Join Our WhatsApp Group

BUSA A MUTU Book 1 Complete Hausa Novel Document by BUSA A MUTU Book 1


BUSA A MUTU Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17686



BUSA A MUTU Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 93.24 kb

File Type: txt

Views: 2227+

Download: 799+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

BUSA A MUTU!!!
Littafi Na Daya (1)
Part A

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

Marubucin ya fara da cewa...

A YARIN Fatake ne da 'yan gudun hijira daga
wata babbar kasa da ake kira Lairus.
Yawansu ya kai dubu uku, wasu akan
dawakai suke tafiya, wasu a rakuma da alfadarai. A
kalla wadannan mutane sun shafe kwana tara suna
tafiya a cikin daji suna keta kwazazza bai, koramai da
duhuwoyi. A cikinsu akwai zaratan samari majiya
Rarfi, sannan akwai mata, yara da tso fafffi kuma
yawancinsu iyalai ne, wato wani zaka ga tarc yakc da
matarsa da kuma dansa ko 'yarsa ko kuma 'ya'yansa
guda biyu ko uku. Wani kuwa tarc yake da mahaifinsa
ko mahaifiyarsa. Wani yana tare da dan uwa ko 'yar
uwa. Kuma gashi suna daukc da dukiyoyinsu wasu ma
har da dabbobinsu.

Abin tambaya anan shi nc, ina wannan ayari suka
nuta, kuma daga ina suka fito, sannan ina suka dosa?
Ba wani abu banc ya sa wannan ayari suka yi
gudun hijira ba face masifar yaki da ta 6arkc a kasar
tasu ta Lairus wadda ta haddasa asarar miliyoyin
rayuka da dukiya.
Shi dai wannan yaki ya faru nc sakamakon
wadansu 'yan tawaye wadanda suka yiwa Sarki
Muraisu borc domin tabbatar da cewa sun tunkude
mulkinsa da karfin tsiya saboda kawai ganin cewa shi.
mutum ne adali wanda baya zalunckuma bai yarda da zalunci ba
Su dai wadannan 'yan tawaye sai da suka shekara
bakwai suna tanadi na wannan yaki suna tara dakaru a
baye a can wata kasar daban gami da kayan yaki. Sai
da suka tara mayaka miliyan biyu da rabi kuma ya
zamana cewa kullum a cikin basu sabbabbin horon
yaki ake.
Babban abin takaici shi ne ba wani bane ya dauki
nauyin wadanma Dakarun iawayc ba face Yarima
Huraisu kanin Sarki Muraisu wanda suka kasance uwa
daya uba daya.
Tun Muraisu da Huraisu suna yara kanane suka
taso basa jituwa saboda bambancin halaye sa ra'ayi
suka zama tankar abokan gaba, ya zamar.a ccwa basa
yiwa juna ga maciji. Babu abinda ya tsananta gaba a
tsakaninsu face Huraisu ya san ceva idan mahaifinsu
Sarki Salmar ya mutu, Muraisu ne zai hau kan karaga
saboda tuni Sarki Salma ya yi nuni da hakan har ma ya
bar wasiyar hakan.
Halayen Sarki Saimar iri dayane dana Muraisu
wato suna da son taiakawa,tausayi da taimako. Kwata-
kwata abin duniya bai danesu ba. Begu da kari
Muraisu ya kasance saurayin mai farin jini matuka a
wajcn jama ar gari saboda ganin cewa ya taso da
halaye na mahaifinsa. Duk inda ya wuce ma sai dai ka
J1 ana yi masa kirari da Magajin Sarki. Shi kuwa
Huraisu jama'a sun tsaneshi kamar yadda suka tsani
Mutuwarsu saboda bakar zuciyarsa ta zalunci. Ko
kallonsa mutum ya yi ya tsargu Sai ya zare makami
nan take ya sareshi. Idan ya ga budurwa mai kyau ko
'yar gidan uban waye sai ya yi ma ta fyade haka kurma
duk dukiyar da ya gani in dai ya ji yana bukatarta to fa
sai ya kwaccta.
A duk sa'adda Huraisu ya yi irin wannan mugun
aiki baya yarda ya dawo gida sai dai ya shiga daji ya
buya saboda sanin cewa saii Sarki ya sa an yi masa
hukunci mai tsauri dai-dai da laifin da ya aikata.
Sarki ya sha sawa a yiwa Yarima Huraisu bulala
arba'in ko hamsin a farfasa masa jiki har sai ya yi
jinya. Kuma duk sa'adda ya aikata laifin ya gudu daj
babu mai iya zuwa ya kamoshi da karfin tsiya sai dan
uwansa Muraisu.
Muraisu da Huraisu sun kasance gawurattun
Sadaukai na gaban kwatance kuma kwararrun mayaka
wadanda suka yi shuhura a cikin nahiyarsu sai dai
Muraisu ya fi Huraisu karfi, jarumtaka da iya yaki
nesa ba kusa ba.
Wani lokaci idan Muraisu ya tafka laifi sai Sarki
ya sa a daureshi tamau a sama a jikin dirka a gasashi a
cikin rana, ba ci ba sha har tsawon sa'a ashirin da hudu
amma saboda naci da bakin hali idan aka sakeshi gobe
ma sai ya kara aikata wani laifin da ya fi na baya.
Azaba ko bazarana ba ta firgita Huraisu koda
kuwa ya san cewa zai iya rasa rayuwarsa sakamakon
azabar da za a yi masa.
Sarki Samral yana matukar kaunar Yarima
Muraisu saboda ladabinsa da biyayyarsa da kuma
halayensa da ya gado gami da yadda ya ga jama'ar
birnin Lairus ke tsananin kaunarsa suke girmamashi.
Ko kara Sarki Salmar ya ajiye Muraisu ba zai ketarce
ba.
Mahaifiyar Muraisu ta rasu ne a ranar da ta
haifesu suka zo duniya lokaci guda tagwaye. Muraisu
da Huraisu suna matukar kama da junansu tamkar an
tsaga kara.
A wannan rana an cc Sarki Samral ya yi
matsanaicin kuka da bakin ciki. Al'amarin da ya
matukar baiwa mutanen kasar gaba dayansu mamaki
ke nan, domin a tarihin rayuwar Sarki Samral tun daga
kuruciyarsa kawo izuwa girmansa ba a taba ganin
kwalla ba a idanunsa, amma sai gashi an ga ranar da
yake ta kuka kishin6ar! da hawaye daki-daki, wani na
bin wani.
Sarki Samral kasaitaccen sadauki ne kuma
gabjcjen mutum mai kirar mutanen farko, domin duk
sa'adda yaje nahiyar da ba a sanshi ba da zarar mutane
sun ganshi sai su firgice su kama guje-gujc, wasu su ce
sun yi gamo da aljani, wasu kuma su ce ai fatalwa ce.
Komai girman bishiya da hannu daya Sarki
Samral ke hankadeta ta fadi kasa. Komai girman dutse
da nauyinsa idan har ya ritsashi da hannayensa biyu to
fa zai iya rabashi da kasa ya dagashi sama ya yi
doguwar tafiya da shi ba tare da ya gaji ba.. Idan kuwa
zai fita yaki saj dai a tanaji giwaye kamar guda arba in
a matsayin ababcn hawansa, kumna babu wacce za ta
, AA Misau Nake, iya daukarsa sama da tsawon rabin sa'a ba tare da ta
gaji ba ta durkushe kasa saboda tsananin nauyinsa. Kai
idan Sarki Samral ya fusata yana iya daukar ita kanta
giwar ya yi wurgi da ita tamkar ya yi wurgi da hoge.
Labarin Jarumtakar Sarki Samral ya bazu ko ina
a nahiyarsu har ma da sauran nahiyoyin da ba nasu ba.
Kuma ba a ta6a samun GWARZON MAYAKI ba
kamarsa. A tarihin yake-yaken da ya yi a rayuwarsa
tun kafin ya hau karagar mulki har izuwa sa'adda ya
bar duniya ba a taba cinsa da yaki ba, kuma ba a taba
ji masa ciwo ba. Idan yana tsakiyar abokan gaba yana
saransu da sukarsu da takobinsa sai ya shafe sa'a goma
sha biyu bai gaji ba, kuma tsananin zafin namansa da
Rarfin gudunsa ya wuce misali kamar iska ce ke
sarrafa gababen jikinsa.
Da yake mutum ya kan haifi kansa sai gashi
Sarki Samral ya haifo zakwakuran sedaukai da suka
gado wannan girman jiki irin nasa da kuma jarurntaka
tasa sai dai inda aka sami akasi Muraisu ya fi Huraisu
komai ya ma ninkashi.

Lokacin da fitinar Huraisu ta yi yawa kuma ta
damu Sarki Samral ya zamana cewa duk irin azabar da
aka vi masa da irin hukuncin da ake yi masa mai tsauri
a duk sa'adda ya aikata laifi sun zama a banza sai Sarki
ya kafa masa doka ta karshe ya sanar da shi cewa dukLa
ranar da aka sake kamashi da laifin yin fyade ko sata
ko kuma cin zali sai an yanke masa hannayensa biyu
Domin kowa ya huta da fargabarsa saboda ya addabi
Gaba dayan jama'ar birnin da Rauyuka.
Sa'adda mutane suka ji wannan gagarumin
bukunci da aka dauka akan azzalumi Huraisu sai suka
cika da tsananin farin ciki. Tun daga wannan rana
kyawawan 'yan mata suka sami 'yancin yawo a ko ina,
attajirai suka rinka fatauci a ko ina a kasar cikin
kwanciyar hankali, sabanin da can da 'yan fashi suka
yawaita a ko ina a cikin kasar, kuma gaba dayan 'yan
fashin yaran Yarima Huraisu ne.
Lokacin da Yarima Huraisu ya ke kan sharafinsa
na aikata duk irin laifin da ya ga dama ne ya tara yara
a karkashinsa sama da dubu dari, kuma a kowanne
birni da ke cikin kasar yana da wakilai.
Duk sa'adda Fatake za su ratsa wata hanya ko
kuma a duk inda za a yi wani gagarumin kasuwanci da
dukiya mai yawa sai labari ya riskeshi sai dai kawai
aga shi da yaransa sun baiyana a wajen sun tafka
gagarumar 6arna. Ran biladama kuwa sun mai da shi
tamkar na kiyashi.
A wannan lokaci ne Huraisu ya tara dukiya mai
tsananin yawan gaske saboda haka sai ya så aka gina
masa wani tafkcken gida a tsakiyar waii daji da akc
Kira Kirzufa, wanda ke tsakanin iyakar birnin Lairus
da wani birni mai suna Hutaira.
Shi dai wannan daji na Kirzufa dade ana rigima a
Kansa a tsakanin kasashen biyu domin kowacce kasa
kuma sau ashirin da daya ana yaki a zamanin Sarki
Samral akan dajin, amma duk sa'adda aka yi yakin sai
dai ayi ragas, duk da cewa Sarki Samral ya zama
dodon maza kuma gagaraba dau. ba komai ne ya janyo
Madakin Gini
hakan ba face tsananin yawan mnayakan birnin Hutaira
ya wuce misali.
Akwai lokacin da Sarki Samral ya kwana arba'in
Cif yana yaki da su shi kadai amma sai ya kasa karar
da koda rabinsu, suma suka kasa hallakashi ko kaishi
Ras.
Duk sa'adda ya ga ya gaji ainun sai ya falfala da
matsanaicin gudu su kasa cimmasa har yaje wani
wurin ya buya sai ya huta sannan ya dawo a ci gaba da
gumurzu. Gashi dai yana kashesu tamkar ana kakkabe
ganyaycn bishiyoyi a daji, amma sai ka ga kamar
matattu ne suke tashi saboda azabar yawansu. Kai a
wannan zamani sai da masu bincike suka gano cewa
ko mutan cn birnin Sin ba su kai rabin yawan mutancn
birmin Hutaira ba.
A karshe bisa dole Sarki Samral ya janye yakin
da kansa ya koma birninsa ya hakura da mallakar dajin
Kirzufa. Har Sarki Samral ya bar duniya da takaicin
rashin mallakar dajin Kirzufa ya tafi, kuma kafin ya
mutu sai da ya barwa Muraisu wasiyyar cewa duk
yadda zai yi ya tabbatar da cewa ya mallaki dajin
Kirzufa kafin shima ya bar duniya. Muraisu ya dauki
alkawarin cewar koda kuwa zai rasa rayuwarsa a
kokarin mallakar dajin Kirzufa ba zai Gaza ba
Sarkin da ke mulkin birnin Hutaira, wani
gawurtaccen boka ne mai suna Ishmar ibiní Suraifa.
Shima Sarki Ishmar babu abinda bai yi ba akan
ya ga bayan Sarki Salmar domin ya mallaki dajin
Kirzufa amma abu ya gagara.
Abinda yake daurc masa kai shi ne, "Me ya sa
tsafī baya tasiri akan Sarki Samral?
Babu irin binciken da bai yi ba a hallarar tsafi
domin ya gano wannan matsala amma abu ya gagara.
Kawai abin da ya iya ganowa shi ne akwai wani
babban sirri a tarc da Sarki Salmar wanda yasa tsafi
baya tasiri a jikinsa kuma ya ziyarci bokaye da yawa a
duniya wadanda ma suka fi shi karfin sihiri amma
dukkaninsu sun kasa gano wannan sirri. Abinda
bokaye suka gaya masa shi ne duk duniya babu wanda
ya san wannan sirri face shi kansa Sarki Samral kuimna
kafin ya bar duniya sirrin zai koma kan dansa Muraisu,
shima kafin ya mutu dansa zai gaji wannan sirri.
Haka al'arnarin zai ta bibiyar zuri'arsu shckara da
shekaru, zamani bayan zamani. Ba za a taba rabasu da
wannan sirri ba face a ranar da aka kai mai sirrín kas a
filin yaki aka sami nasarar hallakashi. A sannan nc za
a tsaga kirjinsa a ciwo wannan sirri wanda ya kasance
dan siriri tamkar silin gashin da ke wuyan doki guda
daya.
Sa'adda Sarki Ishmar ya ji wannan jawabi sai
hankalinsu ya dugunzuma ainun, domin ya san cewa
, AA misau nake, : shi dai abu ne mawuyaci a zamaninsa ya ga wannan
rana sai dai nan gaba a zamanin 'ya'yansa ko jikokinsa.
Akan haka ne ya rungumi kaddara bisa tunanin
mallakar dajin Kirzufa a wannan lokaci amma sai ya
ayyana a ransa cewa komai darcn dadewa sai an sami
wani daga cikin zuri'arsa ya mallaki wannan sirri.
Shi dai Sarki Ishmar Allah Ya albarkaceshi da
yayye har guda talatin da tara, amma gaba dayansu
mazane babu mace ko guda daya, kuma a binciken da
ya yi zuri'arsa ba za ta taba samun damar mallakar
wannan sirri ba na Sarki Samral face an haifi
gagarumar BASADAUKIYA jininsa wacce za ta
shahara a ko ina cikin duniya.
Wani babban abin
takaici
shi
ne
gaba
daya
'ya'yan
Sarki
Ishmar
manya
wadanda suka yi aure duk
wanda
matarsa
za
ta haihu
sai aga
namiji ta haifa ba a taba samun wacce ta haifi
'ya
mace
ba bare Sarkı
İshmar ya
sa
ran
cewa
ita
ce
za
ta kar6i wannan sirri ga
zuri'ar Sarki Samral.
Saboda wannan dalili. ne duk sa'adda aka yi
haihuwa Sarki Ishmar ya ga namiji aka samu sai ya
kamu da tsananin bakin ciki ya rufe kansa a cikin daki
ya yi ta kuka domin ya san cewa har abada ba zai ga
ranar da zai raba Sarki Samral da wannan suri na sa ba
Wanda zai sami damar cuiar da shi da zuri'arsa da
Carfin sihirin tsafi. Babban abin takaici a gareshi shi ne
lsufa ya riskeshi ya shekara tamanin da hudua dunivai ya
san cewa ajali ko yaushe
ajali zai iya riskarsa
: De jin Kirzufa wani irin sihirtaccen daji ne
wanda sama da shekaru dari baya ba a aba samun
mahaluin da ya shiga cikinsa ya iya dauko wani abu
ba face mutum aya rak, wato Sarki Samral.
a wannan
ikokinsa.
Shi
dai wannan daji na Kirzufa
Allah
Ya
albarkaceshi da tsuntsaye iri-iri gami da dabbobin daji
kala-kala masu yawan tsiya. Wata dabbar ma ko a
labari mutum bai taba jin labarinta ba.
Babban sirrin dajin Kirzufa shi ne, idan mutum
ya shigeshi in dai bai yi ko Rarin đaukar wani abu ba
ko cutar da wata dabba ba to fa zai shiga lafiya kuma
ya fito lafiya, amma da zarar ya yi yunkurin daukar
wani abu ko cutar da wata halitta, to fa sunansa gawa!

Mafarauta da mayaka sun sha hada runduna su
shiga dajin don đebo albarkatun cikinsa, amma
dayansu baya dawowa a raye.
Shi kansa Sarki Samral sau daya ya taba shiga
dajin ya yi farauta inda ya kamo wadansu giwaye guda
shida. Nan take ya kashe guda hudu ya ciro haure
guda biyu kuwa ya sabosu a kafadunsa ya fito da su
daga cikin dajin.

Koda va iso inda ya bar Dakaru hamsin wadanda suka
yi masa rakiya izuwa farautar suka ganshi da
wadenan giwaye da kuma haure sai suka cika da
tsananin mamaki suka rinka shewa suna yi masa
iinjina domin shi ne mutum na farko da ya karya
alkadarin dajin Kirzufa.....

Sbd haka Nima Ku Tafamin😂
Dafatan Kowa yana lafiya
SaikumA Mun sake haduwa a part BBUSA A MUTU!!!
Littafi Na Daya (1)
Part B

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gino

Marubucin yaci gaba da cewa....

Nan da nan labarin wannan jarumtaka da ya yı ya
bazu a ko ina a nahivar. Wani abin mamaki shi nc,
hauren giwayen da ya farauto a cikin dajin sai da suka
zamo sanadiyar samun dukiyarsa mai tsananin yawa
irin wacce bai taba samu ba a rayuwarsa domin
manya-manyan Sarakunan duniya ne suka rinka yin
tattaki suna zuwa har birnin Lairus suna siyan hauren
giwa daya jal akan miliyoyin dirhami.
Duk wanda ya sayi hauren giwar sai ya kaishi
masarautarsa ya adanashi a gidan tarihi mutane suna
Zuwa suna gani suna biyan kudi. Shima ya sami abin
samun kudi.
Shima Sarki Samral sai da ya ajiye hauren giwar
guda daya jal a tsakiyar fadarsa saboda barin tarihi,
kuma yasa aka sassa ka gunki mai kamanninsa da
girmansa sak! Yana gumurzu da giwaye shida na
gumaka.
Duk mutumin da ya shigo fadar Sarki Samral ya
ga wadannan gumaka na giwaye shi da Sarki Samral
dole ne ya yi sha'awarsu domin sun yi matukar kyau,
kasancewar an yi su ne da zallan zinare, kuma
masassakin ya kwarance ainun, da ka kallesu sai ka ga
kamar za su yi motsi tamkar na gaske ne ba gumaka
ba,
Daga wannan rana da Sarki Samral ya shiga dajin
Kirzufa ya yi wannan farauta ya dawo gida bai sake
sha'awar sake zuwa daji ba Shekara na zagayowa ne ya kamu da cutar ajali.
ya kwanta ciwo. Kuma a wannan lokaci ne Yarima
Huraisu ya yi fishi ya bar birnin Lairus ya koma can
daji inda aka gina masa wannan tafkcken gida ya
zauna tare da yaransa manya-manyan 'yan fashi suka ci
gaba da sharholiyarsu.
A sannan ne labari ya riski Yarima Huraisu
cewar mahaifinsa Sarki Samral ya kwanta cutar ajali.
Koda samun wannan labari sai Huraisu ya cika da
matukar farin ciki ya fara tunanin hanyar...


Read / Download BUSA A MUTU Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On BUSA A MUTU Book 1
avatar
shuraihu-usman-1

7 months ago

Reply

Aha

avatar
bilkisu-adam-yusuf

3 months ago

Reply

Littafin yayai dadi

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album