Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BANI DA ZABI Complete Hausa Novel Document by BANI DA ZABI


BANI DA ZABI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 108311



BANI DA ZABI

Reading Time: 9 Hours

Added On: 27, Feb 2025

Author: Hafsatou Amjad ,Mhizz Jiddherr ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 582.11 kb

File Type: txt

Views: 66+

Download: 128+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: [9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋

```
Love,fate,Sympathetic and romance story ```

©️®️
Hafsatouamjad*

&

*Mhizz jidderh*





*Page 1.*







1:40pm daidai agogon office din ya nuna, ɗago kansa yayi cike da gajiya sannan ya mike a nutse bayan ya Tattara files ɗin dake gaban shi ya mayar da komai position ɗinsa, wayar sa yayi packing da briefcase ɗinsa sannan ya fito daga office ɗin, direct parking space ya nufa motor sa ya shiga sannan ya fice daga babbar maikatar tasu.



A daidai wata unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi yayi parking a daidai inda yasan take wucewa, seat ɗin ya ɗan ja baya sannan ya ɗan kwanta akan kujeran cike da gajiya ya lumshe idon sa tsayuwar sa baifi da 5min ba, wata kyakyawar yarinya ta b’ullo daga wani street kanta akasa take tafiya , tana Sanƴe da uniform ɗinta blue and white da sukayi matuƙar amsar ta, mini skirt ne blue se rigar data kasance white babu ɗankwali akan ta tayi parking yalwataccen gashinta da ribbon, physical appearance ɗinta kawai ze tabbatar maka da Christian ce .



Bude idon sa yayi tarr akan ta ganin yanda a kullum take kara masa kyau a ido, zuciyan sa yana tafarfasa ganin yanda santala-santalan cinƴoƴin ta suke a bude, runtse idanun sa yayi yana jin babu daɗi aran sa da yanayin shigar tata.



Har ta ƙaraso kusa da motor sa zata shige street ɗinsu da sauri ya bude motor ya fito

"Jennifer?"



Ya kira sunan ta, for the first time da taji ya bata tausayi saboda yanayin yanda ya kira sunan nata in a pitty voice.



Dake wa tayi sannan ta juyo a hankali ta kalle sa.



Kuma marairaicewa yayi kamar zeyi kuka yace "Jennifer maiyasa kike azabtar dani?."



Ta6e baki tayi ba tare da tace masa komai ba

"For God sake ki bani dama please" shiru ta Kuma yi ba tare da ta ce masa komai ba.



Kneeling yayi da gwiyoyin sa a ƙasa yayi rolling hannun sa alamun seeking.



Zaro ido Jennifer tayi tace "Get up."

Maƙe kafaɗa yayi yace "Bazan tashi ba har sai kin yi accepting."



Ba yanda bata yi ba amman yaƙi tashi, ganin da gaske ba zai tashi ba yasa fargaba ta kamata

kar brother ta yazo ya Sameta Dan tasan definetly sai ya faɗawa Mama.



"Get up please" ta sake faɗa.





"No I Won't."



Jujjuyawa tayi ganin Gang ɗin su Emeka yasa tace "tam ka tashi naji I will think about it."



Miƙewa yayi cike da farin ciki yace “Yeeessss, am coming back tomorrow early in the morning I can’t wait."



Ya fada yana ƙayattacen murmushin da ya ƙara mishi kyau.



Kallon shi tayi tace "See you."

"Thank you puppy love" ya faɗa.



Murmushi tayi tayi gaba da sauri kar Emeka ya sameta.



Cike da farin ciki Ousman ya shiga motor sa yana jin nishaɗi aran sa.



Tun lokacin daya fara ganin Jennifer ya fara sonta, he can’t express his feelings akan ta, bai ta6a son wata mace a duniya ba sai Jennifer duk da ƴan mata da yawa suna crushing akan sa, bai ta6a basu fuska ba kasancewar sa kamili mai nutsuwa da ruƙon addini yasa yake da ƙwarjini a idon mutane.



Yau kimanin 3weeks kenan kullum sai yazo, amman in zai yi maganar duniya Jennifer bata kula sa.



Sai yau!, Shiyasa ya tsinci kansa a cikin matsanancin farin ciki .

Dan he never think ma zata kula shin

Yana driving yana murmushi harya ƙaraso gida.



Horn yayi mai gadi ya buɗe masa ya Wulla hancin motor sa cikin farfajiyar gidan, inda aka tanada Dan killace motoci ya nufa yayi parking motor sa cikeda kwarew, sannan ya fito ahankali.





Cikin gida ya nufa hannun sa riƙe da wayan sa dayan hannun kuma dauke da briefcase ɗin sa.



Boys quarters din su ya nufa ya shiga side ɗin sa wanka ya fara yi first, yana fitowa ya shirya cikin ƙananun kaya da suka amshe sa, sannan ya shiga cikin gida ya shiga dan yin lunch.





********************



Yana wucewa tayi saurin shiga street ɗinsu, kafin su idda ƙarasowa ta shiga gida.



Sanin da tayi Mama nacan tana jiran ta yasa tayi sauri ta cire uniform ɗinta, ta saka rigar ta data tsaya mata iya gwiwar ta sannan ta fito a ɗakin, Emeka tayi ma sallama ta fito daga gidan.



A bakin tasha inda rumfar mama ta saida abinci take, anan tayi Landing tana zuwa ta gaida mama sannan ta kama mata aiki sunayi suna hira gwanin ban sha'awa.





***************



Bayan ya gama cin abinci a cikin gida ya dawo side ɗinsa, coz he have a lot to cover, study room ɗinsa ya shiga ya fara aiki a laptop nasa.





Washe gari da safe before yaje Company sai da ya fara tsayawa a street ɗin su Jennifer, tsayuwan sa bai fi da 3mins ba sai gata nan ta taho as usual cike da nutsuwa abunda yake ƙara sawa ousman sonta kenan, Tana ganin motor sa gaban ta ya faɗi ,dakewa tayi sannan ta karaso.



Fitowa yayi ya tsaya tare da Folding arm ɗinsa yana jiran answer ta.



Sunkuyar da kanta kasa tayi sannan tace "Yes."



Wani zaro ido yayi cike da farin ciki yana kallon ta kamar zai maidata ciki "Jennifer?."

Dagowa tayi ta kallesa, ganin irin mayattacen kallon da yake mata ne yasa tayi ƙasa da kanta tana smiling ita kanta tasan she have feelings for Him.



"Thank you puppy love, I promise to take good care of you bazan bari kiyi kuka ba."



Girgiza kanta kawai tayi cike da shauƙi, finally she is in love.



Ganin da tayi lokaci na ƙurewa kar Emeka yazo ya sameta yasa tace masa "Zanyi late."



"Toh take care of yourself am coming back later."



Wucewa tayi ba tare da tace mishi komai ba, cike da farin ciki ya koma motor sa yaja da sauri yana cikin nishaɗi.







*BAYAN SATI BIYU*





Zuwa yanzu soyayyah Jennifer da Ousman tayi ƙarfi, sunyi matuƙar shaƙuwar da su kansu suke mamakin kansu cikin sati 2 kawai komai ya canza wa Jennifer, kullum inya tashi daga aiki zai zo as usual su ɗan ta6a hira kafin ya wuce sai da yamma ya kuma zuwa a street ɗin kasuwa suke tsayawa inda ba wanda zai ganta.



Ousman bashi da burin daya wuce ya saka Jennifer cikin farin ciki a koda yaushe yana faranta mata, ko cikin damuwa ya ganta kafin ya tafi sai ya tabbatar da ya saka ta farin ciki.

Yayi matuƙar winning heart ɗin jennifer sunyi tsaftacacciyar shaɗuwa da juna.



Duk da yasan Bambancin addinin su da al'adar su hakan bai ta6a bashi damar yi mata misbehaving ba ko ya ta6a ta ba, kasancewar sa kamilun mutum ,hakan ne kuma yasa jennifer take ƙara jinta comfortable duk lokacin da suke tare, baya mata wani zance da bai kamata ba Bare yayi requesting ta6a ta.



Saboda shi soyayyar da yake mata acikin jinin sa yake bai ta6a jin son wata ƴa mace a zuciyarsa ba kamar ta m, ji yake in babu ita ba zai rayu ba.





Jennifer ce zaune a class ta rabka uban tagumi, a duk lokacin da zata zauna tana tunanin ya Mama zata fahimta al'amarin nan idan ta gane tana soyayyah da ɗan Muslimi, yanda mama a kullum Jan kunnen ta akan ta shine ta guji soyayyah da musulmai, musulmi basu da kirki basa rike aure.



Ita kuma yanzu tazo stage ɗin da ba zata iya rayuwa babu Ousman ba, duk lokacin da ta zauna bata da tunani sai nashi, tsabar soyayyah da take mishi in ta tunashi har kuka take, yana da kirki sosai yana kyautata mata shiyasa zuciyar ta ta aminta dashi takejin shi acikin jinin ta.





Ngozi da tun ɗazu ta zauna kusa da Jennifer tana ta mata magana, ganin hankalin ta baya kanta yasa ta ta6a ta.



Zabura Jennifer tayi dan ba kaɗan ba ta shiga duniyar tunani.



Kallon ta tsaf Ngozi tayi tace "Jennifer meke damun ki haka, kina so ki jama kanki wata matsala ne?, kin zauna kina ta tunanin abunda ba zai fitar dake ba, What’s wrong with you?"....................









_*Idan kin karanta kiyi sharing fisabilillah👏🏽*_







*Ku sani yawan Comment ɗinku shine ƙwarin guiwar mu, ba zamuyi posting next page ba sai kun nuna mana soyayya ta yadda zamu fahimci lallai kunji daɗin wannan labari da yazo da salo na musamman🥰*









*AMJID...........✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋


©️®️
*Hafsatouamjad*

&

*Mhizz Jidderh*





*Page 2*









✍️Fuskar tausayi Jennifer tayi sannan tace "Ngozi am in problem.



Zaro ido tayi tace "toh fah, what’s wrong tell me please."



Batare da Jennifer taji nauyin ta ba ta zayyane mata komai kasancewar ta babban aminiyar ta a kaf makarantar.



Jugum Ngozi tayi tana kiyastawa aranta daman itace ta samu dama irinta Jennifer .

"Karki damu kanki, tunda kina sonshi kuma yana sonki, and kince yana da kuɗi sosai duk da nasan ke you’re not concerning about his wealth, dani na
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BANI DA ZABI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album