Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RAMADAN GIFT KWALLIYA Complete Hausa Novel Document by RAMADAN GIFT KWALLIYA


RAMADAN GIFT KWALLIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 5186



RAMADAN GIFT KWALLIYA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 09, May 2023

Author: Fadila Sani Bakori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 08063830828

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 29.08 kb

File Type: txt

Views: 926+

Download: 313+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: 👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikin ki)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT

Assalamu alaikum.Barkanmu da shigowa wannan wata mai albarka watan Ramadana. Allah Ubangiji ya karb'i ibadun mu amin.
Auntyna Bashaushe ya ce in ki na da kyau ki k'ara da wanka .Amarya,Uwargida har da ma 'yanmata, wannan garab'asa ce gare ku, wadda za ku gyara jikinku da kud'i k'alilan, ba tare da kin kashe kud'i masu yawa ba wajan siyan man bleaching ,wanda amfani da shi had'ari ne ,dan zai iya b'ata miki fatar jiki ko ya sa miki Pimples ,ko sunburn, da dai dauransu.
Auntyna wannan hanya ce da za ki gyara kanki da kanki ta hanyar amfani da kayanmu na gida,wato kayan gargajiya.

Wato ita dai ranar sallah rana ce wadda Uwargida take k'ure take son kure wankanta wajan yin adon da zata birge mai gida da sauran k'awayanta da zata ziyarta.Hakan ne ya sa na ka kawo muku wannan garab'asa.

Auntyna ki sani duk adon da za ki idan ya kasance fatar jikinki na da matsala irin ta black sport, ko Pimples ,sunburn da sauran su suna tauye mi ki kyan ado.

Idan ki na so ki ga fatar ki ta yi fresh ,ki ga tana glowing, ya zama dole sai kin kiyaye wa'innan abubuwa guda Bakwai (7) da zan lissafo.

Yawan Aitaka wad'annan abubuwan guda Bakwai (7) na sanya fata saurin tsufa da Yamutsewa.

Kowane mai rai dole ne wata rana ya tsufa. Amma akwai abin da in aka yi wa fata zai sanya ta tsufa da wuri. Kuma dole ne mu yi iya kokarin barinsu. Abubuwa da suka hada da  rashin bacci da yawan gajiya da amfani da kayan kwalliyar da ba ta dace da fata ba. Yawan shan taba da kuma yawan cin naman shanu bayan an bai wa shekara arba’in baya.
1)- Gajiya: Yawan gajiya da shiga damuwa na matukar sanya fatar jiki tsufa. Idan mutum ya shiga damuwa, fatar na fitar da wani abu ‘cortisol’. Wannan ‘cortis’ din yana yi wa fata dameji. Sai a ga mutum ya tsufa da wuri. Shi ya sa sai a ga wanda yake cikin damuwa da talauci yana riga sa’anninsa tsufa da ke birni,  kuma cikin jin dadi. Don haka sai a yi iya kokarin rage sanya kai tunani da damuwa.

2)- Kayan kwalliya: Akwai wasu kayan kwalliya da ke dauke da sinadarai kamar su;  zinc odide da dimethicone da propylene suna iya sanya fata tsufa, musamman idan an yawaita amfani da su. Wasu sinadaren suna bata fuska kaikayi daga nan sai fesowar kuraje har fuska.


3)-Taba: Yawan shan taba na sanya tsufar fata da wuri domin wannan sinadarin da ke cikin sigari nicotine, wanda ke toshe magudanar jini. Shan tabar na sanya fata ta sake karfinta. A rage shan taba saboda tana janyo tsufar fata.

4)- Yawan cin soyayyen abinci da cin abinci a kan kari ba don yunwa ba na sanya fatar jiki kiba, kuma hakan zai janyo fatar fuska cika, sai a ga mutum tsabagen kiba ya fi shekarunsa.

5)- Yana da kyau mutum ya san irin nau’in fatarsa kafin ya yi amfani da kowane irin sabulu. Idan sabulu bai dace da fatar mutum ba, zai iya sanya tsufan fata.

6)- A rage cin abinci mai dauke da mai, musamman idan shekaru sun ja. Bai kamata idan an kai shekaru arba’in a rika cin naman shanu ba. Yawan cin irin wadannan  abubuwa yana janyo ciwon kafa da sanya mutum tsufa.

7)- Yana da kyau a rika samun barci a kalla awa bakwai a kullum. Rashin samun barci a kan kari na sanya tsufa da wuri.

Fadila Sani Bakori ce.


👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828

RAMADAN GIFT

Assalamu aliakum, barkan mu da warhaka,Ya ibada .Allah ya karb'i ibadunmu ameen.

Auntyna ki gwada wannan had'in ki gani kafin Sallah za ki ga yadda fatar jikinki za ta yi fresh tana glowing ,ta na d'auke ido kamar wata Zinariya.


Shin ko kinsan sirrin da ke d'auke da Kurkum .Gwada bin Hanyoyin nan ki sha mamaki 👇🏻

Yana da kyau a kullum bayan kin yi amfani da hanyoyin da za mu kawo mi ki ki kasan ce mai yawan wanke fuskarki, kafin ki kwanta barci, ya kasance babu maik'o a jikinta.Hakan na taimakawa sosai wajan k'ara fito da kyawun fuska.


Ki samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun. 

Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi.

Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata. 

Yadda za ki yi amfani da Kurkum Wajen Gyara Fatarki Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni ba . 

Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da amfani da kurkum idan an zo kwalliya.hakan zai kara haska fuskarki.


Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar ta fita 

- A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi. 


Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. 

Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako. 

- Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka. 

- Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.


 - Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsawon mintuna 10-15 kamin a wanke ki sha mamaki Auntyna.

Kurkum,na taimakawa sosai wajan magance matsaloli irinsu, Pimples,Sunburn, Black sport da sauransu.


Fadila Sani Bakori ce

👑 KWALLIYA 👑

(Hanyoyin da za ki bi ki gyara jikinki)



🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌


Daga Fadila Sani Bakori
08063830828


RAMADAN GIFT



ABUBUWAN DAKE KAWO KURAJEN FUSKA DA YADDA ZA A MAGANCE SU.


Kurajen fuska suna taka mihimmiyar rawa wajan dishashewar kwaliyar uwargida,hakan ya sa yau na zo muku da hanyoyin masu sauki da za ku bi dan magance su.


Kurajen fuska na pimples matsala ce da ta'addabi matasa Mata da Maza musamman masu kananan shekaru wadan da suka fara balaga saboda samun canji daga sinadaran hormones. 

Duk da kurajen fuska suna Kama Mata da maza, Amma Mata sunfi damuwa saboda za kaga har nikab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga ta’adin da kurajen su ka yi musu a fuska.

Kurajen pimples ba a fuska kadai suke fita ba suna fita a wadannan wuraren:

- Kirji 

- gadon baya

- Cinya

- wuya 

Abubuwan da suke taimakawa wajen tunzura kurajen fuska:
-  Yawan cin Abu Mai maiko.

- Amfani da mayukan da Basu dace da fatar jiki ba

- Kwayoyin cuta

- Shiga rana sosai

-  Shan wasu magunguna

Abin da ya kamata ayi domin kariyar yawaitar kurajen fuska da samun waraka sune:

1- A rage amfani da abinci masu maiko dayawa.

2- Idan kuraje suka fito kada a yawaita tabawa.


3- Idan za ki yi doguwar waya kada ki daura wayar a fuskar ki ko kusa da kurajen.


4- A samu ruwan dumi a matsa lemon tsami a wanke fuska da shi a kalla so biyu a rana.


5- Idan kurajen a kirji ko baya ka da ayi amfani da matsattsen kaya saboda samun iska.


6- Za'a iya shafa zuma bayan dan mintuna a wanke da
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RAMADAN GIFT KWALLIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album