu,a zaki gaskiya sabida kin riga da kin nunawa Abdul - Naseer ƙololuwar ƙiyayyar da baze manta dake ba agaban idanunsa kin nuna bakya sonsa agaban mahaifanku ma haka agaban kawayeni agaban abokansa! tayaya zaki fahimtar dashi kina sonsa bayan kin gama nuna masa hakan wannan fa bakin cikin baze bar ran yaron nan ba wallahi ban taɓa ganin Abdul yay kuka akan abu ba se akanki amman kika baɗewa idanunki toka kika ki sekije ki addu,a idan da alkairi ALLAH ya dai daitaku".takai maganar tana tashi jin ana kiran sallah ashe bakaramin dadewa mukaiba.


Cikin sanyi jiki nima na mike tare da nufar hanyar fita cikin rashin makama duk jikina yayi sanyi, adai dai parking space na hango mota tana gyara tsaiwa cikin mintuna kaɗan rahina ta fito tare da afra da sadiq se Yaya dake fitowa shima daga ɗayan side ɗin cikin sauri su rahina suka nufi part ɗin ummi shikuwa bayan ya gama gyara komai part ɗin hajja fulani ya nufa, cikin sauri nima na take masa baya yau ayita ta ƙare................


*DA IZZATA NA KUƊINE 08142105218*
6/30/21, 11:16 PM - Buhainat: DZ


23 - 24


*Hy my fans gana gobe da safe sabida insha ALLAH zanyi uzuri bazan sami typing ba ina bukatar sharhinku sosai mussamman ƴan normal group ɗina sabida yaufa ƴan vip sun riƙe wuta sosai*


Ban damu da yadda bayi ke shawagi acikin harabar masarautar tamu ba, haka naja kafafuna cikin sauri nake bin bayansa sabida yadda yake tafiya cikin zafin namansa wanda yake cike da ƙarfi da lafiya tare da ƙuruciya, ganin ya wuce kofar falon hajja fulani ya zaga ta baya nasan part ɗinsa ze shiga na ɓangaren cikin azama na kuma hamzarta saurin nawa, yana gaf daze turo kofar falonsa na dannata da karfi tare da faɗawa cikin ƙayataccen falon nasa wanda yagaji da haɗuwa gefe guda gawasu haɗaɗɗun royal chair's masu uban kyau masu kalar royal blue and golden. lumshe idanuna nai tare da zubo da ruwan hawaye hancina yana shakar kamshin turaren daya cika falon, zuciyata rawa takemin haka zalika ina jin wani irin sanyi tare da tausayin kaina ainin, buɗesu nayi tarwai akansa yana tsaye agabana tare da zube hannayensa cikin aljihun wandon farar shaddar jikinsa kansa babu hula se tulin sumar daya kwantar da ita tasha uban gyara bakaramin kyau yay min ahakan ba jinake daman mu dauwama ahakan sake ware idanuna nai akansa gani nake tamkar yana hararata, sosai naga ya hade ransa tare da zaromin mayun idanunsa waɗan da ada suke min wani iri amman a yanzu tsoro suka bani tare da kwarjini"Menene kika biyoni kasheni kika zo kiyi?" yafaɗa yana kallonta ganin yadda ta kuma zaro idanunta waje alamun tsoro kallo guda ɗaya yay mata ya gano lagonta.........Rau rau nai da idanuna"Nibazan kashe kaba amman kai zaka kasheni".nabasa amsa kaina tsaye"Akanme zan kasheki sedai keda bakya kaunata ki kashe kanki sabida kina takaicin ganina a duniya koh?" yakai maganar yana ɗagemin girar saman idanunsa........awannan karon na kasa daurewa kuka na saka tare da dafoshi duk da yadda tsahona bai kaiba"Wallahi ina sonka kada ka yarda su rabamu" ban kai karsheba sabida kukan dayaci ƙarfina.........Lumshe idanunsa yayi tare da cije ƙasan laɓɓansa yanajin dukkan tsigar jikinsa ta miƙe"Kin makaro asmah lokacinki ya kure bai kamata ki faɗi hakan a yanzu ba sabida lokacin daya dace ki furta hakan ya tafi shiyasa lokaci keda matukar mahimmanci ga ɗan adam".....yana kuma gayamin haka ya cire hannuna daga jikinsa "Idan kin gama kijamin kofata" yafaɗa tare da nufar cikin bedroom ɗinsa da sauri.......cikin wani irin yanayi na saki kukan takaici banyi wata wata ba na mara masa baya cikin xafin nama nakai cikin room ɗin nasa kwance na hangoshi saman gado yay ruf da ciki kamar shima yana cikin damuwa, kuka na saki da karfin gaske tare da binsa cikin wani irin yanayi na faɗa saman bayansa hannayena na saka duka biyun na rungumo kirjinsa tare da zuba masa dukkan nauyin samana"Yaya duk bakin dayace so baya komawa yace ƙi kasan ALLAH ka auri rahina kashe kaina xanyi........nakai maganar ina gunjin kuka.......sam ya gasa taɓuka komai wannan yarinyar xata kasheshi ne ta riga ta sakar masa kasala tun a farko gashi kuma yanzu tazo ta zuba masa uban breast ɗinta ajikinsa.....lumshe idanunsa yayi tare da yaƙi wajan jawo numfashinsa sannan ya aro jarumta wajan birkitota gabansa hannayensa guda biyun ya saka ya bata waje akan cinyarsa yana jin yadda kirjinta ke faman rawa ga hawaye da majina na gudu bisa kirjinsa yana mata zaton mata masu kishin tsiya wanda ta kasa boyeshi akan ƙanwarta........saukar hannunsa naji akan fuskata yana ɗaukemin hawayena kallonsa nai da jar fuskata ganin babu alamun wargi yasa nai luff ina jin sautin bugun zuciyarsa, "Saukarmin akan cinya anty nifa surukine tayaya da izzarki zakina kuka akan mijin ƙanwarki kuma ƙasƙantaccen mutum ɗan ball ɗin daya rasa club?".........ya furta hakan a wawware tare da tureni daga jikinsa cikin wani yanayi na rashin makama na kuma cakumarsa tare da rungumeshi ƙam tamkar zan haɗeshi"Nifa wallahi ba yadda kake xato bane yaya babu wanda ya kaini sonka wallahi ko mameey sedai ta nunan ita uwace dan ALLAH kaimin hakuri baxan.......,ban idaba naji ya tureni ɗagowa nai ina kallonsa idanunsa ya kaɗa yay jajur tamkar gaushin wuta"Asma idan kika kasheni seki xuba ruwa a kasa kisha duk wannan masifar da bala'in ubanwa yaja mana so kike ki jefani a halaka agaban kowa kika nuna bakya sona sanin kankine iyayenmu basa magana biyu bare akanmu su soma sabida haka kiyi hakuri ALLAH yayi ni ba mijinki bane and kuma ina son ki daina raɓoni sabida gudun halaka".......yana faɗamin haka ya tureni baki ɗaya ya mike yay hanyar toilet"ya......., ban karasaba"Shii dan ubanki maza tashi kibarmin ɗakina uwarwa tace kije kiyi hauka ai gashi nan tun yanzu kin soma gani wallahi na kuma ganin ki a side ɗina sena ɓallaki banza shasha sha kuma kije ALLAH ya isana......." yana kaiwa nan ya banko kofar ban ɗakin cikin fushi yana ayyana asmah! ta cuceshi ta gama da shi baze yafe mata ba wallahi harse ya aureta.......kuka na saka ina bin kofar da kallo cikin rawar jiki nabar ɗakin.............


AFUWAN🙏
6/30/21, 11:16 PM - Buhainat: DZ


25 - 26

*SAƘON GAISUWA GAREKU MY VIP GROUP ABDUL NASEER ALIYU ADAM DAULA! YACE YANA MUKU SONSO KAMAR YADDA KUKE MASA YAKUMA CE KUYI HAƘURI MEEMA TA GAMA NATA LOKACIN SHIMA YANZU NASA YA KAMA*

Cikin sauri nake taka ƙafafuna ina yi ina sharar hawaye batare dana san inda na nufa ba, tsayawa nai a bakin ɓangaren hajja fulani zuciyata tayi niyyar shiga wajanta amman tuna masifar tsohuwar yasa na kuma jan ƙafafuna nabar wajan direct hanyar fadar baba nayi abin takaici yawan fadawa da dogarin dana gani a bakin wajan nasan cewar yau ana zaman majalissar fadane nasan baba baya da lokacina acikin irin wannan yanayi,Cikin rawar jiki nabar wajan hanyar garden nayi batare danai tunanin komai ba na dakata a bakin katuwar bishiyar mangoron dake garden ɗin batare danai nazarin magariba tayi ba haka na zauna a wajan na tusa kaina cikin tsakiyar cinyoyina kuka! na saka mai ƙarfin gaske sanin babu wanda ze jini tabbas nasan nai kuskure a baya amman miyasa sam Abdul-Naseer yaƙi fahimtata mai yasa ummi bata bani ƙwarin gwiwa akan saba? kodai akwai matsalane? sosai nake kuka acikin wannan Yanayi wanda zuwa wani lokaci zazzafan zazzaɓi ya rufeni ko gani banayi kaina kemin mugun ciwo a hankali na mike ganin duhu ya shigo ciki sosai idan banda ƙarar kukan tsuntsaye babu abinda kakeji acikin garden ɗin. Ina gaf da fita naji wani irin danshi ta cikin tsakiyar ƙafafuna kafin wani lokaci wani mahaukacin zafi ya ziyarci cikin jikina baki ɗaya, bansan lokacin dana zabga wani irin ihu! ba wanda ya amsa ilahirin cikin wajan ban kuma sanin ina kaina ikeba, nidai na farka naganni a kan gadon fulani umma duk su umma harma dasu Rahina suna zazzaune agefena hannuna ɗaya yana cikin na Rahina ƙanwata wadda taketa faman share hawaye, mirginawa nai kaɗan tare da ɗago ƙafata amman naji na ƙasa"Lah adda meema ta bude idanunta" Cewar rahina wadda ta faɗa cikin sauri, kafin naga dukkansu sunyo kaina suna faman min sannu"Keko meema miya kaiki garden da daddaren nan har maciji ya cijeki a ƙafa?" Cewar umma kenan wadda fuskarta take babu yabo babu fallasa"Haba umma dame zataji da tambayarki koda zafin ciwonta ai tambayarta ya jikin ya dace ki somayi".Cewar adda zainaba kenan ɗiyar umma ta biyu wadda daman duk cikin ƴaƴan umma tafi sona saninta tun asali ita bata da ruwa da halin umma,Babu wanda ya tanka mata idan banda sannun da ake faman yimin jakadiyace a gefena cikin sauri ta mikomin wani magani tare da ɗago kaina ta bani na sha sannan tai min sannu ta kuma ficewa, itama umma fita tai haka zalika adda sakina da amira suka fice, Saura ya rage Rahina da adda zainab idan banda sannu babu abinda rahina kemin wadda daga gani jitake kamar ciwon ya dawo jikinta, wannan magani da jakadiya ta bani shiya sakani naɗanji saukin zafin ƙafar tawa duk da anyi min allurar kashe dafi, "Rahina ɗagoni muje ɗakina zanyi alwala" nafada cikin aro jarumta sabida yadda zazzaɓin ke kuma kawon cafka cikin kulawa adda zainab tare da rahina suka tarairayen muka fita a zaune muka wuce umma tare da adda sakina da amira waɗanda basu wani damu da halin danake cikiba, bayan mun kai ɗakina dakanta adda zainab ta haɗamin ruwa mai zafi ta taimakamin na shiga wanka tana tsaye abakin kofar na gama na fito ta kuma bani nai alwala, ita kuma rahina ta shinfida min abin sallah wadda naita da ƙyar sabida rawar da jikina kemin, fita rahina tayi mintuna kusan goma suka taho tare da bayi guda biyu hannunsu ɗauke da manyan tire anjeron kayan abinci seda adda zainab taimin jan ido nasha ruwan shayi sannan ta ɓallomin paracetamol, nasha ina kakarin amai sanin bana ƙaunar shan magani ko kaɗan, sallama adda zainab taimin tace xataje ɗaki tai karatu gobe tana da exams, nima mikewa nayi da ƙyar na haye kan gado ina rawar ɗari, cikin tausayi rahina tayo kaina"Adda meema zan kwana wajanki sabida naga baki da lafiya bansan mi dare zeba, gashi ummi tace karmu zo part ɗinta sabida baba ze faɗa" tafada kamar zatai min kuka!"A,a rahina je abinki karki damu nagode da kaluwa" nafadi maganar a rarrabe sabida yadda hakorana ke faman karo dana juna, Kamar zatai kuka ta juya tabar ɗakin bada ban anbamu tarbiyar bin maganar babba ba nasan da babu abinda ze hana Rahina ta kwana a ɗakina ganin yadda tai kamar zata saka kuka araina na ayyana lallai naka nakane, Cikin rawar jiki naja katon bargon daya rufen ko ina na kwanta ina curewa waje ɗaya.


Abdul-Naseer bayan ya shiga bathroom ɗinsa dafe bango yayi yana ɗigar da hawaye yana ji acikin ransa babu wanda ya musu wannan cutar kamar meema badaban taki basa haɗin kaiba ai da tuni yanzu anwuce wurin ko ɗazu bayan yabar wajan baba waziri seda yaje har cikin fada wajan sarki, akaro na farko a rayuwarsa daya taɓa roƙar sarki abubakar alfarma akan dan ALLAH ya janye aurensa da Rahina shiyaji ya yarda ze zauna da meema koda bata sonsa ne amman sarki yaƙi daga ƙarshe ma yace aikin gama ya gama, wannan baƙin cikin shiya kuma sakawa ya ƙara jin haushin meema sabida ya dangana abun da itace silar wargaza masa farin cikinsa wanda baya fatan yaji wannan takaicin shi kaɗai yafi son itama taji kamar yadda yaji.......seda yaji fitarta sannan yay alwala jin ana kiran magrib ya fito waje kai tsaye hanyar masallaci ya nufa koda aka idar da sallah wajan hajja fulani ya tafi.........tana zaune a falo baiwa guda tana dama mata fura ganinsa yasa ta faɗaɗa far,arta tare da sallamar baiwar sabida tasan mutumin nata bayason mutane sosai......da kanta ta karasa damun furarta bayan ta gama tai masa tayi amman fafur yaƙi sha kamo tashar kallon ƙwallon ƙafa yayi"Kaifa tsiyata dakai kenan kana zuwa zaka damen da wannan shirmen naku" takai maganar tana jan tsaki kaɗan.......murmushi ya sauke "Haba hajiya sana,ar danake son na kaiki makka da ita shine kike cewa shirme"......yakai hakan yana dariya daman yasan idan yazo wajan hajiya koba komai zeji sanyi a ransa"Nikam ALLAH ya suttura duk makkan danaje ada aiba kai ka kainiba tun ubanka yana goye nake zuwa hajji dan kaji" takai maganar cikin zolaya........."Nima ina son na kaiki da kuɗina da gumina hajiyata kedai kimin addu,a kawai" yakai maganar cikin serious........"Addu,a kam kana shanta ɗan albarka nidai fatana idan katafi da yarinyar nan can ƙasar ka riketa amana kodan ƴan hassadar gidannan suyi kuka" shafa sumar kansa yayi tare da kallon hajiya batare dayace komiba ya tashi ya nufi hanyar waje"A,a Naseeru ina zakaje kuma ina maka maganar arziki" shafa kwantaccen sajen fuskarsa yayi "Hajiya zanje wajansu faisal nai kallon ne naga anan zaki damen da surutunki kamar aku" yakai maganar yana daka tsalle yabar falon sabida yasan bazata barsaba...........koda ya fita daganan masallaci ya kuma nufa still yay sallar isha'i sannan yay part ɗin ummi yana son yaci abinci anan ɗin.
Sallama yayi a babban falon ummi tana zaune akan dadduma tana lazimi rahina kuwa ta rafka tagumi itafa hankalinta yana kan addarta, sam ta kasa nutsuwa tunda ta baro meema tai kukan tai kukan harta gaji ummi bata kulata ba"Beby mike damunku keda my afra naga kowa fuska babu daɗi?"yafaɗa tare da ɗaga afra ya ɗora akan cinyarsa yana ji da afra yarinyar babu inda tabar asmeen sa shiyasa yake sonta..........shuru rahina tai masa batare datace masa komiba sedai hawayen datake saukewa da hannunta......ummi ce ta dubesa bayan ta shafa addu,arta"Rabu da shirmenta wai meema ce maciji ya ciza a ƙafa dan na hana suzomin nan shine take kuka".ummi takai maganar tare

Please Login or Register in order to submit comment