Join Our WhatsApp Group

DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1 Complete Hausa Novel Document by DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1


DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11781



DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 01, Nov 2023

Author: Aisha Biciki ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 67.3 kb

File Type: txt

Views: 2042+

Download: 814+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: ο»ΏAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_

Page 1


πŸ”œ
_Alhamdulillah dukkan godiya yanaga Allah daya sake bani aron lokaci domin rubuta DAN DAUDU KO DAN LUWADI wanda na dad'e inaso na rubuta saidai abubuwa sukasha kaina_

_Labari ne daya k'unshi fad'akarwa, ilimantarwa, zaburarwa, gami da nishad'arwa hardama soyayyah._

_ina fatan Allah yabani ikon rubuta abunda zamu k'aru dashi, ya haneni rubuta abunda zai zamo silar lalacewar mu, ina fatan idan kun karanta kuyi aiki dashi musamman iyaye mata da matasa._


*Ina maraba da dukka masoyana a duk inda suke a fad'in duniya, harma mak'iyana ina alfahari dasu sai dai ina rok'on Allah yayi mun tsari da sharrin su*


Don Allah duk wacce takaranta tayi share basai anyi nisa kuyi ta cewa daga farko ba plxπŸ™







✍
SABITU kyakkyawan saurayi ne matashi wanda a k'alla zai kai shekaru 27, zaune suke shida abokan sa'idon sa a bakin titi jikin shagon abokin su, kullum anan suke wuni sa'ido kasancewar basuda wani sana'ar yi, duk wanda yazo wuce wa sai sun tofa albarkacin bakin su, ko mota ce ta wuce sai sunyi magana akanta kullum aikin kenan.

Yauma kamar kullum zaune suke sun jeru akan bencin dake jikin shagon, wata dalleliyar motace ta tsaya a gabansu, dagani kasan kud'in ta ta zarce tunani, sake baki Sabitu yayi yana ayyanawa a ranshi inama shine a cikin wannan motar, har hangoshi yayi tare da sabowar budurwar shi aciki suna zaga gari, don dama Sabitu badai neman mata ba, zungurin da abokinsa Nasir yayi masa ne ya dawo dashi daga duniyar tunani.

"kai d'an iska tunanin me kakeyi ne haka".

Nasir yafad'a idon shi akan motar, burin su suga wani hamshak'in ne aciki, duk sun zuba ido burin su suga mutumin dazai fito aciki, koma yayane dai sun san ba k'aramin mutum bane.

Sabitu ya bud'e baki zaiyi magana wata had'add'iyar budurwa ta fito aciki, gaba d'aya zuba ido sukayi harda hanci suka kasa motsi domin ba k'arya ta had'u iya had'uwa.

A gabansu ta tsaya muryar ta ashak'e kamar me mura ta ce "don Allah ina tambaya ne"!

Da sauri Nasir ya ce "kiyi tambayar ki domin babu wanda bamu sani ba a anguwar nan".
Taji dad'in amsar don haka ta ce "Alhaji Ma'aruf! Ko kunsan gidan shi"?
Ai kafin wani yayi magana Sabitu ya amshe da fad'in mak'wabcina ne muje nakai ki har gidan shi".
Nasir najin haka ya ce shima wlh sai yaje don Sabitu bazaiyi rakiya shi kad'ai ba, sauran nata washe baki sunga had'add'iyar budurwa.

Wani irin k'amshi me dad'i motar take fitarwa, gaba d'aya sun shagala ganin cikin motar komi nata daban, duk gayu irinna Sabitu yau yayi mummunan raina gayun nashi.

Har k'ofar gidan suka kai ta, Sabitu duk shi ke kwatancen gidan, Alhaji Ma'aruf shima babban mutum ne duk anguwar ba wanda yakaishi arziki.

Wani irin kallo me wuyar fassarawa budurwar ta jefi Sabitu dashi wanda sai da tsik'ar jikin shi ta tashi, murmushi ta sakar mishi a karo na farko cike da jan hankali ta ce "Nagode k'warai, sai dai baku fad'amun sunan ku ba".
Sabitu da duk jikinshi ya mutu kasa magana yayi, sai Nasir ne ya koro mata sunayen su.

Juya ido tayi ta ce "Malam Sabitu sakamun Numbanka anan".
Ta fad'a tana mik'a mishi tsadadden wayarta, kafin kace kobo ya karb'a ya jera numbansa, bata sake kallon su ta shige gidan ba tare da ko godiya ba.

Jingina Sabitu yayi da katangar gidan yana sauk'e numfashi, Nasir ya ce "yaya dai mutumin, duk naga ka narke".
Murmushi Nasir yayi ya ce "kaje gida ka sauk'e gajiya domin nasan halinka, yanzu haka jarabar ce ta motsa daganin jan jiki".
Ya k'arasa maganar yana dariya, tsuka Sabitu yayi yana harararsa sannan ya wuce abunshi yana tunanin 'yar budurwannan.


Gidan fess k'amshi sai tashi yakeyi, ko sallama beyi ba ya shiga falon nasu, Suwaiba dake kallo a d'an k'aramin Tv ta d'aga kai tana kallonshi, tab'e baki tayi ta ce "jarabebbe wlh yau kam ba'a kaina zaka sauk'e ba, kaje can ka k'arata".

Uban tsuka Sabitu yaja sannan ya wuceta ya shige d'akin barcin su, gaba d'aya Netwok d'inshi ta daina aiki, burinshi kawai yaji service a tare dashi, lumshe idanuwa yayi yana tunanin wace zai k'ira ta rage masa zafi, domin Sabitu bashi da hak'uri ko kad'an, an aura masa Suwaiba amma sam bata isarsa, hasalima kullum cikin fad'a suke.
Juyin da zaiyi yaji wayarsa tana kuwwa, ganin bak'uwar numba yasa bai d'aga da wuri ba, harta kusa katsewa sannan ya d'aga.

"Sunana Saleema, ana k'irana da Leema".

Yaji amfad'a da shak'ekken murya kamar na budurwar d'azu, d'an lumshe ido yayi domin baisan meyasa ba muryarta bata mishi dad'i, amma ita d'in ta had'u sosai, kusanma bai tab'a ganin me kyawun halitta irinta ba.

Cikin sanyin murya ya ce "ban gane wacce take magana ba".

Wani iska ta hura cikin jan hankali ta ce "wacce kukayi wa rakiya d'azu, na k'irane nace maka nagode".

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk'e.
"Haba godiya kamar wani aiki".

"Aiki ne mana tunda na tayar daku kuna hutawa".

D'an dariya Sabitu yayi ya ce "aikin da mukayi ai yafi zaman banzan".

Salima tayi murmushi na kazo hanu yaro, "baka tambayeni meyasa na karb'a numbanka ba"?

Gyara kwanciya yayi yana tunano irin daular daya gani tattare da ita amma harta iya magana dashi yana talaka, talakanma wanda ko ciyar dakan shi baya iya yi, hatta kayan sawarsa mahaifiyar sa ke d'inka masa...
Tunaninsa ya katse da yaji tana cewa "tunda naganka naji nakamu da sonka".

Wani wawan runguma yayi wa pilow ya ce "me kikace"?

Dariya tayi ta ce "kazo da dare muyi magana".

Zumud'i ya kashe Sabitu baima san ta kashe wayarba, wani mahaukacin ihu yayi dayasa Suwaiba shiga d'akin da gudu, ganin ihun farinciki ne yasa taja ta tsaya tana takaici, yanzu hakan akan mace yake wannan ihun, mtsss taja tsuka ta ce "kadai sa Allah a ranka Sabitu, ina rabaka da d'aukan alhakina".
Ko kallon ta beyi ba ya mirgina yayi rub da ciki yana murmushi.
2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Page 2

_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_



_Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_


✍
Wanka Sabitu yayi na kece raini, ba laifi yayi kyau sosai, Suwaiba sai kallon shi takeyi ba bakin magana, tana son mijinta sosai amma rayuwarshi yana bata haushi, kallonta yayi ya ce "kin kafeni da ido, ina fatan ba hanani fita zakiyi ba"?
Haushi ya kamata ta ce "ina ruwana da fitarka, Allah ya had'aka da aljanar dare".
Dariya yayi Sabitu yayi ya ce "indai macece aljanar ta kwana gidan sauk'i".
Fuskar shi fal dariya ya fita, hawayene ya gangaro a fuskar Suwaiba, a fili ta ce "dole na nemar wa kaina mafita, ga talauci ga rashin kulawa ga neman mata, da wanne zanji".
Kuka ta fashe dashi kamar koda yaushe.


Gidan Alhaji Ma'aruf ya nufa, tun daga nesa kana hango hasken wutan lantarki daya zagaye gidan duk da kasancewar babu wutan nepa a lokacin, wayar shi ya ciro ya danna k'iran Saleema, wacce yayi saven da Leema, sai da yak'ira sau biyu kafin ta d'aga, muryarta me bashi haushi yaji tana cewa "ka iso ne masoyi"?
"Na iso".
Ya fad'a yana takaicin jin muryar.

Minti 2 tsakani tafito harabar gidan, umurni tayi wa megadi akan ya shigo da Sabitu cikin gidan.

Har Falon Alhaji Ma'aruf aka kai Sabitu, sai zare ido yakeyi yana ganin had'uwar wajen, "gaskiya kud'i yayi a rayuwa".
Ya fad'a a ranshi.

Alhaji Ma'aruf ya hango cikin kujera, gefensa Saleema ce zaune tana tsiyaya ruwa a cup, wani yawu ya had'iye ganin shigarta, dogon riga ta saka amma duk halittar yanayin jikin ta a bayyane, komi motsawa yakeyi, take kanshi ya d'au caji, tunda ya shiga Alhaji Ma'aruf ya kafe shi da ido yana wani irin murmushi.

Muryar Saleema ya tsink'aya tana ce wa "k'araso ku gaisa da kawuna Masoyi".

Tafiya yake kamar me sand'a, sunkuya wa yayi a gaban Alhaji Ma'aruf yace "Barka da dare alhaji".
Memakon ya amsa sai hanunshi ya mik'a mishi alamar musabaha zasuyi, da sauri Sabitu ya mik'a mishi yana sunkuyar dakai kaman mumini, wani irin damk'a yayi wa hanun Sabitu daya sashi d'agowa da sauri, gani yayi Alhaji fa ya wani lumshe ido.

Murmushi Saleema tayi ta janyo Sabitu ta ce "masoyi muje muyi magana".
Kunya duk ta kama Alhaji ya wayince yana susa kai.

Tana rik'e da hanun Sabitu suka b'ulla wani k'aramin Falo, hanunta laushi kamar auduga don haka Sabitu yayi ta matsawa a hankali.

Sai da ta zaunar dashi sannan ta ce "ka saki jikin ka nan gidan kawuna ne, nan part d'inshi ne, part d'in matan shi yana sama".

Kan Sabitu ya d'aure yana tunanin meyasa Saleema bata kaishi saman ba toh, kamar tasan tunanin da yakeyi ta ce "hayaniya yayi yawa acan shiyasa na rok'eshi ya bamu aron nan.

*GARIN GOMBE*

Farar yarinya ce wacce bazata wuce shekaru 6 ba, shinkafa da mai da yaji takeci wanda ta zuba yaji har abincin yayi jaa, tana ci tana shushutu, zafin yajin yasa da k'yar take magana.

"Innah yaushe Yaya Saleem zai zo ne".

Innah ta dungure mata kai cikin takaici ta ce "ban sani ba ja'ira, ina raba ki da cin yaji taurin kunne ya miki yawa".
Zunb'ura baki Elham tayi tafara gunguni, ganin ranta ya b'aci Innah ta hau dariya tana rarrashin ta.

***************

Hira sukayi ba wani me yawa ba Sabitu ya tafi cikin farinciki domin Salima tayi masa alk'awarin zata aure shi, kai tsaye gidan Umman shi ya nufa, tana kishingid'e ta fara bacci taji Sallamar tilon d'an nata, zama ta gyara tana washe baki ganin yanda yayi kyau.

"ina aka fito haka naji sai k'amshi kakeyi".

Ta fad'a tana matsa mishi gefen ta alamun ya zauna, zama yayi ajikinta lamar k'aramin yaro yace "daga gida nake Umma, Suwaiba ma tana gaishe ki".
Tayi dariyar jin dad'i ta ce "lafiyan ta k'alau ko, Allah yasa dai kana kula da 'yar mutane, kasan mutanennan sun maka gata".
Rausaya kai yayi kalan tausayi ya ce "haba Ummah, bazaki tambaya ko ina jin dad'in zama da itaba sai kiyi ta cewa ina mata wani abun".
Kama baki tayi tana kallon shi.

"Yoh dan ubanka wazan tambaya".

"to Umma ni ba wannan ba, dama nazo nafad'a miki ne aure zan k'ara".

Tsananin mamaki yasa Umma sake baki tana kallon shi, b'acin rai fal ranta ta ce "Sabitu kasan me kake fad'a kuwa? Ka kiyayeni fa, tashi ka tafi tun kafin raina yagama b'aci".

Sum sum ya tashi yafita yana k'ananun magana.





Sai kunjini anjuma
2/1/20, 5:08 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Page 3

_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_



*Na sadauk'ar da wannan page d'in ga _AISHA BICHIKI FANS_ da _BICHIKI HAUSA NOVELS_*

*KUCI GABA DA CMMNT AISHA BICHIKI TAKU CE*



✍
Tun safe take zun
b'ura baki Innah ta kasa gane kanta, fushi takeyi sosai k'iris take jira ta fashe da kuka.

"Elhaman Innah me kike so ne, wannan b'ata ran duk na menene, kina so Inna ta shiga damuwa ne"?

Turo baki Elham tayi ta ce "ki kaini gidan Uncle".

Kamota Innah tayi gami da d'aurata a cinya ta ce "shine kike b'ata rai, ki karya maza yau ana tashi a makaranta zan kai ki can".
Tsalle ta farayi a jikin Innah tana kai mata kiss ta ko ina, kallon yarinyar Innah keyi tana murmushi, ganin ta fara hajijiya ta ce "kinga zo na shafa miki mai ki...


Read / Download DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
2 Comments On DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1
avatar
hamidu

5 months ago

Reply

Wasu novels nakudine, idan nayi subscription naku zansamu complete na books dinne? Kosai nabiya a wurin marubuciya?

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to hamidu

Muddin Novel na kudi ne koda ace ka yi subscribtion na mu ba zaka samu complete na shi ba dole sai ka siya a wurin marubuciya, shi yasa ma novel na kudi su ana iya downloading na su koda ba a yi subscribtion ba

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album