Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR BIRNIN DUWATSU


HIKAYAR BIRNIN DUWATSU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22407



HIKAYAR BIRNIN DUWATSU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 26, Aug 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 117.14 kb

File Type: txt

Views: 622+

Download: 234+

Last download: 7 days ago

Description/Story: 01. BIRNIN DUWATSU:
Hikayar Abdullahi
dan Falilu da 'yan uwansa
Copied
AA Misau Ke Magana
E-book Suleiman Zidane Kd
08161272634An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Wata rana Halifa Haruna Rashid na duba
harajin da sarakuna da hakimansa suka aiko
da shi cikin wannan shekara, sai ya lura
cewa Sarkin Basara ne kadai bai aiko da
nasa harajin ba. Don haka sai Halifa ya tara
'yan majalisarsa. Da suka taru sai ya ce, "Ina
Waziri Ja'afaru?"
Waziri Ja'afaru ya zo kusa ga Halifa ya
tsaya ya ce, "Ga ni, Allah ya daukaki
mulkinka."
Halifa ya ce, "Harajin kowane sarki da ke
karkashina ya shiga baitulmali, amma babu
harajin Basara."
Ja'afaru ya dukar da kai ya ce, "Ya
Shugaban Muminai, watakila akwai wani
babban al'amari da ya faru ga Sarkin Basara
da ya sa shi sha'afa da aiko da nasa
harajin."
Halifa ya ce, "Yau kwana ashirin da gama
tattara haraji, idan har wani al'amari ya
same shi, mi ya sa bai aiko mana ba, domin
mu san halin da yake ciki?"
Waziri ya amsa masa, "Allah ya taimake ka,
ina ganin mu aika masa da manzo wanda zai
dawo mana da labari."
Halifa ya ce, "Ka tura Abu Is'haka al-Mausili,
daya daga cikin amintattunmu."
"Na ji, na amince. Ina mai biyayya ga Allah,
ina mai biyayya gare ka, ya Shugaban
Muminai." In ji Ja'afaru.
Nan da nan sai Ja'afaru ya sa aka kira masa
Abu Is'haka zuwa gidansa.
Da ya zo sai ya
rubuta takarda a madadin Halifa, ya ba shi
ya ce, "Karbi wannan takarda ka kai wa
Abdullahi dan Falilu, Sarkin Basara. Halifa ya
duba dukkan harajin da sarakunansa suka
aiko amma bai ga na Sarkin Basara ba. Idan
ya tattara harajin ka karbo ka dawo mini da
shi, idan kuwa bai tattara ba, to ka zo tare
da shi, ya fada wa Halifa da bakinsa abin da
ya hana shi aiko da nasa haraji."
Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na amince." Waziri
Ja'afaru ya hada shi da mahaya dubu biyar
suka nufi Basara. Yayin da suka yi kusa da
birnin Basara sai Abdullahi dan Falilu ya
sami labarin zuwansa. Nan take ya fita da
runduna ya tarye shi, suka dawo cikin birni
tare, har suka isa fada. 'Yan rakiya kuma sai
suka kafa tantuna a bayan gari, aka aika
musu da dukkan abin da suke bukata na
abinci da abin sha da shimfidu.
Lokacin da Abdullahi dan Falilu da Abu
Is'haka suka shiga fada, sai Abu Is'haka ya
zauna bisa karaga, ya zaunar da Abdullahi
dan Falilu kusa gare shi. Wazirai da fadawa
kowa ya zauna gwargwadon matsayinsa.
Da
fada ta nutsu, sai Abdullahi dan Falilu ya
mike. Bayan ya yi sallama da gaisuwa ga
Abu Is'haka sai ya ce, "Ya shugabana, ko
akwai wani sako ne da ka zo mana da shi?"
Bako ya amsa, "I. Na zo ne domin na karbi
harajin kasarka. Kowa ya aika da harajinsa
amma Halifa bai ga naka ba, ga shi har
lokacin karba ya wuce."
Abdullah dan Falilu ya yi murmushi ya ce,
"Allah Sarki, an ce rashin sani ya fi dare
duhu. Da ka sani da ba ka walar da kanka
garin zuwa ba.
Haraji na nan na kammala
hadawa, da gobe nake niyyar aikawa da shi.
Amma tun da ka zo zan damka shi ga
hannunka, ka wuce wa Halifa da shi.
Yanzu
sai ka zauna ka huta zuwa kwana uku, mu
shirya maka liyafa ta musamman domin
karramawa da kuma girmama Halifa, a
kwana na hudu sai na ba ka harajin tare da
tsarabar da za ka tafi da ita."
Abu Is'haka ya ce, "Babu laifi ga wannan."
Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya sallami
kowa. Da aka watse sai ya ja bakonsa zuwa
wani kayataccen soro da babu kamarsa ga
kyawu. Ya sa aka jera akussan abinci domin
Abu Is'haka da manyan na hannun damarsa.
Suka ci suna raha har suka bankare
cikannansu. Da suka koshi sai aka kawar da
akussa aka jera gorunan gahawa da abin
sha.
Suka yi ta sha suna hira, ba su ankara
ba har dare ya raba. Aka shirya wa Abu
Is'haka shimfida mai taushi bisa gadon
zumarrazi da aka shafe da ruwan zinariya
mai kyalkyali.
Admin
AA Misau Ke Magana
Suleiman Zidane
02. HIKAYAR BIRNIN DUWATSU:
Copied
AA Misau Ke Magana
.
Suka yi ta sha suna hira, ba su
ankara ba har dare ya raba. Aka
shirya wa Abu Is'haka shimfida mai
taushi bisa gadon zumarrazi da aka
shafe da ruwan zinariya mai
kyalkyali.
Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa
gare shi, amma a nasa gadon daban.
Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi
barci amma barcin bai dauke shi ba.
Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa,
wani lokaci kuma sai ya rera baitoci
a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi
mutum ne gwanin hikima, ga shi
kuma gwanin bayar da labari, shi ya
sa Halifa ke son sa kwarai da gaske
har ya sanya shi daya daga cikin
amintattunsa. Haka ya ci gaba da
karatunsa yana rera wakoki har zuwa
talatainin dare. Daga nan sai ya ga
Abdullahi dan Falilu ya tashi daga
kan gadonsa, ya daura damara ga
kugunsa, ya bude wani dan akwati ya
dauki bulala da shama'a kunnaniya,
ya fice daga cikin soron da suke
kwance, yana tsammani bakonsa
barci yake yi.
Yayin da Abu Is'haka ya ga haka sai
mamaki ya kama shi, ya ce a cikin
ransa, "Ina Abdullahi dan Falilu za ya
da bulala cikin dare? Yalla ko yana
nufin ya azabta wani. Bari dai na bi
shi in ga abin da zai yi cikin wannan
tsohon dare."
Yayin da Abu Is'haka ya tashi ya bi
bayansa yana sanda a hankali yadda
ba za a ji tafiyarsa ba. Ya ga
Abdullah ya bude taska ya fito da
kabaki daga cikinta da tasoshi hudu
a gabansa cike da waina da nama,
da kasaken ruwa. Ya dauki kabakin
ya tafi, Abu Is'haka ya ci gaba da bin
sa a hankali, har ya shiga daki. Da
Abu Is'haka ya ga ya shiga cikin daki
sai ya ja ya tsaya daga bakin kofa, ya
zama yana leken cikin dakin. Ya ga
dakin mayalwaci, an shimfide shi da
shimfidu na alfarma. A tsakiyar dakin
an kafa gado na li'aji zananne da
zinariya, a jikin gadon an daure
karnuka biyu da sarkoki na zinariya.
Abdullahi ya ajiye kabaki daga kuryar
daki, ya zare damuttsansa, ya
kwance kare na farko. Kare ya zama
yana wutsilniya yana turmusa
hancinsa ga kasa, ka ce shi yana
sumbatar kasa ne gaba ga Abdullahi,
yana kuka kasa-kasa da murya mai
mai ban tausayi. Duk wannan abu da
karen nan ke yi, Abdullahi bai kula ba,
ya rife shi ya buga ga kasa, ya daure
kafafun. Ya zari bulala ya sabkar
masa da bugu, bugu mai karfi ba da
tausayi ba. Kare ya yi ta wutsilniya
yana kuka, kuka mai tsanani, amma
Abdullahi bai dakata da bugun sa ba
har sai da ya ji ya bar motsi ya
suma. Yayin nan ya ja shi kasa ya
kai ga gadon nan ya daure shi ga
bigirensa. Ya kwance kare na biyu, ya
aikata bugu gare shi kamar yadda ya
yi wa na fari. Daga nan sai ya ciro
adiko ya riga goge musu jikinsu yana
ba su hakuri yana cewa, "Kada ku rike
ni da wannan abu, ba da son raina na
aikata muku shi ba. Allah ya ba ku
sauki ya kawo muku mafita."
Ya ci gaba da yi wa karnukan nan
addu'a yana shafa jikinsu.
Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki.Bayan karnuka sun farfado, sai Abdullahi ya jawo kabakin nan ya rika ba su abinci da hannunsa suna ci har suka koshi. Ya goge musu bakuna. Ya dauko kaskon ruwaya ya shayar da su. Daga nan sai ya dauki kabaki da bulala ya riki shama'a ya nufi kofar fita. Abu Is'haka ya yi sauri ya koma bisa gadonsa, ba tare da Abdullahi ya gan shi ko ya ji motsinsa ba, ya kwanta kamar yana barci. Abdullahi ya mayar da kabaki da kaskon ruwa a cikin taska, ya dawo cikin soro ya mayar da bulala cikin akwati, ya kwance damara, sa'annan ya kwanta bisa gadonsa. Abu Is'haka kuwa yana kwance ya kasa barci saboda tunanin wannan abu da ya gani, sai mamaki ke cin sa. Ya rika cewa a cikin ransa, "Ina mamakin dalilin wannan abu da na gani." Ba shi ya daina tunani da al'ajabi ba sai da gari ya waye. Yayin nan suka tashi suka sallaci sallar asubahi suka karya kumallo suka sha abin sha, sa'annan suka shirya suka fita fada.Zuciyar Abu Is'haka ta cika da tunanin al'amarin da ya gani mai ban mamaki, har aka yi fadanci aka tashi hankalinsa ba ya tare da shi, kuma bai tambayi Abdullahi dalilin wannan abu ba. A dare na biyu Abu Is'haka ya sake bin Abdullahi a baya, ya ga ya aikata wa karnukan nan abin da ya yi musu a daren jiya. Ya buge su da bulala, yashafe musu jiki yana ba su hakuri, sa'annan ya ba su abinci da abin sha. Hakakuma a dare na uku ya aikata musu. A ranata hudu sai Abdullahi ya kawo haraji ya ba Abu Is'haka tare da tsaraba mai yawa, suka yi ban kwana ya tafi, ba tare da ya tambayi sababin bugun karnuka ba, ya bar abin a cikin ransa.Kwanci tashi har ya iso birnin Bagadaza, ya ba Halifa haraji wanda ya tambayi dalilin jinkirin kawo shi. Abu Is'haka ya amsa masa, "Ya Shugaban Muminai, ko dana isa na tarar da ya gama tattara harajin har ya yi nufin aikowa da shi, da a ce ma na kara kwana daya ban isa ba, da na haduda manzanninsa a hanya. Amma ya Shugaban Muminai, na ga wani abu da ya daure mini kai, ya sanya ni cikin tunani da al'ajabi mai girma, tare da Abdullahi dan Falilu. Ban taba ganin wannan abu ko jin labarinsa ba tun da nake.""Wane abu ne wannan da ka gani mai ban mamaki, ya Abu Is'haka?" Halifa ya tambaya.Abu Is'haka ya amsa, "Na ga abu kaza da kaza." Ya kwashe labarin abin da ya ga Sarkin Basara na aikata wa karnuka cikin dare ya fada masa. Ya kara da cewa, "Hakana ga yana yi tsawon dare uku da na kwana tare da shi. Da farko sai ya bugi karnukan sai sun suma, sa'annan ya rika shafe jikinsu da kyalle yana rarrashi. Idan suka farfado sai ya ciyar da su abinci ya shayar da su ruwa. Ni kuwa ina make dagawajen dakin ina kallonsa, bai taba lura da ni ba."Halifa ya tambaye shi, "Ka tambaye shi dalilin wannan al'amari?"Abu Is'haka ya amsa, "A'a, Allah ya ja zamanin Sarkin Musulmi."Halifa ya cika da mamaki. Ya dubi Abu Is'haka ya ce, "Maza ka koma Basara ka taho mini da Abdullahi dan Falilu da karnukan nan biyu."Abu Is'haka ya sunkuyar da kai kasa ya ce,"Ya shugaban Muminai, ka dora mini aiki mai nauyi. Abdullahi ya girmamani ya kuma yi mini alheri mai yawa lokacin da nasauka gare shi. Wannan abu da na gani sirri ne gare shi da ba ya son kowa ya sani.Yanzu da wace fuska zan tinkare shi har nayi masa maganar karnukan nan duk da irin alherin da ya yi mini, Wallahi ina jin kunyar yin haka. Da zai yiwu, sai Sarkin Musulmi ya aika wani manzo da takarda yana umurtar Abdullahi ya zo tare da karnukan."Halifa ya yi murmushi ya ce, "Idan na aika wani zai iya musantawa ya ce, 'ni ba ni da wasu karnuka,' amma idan kai ka tafi ka ce masa, 'na gan su da idona' ba shi da ikon musantawa. Don haka dole kai za ka tafi kazo mini da shi da karnukan nan, idan kuwa ba haka ba ina yanka ka."Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na dauka, ya Sarkin Musulmi, Allah ya agaje mu. Da ma an ce harshe shi ke yanka wuya. Laifina ne da na gaya maka wannan labari, amma inaso ka rubuta mini takarda da hannunka wadda zan ba shi."Halifa ya rubuta takarda ya ba shi, ya karba ya kama hanyar Basara. Yayin da Sarkin Basara ya ga ya komo nan da nan, sai ya ce, "Allah ya sa dai lafiya ka koma haka da wurwuri, ya Abu Is'haka? Ko harajin ne ya yi kadan Halifa ya ki karba?"Abu Is'haka ya dube shi cikin jin kunya ya ce, "Ya Sarki Abdullahi, harajinku ya cika daidai, Halifa ya karba cikin farin ciki. Amma ka gafarce ni saboda na ci amanar bakunta, wannan kuwa sharrin Shaidan ne!"Abdullahi ya tambaye shi cikin mamaki,"Wace amana ka ci tamu?""Ka sani kwana uku da na yi tare da kai, a cikin kowane dare nakan bi bayanka, ba tare da ka sani ba, har zuwa dakin da kake bugun wasu karnuka biyu. Wannan al'amari ya sa ni mamaki matukar mamaki,ni kuma sai na ji kunyar na tambaye ka. Yayin da na koma Bagadaza sai kaikayin baki ya ja ni, na gaya wa Halifa wannan labari. Da na san zai nemi na dawo na tafi da kai tare da karnukan da ban gaya masa labarin ba, to amma kaddara ta riga fata, babu wanda ya isa ya canja kaddarar Ubangiji. Ga takarda Halifa ya ce a ba ka, a ciki yana umurtarka da ka tafi gare shi tare da karnukan nan. Amma don Allah ka yafe mini wannan laifi da na aikata maka." Ya duka ya yi...


Read / Download HIKAYAR BIRNIN DUWATSU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album